Showing 108001 words to 111000 words out of 189984 words
Chapter 37 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
kallon Ruby da ta fara kumshe idanu tare da ci gaba da sambatun haukanta, ta ce ruby daga yau taki ta kare daga ke har RAIHAN ɗin yanzu zan fara samun salama a cikin rayuwata,Yes koda ban auri wazer ba dole sai na tabbatar da cewa babu wata mace da tayi saura a cikin rayuwarsa,idan ban aureshi ba to babu wacce ta isa ta aure shi indai ina numfashi,daga haka ta fice daga dakin, a falo ta dauki jakarta da mayafinta wanda dashi Gara babu ta fice daga gidan ranta fes.
CHIBAƊO FM
Duk sanda Raihan ta gama gabatar da shirinta na siyasarmu a yau sai ta shigar da cikiyar cp haidar ringim,abun yana matukar damunta kuma tana nan kan bakanta na nemo shi a duk inda yake a raye ko a mace ko kuma labarin mutuwarsa ko inda ya mutu insha Allah.
ALHAJi MUHAMMAD NUR HOUSE.......
Shirun da Hanne taji yasa ta dan fara sakankancewa da cewa dama duk burga ce murja ba abinda zata iya,ko kuma wannan labarin na cewa Company da aka bawa rufa i ba shi kadai bane kadarar Raihan kamar yadda suka zata shi yasa ta aje makamanta tana neman mafita kamar yadda itama a yanzu mafitar suke nema na ganin sun kwace komai daga hannun ur exsellency,kawai sai ta aje tunanin murja ta koma neman mafita,tabbas ba za su samu cika burinsu ba har sai dai idan mutuwa waɗan mutane biyu su kayi ,ur exsellency da kuma nur, ita dama RAIHAN gaibu ce tunda ba yar kowa ba ce sun san dole a raba dukiyarta a bawa yaransu maza,to tayaya zasu mutu? Zuciiyarta ce tayi mata wannan tambaya,dole ne su mutu kuwa ko ta halin yaya ne,ta faɗa cike da confidence,kai hatta da su Rahim din ma da sauran yaran murja duk ya kamata su wuce dan haka ne kadai zai basu damar cin karensu ba babbaka,dan ta wadannan tsofaffin mai sauki ne,wata dariya ta sheƙe da ita kai kace ta samu abinda take so ta gama..
Affan ne tafe kan hanyarshi ta dawowa gida bayan ya tashi daga office,yana gab da karasawa gida wayarshi ta yi haske alamar shigowar sako,ganin cewa sako ne yasa shi dauka ya buɗe sakon.
Kashiryawa mutuwarka nan kusa, ina gaya maka haka ne domin kar ka shagala ka dinga sa rai za kayi tsawon rayuwa wannan damace muka baka.
Cikin gaggawa ya shiga duba daga inda sakon yake sai dai ina babu wata alama da mai sakon ya bari da za a iya gano shi,sosai fa hankalin affan ya fara tashi,saura kiris ya bugawa wata anaconda ya samu ya kauce batare da ya buga din ba, cikin wannan tashin hankalin ya karasa gida, cikin wani irin fushi yake danna hon,ta yadda su kansu securitys din sun gane cewa akwai wani abu,ko rufe motar baiyi ba bare ya kwashi tarkacensa, wayoyinsu kawai ya dauka ya shige bangaren mamansa kamar zai kifa.
Mama mama mama", ya shiga kwala mata kira da shigar shi main falon maman. fitowa ta yi da sauri har tana cin tuntube da dan damalin da zaka haura daga koridon da zai kaika dakinnata zuwa falo,lafiya Affan kake min irin wannan kira kamar wani mafarauci? Ba tare da ya bata amsar tambayar da tayi mishi ba ya karasa inda take tsaye yana nuna mata wayarshi ya ce", mama Kinga yanzu ina kan hanyata ta dawowa gida sai naji karar shigowar sako to da na duba Kinga abinda na gani",ya karasa fada yana mika mata wayar.zaro ido tayi baki bude ganin makamancin sakon da aka Turo mata kwanaki biyu da suka wuce,daɓar ta zauna kan kujerar da tafi kusanci da ita,duba sakon ta kuma yi yanzu dai kam ta tabbatar da cewa Hanne ce keson ganin bayansu,wato saboda taji wannan labarin na dukiyar Raihan yasa ta kara kaimi akan shirinta, yanzu dai ta fahimta Hanne so take ta kashe kowa ta gaje dukiyar ita da ƴaƴanta to wallahi bata isa ba kuma tayi kadan,mu zuba Ni dake", wai mama lafiya? Kin barni tsaye kina tunani,zauna Affan ta faɗa fuskarta babu alamun wasa,zama ya yi yana kallonta cike da mamaki,dubanshi ta yi sannan ta ce", Affan kasan me nake so da kai? Girgiza kai ya yi yana kallonta da dukkan nutsuwarsa,gyara zama ta yi ta ci gaba da cewa ina so ka nutsu kasa mana ido akan waccan matar da ƴaƴanta saboda zargina ya tabbata cewa ita ce take son ganin bayana nida ahlina baki daya", cikin mamaki Affan ya ce", me yasa kika ce haka mama naga fa duk tare muke kulle_kullen kwace dukiyarnan? Wayarta ta dauko ta kunna kai tsaye ta shiga inbox message din ta shiga nema Sa dai kuma wani abin mamaki babu shi babu labarinsa ,to ita dai da hannunta tasan bata goge ba kuma ba wani ne yake daukar wayarta ba sannan babu kowa a cikin gidan daga ita sai mai aikinta duka yaranta suna bangarensu da iyalansu to me hakan yake nufi? Wa ye ya goge sakon? Wannan amsar take bukata sai dai bata san ta inda zata sameta ba", mama mama mama Affan ya fada da karfi ganin yadda maman tayi zurfi cikin tunani,me Zakaria nuna min ? Anya ko mama lafiyarki lau? Cikin tashin hankalin da ta fara shiga ta ce ", Affan na shiga ruɗani kaina ya kulle anya ko hannece take mana wannan barazanar? Yanzu gaskiya na shiga kokonto,me yasa sakon ya goge? Waye ya goge shi? Sako zai goge kansa ne? Me yasa babu abinda ya goge akan wayar sai iya shi kaɗai?mama ki yi min bayani saboda Ni kaina na shiga ruɗani bana gane komai", Affan ya fada cikin damuwa.
Da kyar ta iya saita kanta ta bawa Affan labarin sakon da aka tura mata da abinda ya kunsa,ta ɗora da cewa amma Affan abin mamakin shine yanzu na duba wayar zan nuna maka dan ka ganewa idonka sai dai kuma babu sakon babu dalilinsa abin ya razanani Affan ina cikin ruɗani karfa abinda aka fada nake daukarshi a barazana ya tabbata", ta karasa maganar cikin zubar hawaye zuciyarta kuwa tuni ta karaya tana jin damuwar rasa ƴaƴanta da take kallo a matsayin ƙadara ya'yan da ta kwallafa rai da su,shi kansa Affan da yake namiji ya shiga tashin hankali da kyar dai ya boye nasa damuwar ya rarrashi maman,duk da haka bata samu nutsuwa ba sai da ya kira mata rufa'i da yake Kano taji lafiyarsa tukunna ta danji sanyi Idris ma da yake kusa da ita sai da ta tabbatar yana lafiya kafin nan Affan ya nufi bangarensa.
Dukkan su sun kasa samun nutsuwar zuciya,momy Hanne mama rabi da kuma Affan da yake cikin tsoran test din da a kayi masa,ko wa da abinda yale sakawa kuma yale zato a ransa,shi dai affyya kasa yin tunanin komai domin bai zargi kowa ba tunda su har yanzu kananun kwari ne akan neman duniya har yanzu ba su taka wani matsayi ko buri aiam dukiyar da suke ikirarin ta su ba ce,hasalima wani abin duk kurine iyayensu ma sun fi su kwarin gwiwa da nuna cewa zasu iya komai akan Dukiyar,shi yasa duk yabi ya razana dan ragowar burin da yake dashi na neman sarayewa.
*RAIHAN*
Tsaf ta gama shirin baccinta, tayi kyau tamkar ka saceta ka gudu,rufke gashinta ta yi ta saki jekarsa kan kafadarta,fuskarta sheki take da akwai yanayinta na shagwaɓa da ya kama jikinta,wanda da yawa mutane suke mata kallon sakaran namiji me yanayi da mata.
Zama ta yi gefan gadonta tana murza turarenta na gabon tare da kwalaccarta me sanyi kanshi wanda ya riga ya kama ko ina nata, laptop ɗinta ta jawo ta buɗe.
Cikin nutsuwa ta fara binciken shafin tree full y trues,haka nan take jin yanzu kamar ya zama mata dole akan ta nemi taimakon ko su waye waɗannan tree full y trues din dan ajikinta take jin cewa ba mutum daya ba ne sai dai idan kungiya ce me zamanta kanta.
Wayarta ce ta yi alamun haske ɗan dakatawa ta yi da abinda ta fara tana duban wayar,kamar ba zata daga ba sai kuma ta dauka tare da karanta abinda aka turo mata,me kike yi har yanzu baki bacci ba? Abinda Wazer ya rubuta a sakon ke nan.zubawa rubutun ido ta yi fuskarta na kokarin tona abinda ke cikin zuciyarta duk kuwa da cewa tana kokarin kaucewa hakan,a ta wani bangaren kuma ta so yin mamakin yadda akayi yasan cewa batayi bacci ba,me gani har hanji ta faɗa saman lebanta,tana kokarin maida masa kiranshi ya shigo,sai da ta yi ringing ta ta mutu ya kuma kira sannan ta dauka tare da yin sallama cikin nutsuwa da dan fidda sautin da zai nuna cewa daga bacci ta tashi,tura karamin bakinta tayi jin yaki cewa komai cikin yanayin ƙunkuni me haɗe da shagwaɓa tace", nikam ina jin bacci", da me ya hana ki yi? Ya tambayeta cikin Muryarshi me cike da wani irin sautin da ke nuna cewa shi ɗin fa miskiline na bugawa a jarida,umm Ni ", shiiiiii ya katseta yana kuma cewa na sani baki bacci ba me kike da computer?da sauri Raihan ta fara juye_ juye dan yanzu ta fara tunanin ko dai tana cikin dakinne? Idan ba haka ba me yasa yasan duk abinda take yi yanzu", kafin ta Ankara ya maida kiran video, saurin kallon jikinta tayi dan ganin wace irin shiga ce a jikinta dan zuwa yanzu wazer ya shafe komai na tunaninta ko mai sai ta tuna shi a wannan gabar, wazer ya wuce duk yadda take tunaninsa wani irin mutum ne dan baiwa wanda yake tare da wasu ilhamomi shi yasa yake da kwarjinin da kowa ke kasa tunkararsa kai tsaye.
Ganin yadda take yi din sai abun ya dan bashi dariya ,amma ba zaka raba fuskanta ba domin babu komai saman kyakkyawar fuskarshi sai gizagonshi da kuma wani sirri da yake boye can cikin kasan zuciyarshi.
A hankali ya maida idanunshi ya lumshe su yana mai dan fesar da iskar bakinshi,zuciyarshi na bugawa a hankali,jikinshi na wani irin sakewa da irin sakewar da yake yi duk lokacin da idaniyarshi suka yi arba da Raihan,kasa_ kasa yake ci gaba da karewa halittarta jikinta da ta bayyana cikin ƙananan kayan baccin da tasa,wanda ita a yanzu take da ta sanin sawa da tasan cewa zai yi mata irin wannan kiran,yana kallon yadda take ta muku_ muku tana kakkare ƙirjinta da ya fi komai bayyana cikin kayan baccin.
A hankali cikin son basar da abinda ke tsunkulin zuciya da gangar jikinsa ya ce",baki bani amsa ba", a hankali ta kalli fuskar wayar fuskarta da zuciiyarta na son kasa daukar abinda take ji,ta ce", yanzu zanyi", ko dai kina son nazo ne? Diri diri ta fara yi jin tambayar da yayi mata,kafin ta fita daga kunyar da ya jefa ya kuma sakin mata wani zancen da cewa,kina son nazo na sumbace ki fiye da na ɗazu kina son ki kwanta jikinsa fiye da yadda ki kayi dazun uhm bani amsa mana Raihan ", tuni jikin Raihan ya shiga wata irin rawa da wani irin sanyi kai har da wani irin tashi da duk wata tsigar jikinta ta shiga yi,da kyar ta budi baki cikin rawar bakin ta ce", plz dan Allah Hamma wazer kayi HAKURI ", nayi hakurin shike nan kwanta ba zan sake ba sai idan muna tare", da sauri ta kuma duban shi sosai ta kalli bakinshi da fuskarshi sai take ganin kamar bashi ne ya yi duk wannan din ba,dage mata gira ya yi ya nuna mata bed dinta da ido, cikin mutuwar jiki ta kwanta kamar yadda ya umarceta nuna mata yya kuuma yi ta ja bargo ta rufe jikinta dan da alama dai maganar da yayi yanzun har ta gaji da shi,nan ma bata Musa ba ta rufe jikinta sai kuma addu'a da yasa ta yi,karshe dai bai kashe wayar ba har sai da ya tabbatar ta yi bacci.
Kashe wayar ya yi yana ɗan sakin murmushin da ace da mutane a kusa dashi tsaf za suyi suman wucin gadi saboda tsananin kyawun da ya yi wa fuskarsa,ta shi ya yi ya shiga bathroom zuciyarshi cike da tunanin Raihan da komai nata, wannan hirar da yayi da Raihan ita ta mantar da shi duk wani ɓacin ransa akan rabi.
*Washe gari*
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page39 ```
*RUBY*
A hankali take bude idanunta,dishi dishi ta fara gani, sai da ta yi kusan sakonni goma kafin ganinta ya dawo dai-dai,take mafarkin da ta yi ya shiga dawo mata, da sauri ta tashi zaune tana dube dube kayan dai dake jikinta a mafarkin sune har yanzu a jikinta, wannan wane irin mafarki ne haka? Bata taba yin mafarki ta yi addu'a ba sai yau, hannu ta daga sama ta ce", ya Allah ina rokonka kar na sake maimaita irin wannan mafarkin bare har ya kasance haka ta faru a gaske ,tashi ta yi tana kallon agogon dakin da ya nuna karfe takwas daidai na safiya a ranta ta kissima cewa bata makara ba dan haka cikin sauri ta shirya ta dauki jakarta ta fito,ba ko kalli bangaren wazir ba dan tasan yanzu ya tsufa a office.
Da kanta ta tuƙa kanta zuwa office.
*RAIHAN*
Tunda tazo ta kashe wayarta a cewarta wazer da kiranshi suna son hanata aiki,to amaimakon ta samu sukunin aikin tunda ta kashe wayar sai hakan bata samu ba,tunaninshi da duk wasu alamuransa sunyi cunkus a zuciiyarta, idan ta tuna moment dinsu na jiya zuwa hirarsa ta daren jiyan se ta ji duk jikinta ya mutu,, ko me take yi kuwa sai ta dakata sosai take kokarin ganin takawar da duk wasu tunanin wazer ɗin amma hakan ya gagara.
Wazir shi kansa bai neme ta ba don a ranshi yaji kamar idan ya ci gaba da irin hakan tabbas wataran zai zubda girmanshi a idanun yarinyar,kwarin gwiwa ya shiga son bawa kanshi tare da kokarin danne abinda yake kokarin gagararshi rikewa.
Ruby tana zuwa kai tsaye dakin daukar rahoto ta nufa,ji tayi zuciiyarta na ta buga da karfi lokacin da ta yi arangama da Raihan,tsayawa ta yi ta zuba mata ido tana tuni mafarkinta na jiya,jin kamar numafashinta na san daukewa yasa ta yi saurin kawar da abin a ranta,dan bata son ta zurfafa bincike har abinda take gudu din ya zama gaskiya,karasowa ta yi ta zauna tana dan sake fuskarta,su abu Huraira ne suka gaisa da ita, ita ko Raihan ko nuna alama na cewa tasan wani ya shigo ba tayi ba,ruby dince ta hadiye wani irin yawu me daci da kauri ta ce", Rahim kai baka iya gaisuwa ba ne? Ko manya ba su koya maka ba? Ba tare da Raihan ta dubi inda take ba tana kuma ci gaba da aikinta ta ce", ey mana basu koya min gaida wanda bai iya sallama ba", cikin harzukar da ma aikatan basu san dalilinta ba,ruby ta ce", kai dan daudu bana son fitsara da rashin kunya maza ka saita kanka ba agaban kawayenka yan daudu kake ba bare kayi min karairaya da salon iskanci", ɗif dakin ya kuma ɗaukar shiru har da wadanda suka tsaida aiyukansu duk a sanadin furucin da ruby ta yi.
Ita kanta Raihan maganar ba karamin shigarta ta yi ba bare kuma wazer da yake kawo kansa cikin gurin a kuma daidai lokacin da ruby ke yabawa Raihan mummunan kalaman,ba tare da Raihan ta tanka mata ba ta mike dama ta gama gabatar da shirinta, sai da ta zo fita ne ragowar suka san da zuwan wazer,ita kam Raihan dama tuni yasan da zuwansa saboda yadda taji yanayin bugun zuciiyarta ya sauya hancinta kuma ya shako mata ƙamshinsa da ya zama hadda a gareta,tuni kowa ya cigaba da aikin gabansa suna nuna alamun tsoro na tasirin kwarjininsa,ita kanta Ruby ba karamin shiga shock ta yi da ganin nasa ba,amma dake yar duniya ce tuni ta fiske ta dubi wazer ɗin tana murmushi ta ce ", my Suger ƙaraso mana idan kana son ganina ai sai ka kirani ba sai ka zo dakanka ka wahalar min da kanka ba", wani irin kallo ya wullah mata wanda babu shiri ta shiga taitayinta,juyawa yayi ya fita, ba tare da ya tankawa kowa ba.
Kasa_ƙasa staf din suka fara dariyar dizgin da wazer yayiwa wadda take ta jin kai tana tutiyar ita din matarsa ce,wasu kuma wadanda da yawa suke jin haushin Rahim na yadda yazo a bayansu lokaci daya yayi musu kaka gida ya tare gaba da baya na cigabansu acewarsu,suka shiga tunani akan maganar ruby harma maganar daudun ta zauna daram a kansu da kwakwalwarsu.
Tuni ruby ta kuma shaka ta kuma ci alwashin cewa sai ta rama akan Raihan, wannan wulakancin da akayi mata sai tasa anyiwa Raihan gomanshi.
Raihan tana fita kai tsaye waje ta nufa ba tare da tasan inda ta nufa ba, wannan kalmar ba ba bakuwar kalma bace a cikin kunnuwanta sai dai ba ita ake kira da ita ba,tana dai ganin masu halaiyyar ta kuma san me kalmar ke nufi tunda har da case din a cikin case din da take shirin tonawa na su shugaban jam'iya,shi yasa tayi matukar yi mata ɗaci,sai take ganin wata ƙil ma da yawan mutane da abinda suke kallonta ke nan tunda da yawa suna cewa muryarta na kama da ta mata ko tafiyarta ko salonta da dai makamancin wannan,bata taɓa tsayawa tayi nazari akan hakan ba sai yanzu da rubby ta kasa sakayawa kamar yadda mutane suke sakayawar ta jefe ta da kalmar kai tsaye,ji tayi wani tattusan hannu ya riko nata hannun bata yi wani dogon nazari ba tasan cewa wazer ne,dago idanuta da suka cika da ƙwallah ta yi tana kallon ta shi dake hade kamar hadarin gabas,bai ce mata komai ba ya yi mata nuni da motar da ya fito da ita,bata Musa masa ba ta shiga,shima zagawa yayi ya shiga ya fizgeta da gudu,wanda ta hakanne Raihan ta gane ransa a matukar ɓace yake.
Shiru ne ya ratsa tsakaninsu,a hankali ya koma tafiya bayan