Showing 21001 words to 24000 words out of 189984 words
ne ciki ɗaya,dan haka ka yi saurin kawar da wannan tunanin daga ranka ,dan idan Muhammad nuurr ya ji ransa zaiyi matukar ɓaci",yana rufe baki Alh Muhammad nuurr ya shigo ɗakin tattaunawar bakin sa dauke da sallama,amsawa su kayi tare da fara yin musabaha da juna,kafin cikin kamalar sa da Dattaku ya zauna idanun shi akan mutane biyu da yake kauna wato dan uwansa da amininsa.
Ina ga ba sai muunyi wani dogon surutu ba, dan kuma kun san halin da ake ciki wanda shine makasudin zaman nan namu,gaba daya suka jinjina kai cike da tabbatar da hakan,cikin nutsuwa ya ci gaba da cewa,halin da jahar mu ke ciki kullum sai karuwa lamarin yake,wanda kuma idan har ba mu ta shi tsaye an magance matsalar ba to tabbas za mu iya wayar gari an karar da mu baki daya,dan tun ana taba kananun yara da matasa gaba kan iyaye da kakanni za a koma in dai ba mu dau mataki ba,"wannan magana haka take cewar ur exsellency ya ɗora da cewa kuma duk abin da ya faru lefin mu ne,saboda a karkashin mu jama'a take dole mune muke da hakkin kulawa da ita",
Abba yahya ya ce abu na gaba kuma shine yadda mutane suke mana wani kallo kan rashin daukar matakin har sun fara zargin mu akan al'amarin dan duk inda ka je zancen ɗaya ne shi ake ta maimatawa,gaskiya ne wannan cewar defity Alh Ibrahim mangal wanda tun da aka fara tattaunawar sai yanzu ya magantu,ya ci gaba da cewa duk maganar da ku ka yi gaskiya ne,dan haka Ni shawarar da zan bayar ta farko shine ,mu sa jami'an sirri masu amana da gaskiya su yi bincike ta kan duk wani da ake tunanin da sa hannun sa, sannan kuma mu nemi dan jaridar nan AHMAD WAZIR CHIBADO shima ya yi mana aikin binciken ta can karkashin kasa,ina ga Ni dai shawarar da nake da ita ke nan ",jinjina kai su kayi gaba daya cike da gamsuwa da shawarar da defity ya kawo,daga nan suka cigaba da tattaunawa duk akan yadda za a samu sauƙin matsalar.
A cikin wannan ruguntsumin Raihan ta kammala karatun ta,cike da tarin nasarori,farincikin da iyayenta da abokinta A Wazir suka shiga ma kadai ya ishe ta farinciki,Abbi ne da kanshi ya bar duk abinda yake ya dauko Rahim suka dawo gida cike da shaukin ganin yan uwan shi.
Kwanan ta biyu da dawowa,A Wazir ya dira a gidan su dan yi wa abokin shi Raihan sannu da zuwa ta musamman.
A hankali ya danna hon , da sauri,me gadin dake bakin gate din ya leko dan ganin waye, kamilalliyar fuskar A Wazir ba biyayya ba ce ,dan haka take me gadi ya wangale mishi kofa ,shi kuma ya danna hancin motarsa wacce tayi matukar dacewa da yanayin tsarin sa,cikin girmamawa suka gaisa da me gadin kafin ya shiga cikin gidan dan sanar da Rahim zuwan A Wazir chibado.
Kamar daga sama RAIHAN dake can cikin kiching ta tsinkayi sakon da taji shi tamkar bushara,cikin sauri ta dauki ƙatuwar rigar sanyin ta ta zura,tare da ƙara gyara dogon gashin da tuni ta daina aske shi dan sanin hukun cin hakan a musulunci,cusa shi tayi cikin hular sanyin dake kanta,kafin ta fito cikin takun ta na nutsuwa wanda ko takun ka duba sai ka fahimci cewa indai wannan namiji ne to tabbas yana da tarin nutsuwa.
Kai tsaye ta fita daga falon dan so take ta tabbatar da abin da kunnuwan ta suka ji mata,
Zubawa kyakkyawar bakar motar dake fake daga can wajen aje motoci ido ta yi,kafin cikin san gyara takun ta ,ta isa gab da motar Ba tare da ta dauke idanun ta daga kan motar ba.
Bude murfin motar ta bangaren driver ta ga anyi,a hankali ya zuro kyakkyawar kafar shi wadda take sanye cikin rufaffun takalma,kafin a hankali ya fito da gangar jikinsa da kuma fuskarsa me cike da kyawu da annuri da wani irin kwarjini me tsuma zuciyar matsoraci,
Tuni zuciyar Raihan ta shiga wani irin bugu me karfi,duk da cewa ta taba ganin fuskarsa sau daya a tv,to Amma yanzu ji tayi kamar bata taba ganin sa ba,haka kuma gani take kamar camara ta rage tamanin cikin dari na kyau da kwarjinin sa,wani irin jan numfashi ta yi saboda yadda taga yana kusantota da wani irin murmushin da kana gani kasan ba koda yaushe yake yin sa ba, tare da takun da ke cike da nutsuwa tamkar me tafiya saman gajimare.
Jin shi tayi daf da ita ,wanda kafin ta dawowa duniya ,ta kuma tsinkayar tattausan hannayen sa cikin nata hannun,a lokaci daya kuma yana magana cikin muryarshi me fita ɗai-ɗai,ya ce" my friend nayi maka ba zata ko? Shiɗewa ne kawai Raihan ba tayi ba,saboda kafin ta bude baki taji ta cikin jikin A wazir yana mai ɗan bubbuga bayan ta tare da cewa ya kamata ka dawo hayyacin ka, rahim wannan mamakin ya isa haka".
Samun kanta tayi da cusa fuskarta cikin jikin shi tana mai kara shaƙar daddaɗan kamshinsa,idan ta ce ba ta yi mamakin zuwansa ba tabbas ta yi karya,ita shaida ce akan halin wazir da tsananin ajinsa,duk da kuwa cewa ita din ta daban ce a gurin sa amma hakan baisa ya kasa gwada mata halin tsumewarsa da yake halittarsa ba.
Tabbas A Wazir idan ya ce bai ji wani sauyin yanayi a tare da shi ba yayi karya,sai dai kuma bai kawo komai a zuciyar shi ba,saima korar shaidan da yayi,dan a ganin sa duk sharrin sa ne tun da Rahim namiji ne shi ma namiji ne dan haka bai ga amfanin jin yanayin da yaji lokacin da ya rungume Rahim ba...
Fateemah y Adam..........✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page7 ```
Ɗago fuskarta da take ta cusawa a jikin shi yayi,tare dage mata gira , ya ce" aboki saukar da za Amin ke nan? Kunya ce ta kama Raihan,hakan ya sa ta yi saurin sakin sa ta wuce gaba da sassarfa tana cewa sorry Hamma wazir taho mu shiga ciki Abbie ma suna shida Abba yahya bai koma ba" bin bayanta cikin takun shi na nutsuwa fuskar shi kadaran kadaran babu Murmushi kuma ba tsumewarsa da ya saba.
Sosai A Wazir ya samu karba daga gurin Abbie da Abba yahya, antyy amarya kuwa kamar ta goya shi saboda karramawa,har wajen su momy sai da antyy amarya ta ce suje su gaisa daga nan kuma suka dire bangaren Hajiya goggo,anan kam jiddo da ita ma ta dawo daga school kafin dawowar Raihan ta saki baki da hanci tana kallon A Wazir,wanda har sai da Raihan ta taɓa ta, sannan ta dawo hayyacinta gaishe shi ta yi cikin nutsuwa da son jawo hankalin sa kanta,amsawa ya yi ba tare da ya maida hankalin shi kanta ba,hasali ma hankalin shi na kan Hajiya goggo da suke tattaunawa akan batun halin da ake ciki na binciken masu kashe kashen nan saboda yanzu abin kamar yawa yake yi a maimakon ya ragu,jiddo dai bata so haka ba ,to amma ta sawa ranta cewa ai bata da damuwa akan A Wazir tun da har ya iya zuwa gidan su saboda Rahim to tabbas tasan zata iya cin albarkacin rahim ɗin yaso ta harma ta ya aurenta(tofa su jiddi an fada)akan wannan tunanin ta tsaya kuma take ganin shi zai kawo mata mafitar son A wazir da ya dade da kama zuciyarta.
Abbie ya dade da sanin AHMAD WAZIR CHIBADO tare da Rahim dan duk gidan babu wanda bai san yadda Rahim ya dauki A.wazir da muhimmanci ba,Abbie ya ji dadin tarayyar su dan sun jima da sanin juna da mahaifinsa kuma har yanzu ana mutunci da gaisawa harma idan wani abu ya faru da daya suna gaiyatar juna.
Lokacin da zai tafi ne suka tattauna da Abbie akan batun aikin Rahim, Abbie ya dubi A Wazir cikin son ya bashi hankalin sa ,ya ce" Ahmad hakika na yaba da hankalinka ,kuma na yaba da amincin da ke tsakanin ka da Rahim,dan haka zan roki alfarma a gurin ka,ina so zan nemawa Rahim aiki a wajen ku,saboda wasu dalilai.bayan wadan da nasanar da kai"murmushi A Wazir ya yi kafin cikin ladabi ya ce" Abbie kar ka damu tuntuni Rahim ya samu gurbin aiki a wajen mu jiran dawowarsa kawai muke,kuma shine babban dalilin da yasa na aje komai nayi tattaki nazo gida saboda nayi muku bayani yadda zaku gamsu" Cikin farinciki Abbi ya ce" to alhamdulillah amma kuma ɗaukar Rahim aiki kai tsaye ba tare da anyi masa interview ba hakan zai yuwu? A wazir ya dan gyara zaman sa ,kana cikin nutsuwarsa ya ce" Abbie na riga da munyiwa Rahim interview kuma ya cancanci aiki tare da mu, Abbie ina tabbatar maka da cewa ba son zuciya na bi na dauki Rahim aiki ba,cancantar sa ce ta kawo shi matsayin da muka bashi,dan haka kar ka damu ko yaushe ya shirya zai iya fara zuwa aiki" Murmushin manya Abbie yayi tare da cewa shike nan Ahmad na gode Allah ya taimaka ya ci gaba da baku ikon zakulo gaskiya a duk inda take" Amin ya Allah A Wazir ya fada cikin jin dadin addu'ar,sallama su kayi da alkawarin Rahim zai shiga office ran Monday,daga nan fitowa ya yi daga falon Abbien inda ya samu Raihan na zaman jiransa,sallama ya yi da aunty amarya,daga nan suka fito shida Raihan.
Duban shi ta yi cikin marairaita ta ce", Hamma wazir saura alfarma daya nake so ka yi min, duban ta ya yi kawai ba tare da ya ce",ko mai ba,dan surtun da ya yi har ya sa mishi ciwon kai dauriya kawai yake yi,nuna mishi wani bangare ta yi dake gab da fita babban gate ta ce",ina so ka gaisa da inna maimuna innata tama so na ita ce matar Abba yahya ta karasa maganar cikin hade hannuwa alamar roko,jinjina kai kawai ya yi fuskar shi na dan nuna alamun gajiya,ina ita Raihan sam bata ma lura da yanayin nashi ba tun da ba sabon gani da ido ta yi.da shi ba bare ta fara gane yanayin shi,abu daya ta haddace a muamalar su shine maganar sa ta kurmanci ko da ido ya yi mata magana sai ta gane abin da yake nufi,jan shi ta yi suka fara tafiya ganin baya son Surutu yasa itama nata miskilancin ya motsa dan haka tafiyar kurame su kayi har suka karasa gate din inna maimuna.
Ai ko inna maimuna ba karamin farinciki ta yi ba,tarbar ta yi masa itama ta mutunci da nuna muhimmancin mutum a guri,daga nan bai zauna ba ya yi mata sallama tare da kyautar kudi masu yawa,kamar yadda ya zubewa aunty da goggo,godiya sosai inna maimuna ta yi masa, Raihan ma ta ji dadin karamcin da wazir ya yi wa iyayenta.
Bayan tafiyar A. wazir aka sanar mata batun aikinta
Murnar da Raihan ta yi ba kadan ba ce,burinta ya cika na zama yar jarida, sannan zata yi aiki tare da wadanda suka san mutumcin aikin.
Sosai Abbie da Antyy amarya Inna maimuna da Hajiya goggo su kai mata fada tare da nasiha me ratsa zuciya akan riko da gaskiya da amana.
Kebantacciyar nasihar antyy amarya ga Raihan kuwa bai wuce ta kula da kanta ba, saboda nan ba kasar waje ba ce ,kuskure kadan za ta yi a gano ko ita din wacece,ba karamin sanyi jikin Raihan ya yi da tunatarwar antyy amarya ba,ita fa gaskiya ta gaji da wannan abin dan dai kawai babu yadda zata yi ne,da tunanin yadda zata fara mu amala da sabbin mutane a matsayin namiji ta fara shirin tunkarar Monday.
*********
Tunda driver ya sauke ta cikin gidan jarida ta CHIBADO FM,take bin ko ina da kallon sha awa,hakika ma aikatar ba karamin burge Raihan ta yi ba,musamman yadda taga ko ina an tsara shi da kalar fentin da take matukar so,a hankali ta shiga takawa har zuwa bakin katon reseption din da zai kai ka ko wane office dake sama da kasa,tana nan tsaye tana yan dube_dube da tunanin wanda zata tambaya ya Kaita babban office din A. wazir,daga bayanta ta ji anyi sallama,juyawa ta yi tare da amsawa tana mai duban me sallamar,yauwa ina fata kaine Rahim Muhammad nurr? murmushi me kyau ne ya baiyana akan fuskar Raihan kafin ta ce"ey nine"cikin girmamawa mutumin ya ce"nazo ne nayi maka iso wajen sir wazir"na gode Raihan ta faɗa tana mai bin bayan mutumin.
Sama suka hau daga nan suka kuma bin wata doguwar baranda wadda kai tsaye ta sada su da wani katon office me ƙatuwar kofar glass,suna shiga suka tarar da wani dan kebantaccen guri ga dukkan alamu wajen sakatare ko sakatariya ne,ba tare da sun dakata a wajen ba mutumin ya kuma nufar wata kofar glass ɗin me fadi,wani abu ya danna wanda kai tsaye ya bude kofar,shiga ya yi RAIHAN ta bishi a baya.
Zaune yake saman kujerar da take ta faman juyi da shi kan shi a kasa yana duban takardun dake gabanshi,zubawa kwantacciyar sumar shi dake ta kyalli ido ta yi,kafin a hankali taji bugun zuciyarta na sauyawa.
A hankali kyakkyawan matashin me lunkume da shekarun da basu wuce talatin da daya ba, ya ɗago kanshi dake sunkuye wanda tun shigowar su yaji idanun Rahim din na yawo a kanshi,mutumin nan ne ya katse su da cewa yauwa oga ga baƙon naka"jin jina mishi kai kawai A Wazir ya yi, cikin ladabi mutumin ya juya dan yasan ba amsar baka zai samu ba,nunawa Rahim din wajen zama ya yi fuskar shi na ɗan sassutawa daga kamewar da tayi da wan ba kowa ke samu daga gare shi ba,a hankali Raihan ta matsa tare da zama a wajen da ya nuna mata,cikin sauyin yanayin da ta samu kanta a ciki ta bude baki cikin siririyar muryar ta mai matukar ɗadin saurare ta ce"good morning Hamma wazir? morning dear Rahim"A Wazir ya amsa idanun sa akan Rahim din da ya kula kamar ba a sake yake ba,ɗan gyaran murya ya yi tare da kama hannun Rahim ɗin da yake ta faman ƙasƙas da su, ya ce Rahim what happened? Jujjuya Kai Raihan ta shiga yi saboda bata san me zata ce ba ,itama ba tasan me take ji ba,kuma bata san me ke faruwa da ita ba,abu daya ta sani shine duk sanda ta ganshi ko taji muryarshi sai zuciyarta ta buga da wani irin ƙarfi haka kuma sai ta samu kanta cikin yanayin zazzaɓi me ɓalle ƙasusuwan jiki,to amma kuma ai bata san me ke jawo hakan ba dan haka bata da amsar da zata iya bashi kai tsaye.
Murza yatsun ta dake cikin nashi da yayi shine ya dawo da ita hayyacin ta,cikin rashin abinyi ta langabar da kanta se kawai ga ruwan hawaye a cikin kwayar farar idaniyarta,ya Salam A Wazir ya fada tare da ta shi daga gurin zaman sa zagayowa ya yi inda take zaune tare da durkusawa a gabanta ,ya ce" Rahim wai me ke damunka ko wani yayi maka wani abu ne daka shigo?girgiza kanta ta yi saurin yi tare da kirkiro karyar da ya zama dole ta yi "Hamma wazir kawai haka nan na tsinci kaina da shiga fargaba sai nake ji kamar wani abu zai same Ni ta sanadin aikin jarida tunda na riga nayi kudirin rike gaskiya da kamantata a kan aiki na"hannu yasa ya share mata hawayen da suka gangaro tare da tashi tsaye ya koma mazaunin sa wanda hakanne ya ɗan samarwa da Raihan nutsuwa,zama ya yi ya shiga binciken takardu sai da ya ɗibi wasu mintina kana ya ce" Rahim babu abinda zai same ka tunda kaima ka fada ka rike gaskiya kuma zaka ci gaba da rike ta , dan haka ka saki ranka ka fara aiki cikin kwarin gwiwa da karsashi"ya fada yana mai ɗago kansa da sakarwa Raihan murmushin da ya kusa tafiya da dukkan numfashinta,ina fatan ka fahimta A Wazir ya fada idanun shi akan Raihan da ke neman kasa rike kanta,da sauri ta daga kanta tare da share guntun hawayen da itama ba tasan ko na meye ba.
Daga nan ya samu hankalinta ya yi mata dukkan bayanin da zata fahimta,da kanshi ya tashi ya fara zagawa da ita cikin ma aikatar ,kafin ya sa sakatariyar sa Ruma ta sanar da kowa ne staff cewa suna da mittin karfe biyu na rana.
Saboda sanin muhimmanci na lokaci da A. Wazir ya koyawa ma aikatansa yasa karfe biyu daidai kowa ya halatta a cikin katon dakin taron, ba tare da wani jan lokaci ba ya gabatar musu da makasudin taron wato sabon ma'aikaci Rahim Muhammad nurr wanda zai dinga gudanar da shiri akan siyasar mu a yau da kuma hira da su dan jin manufofin su, sannan zata karbi shirin labarin masoya wanda A.qazir ke gabatarwa. daga nan Raihan ta yi dan takaitaccen bayani da kuma godiya ,sai kuma ko wane ma aikaci ya tashi ya gabatar da kansa da kuma ɓangaren da yake dauka,karfe hudu suka tashi daga taron kowa ya nufi masallaci dan yin sallah mata kuma suka nufi nasu masallacin.
Halima ita ce mataimakiyar Raihan,dan haka ko da kowa ya dawo kai tsaye da ita A Wazir ya haɗa Raihan,saboda itama tana da hazaka wajen zakulo gaskiya,ita ce take binciken yan siyasa a sirrance sai dai kuma yanzu dole duk abin da ta gano ko ta binciko sai ta sanar da oganta Rahim, Wannan aikin yana bukatar masu gaskiya shi yasa A Wazir ya dora Rahim a matsayin shugaban halima da ita kanta halimar.wannan ke nan.
A hankali Raihan ta fara gudanar da aikin ta cikin tarin nutsuwar da Ubangiji ya bata,cikin kankanin lokaci ta fara tara masoya,saboda yadda ta iya sarrafa harshe gurin tambaya da kuma yadda take bada hankalinta gurin zakulo ra ayin mutane, musamman a bangaren talakawan mu da kuma jin ra ayoyin su.
Ta fannoni da dama Raihan wadda duniya ta fi sani da RAHIM,ta kawo ci gaba a gidan rediyon CHIBADO FM,kafin wani lokaci sauran gidajen rediyo sun fara kawowa Rahim kokon baransu na san zamowa daya daga