Showing 87001 words to 90000 words out of 189984 words
Chapter 30 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
me matukar wuya wazir ya kuma dawowa gareta,kukan da nasani ta kuma rushewa da shi tana Dada jin haushin kanta.
Tare suka fito da Abbun daga masallaci bayan idar da sallar Isha,kamar yadda ya saba bin Abbun ya yi zuwa sashen innawuro inda suke haduwa tun can baya dan yin dinner.
Suna shiga innawuro ta fara washe baki tana dan tsokanar sa,bai nuna yadda da shirin da ta ke nema kai tsaye ba dan ya ɗora masa ayar tambaya,hakan yasa ya yi mata fuskar shi ta ko yaushe wato ya gaida ta cikin fuskar shi ta gizago babu yabo babu fallasa,bata damu da yanayinna shi ba,ta ci gaba da yi masa magana cikin yanayin kauna kamar yadda ta saba mishi a can baya kafin rabi a ta shigo ta fara hada su fada,wazirin gida yau nayi maka tuwon da kake so nasan za kayi murna", thanks ya fada saman labbansa yana neman guri kusa da Ammi yana zama, rike hannun Ammin ya yi yana gaidata cikin kaunar ta dake dulmiye cikin ran shi,itama cikin kulawa ta amsa tana tambayar shi lafiyar rabi a,bai kula da tambayar ba bare ya amsa sai ma maida hankali da ya yi kan labaran da ake yi a tashar su.
Kamar yadda innawuro ta faɗa kuwa ,ya ci tuwon alkamar sosai,daga nan bayan duk sun gama suka koma falo,shukrah dakin innawuro ta wuce ta bar su dan wannan ce tarbiyyar da Ammi ta yi musu,duk lokacin da suka ga alamar za a yi wata magana da bata shafe su ba to sam basa zama a gurin sai dai In neman su aka yi.
Gyaran murya Abbu ya yi yana d'an gyara zamansa ta hanyar barin bayan sa daga jikin makarin kujerar yana duban wazir da yake ta dan danna waya,ganin haka yasa wazir din dakatawa da danna wayar ya maida hankalinsa kan Abbun,cikin nutsuwa Abbun ya yi masa bayani kamar yadda ruby ta zo masa da shi , sannan ya dora da cewa sai ka duba wajen da ya kamata ka sata amma dai banda bangaren tv tun da kasan ba wai takaranci abin ba ne sai dan shi aikin jarida yana da bangarori da dama wanda yasa ake iya daukar mutum ko da baiyi karatun ba", innawuro ce ta fara magana ,to ya za ai ka yi masa haka bayan baka tambaye shi ko yana da ra ayin matarshi ta yi aikin ba?ta karasa maganar idanunta akan wazir da har yanzu bai ce komai ba,sai dai jin maganar da innawuro ta yi yasa ya ɗago ya dubi Abbun dan ganin yadda zai karbi zancen na innawuro,sai dai kuma kallon da Abbun ya yi masa take yasa ya karaya ya kuma gane karatun kurmancin nasa,dole ne ya hakura rabi a ta yi aiki tunda Raihan ma aikin take yasan da wannan Abbu ya yi amfani wajen kin ba shi damar jin ta bakinshi,to amma ai shi abbu bai san wacece rabi a ba, shi ka dai yasan wacece rabi a halin yanzu.
Cikin kamammiyar Muryar shi ya ce",shike nan Abbu akwai wajen da zamu bata idan tana bukata sai ta zo ta maye gurbin",da ga haka ya mike yana musu sallama,Bin shi da kallo Ammi ta yi tana jin babu dadi akan yadda ake yawan tursasawa yaronta,ita kadai take gane karatun zucin wazir duk kuwa yadda ya kai ga boye abin da ke cikinta,yanzun ma kallo daya ta yi masa ta tabbatar da cewa bai gamsu da wannan bukata ta rabi a ba,zai yi biyayya ne kawai kamar yadda ya saba yi,bata da abin cewa tun da ba zata ce da wazir kar ya yi wa Abbun shi biyayya ba dan haka fatan Alkhairi ne kawai abin yinta.
A hankali ya janye kofar gilas din da ta mamaye rabin bangon kofar,cikin nutsuwarsa ya saka zara zaran kafafunsa wanda take suka lume cikin tattausan Grass Capet din da ya mamaye dukan falon,bakin shi dauke da yar karamar sallama fuskar nan a kimtse babu alamun ya taba fara a ma bare kuma dariya.
Zumbur ta mike daga zaman jiran shigowar ta sa kamar yadda ta yi alwashi ko da ba zai kula ta ba dole ne ta san matsayinta indai har ba so yake to koma ruwa ba.
Da sauri tasha gaban sa duk da irin bugun da kirjinta yake saboda tsananin tsoro,Hamma wazir ta faɗa cikin rawar murya da aro jarumta,cak ya tsaya yana kallon yadda ta tare masa hanya,sosai ta boye yadda kwayar idanunshi da tsananin kwarjininsa ya daki fuskarta da zuciyarta har ya fara sata rawar kafa,Hamma wazir ta kuma fada cikin dakiya,yadda ya tsaya bai wuce ta ba shi ya nuna cewa yana sauraron ta, dan haka cikin dan kwarin gwiwar da ta samu ta fara magana cikin marairaita da son ya tausaya mata ta durkusa akan gwiwowin ta ce",dan Allah hamma wazir ka tausaya min wlh idan baka dawo gare Ni ba zan shiga cikin masifa wannan abun da ya faru tsautsayi ne,amma dan Allah kar ka juya min baya na yadda ka yi min duk hukuncin da zaka iya amma kar ka barni,kar fa ka manta Ni matarka ce kuma ina da hakki akanka wlh ina tabbatar maka idan baka sauke hakkina ba ko mai zai iya faruwa da Ni daga ciki kuwa har da komawa ta aikin da na riga na daina tun kafin muyi aure",wata irin tsawa ya daka mata wadda bata san sanda ta koma bayan kujera ta makure ba,tuni kanta ya hau juyawa saboda tsananin tasirin da tsawar ta yi a kanta,nuna ta ya yi da yatsa cikin wani irin ɓacin rai da bata taba gani akan fuskarsa ba,da wani irin sauti da ke fitowa da kauri da amo mai gigita wanda ake yiwa,ya ce",rabi a dan Allah ki koma idan kin ga dama ki dinga kwana da maza goma bai shafe Ni ba,yaushe kika rainani da har kika tsaya a gabana kina bani wasu shirmen zantukan ki?yaushe na zama sa anki?ya tambaye ta yana kuma zaro mata manyan idanunshi kamar dai yadda ake yiwa yaro idan ya yi abin rashin ji.
Girgiza kai ta shiga yi jikinta na bari hawaye kuwa kamar an bude famfo.
To ki sa a ranki cewa Ni dake har a bada in dai a shimfida ne domin ba zan ci gaba da kwana da kazama ba,yanzu ma dan baki san ko Ni waye a kan kyamar maxinaci ba shi yasa kika zo kina Min shirme,daga yau bana bukatar ko mai daga gare ki,in kin so ki ci gaba da aikin na ki da kika daina tun kafin auren, stupid girl ",ya fada tare da barin wajen cikin bacin ransa da ya gama bayyana saman kyakkyawar fuskarsa.
Wani irin kuka ta sa har da birgima kamar karamar yarinya,tana yi tana dukan kanta kamar wata sabon kamu.
Kai tsaye toilet ya fada tare dasakarwa kanshi shaya,idanun shi a lumshe yana kokarin saita kan shi da son mantawa da damuwar rabi a wadda yake ganin sam bata da wani amfani,ya jima kafin ya daura alwala ya fito.
Zama ya yi kugun shi daure da karamin towel ruwa na sullbewa da ga lallausar fatar shi,hannun shi ya mika ya dauko wayar shi,haka nan zuciyar shi ta dinga jan shi tana rada mishi sunan Raihan ta na kuma zana mishi taswirar hotanta cikin idanunshi sannan kuma take nuna mishi kamar nan ne in da zai samu nutsuwarsa da rabi a ta yi fatali da ita.
RAIHAN.........
Fitowar ta ke nan daga bathroom wanka ta yi jikin ta daure da karamin towel din da ko cinyiyin ta bai rufe ba,haka kuma bai ritsa ta ba dan haka riko shi ta yi da hannu daya da niyar da ta shigo ta sa kayan bacci ta kwanta dan yau din ta gaji ba laifi.
A kan wayar ta dake haske idanun ta suka sauka,hakan yasa ta karasa saman gadon da wayar ke yashe ta dauka,dan yatsina fuska ta yi tana jin haushinsa da na rabi a da ya kasa barin zuciyarta,dannawa ta yi ba tare da ta kula ba a bazata kuma ta ci karo da kyakkyawar fusk
ar shi tare da kirar shi ta karfi da ke nuna alamun suna yawan samun giming,sakin wayar ta yi tana dan fiddo da fararen idanunta waje,da sauri kuma ta dauki wayar zata kashe,ganin me take son yi shi kuma ya bata kyakkyawan kashedi cikin kamammiyar Muryarsa,idan kika kashe wayar nan ko mintuna goma ba za ai ba zanzo har cikin gidan na dauko ki a gaban kowa da kowa na kawo ki nan ki kwana a cikin dakin nan a kuma kan kirjin nan",ya fada yana yi mata nuni da faffadan kirjinsa wanda ke cike da kwantaccen gashi baki sidik.
Wani irin numfashi ta furzar tare da gyara wayar ta ajiye ta saitin ta, Sannan ta koma ta sunkuyar da kanta tana kananun hawaye tare da kumbura baki kamar fulawar da aka sawa yis,ita sam ta ma manta da yadda take ta idanuwanta kawai take da suke kara hasko mata kirar mazan takar AHMAD WAZIR CHIBADO.
A hankali ya koma da kan sa ya kafe jikin gadon yana mata wani irin kallo na kurilla wanda take jin sa a cikin jikinta,wani kakkauran miyau ya hadiya saboda idanun shi da suka fara gano mishi tundun na Fulaninta wanda towel din da ta daura ya dan zame ya sauka, shine kuma ya bashi damar dan ganin nasu,jin yana neman kashe ta da kallon shi da yake tsira mata har can kasan zuciya yasa ta dan ɗago domin ganin me yake yi anya ma kuwa yana kan layi ba bacci yake ba?.
Zuruf idanunta suka fada cikin nasa da ya ɗagosu daga kallon kirjinta ya dawo da su kan fuskarta da take wani irin glowing wanda ya yi sa a ita ma ta ɗago nata suka shige cikin nasa,bai yi kasa a gwiwa ba kuwa wajen sarkesu katamau cikin nasa ta yadda ta kasa fuzgewa daga kallon kwayar idanun sa.
..............✍🏽
[12/21, 12:40] : *Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page30 ```
Ƙif_ƙifta idanun ta shiga yi bayan kallon juna da suka yi na kusan mintuna biyu,da kyar ta samu ta kaucewa kallon kaifafan idanun nashi masu kama da mai jin bacci.
Mulmula baki ta shiga yi cikin takaicinsa da ke kume a ranta.
Kina magana ne?
Ya tambaye ta cikin wani irin sauti da salon da yasa jikinta karasa macewa wanda har bata san lokacin da ta saki towel din dake jikinta ba,numfashin da ta ji ya saki kamar wani mai ciwon asma ne yasa ta bude idanunta da ta rufe su da tafukan hannayenta satar kallon shi ta yi take ta ci karo da idanun shi da ke tsaye kyam akan na shanunta da towel ya zame daga kansu ba tare da tasan da hakan ba,wata irin zabura ta yi tare da cukyikyiyewa cikin tattausan bargonta tana jin kamar kasa ta tsage ta shige ciki.
Lumshe idanunsa da suka dan sauya ya yi tare da kashe wayar gaba daya, addu'a'in shi ya yi ya shige cikin bargo ba tare da ya sa ko kaya ba,dan ji ya yi ba shi da wannan zarrar zuciyarshi da jikin shi har ma da ruhin shi gaba daya sun mutu da wani irin dafi me zafi dafin da ya kasa tantance ko na meye har yanzu.
Ita ma Raihan a haka ta yi bacci da towel da kuma tsananin kunyar da AHMAD WAZIR CHIBADO ya sanya ta.
Rabi a kuwa haka ta kwana cikin kuka da takaicin wazir,tare da cin alwashi akan duk wata mace da ta yi sa ar sace zuciyarsa,ta yi alkawarin yadda bata samu wazir ba babu Macen da ta isa ta same shi,tabbas ta ci buri akan wazir kuma yanzun ma bata fidda rai ba,sai dai kuma ta hakura da samunsa a yanzu amma fa babu wadda zata same shi,dan ko zata yi yawo babu takalmi sai ta halaka ko ko nakasta duk wadda zuciyar wazir ke kanta, wannan alwashi ne da kuma alkawari me girma da ta daukarwa kanta.
Dudu da shushu uban mashurikai dama sauran mabiya bayansu,yanzu hankalinsu ya kwanta dukkan su sun maida hankalinsu kan abin da ke gabansu wato siyasa dake gabatowa,kowa ya kwanta bacci da niyar wayar gari da ɗorawa daga inda ya tsaya da sababbin shirye shirye da suka samu daga uwar goyon su tsohuwa mai jini.
Washe gari da mutuwar jikin da har yanzu bata sake ta ba Raihan ta tashi,tana gama shiryawa ta shiga dakin hajiyar agades,tsayawa ta yi tana kallon hajiyar da ta ga kamar bata ji dadin shigowar ta dakin ba,kai kamar ma wani abu take yi ganin Raihan din ya dakatar da ita,sharewa ta yi da yanayin nata ta shiga gaidata,sama sama ta amsa,ganin da Raihan ta yi kamar hajiyar agades din a kagare take da ta fita daga dakin sai kawai ta yi mata sallama ta juya dan fita daga dakin,Muryar hajiyar ta ji tana cewa Raihan ina so ki dinga kulawa sosai da duk wani na kusa da ke saboda kowa yanzu ba abin yarda ba ne",a mamakance Raihan din ta juyo tana duban hajiyar agades din da ta yi tamkar ba ita ce ta yi magana ba,dama ke ma kin sanni a matsayin Raihan?ta tambayi hajiyar cike da mamakin da ya kasa barinta,hajiyar bata ce mata komai ba,ita kuma Raihan ta kasa fita,wani dan tunani ta yi ashe fa kakan ta yasan ko mai to in haka ne kuwa ba abin mamaki ba ne dan hajiyar agades ta sani,to amma me yasa shi ita hajiyar su ta nan a ka ki sanar da ita me hakan yake nufi?me yasa kakanta ya sanar da hajiyar agades?
Idan kika takurawa kanki da tunanin sanin abinda ke boye tabbas zaki saka kanki a rudani,kawai ki tafi da yadda kika fahimta wannan shine shawarata,cewar Hajiyar ta faɗa tana kokarin shiga bathroom,jin jina kai kawai Raihan din ta yi tare da ficewa daga dakin ƙwaƙwalwarta kuma na son fassara maganar Hajiyar agades.
Yau bata tsaya jiran kowa ba,duk da dama can ba jiran take ba, da kanta ta tafi ba tare da mashin ko mota ba,dan sahu ta tare ta shiga.
Kalle_kalle take yi kamar ance kalli can idanunta suka hango mata wata bakar mota me bakin galas,tare da wasu zaratan maza zabga zabga suna kokarin cusa wasu yanmata guda uku a cikin motar,dukkansu fuskarsu a rufe matan kuma da alama sun sumar da su dan cikin kwanciyar hankali suke saka su cikin motar kasancewar safiya ce babu yawan zirga zirga kuma area ɗin babu yawan jama'a.
Cikin sauri Raihan ta ce",da me nafef,yi sauri kabi min motar nan amma dan Allah kar ka bari su fuskanci su muke bi,ok badamuwa me maching ya fada yana sawa adaidaitansa wuta.
Daidai lokacin kuma Wazir dake kwance cikin lafiyayyar motar shi Ramadan drivan shi da kuma securityn shi suna gaba,ya bude idanunshi dake lumshe yana duban gefan hanyar da zata sada shi da gidan su Raihan wanda tafiya ƙalilan ta rage musu su karasa gidan,wani irin yanayi ne ya ziyarci gangar jikin shi, a hankali bugun zuciyarshi ya sauya,yanayin da yasan cewa sai Raihan na kusanto shi yake ji ya mamaye shi,bude manyan idanunshi ya yi sosai yana kallon hanyar wanda da sam hankalin shi ba akanta yake ba,giftawar adaidaitan kawai ya gani zuciyar shi ta tabbatar mishi da cewa Raihan ce a ciki,ku juya mu bi dan sahun ya fada cikin Muryar shi dake fita cikin dan kakkauran sauti.
Ok oga,Ramadan ya fada yana gaggawar juya motar kamar yadda ya fahimci Muryar ogan nasa shima a gaggauce ya ba shi umarnin.
Cikin kwarewa da sanin makaman aikinsa me nafef yadinga kurdawa yana bin motar nan ba tare da sun Ankara da hakan ba,
Can cikin zuciyar wazir kuwa mamaki ne da jinjinawa dakiya irin ta Raihan,saboda lokaci kadan ya fuskanci me take shirin yi,tun bayan da yaga sun kaucewa hanyar office ɗin su.
Can bangaren su Alhaji sale da su sanet tare da sauran memba da suke tare kuwa suna gidan gonar da yake mallakin Dr sanate suna jiran aikin da suka bada a yi musu,shugaban jam'iya bai san da wannan aikin ba,hasali ma bai san cewa suna munafuntarsa ta bayan fage ba,sai dai kuma abin da bai sani ba shine kamar yadda yake munafuntar uban gidansa gwamna Alhaji Garba to shima haka wadan da ya bawa yarda da amana suke munafuntarsa da son kokarin ganin sun mayar da wani gurbin sa.
Zaman jiransu ne ya kare a daidai lokacin da bakar motar ta Kunno Kai cikin gidan gonar,gaba dayansu suka mike bakinsu a washe saboda ganin alamun samun nasarar aikin da suka tura ayi musu,Dr sanate ne ya fara takawa zuwa wajen motar wadda yake binta da kallon tsaf kamar yana son gano wani abu ajikinta,ganin haka yasa sauran ma suka bi bayansa sai dai su hankalin su ba akan motar yake ba ,yana kan yaransu dake fitowa daga cikin motar.
Raihan dake daga bayan su ta inda ba kowa zai lura da ita ba,ta yi saurin saita camarar ta ta fara daukar su da fuskokin su daya bayan daya har zuwa kan yaran da motar wanda ta biyo baya,gani ta yi gaba daya sun yi cikin falon dake hagu da su,hakanne ya bata damar fitowa sosai tare da yin azamar zuwa ga motar dan tseratar da yaran da aka kwamushe.
Tana sa hannu dan bude motar da bata da tabbacin a bude take taji wani sassanyan ƙamshin da hancinta ya jima da hadda ce shi,da sauri ta juya da mamakin da take ji taci karo da kyakkyawar fuskarsa nan me cike da kwarjini da wani irin haiba dake nuni da shi din cikakken namiji ne me tarin nutsuwa,waro ido ta yi tana buɗe baki dan fidda mamakinta na ganin nasa anan ɗin,kafin tace komai ya riga ta ta hanyar janyo ta daga jikin motar yana cewa kina kiyaye igiyar aure yarinya me karambani",daga hakan yasa hannu ya bude motar,take kuwa motar ta budu, kallon yanmatan dake kwance bayan motar su kayi kowa da irin tunanin dake ransa,mu bar gurin nan ya fada yana janyo hannunta,cijewa ta yi tana