Showing 48001 words to 51000 words out of 189984 words
Chapter 17 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
ba,tana can tana zuba murmushi me kama da dariya saboda labarin da Hamma idi yake bata na wata budurwar sa beyerabiya,,rufe motar ta yi tana daga mishi hannu,zan dawo na dauke ka, idan ka tashi ka sanar da Ni, Hamma idi ya fada yana tada motar,ok zan kiraye ka Rahim din ya fada yana juyawa dan shiga bangaren office din su.
Ganin ta juyo yasa shi saurin dauke idanun daga kanta wanda ya zuba mata tun bayan fitowar ta,wuce wa ya yi ba tare da ya bari ta karaso in da yake ba,tura baki ta yi tana cewa zan biyo ka ne amma kayi ka gama fushin naka ,dan ba zanzo kana ci min magani kamar wani boss ba,da wannan kunkunin ta yi wucewar ta office din su....
________________
Dr kana ganin yaron nan zai kawo mana sakamakon nan kuwa,tun fa dazu muke jiran sa amma gashi sama da'awa daya bai zo ba"cewar shugaban jam'iyya ke nan da duk yake a kage da son sanin wanda halima ta turawa sako,kafin Dr ya yi magana wayar shi ta yi kara,yauwa ga jagwal din nan, ya fada yana daga wayar,ka shigo kawai kai muke jira amma dai ka tabbatar babu wanda ya ga shigowar ka ko? Ok tom shike nan,daga haka ya katse wayar,cikin mintuna biyar jagwal ya shigo falon,mika masa hannu kawai shugaban jam'iya ya yi tare da cewa bani sai ka yi min bayanin yadda zan fahimta,mika masa takardun bayanan jagwal ya yi yana cewa,anyi nasara sir na gano har gidan da yaron yake me suna Rahim kuma shima ma aikaci ne a chibado fm,kuma na yi kokarin gano ai nahin sakon da aka tura masa" .
Wata irin zabura shugaban jam'iya ya yi fuskar sa cike da wani irin annuri ya ce"Masha Allah yaro kayi abin da bazan manta da kai ba,dan haka za a ci gaba da tafiya me kyau da kai, Allah ya taimakeka yarinyar nan ta yi sanadin arzikin ka,dama ance mutuwar wani tashin wani,yi saurin sanar da Ni abin sakon ya kunsa",gashi nan a jikin wannan takardar kawo na karanta maka sir,ya fada jikin shi yana rawar farincikin tsintar dami a kala.
Mika mishi ya yi,cikin ta rawar jiki jagwal ya fara karantto sakon kamar yadda halima ta rubutawa Rahim,babu kuskure ko guda har inda ta ajiye camarar,,,,,,tofa kaka tsara kaka Rahim baka dauko camara ba an gano inda camara take ya abin zai kasance ne,yaya gumurzun zai fara tsakanin Rahim da shugaban jam'iya harma da ragowar tsumammun da bamu san su ba.......✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page15 ```
Wata shegiyar dariya suka saki gaba dayan su irin ta manyan basawan nan,kafin su gimtse fuska duk alokaci guda,Dr ya ce"muyi gaggawar shiga gurin nan sai dai matsalar su tk basa kusa,kuma dole su ya kamata su je gurin tun da su ne suka sani,shugaban jam'iya ya shafa sankon kansa tare da cewa kuma bai kamata muyi jinkirin dauko camarar nan ba,tun da dai mun samu tabbacin bai dauke ta ba,saboda umarnin da yarinyar ta bashi na cewar kar aje dauko camarar a kusan nan"haka ne amma duk da haka sai munyi da jiki saboda samun matsala,waya ya dauko ya kira su tk,ya akai tk kun dawo daga wancan aikin ne? To maza yanzu ku jiyo ga abin da yafi wannan muhimmaci mu hadu a wancan gidan na bayan gari"daga haka ya kashe wayar,ya dubi shugaban jam'iya ya ce"ai sai muyi gaggawar isa kafin su karaso,sallamar jagwal su kayi sannan suka wuce a motar sirri wadda suke irin wannan fitar da Ita.
RAIHAN....
Tana gama gabatar da shirinta na siyasarmu a yau,ta fito daga dakin daukar labarai, tana dan fitar da numfashin gajiya,duba lokaci ta yi wanda hakan ya yi daidai da wata irin mummunan faduwa da gabanta ya yi,dafe kanta da ya shiga sarawa ta yi kirjin ta na wani irin sama da kasa,kawai sai ta samu kanta da fasa shiga office ɗin,take wani tunani ya zo mata wanda sam babu shi a schedules din ta na yau,cikin sauri ta juya ta fita daga reseption din,daga nan tabi wata hanya ta bar cikin gidan rediyon.
A.WAZIR.....
Tun shigar sa office din yake jiran yaga ko zata shigo,amma shuru har lokacin break and prayer ya yi, cikin nutsuwarsa ya fito daga office ya hau lifter dan ragewa kan shi wahalar sauka, ta bangaren su RAIHAN yabi ,a daidai lokacin da su salim suka fito dan zuwa Sallah,gaisuwar Barka da rana suka mika,kafin su wuce,bin su ya yi da kallo miskilanci ya hana shi tambayar ina Rahim yake,fita ya yi kawai ba tare da ya samu ya fitar da abin da ke ranshi ba.
RAIHAN.....
Nafef ta samu ta hau, ta kuma yi kokarin samarwa kanta nutsuwa duk da yadda take ji kirjinta na duka da wani irin ƙarfi kamar zai hudo kirjinta ya fito,kasancewar wajen garine,wato hanyar barin gari yasa su ka yi tafiya ta kusan awa ɗaya,mika masa kudin sa ta yi tana mai duban hanyar da tunanin ta inda zata fara,sai da taga ƙulewar me nafef din sannan ta yi addu'a tare da bin hanyar da halima ta kwatanta mata,cikin bugun zuciyarta da ya zarta bugun da ake bukata ya yi, sosai take kurɗawa cikin ciyayi tana Daɗa nazarin hanyar dan kar taje ta kauce hanyar.
.......
Shugaban jam'iya ne ya duba agogon da ke daure a tsintsiyar hannun shi,tare da sakin tsaki,ya ce"wlh ba daban karmu kuskure wajen ba da sai mu tafi haba tun tsawon awa daya muke jira amma sunki karasowa,da anyi magana sai su ce hodldop ya tare su,Dr ya ce" muyi hakuri dai mu jira da hakuri da rashin sa takin ƙalilan ne".
Gaban ta ne ya kara faduwa saboda hango mota da tayi gaban wani kyakkyawan gida me matsakaicin girma,idan tunanin ta ya bata dai dai ke nan wannan ne gidan da mutanen suke kuma nan ne inda halima ta zo,da sauri ta kuma samun maboya ba tare da tsayawa wani tunani ba ta cigaba da bin kwatancen halima.
A daidai wannan lokaci kuma su tk suka karaso, kuma ba tare da bata lokaci ba ,suka wuce gaba dayan su dan dauko camarar da suke da tabbacin cewa har yanzu tana nan a wajen.
______________
A wazir yana dawowa daga masallaci maimakon ya bi ta lifter ya wuce office din sa,sai kawai ya kuma biyawa ta wajen office din staff,a nan ya dan yi dube duben sa kamar irin yana duba aiyuka ne,nan kuwa so yake kawai yaga ta inda Raihan zata ɓullo,sai dai haka ta gama bin gurin da kallo baiga ko mai kama da ita ba,fita ya yi duk ranshi da zuciyar shi babu dadi,sai dai kuma babu mai gane hakan.
Yana shiga office ya wuce toilet ya zubawa kanshi zuwa fuskar shi ruwa,haka nan yake ji kamar ba lafiya ba,duk inda Rahim yake baya cikin nutsuwar zuciya,saboda yadda yake jin tashi zuciyar na tsanani akan tashin hankalin rashin ganin nata,rufe idanun shi yayi yana jan hazbunallahu wani Imal wakil,fitowa ya yi tare da ɗaukar wayar shi ya shiga dealing nomber ta.
RAIHAN,,,,,,,,,,
Ta so ta samu matsala gurin gane ainahin gurin da halima ta binne camarar ,sai dai kuma cikin karfin addu'ar da ta rike a bakinta da kuma kyakkyawan niyar ta,tasa taga gurin ,cikin ƙanƙanin lokaci ta fito da dan karfen da ta zo da shi ta fara tone ramin,jin takun tafiya tayi harma da yan surutai daga dan nesa da inda take,gaban ta ne ya sake faduwa , addu'a da ta janyo ne ya bata karfin gwiwa wajen ci gaba da tone ramin.
Su kuma tk da su shugaban jam'iya suna daf da karasowa wajen ne ƙaya ta soke Dr ta kasan takalmin shi wanda har ya faso cikin tafin kafar shi,suna kokarin dakatawa ya ce da su,maza ku wuce ku bari na biyo ku idan na cire" haka ne yasa suka ci gaba da tafiya.
Jin karfin takun na ƙaruwa da kuma maganganun da take iya jiyo abin da suke fada yanzu yasa hankalin ta mummunan ta shi,ya akayi suka san camarar nan tana nan,me yasa sai yau suka zo dubawa? Ko dama sunyi mata tarko ne? Ji ta yi numfashinta na neman daukewa lokacin da ta hango wani garjejan basamude,ai kuwa da wani irin speed ta finciko camarar da dama ta zo gab da fitowa, saidai lokacin kuma su tk da shugaban jam'iyyar da sauran yaran sa suka bayyana a wajen,daji ne wanda yake da gonannaki tare da yalwar ciyayi hakan ne ya bawa Raihan damar ɓuya, wanda da har tayi tsammanin sun ganta saboda kusancin dake tsakanin su da kuma tazarar matsawarta daga gurin zuwa bayyanar su.
A hankali suka fara bin gurin da kallo saboda son gano inda alamar da halima ta ajiye take,karaf kuwa tk ya gano gurin sai dai kuma abin da ya tsananta mamaki a gare su shine yadda suka.ga an tone gurin,da sauri suka karasa dukan su tare da yi wa wajen rumfa, cikin mamaki shugaban jam'iya ya ce" kuna nufin nan ne gurin??
Tabbas nan ne gurin cewar tk da sauran yaransa,to ai gashi alama ya nuna cewa an dauke camarar"shuru su kayi gaba dayan su suna mai zubawa gurin ido tare da nazarin wani abu,shugaba ne ya fara magana cikin tashin hankali ya ce" tabbas wajen nan yanzun nan aka gama tone shi dan alamu ya nuna hakan,ke nan duk wanda ya tone yana cikin jejin nan bai kai ga fita ba",tabbas oga maganar ka haka yake cewar duguja,da ya fara baza jajayen idanun shi kamar zai hango wanda ya tone ramin ya dauke camarar.
Cikin daga sauyi na alamun tunzura da tashin hankali shugaban jam'iya ya ce"maza ku zagaye dajin nan ku nemo min yaron nan duk inda ya shiga ku kawo min shi da ransa",kafin kiftawar ido tuni sun raba kansu zuwa loko da sako na cikin jejin dan cika umarnin ubangidan su.
Daidai inda Raihan ta buya a cikin ciyayi a nan shugaban jam'iya ya tsaya yana huci tare da baza ido ko Allah zai sa ya yi ido hudu da yaron nan.
Kirjin Raihan babu abin da yake sai bugu saboda tsananin tsoratar da ta yi ,a inda take ko kwakkwan motsi ta yi zai iya jiyota,shi yasa ta kuma takure kanta da zuciyarta dake cikin wani irin razani,kara ƙanƙame yar karamar camarar ta yi tana ci gaba da karanto addu'a'in neman tsari,wayar ta dake makale a hannun ta ce ta fara bada sautin baburashin wanda hakan ya jawo hankalin shugaban jam'iya,zaro manyan idanun ta tayi tana mai toshe bakin ta da kukan tashin hankali ke son kufce mata,
Allah Rahimi Maji rokon bayin sa wandanda suka dogara da shi akan shine kadai zai taimake su,juyowar da shugaban jam'iyya zaiyi maimakon yayi ido hudu da Raihan dake bayan shi,sai kawai yayi ido hudu da wani katon maciji ya kanannaɗe jikinsa tare da fasa kai,ihu shugaban jam'iya ya yi tare da yin baya,wanda hakan ya razana Raihan ta yi tunanin ganin ta yayi,sai kuma Allah ya bata kwarin gwiwar kasa motsawa daga gurin,dan tabbas da ta fidda razanar ta a fili da sai sun ganta,sai kawai mcijin nan ya fara silalowa wanda sai lokacin Raihan ta kula da shi,kara fiddo manyan idanunta tayi tare da dauke numfashi dan ta riga ta gama saddakarwa micijin nan gurin ta ya nufo ,shike nan ta kawo kanta inda ko ta mutu ba za a ga gawaarta ba, innalillahiwa'inna ilaihi raji'un ta shiga maimaitawa tare da ambaton kalmar shahada.
A can bangaren A Wazir kuwa mamaki ne da tashin hankali ya kuma yi masa ruftu ganin yana ta kiran Raihan amma bata daga ba,to me ya ke faruwa? Ya tambayi kanshi da dan yin nazarin wasu sakanni,key din motar shi ya dauka ya fito cikin nutsuwa ,baza ka taba gane halin da yake ciki ba,saboda tsananin kamewar sa da nutsuwa,kai tsaye wajen motar ya nufa ya shiga tare da kunna ta ya nufi hanyar barin gidan ,ba tare da yasan inda zai nufa ba........
Rintse idanun ta tayi tana jiran taji daga inda zai bata sara,amma ga mamakin ta sai taji shuuu alamun wucewar sa ta gefan ta har sai da ya dan goge ta,bude idanun ta yi da sauri sai kawai taga ya nufi wajen su shugaban jam'iya kai tsaye yana wani irin huci me tsananin zafi,ganin haka yasa Raihan samun kwarin gwiwa dan haka ta yi saurin silalawa ba tare da sun ganta ba,tabi ta cikin ciyayi ta fita da gudu bayan ta danyi nesa da su.
Tk ne ya saita bindiga zai harbi macijin sai kawai su ka ga ya yi wata girgiza yayo kansu,ai basu san lokacin da suka cika wandunan su da iska ba,hatta da Dr da ya gama cire kaya ya biyo bayan su yana dingishi bai san ya akayi ya mike kafar ya ranta a na kare ba.
Raihan kuwa cikin nishin wahala ta fito bakin titi,cikin ikon Allah ta samu nafef ta shige,tana mai da numfashin wahala.
Yana sauke ta a kofar gidan su,ta hango motar A wazir a wajen da alama ya dan ja wasu mintina da zuwa,kokarin saita kanta take yi ta hanyar kimtsa kanta daga hargitsewar da ta yi.
Zuba mata ido ya yi lokacin da ya karasa inda yake tsaye hannuwan shi a harɗe a kirjin shi,kallo yake mata ciki da bai na san gano abin da take son boye Masan,sunkuyar da kanta ta yi cikin sanyin da gaɓobin ta suka fara yi na kallon da yake mata,
Ina kika je??
Ya tambaye ta cikin cunkushewar murya wadda take nuni da bacin ransa da ba a cika ganewa ba,shuru ta yi saboda tasan ko ta yi masa karya sai ya gano ta,hasali ma bata iya yi masa karyar,kayi hakuri kawai ta iya fada cikin marairaice fuska kamar zata yi kuka,kawar da kanshi ya yi saboda baya san yanayin nata ya sauya shi,wayyo Hamma wazir cikina ya murda bari na shiga ciki",tana gama fadar haka ta juya da dan gudun ta ,buga kofar ta shiga yi da sauri har sai da basamuden me gadin su ya bar abin da yake ya zo ya bude mata kofa,bata saurari komai ba ta Wada gidan da gudu,duk securityn da ke tsaye kamar sojoji da wadan da suke zirga zirga a gidan sai da suka bita da kallo.
Numfashi ya dan furzar yana mai kara lumshe lumsassun idanunsa,yana kuma jin zuciyar sa na daidatuwa da samun nutsuwa na tabbacin lafiyar Raihan,sai dai kuma yasan akwai abinda take ɓoye masa,wani dan murmushi ne ya kufce masa wanda rabon da yayi shi tun ranar da suka je gidan gwamnati,dama ita ka dai ce ke samun murmushin nasa lokaci zuwa lokaci, to ita ma din yanzu Murmushin ya gagareta,ba komai ne ya sa shi murmushi ba sai tunanin wayon da Raihan din ta yi masa,shafa tattausan sumar kan shi ya yi kafin kuma ya shige motar tare da barin layin.
_________________
Amma wannan yaro kwai tantiri,tabbas wannan abin da ya faru ya nuna min cewa zamu yi gumurzu da yaron nan,domin kuwa shu'umi ne,cewar shugaban jam'iya da hankalin sa yake matukar ta she,Alh sale da zuwan shi ke nan, ya ce" Ni ba komai ne yake matukar bani mamaki da tsoratani ba akan yaron ba,sai tunanin yadda akayi yasan zamu nemi camarar nan a yau,ta yaya ya sani bayan gargadin da marigayiya ta yi masa akan kar ya tunkari wajen nan a yanzu???
Dr ya ce" Nima abin da yake sakani a ruɗani ke nan,da kuma tunanin anya ba shi ya turo mana macijin nan ba,saboda Ni macijin nan ya bani mamaki dan se nake ga kamar ma ba maciji ba", shuru su kayi gaba dayan su kowa yana tunanin mafita.
Can Alh sale ya numfasa tare da cewa,duk wannan ba shi ne me muhimmanci ba,yanzu kawai tunanin yadda zamu karbi camarar nan a hannun sa kafin ya tona mana asiri,saboda ko mun kama shi idan har ya saki video nan babu amfani dan wlh nasan hukuma sai ta kama mu", Dr ya ce" bayan kama mu da zata yi bamu da mafita akan dukkan aiyukan da ake aikatawa na lefi a garin nan,kai tsaye mu za a ce ba tare da wani dogon bincike ba", shugaban jam'iya ya mike yana Safa da marwa a tankameman falon nasa na gidan tattaunawar su ta sirri,
Lallai idan ba mu yi da gaske ba to tabbas akwai babbar matsala,na baku daga nan zuwa gobe kowa ya yi tunanin abin da ya dace.......✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page16 ```
A bangarensu ta tarar da Hamma Idris, ɗan hararar ta yayi tare da cewa ba nace idan zaka taho ka kirani naje na dauke ka ba?"dan dafe kanta ta yi cikin nuna alamun mantuwa ta ce"ayya Hamma wlh shaf na sha afa dake ma Hamma wazirrrrrr ne ya taho dani yanzun nan ya wuce"ta faɗa tana wucewa dakinta tare da yin istigfar akan karyar da tayiwa yayan nata,ok shike nan ba damuwa,dama so nayi na dinga kaika ina dawowa da kai kafin zuwa Monday na fara zuwa office kamar yadda Abbie ya ce"ok Hamma ba damuwa ta faɗa tana karasa shigewa dakin dan adana sirrinta.
Chibaɗo's hause....
Bai shiga gidan ba sai da ya tsaya su kayi sallar magriba tare da kawunsa Abban rabi da Abbu,kasancewar kullum dama anan gidan yake sallahr magriba tun da wutowa yake daga office,kuma ka idar su ce sai sunzo gaida mahaifiyar su,
Abban rabi yanzu ya dawo Abuja tun wata daya da suka wuce,saboda matsala da ya samu a wajen aikin sa,dan haka ɗan uwanshi ya ce"ya dawo Abujan ya cigaba da kula da kamfanin fulawar sa dake nan Abujan,tun farko dama yaso ɗan uwannashi ya rike ragamar wasu kamfanonin nasa tun da shi Abbu din yafi ga gidan rediyonsa,to amma sai Abban rabin ya nuna masa Gara dai shima yaje ya danyi aiki da takardunsa da kuma basirar sa,to gashi