Showing 105001 words to 108000 words out of 189984 words
Chapter 36 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
Rahim ba namiji ba ne,domin tunda har kowa ye yasan da wannan tsohon sirrin to ba zai kasa sanin wannan ba,damuwata kar wani abu ya samu Raihan.
Da sauri tayi ƙasa da kanta tana kuma shigewa cikin fulawas din da suke bayan falon ta inda karamin window dake falon yake,babu abinda kake gani a fuskarta saboda yadda ta nannade fuskar da farin rawani tamkar wani buzu,abinda kawai zaisa ka fahimci cewa macece shine shigar jikinta ta doguwar a baya.
Ur exsellency ya ce", kamar motsi nake ji a ta wajen can ko? Ya fada yana duban Abbie,dan zubawa window wajen ido su kayi gaba daya kafin su tashi ba tare da sun kara cewa komai ba.
Shirun da ta ji ne yasa ta bar wajen cikin takatsantsan.
Abbie suna fitowa falon babu kowa sai Hajiya goggo,cike da mamaki Abbie yake kallonta saboda yasan bata cika shigowa bangaren surukanta ba sai dai su suje can din,Hajiya tun yaushe kikazo kuma ke kadai ba na ramlar?a'a Ni ba wajen ramla nazo ba wajen hajiyar agadex nazo hira tunda jiddo dai iyayenta sun rike abarsu",durkusawa ur exsellency yayi yana gaidata,amsawa ta yi tana kallonshi cikin mamaki au wai dama kaine? Ikon Allah wannan irin badda kama haka", Abbie ya ce", to Hajiya aikin san su manya dole sai da irin haka", to wannan wane irin zuwa ne da sai am boye kama? Da sauri Abbie ya kuma tare ta da cewa Hajiya saboda abinda ya faru ne to kinsan yan jaridar nan yadda suke ta son su yi magana da mu", tabe baki ta yi tana binsu da wani kallo kana ta kuma cewa to idan kun san kuna da gaskiya meye na tsoran maganar ? Bari na raka shi saboda ba a san ya fito ba, Abbie ya fada yana takaicin baranbaramar hajiyar tasa.
Ur exsellency ya ce",Nura za mu samu lokaci muyi tunanin abinda ya kamata da kuma wajen da ya kamata mu hadu ban yadda da gidannan naka ba sam............✍🏽
[12/21, 12:40] : *Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page37 ```
Tunda ta baro bakin window take faman zirga zirga ji take kamar zuciyarta zata fashe tunani ya cunkushe kanta,mafita kawai take nema,shin yaya za ta yi ta samu hanyar shiga jikin ur exsellency? Me ya kamata ta yi a wannan bigiren? Waye ya ke da karfin zarrar da zai iya shiga ahlin ur exsellency ya kwaso mata wannan Dukiyar?gaskiya amma Nura ya shammace su,dama ashe wannan campanin da ya bawa yaaran gidannan na auduga su kula da shi ashe ba su ka dai ba ne? Wato yayi hakanne domin ya kawar da kan kowa daga dukiyar Raihan da tunanin yawanta.turkashi lallai jan aiki ne a gabanta domin kuwa tasha alwashin karar da kowa akan wannan burinnata,domin shine asalin abinda ya kawota gidan, wannan burinne yake zaune da ita a gidan,dan haka dole ta samu mafita tun kafin wani yayi mata kutse cikin lamarinta.
CHIBAƊO FM.....
Cikin yanayin damuwar da take ciki ta shiga office ɗin,idanuta sun iankance kana ganinta kasan cewa tana cikin yanayi mara dad'i.
Zuba mata tsumammun idanunsa ya yi ,tuni jikinta ya kuma yin sanyi,sai kawai ta kuma rushewa da wani irin sassanyan kuka wanda shi kansa kukan wani irin salo yake bayarwa tamkar ana busa sarewa,a hankali ya maida idanunsa ya lumshe tare da komawa saman kujerar ya kuma kwantar da kansa yana jin wani iri a cikin jinin jikinsa,jin kukannata yake kamar har cikin bargonsa,tsikar jikinsa ce take wani mimmiƙewa kamar wanda ake sosa masa,tashi yayi cikin wannan kamewartasa da wani taku tamkar a saman gajimare,fuskarshi babu murmushi ko daya sai wannan yanayinnasa na ko da yaushe.
Kanta yana sunkuye bata san lokacin da ya ƙaraso ba sai dai jin tattusan hannunsa ta yi saman wuyanta yana ƙoƙarin dago kanta,saurin dago kannata ta yi tana kallonshi ƙasa ƙasa ba tare da ta bari idanunsu sun haɗu ba,cikin kimtsatstsiyar Muryarshi me dan kauri da sanyin sauti ya ce"me ke damunki?rumtse idanuta tayi sai ga wasu ƙwallan suna rige_rigen sauka saman kuncinta, kwaɓe fuska ta yi tana shirin fasa kukan,kafin ta kai ga yin haka sai jin wani irin sanyi da ƙamshi tare da zaƙi tayi cikin bakinta wanda hakan yasa babu shiri tayiwa kukannata wata irin haɗiya ya koma cikinta tare da hadewa da harshen WAZER,a hankali ya sake tallafo kanta camly kamar wanda ke taba ƙwan da baya son fashewarsa,cikin kwarewarsa da a jinsa wanda yake a jininsa ya shiga bin labbanta da harshenta yana tsotsewa ba tare da shi kansa yasan yadda hakan yake faruwa ba,shi dai abu daya ya sani indai RAIHAN na kusa bai cika gane kansa ba,ta fuskane kawai zaka iya cewa kalau yake amma can kasan zuciyarshi da gangar jikinshi basa iya gane komai indai RAIHAN na kusa,tamkar mayen karfe haka yake jinta a duk lokacin da ta fara kusanto shi,shi yasa baya iya sarrafa kansa da duk wani ajinsa.
RAIHAN kuwa jin kanta take tamkar a sararin samaniya,dama can ita bata da zarrar sarrafa kanta a gaban WAZER, ƙwaƙwalwarta bata gane komai sai ƙamshinsa bata fahimtar komai sai kalamansa bata ganin komai sai kyakkyawar fuskarsa me dauke da 'yar ƙasumbar da ke ƙara masa kyau da kwarjini.
Numfashinta ne taji yana sama_sama saboda yadda ta ji wazer yana ƙoƙarin sauya salon wasan nasa,cikin fitar hayyaci ta rike hannunsa da yake kokarin fara zagawa dashi cikin jikita,da kyar ta yi kokarin zare bakinta dake cikinnasa yana masa wata irin sarrafawa,cikin karkarwar baki ta ce", Hamma WAZEER",
Wani irin shock ne ya kama shi saboda yadda taja sunan a saman harshenta,a maimakon ya sake ta kamar yadda yaso,sai kawai taji sabanin haka dan cusa kansa ya shiga yi cikin wuyanta yana sunsuno daddan kamshin humrarta wanda ta kama jikinta,camly yake sumbatar wuyan yana dada cusa fuskarsa kamar zai hadeta a cikinsa.
Ganin yadda yake dinne kamar wanda ya fita a gayyacinsa yasa ta fashewa da wani irin kuka tana yi tana kame jikinta tare da dan tuttureshi da fuskarta dake saman kanshi,a hankali ya dago kanshi ya kuma mike sosai sabanin da da ya sunkuya saboda tsayin da ya dara mata da shi sosai.rungumeta yayi yana furzar da wani irin huci me sanyi,kana cikin nutsuwarshi da kamewarshi ya ce",umm zaki iya fadin damuwarki ko sai na maimaita? Tura karamin bakinta ta yi sannan cikin tsoran abinda zai kuma yi din ta ce", ba Abbie ne yake fushi da Ni ba saboda abinda ya faru jiya", dan waro ma daidaitan idanunsa masu haske ya yi kana ya ce", shine ya fada miki haka?girgiza kanta dake ƙirjinshi tayi tana matso kwallar shagwaɓa,dan lakuce mata goshi yayi fuskarshi kadaran kadaran kana ya ce", sorry Abbie baya fushi dake damuwarsa akan yadda aka tozarta amininshi ne a idanun duya so kar ki damu uhmm", ya karasa fada yana wani dage mata gira in a emotional way,rufe idanunta ta kuma ta ɗan sakin ajiyar zuciya alamun dai ta samu nutsuwa.
Janyeta yayi daga jikinshi tare da komawa wajen zamanshi yana cewa ki gyara fuskarki ki wuce ki fara aiki", daga haka ya dora dogayen hannayen shi masu cike da kwantacciyar gargasa saman computer shi yana ci gaba da aikinsa.ba tare da tace komai ba ta wuce bathroom dinshi ta wanko fuskarta,fita ta yi ba tare da ta sake masa wata maganaba,dan kuwa sosai itama take koyarshi wajen kamewa da basar da abu ko da ya kula da abun,kasa_kasa ya bita da wannan shu'umin kallonnasa da take jinsa har bargonta.
RUBY.......
Tunda ta gama shirin fita office ta zauna zaman jiran sury,kasancewar tana farkawar ita ce mutum ta farko da ta fara kira tana nema,sai dai kuma gashi sai ja mata rai take tunda gashi tsawon awa daya da rabi da kiran amma har yanzu bata karasoba.
Ita kuwa sury tana can wajen oganta yana shirya mata kalaman da zata yi amfani da su wajen kara cusawa ruby hauka a kan Raihan ta yadda zata yi saurin amsar aikinsu a matsayin shawara a gareta,saida suka gama kulle kullensu sannan suka rabu.
Kai tsaye CHIBAƊO family ta nufa.yayin da shi kuma ogan ta barshi cikin jinyar zuciya da neman mafita akan yadda za ai ya kutsa rayuwar ur exsellency dan cikake babban burinsa.
Da sauri ruby ta rungume sury bayan ta zuge mata kofar glass din da tayiwa rabin bangan kawanya.
Haba sury me yasa zaki min haka? Tun yaushe na kira ki amma dake kinso jamin rai baki ƙaraso ba sai yanzu bayan kuma kinsan zan fita office ",tabe baki sury ta yi tana yin gaba zuwa cikin falon ta ce", to me kike so dani? Duk ma ba wannan ba yanzu ba gani nazo ba dan haka sai ki saurara min da wannan shegen mitartaki,ta karasa fada tana zama daya daga cikin manyan kujerun da suka kara ƙawata falon kamar wani fadar shugaban kasa.
A can cikin gidan CHIBADO family kuwa,Abbu ne zaune gefan innawuro fuskarshi a cunkushe da alama dai akwai wani babban lamari da ya Kunno masa, cikin damuwa innawuro ta ce", yanzu dan nan ma aikatan nan abinda suka shirya ke nan? Me yasa mutane basu da amana ne, wanda kayarda dashi ka bashi amana shine yake cutarwa ? Girgiza kai Abbu ya yi yana cewa a'a innawuro ba kowa ne ba akwai masu gaskiya da amana kawai dai sunyi karanci ne mahainta sunfi yawa,wallahi innawuro ban taba tsammanin za a hada baki da ma'aikatana a cuce Ni ba amma sai gashi lokaci daya hakan ta faru,ban san da me ragesu ba duk wani hakki nasu ina cikawa to amma me zaisa su yi mana haka eye? Ya fada duban innawuro da ta yi zukudi cike da tunanin ta inda matsalar ta ɓullo.
Yaci gaba da cewa ki duba ki gani wannan kwangilar da zamu karba yadda akayi kutu_kutu aka toshe aka hana abani ga kuma yawan asarar da nake tararwa a Company's,idan kuma na tara su sai kowa yaci laya kwanaki har bincike nasa aka fara min amma babu wani abu da zai sa na zargi wani da aka samo to yanzu kuma gashi an samu wani mugun da ga cikin makiyanmu ya siye rabin shares din da muke dasu , saboda duk kudin da muka saka sai an samu wani daga sama ya kara ba tare da nasan waye ba", shigowar abban rabi yasa ya dan dakata daga maganganunshi da yake wanda suke nuna zallar ɓacin ransa.zama abban rabi ya yi yana duban dan uwannashi cikin tausayawa yace", yaya dan Allah kayi hakuri karfa ka manta cewa shares din mu na kafanin da nake riko yana nan bai kuma babu wanda ya janye nasa to dan wancan sun janye nasu wani kuma ya siya ai ina ga ba sai ka daga hankalinka ba,kuma fa duk wannan din ba zai taba komai daga cikin irin arzikin da Allah ya baka ba,kayi hakuri na tura mutanena cikin ma'aikatar domin su sa mana ido sosai ",
Dan numfasawa innawuro ta yi sannan cikin lallashin ɗannata ta ce", Ni gani nake kawai ka dawo da Nasiru da Khalil su cigaba da rike Company's din tunda sati mai zuwa zasu dawo, idan da hali ma rumana ma ta fito ta fara aiki duk ka raba su tunda abin ya zama haka dole idan suna nan wata rana asirin masu yi zai tonu", Masha Allah Abbu ya fada cikin farin cikin shawarar da mahaifiyarsa ta kawo,ya ci gaba da cewa tabbas innawuro kin kawo shawara kuma mafita me kyau kai wallahi dole wanda bai da uwa yayi kuka, ina ganin ma ai har mijin rumanan ya dawo tunda dama a karkashin wancan Company na Alh sale yake hakan sai yafi samun kwanciyar hankali suna tare da matarshi",
Abban rabi ya ce", tabbas wannan shawara ta yi Nima ina goyan baya,kaga an raba ke nan rabi da wazeer suna rike da gidajen media su kuma sauran suna rike da Company's hakan yayi Allah ya kara dora mu akan maƙiya,Amin ya Allah innawuro da Abbu suka fada a tare, innawuro ta ce", kaga sai su dawo a daidai ke nan,wallahi Ni duk na manta banyi wannan tunanin ba ko dan basa kusa da mu ne oho? Abban rabi ya ce", ai gashi yanzu innarmu ta tuna mana hakan ko? Ya fada yana dariya sosai suka ci gaba da taba hira cikin kwanciyar hankali da kaunar junansu.
A can wajen rabi a da sury kuwa,rabi a ce ta dubi sury ta ce,to shike nan naji amma dan Allah kiyi hakuri wallahi na kagu naji me ke bakinki
jiya ko baccin kirki ban samu ba saboda tunanin abinda zaki fadan", to zauna mana ko daga tsaye za kiji ko ma meye? Zama rabi tayi jikinta har rawa yake a kage take matuka da son jin abinda ke bakin sury.
Zuba mata ido suryy ta yi kafin ta ce", ina kwalaben maganin da na baki jiya? Da sauri rabi ta bude jakarta ta dauko su tare da mika mata. A'a Ni ba karba zanyi ba ki rikesu a hannunki ina gama baki labarin zaki sha idan ba haka ba kuwa zaki iya haukacewa", tuni rabi a ta kuma rikicewa cikin rawar baki ta ce", sury ina hadaki da girman Allah ki fada min domin kuwa wannan surutannaki ma kadai sun isa haukatani dan haka ki gaggawa ki sanar dani",kadan sury ta tabe baki kana kuma ta fara magana da cewa", rabi ki nutsu kar ki yi min hauka bana bukatar bakinki anan har sai na kai aya ", ita dai rabi a ba ta ce komai ba saboda idan ta bude baki ashar kawai zata dannawa sury tana yin hakan kuma tasan ta yiwa kanta sury bazata saurareta bare ta sanar da ita labarin",, ganin yadda ruby ta yi yasa suryy ta tabbatar da cewa tarkonta ya gama ɗanuwa dan haka sai ta gyara zamanta tare da yin gyaran murya.
Rabi koyi hakuri na gama duk wani bincike da sanyi akan zuciyar wazer akan wadda ta hanaki shiga zuciyarsa,tabbas da ace bata shiga ransa ba to kuwa ina mai tabbatar miki da cewa WAZEER sai ya soki tunda ke yar uwarsa ce kuma mace,ba dan ta tsare wajen ba to dabararki zata iya kwato miki zuciyar wazer. Cikin tashin hankali ruby ta bude baki zata yi magana, da sauri suryy ta dakatar da ita tana cewa ba haka mu kayi dake ba dole ki dakata na gama kafin ki yi magana", mukut ruby ta haɗiye wani kakkauran miyau me daci ta yi shiru tare da ci gaba da kallon sury idanunta kamar zasu fito waje.
Suryy ta ci gaba da cewa, nadan tambayar da kike son yi min wacece shine abinda kike son tambayata, dan haka na hutashshe dake zan baki amsa,nasan kinsan waye RAHIM,to RAHIM shine ya shiga zuciyar wazer yayi kane kane saboda shi din ba namiji ba ne macece, RAHIM dai ƁOYAYYIYAR RAIHAN ce ,ai Nahin sunanta RAIHAN,kai tsaye tashiga bata labarin dalilin maida Raihan namiji duk da cewa ba komai ta sani ba kamar yadda ogan nata bai san ainahin dalilin da yasa aka boye Raihan dinba,kawai dai yai hasashe ne bai san cewa kasheta aka so yi tun tana jaririya ba.
Iya labarin kawai ya umarceta ta sanar da ruby banda aikin da zata yi musu akan fallasa Raihan ɗin.
Wata irin ƙara ruby ta saka sai kawai sury ta ganta kasa yashe babu alamun numfashi........✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page38 ```
Da gudu sury ta yi kanta tana jijjigata cikin tashin hankali, wayyo Allah nayi kisa shike nan tawa ta kare ba tare da na cika burina na zama matar WAZEER ba", abinda take fada ke nan wanda kuma haka yake har zuciiyarta, sai da ta dauki kusan mintina goma tana neman mafita kafin tunanin zubawa ruby ruwa ya zo mata,da gudu ta tashi ta nufi kiching gorar ruwa me sanyi ta zundumo a prige,tana zuwa bata yi wata_wata ba ta sheka mata a fuskarta,a matukar firgice ruby ta farka bakinta ɗauke da sambatun mafarkin da take tunanin ta yi.
Allah na gode maka da ka tasheni daga wannan mummunan mafarki, ya Allah ina rokonka kar kasa na kuma maimaita ko makamancinsa ne", girgizata sury tayi tana cewa dalla Malama tashi ba mafarki kike ba duk abinda kika ji gaskiya kika ji,kawai ki tashi kiwartsake mu nemo mafita dan wannan haukar ba zata fishsheki ba, ware idanunta tayi sosai kan fuskar sury ba komai take kallo ba sai bakin sury domin ta tabbatar daga bakinta maganar ke fitowa, sai kuma ta yi wata irin zabura ta cukeme sury cikin kumar baki da masifar dake azalzalar zuciiyarta ta ce", karya kike haka bazata taba faruwa ba,ko da ace dau hakurin kallon wata da wazeer to wallahi ba zan taba iyawa da wancan dan iskan yaron da kike cewa mace ne ba,raiha yake ko Raihan ko ma meye bazan taba dauka ba wallahi sai naga bayanta sai na halakata,inaaaaa bazai taba yiwuwaba,tuni ta fara birkita falon duk abinda yazo hannunta wurgi kawai take da shi,ta haɗa uwar zufa kamar wadda tayi tafiyar shekara cikin sahara,dakyar sury ta samu ta riketa,bata yi wata wata ba ta antaya mata magungunan da ta kawo mata jiya ta haɗa mata har da kwaya,cikin kankanin lokaci ruby ta lafke jikinta ya sake abinka da farin shiga,duk da haka dai bakinta bai yi shiru ba,a haka Surry ta samu ta kimtsa ɓannar da tayi ta gyara komai kamar wani abu bai faru ba,bayan ta gama ta dawo inda ruby take tana ta sambatun hauka dan kuwa tuni ta hau kan layi jinta take a can wata duniya,kai hatta da kanta Ruby ta manta,da kyar ta samu ta dagata kamata ta yi ta nufi dakinta da ita,watsar da ita tayi saman gadonta tana sakin wata shu'umar dariya,harde hannunta tayi tana