Showing 129001 words to 132000 words out of 189984 words

Chapter 44 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15639

ta yi cikin jikinshi ya tarairayo fuskarta cikin tafukan hannayenshi,kana a hankali ya ce", kalli nan ki gani",yana nufin idanunshi,dago idan yin ta yi dan ganin abinda yake nuna matan,a maimakon taga wani abu daban sai kawai tsintar idanunta cikin nashi ta yi ,take tafa marmar da kwayar idanunta tana son kufcewa rikon da yayi wa kwayar idonnata,ɗan murmushin gefan baki ne ya kufce masa kana ya kuma cewa", trues me my angel", tsintar kanta kawai ta yi da jinjina mishi kai domin zuciyarta ta ki bata damar kin yadda da wazer sosai take ji a ranta ba zai taba yin abinda aka ce ya yin ba,a hankali ta sauke kanta tare da cusa fuskarta cikin faffadan ƙirjinshi tana sauke ajiyar zuciya,shima ɗin numfashi ya furzar tare da kara kalmasheta suna shaƙar numfashin juna.




__________




Cikin kankanin lokaci labaran nan guda biyu suka fara baza gari labarin Rahim Raihan da kuma kamun da aka yiwa his excellency dumu_dumu yana son kashe amininshi dan kawai ya gaje dukiyar da ya bashi amana.


Sosai labarin ɓoyayyiyar Raihan ya bigi zuciyar mutane,a maimakon wannan ya zama abin tozarci gareta da ahlinta sai ya zama labarin da ya kara haskaka tauraronta,abin mamaki sam babu wanda ya dauki manufar da aka rubuta da wani abu daban kamar yadda ruby ta so,hasalima labarin his excellency shine ya danne na RAIHAN saboda yadda mutane suka jima suna fatan Allah ya bayyana musu wanda yake kashe musu yaya da mata.




Abbie kuwa za mu iya cewa an samu nasarar kashe gubar da ya ci saboda bata riga ta yi aikin da zata iya kasheshi ba,sai dai fa yana cikin mummunan yanayi,an sa masa abin shaƙar numfashi yana kwance tamkar gawa,sai dai ayi fatan farfadowarsa cikin lokaci.




A yanzu duka ahlinshi sun san komai saboda abune da ya haɗa da social media,dan aunty Amarya da hajiyar agadex ma tuni suka baro gidan RAIHAN ce kawai basu bari ta sani ba,saboda halin da take ciki,dakyar aunty Amarya suka ya kicewa tambayoyin yan jarida.




Mama murja duk da halin damuwar rashin danta da take ciki ba karamin shock ta shiga ba lokacin da wannan labarin na RAIHAN ya risketa ,haka momy Hanne ma, sai dai a wannan gabar basu da abincewa.




Tunda suka isa asibitin suka zauna a reseption mama murja take kallon Aunty Amarya,mamakin yadda yarinya kamarta ta iya juya tunaninsu take yi,kuma ita akarankanta tasan ramla ta yi haka ne saboda tsoran kar su cutatawa yarta,lallai Allah mai kudurane,gashi dai duk fadi tashin da suke na kar a samu RAIHAN a zuriyar Muhammad nur sai da Allah ya yi ikonsa,kuma dan yana son tarayu domin izna a garesu ne ya bawa Aunty Amarya basirar badda ita cikin jinsin mata,dake kuma shidin shine me yadda yaso sai yaso zamanta a hakan ba tare da asirinta ya tonuba har sai da yaso hakan lokacin da RAIHAN takai munzalin girma zata kuma iya kare kanta a duk inda ta shiga,kuma yasa igiyar aure tsakaninta da jajurtacce kuma kamilallan mijin da zai iya tsayawa ya kareta a ko ina,take mama murja taji wani tsoran Allah nashirgarta baranma da ta kuma yin nazari kan yadda ta rasa danta,wanda ta yi tsai da ranta ta tabbatar da cewa isharace Allah ya yi mata,lallai ta tabbata cewa akwai wata hikima ta Ubangiji a yin hakan,sai kuma tunaninta ta juya kan his excellency da abinda ya yiwa mujinnasu,sai kuma taga da ace yasan da RAIHAN fa da ita zai fara kashewa,( bata san cewa yasan da zaman RAIHAN ba)jinjina kai kawai take tana kuma jinjina irin wannan cakwakiyar da ita kanta har yanzu bata gama ganeta ba", dole ta ce", haka mana tunda bata san me ya shigo da ƴaƴanta cikin wannan rigimarba da har zai fara yi mata dauki daidai dasu.wata zuciyar ta ce", mata idan babu Muhammad nur ai sune maganadansa dan haka dole ya yi kokarin kawar da duka ahlinsa tare da shi uban gayyar,tabbas haka ne ta faɗa a fili,amma dake hankalinsu ba kwance yake ba babu wanda yasan me take ciki.






Dr Sabo ne ya fito ya basu umarnin ganinshi na yan mintina amma da sharadin ba a bukatar hayaniya ko dogon motsi a dakin dan haka dole su kiyaye", jiki a sanyaye suka shiga dakin don duba shi, tsaf kuwa dakin ya cinye su kasancewarsa babban daki na masu iko.




Addu'ar samun lafiya Baffa da su Hajiya goggo su kayi masa,su kuwa matansa kuka suka saka,dan haka Baffa ya ce su fita duka a rabu da shi dan gudun wata matsalar,ba dan sunso ba suka fita,a wajen ma babu wanda aka bari gaba daya suka wuce gida saboda akwai masu kula dashi.




Kasancewar dare ya yi shi yasa basu samu cincirindon yan jarida masu jiran fitowarsu ba, Abba yahya dai yasha albarka wajen Baffa da Hajiya goggo, Abba Yahya ya kuma shiga ran Baffa saboda yakasance wanda bai manta alkhairi da halaccin da aka yi masa ba.




*RUBY*




Tunda ta baza jaridarta ita da sury suka dawo gida suna jiran sakamako, sai dai har magriba basu komai ba,Surry ce ta ankarar da su cewa babu yadda za ayi su san halin da ake ciki tunda basu kunna tv ba,hakan yasa suka kunna labarai dan kawai su ji sakamakon abinda suka kulla.




Anan ne suka ci karo da abinda yake faruwa,ey labari ya yadu kamar yadda suke so sai dai kuma ta wata fuskar ya juya saboda dai tozarcin da suke so a yiwa Raihan bai samu ba, hankalin ruby har ya fara tashi , Surry ta yi saurin calming dinta,da cewa haba ruby yau fa abinnan ya faru bai kamata mu yanke hukunci tun yanzu ba,muna gobe muna da jibi ina tabbatar miki da cewa gobe za mu iya samun abinda muke so,a yanzu ma wannan labarin na his excellency ne ya doke nata", cikin fargabar da sai yanzu ta fara jinta ruby tace", sury da mun san wannan abun zai faru da mun bar fitar da labarin a yau sai kura ta lafa", harara Surry ta watsa mata sannan cikin takaicinta ta ce", ke kika so hakan ta faru dan nasan a lokacin koda na dakatar dake ba zaki dakatu ba,dan haka Ni babu ruwana da wannan banzar nadamar taki", daga haka ta figi jakarta tana cewa Ni Kinga tafiyata kar wannan dodon mijinnaki ya zo ya sameni",Binta da kallo rubuta yi tana fatan hakanta ya cimma gaci dan idan har ta faɗi a wannan wasan kashe kowa za ta yi duk su yi biyu babu....




*RAIHAN WAZER......*




Yadda yake kulawa da duk wani motsinta sai ka dauka cewa ƙwan tsafin da ba ason fashewarsa ne,a bathroom dimta ya yi alwala,idanunshi akanta har ya fita ya kullota yaje sallah magrib, lokacin da ya dawo ne ya samu hajiyar agadex a falo tana jiran fitowar aunty Amarya su tafi asibiti,sannu da kokari yaron kirki ka yi hakuri da abinda ya faru Ni nasan cewa da wani abu a kasa kuma in sha Allah ko mai zai warware,a nan take sanar da shi kadan daga abinda yake faruwa dan haka ta bashi amanar RAIHAN har suke su dawo......




Wannan shine dalilin yin sallar isharsa a dakin RAIHAN ɗin yana kula da duk wani motsinta,tamkar wadda aka ce za asaceta.......✍🏽
48




*ƁOYAYYIYAR RAIHAN*


A nutse ya mike daga kan abin sallar bayan yayi shafa' i da wuturi,matsawa ya yi dai-dai kanta saboda motsawar da ya ga tana yi alamun dai zata farka.




A hankali take bude idanunta tun suna ganin dishi_dishi har suka bude tarwai akan kyakkyawar fuskarsa dake cike da kamala da wani irin haiba tamkar wani sufi,kura masa ido ta yi cikin mamakin har yanzu yana nan bai tafi ba,maida idanunta kan agogon dakin ta yi sai taga lokaci yaja sosai dan lokacin tara saura kwata,idan kuma bazata manta ba tun wajen biyar yake cikin gidan,kara maida kallonta kansa ta yi fuskarta na ci gaba da nuna mamakinta,kafin cikin sanyin murya ta bude baki ta ce", har yanzu kana nan? Ɗage mata gira ya yi ba tare da ya bata amsa ba,saima dagata da ya fara kokarinyi,ganin hakan yasa ta ɗan ture hannunshi tana cewa barni zan iya tashi da kaina, bai barta din ba kamar yadda ta bukata sai ma ɗaukarta da yayi cak ya nufi bathroom da ita, ɗan bugunshi ta fara yi a kirji cikin sakalci tana cilla kafa duk dan ya sauke ta,bai nuna yasan yanayi ba,dan haka bai direta a ko ina ba sai cikin bath din, sai alokacin ya yi mata magana cikin deep voice dinshi ya ce",ko na yi miki wankan? Ware idanunta ta yi har da baki cikin tsoron kar ya aikata abinda ya fada din,bai nuna ya damu Da mamakin da ta shiga ba ya kuma tambayarta kina bukata ke nan? Baki ta bude zata bashi amsa,sai dai kafin ta bashi amsar shi kuma tuni ya isar mata sakon zuciyarshi ta hanyar rufe bakinta da nashi.mukut ta hadiye maganarta har da ragowar yawunshi saboda jin tattausan harshensa cikin bakinnata,,ji ta yi numfashinta na wani daddaukewa saboda yadda ya fara juya harshennasa cikin bakinta tamkar wani mayunwaci,cikin salonshi wanda ya fahimci yana dauke mata hankali ya fara cire rigar jikinta, RAIHAN bata Ankara ba sai jinta tayi daga ita sai tiet bra dinta da fant,kokarin kwace kanta ta shiga yi saboda jin yana ƙoƙarin cire bra din,gashi babu damar magana dan har yanzu bakinta na cikin nashi yana yadda yake so dashi.




Hannunta ta saka a bayanshi tana ɗan bugunshi tana dan rigarshi,sai dai fa ina wanda yayi nisa baya jin kira, amaimakon ta samu nasara ƙwacewa ma sai motsawar da take yi ya kuma bashi wata dama ta motsawar duk wata gaba dake jikinshi,bai saurara ba har sai da yayi nasarar cire bra dinta zuwa fant din dake jikinta,




Kuka ta saka tare da shigewa jikinsa tana boye jikinta dan kar ya yi nasarar kallonta,babu wani bata lokaci yasa hannu biyu ya karbeta tsaf ta shige cikin ƙirjinshi kai kace babu wata halitta a wajen saboda yadda tayi tsirit a ƙirjinshi,hannu yasa ya banbareta daga jikinshi yaso suyi wankan nan tare to amma idan ya yi wanka ko ya jika kayanshi bashi da wani da zaisa , sai dai kuma idan na RAIHAN ɗin zaisa, takwa anyi abin kunya a gidan surukai ya ayyana hakan a ranshi fuskarshi fidda wani annurin Murmushi.




Cikin kasa da murya ya rada mata da cewa kiyi wankanki babu ruwana ba zan tsaya na kalleki ba, amma fa idan kika jima zan dawo kuma idan na dawo Ni zan sake miki wani wankan," da sauri ta jinjina kanta dake kasa ta kasa haɗa ido da shi, hannu yasa ya dago habarta amma sai ta yi saurin runtse idon hakan ya bawa kwallar da ta cika su damar kwaranyowa kuma ba ta komai ba ce sai ta tsananin kunya,lakace dogon hancinta ya yi Sannan ya juya ya fita cikin nutsuwar zuciya.




Bude idanta ta yi bayan taji alamar fitarsa, kofar ta zubawa ido kamar zata Ganshi ta ciki,sai kuma a hankali cikin sanyin jiki ta bude tap ta fara tsaftace jikinta dama ba sallah za ta yi ba dan haka wankan kawai ta yi da goge baki Sannan ta fito bayan ta rufe jikinta da manyan towel dake bathroom ɗin.






Dai_dai lokacin mutanen gidan suka dawo,Baffa Ali ne ya umarci kowa da yaje ya kwanta zuwa gobe aga abinda Allah zaiyi,amma kafin hakan ya umarce su da su yi sallar dare su riki Allah sauƙin alamura,duk sun gamsu da bayaninsa,har zasu wuce sai ya kuma dakatar da su ya dubi Aunty Amarya cikin nutsuwa kana yace", kafin mu tafi asibiti ina son ganin kowa a falona har da RAIHAN", cak numfashin aunty Amarya ya tsaya tunawa da wannan babban kalubalen da zasu shiga ita da RAIHAN muddin me son ganin bayan RAIHAN ɗin bai saduda ba,dakyar ta amsa masa da in sha Allah", daga nan ya dubi su mama murja ya ce", ina fara za ku amsa kirana akan lokaci saboda muhimmancin maganar da za mu tattauna", amsawa su kayi cikin ladabi daga nan kowa yayi inda ya fi wayo zuciyoyinsu na saka da warwara.






Yana ganin fitowarta ya mike a nutse ya nufeta,fuskar nan babu yabo ba fallasa,dan kallonshi ta yi tana jinjina halin kiskilancinsa,dubeshi kamar ba yanzu ya gama tsotse mata ruwan jiki ba,kamo hannunta da yayi ne ya sa ta dawo hayyacinta daga ɗan gajeren tunanin da ta tafi,zaunar da ita yayi kan stole din madubi yayin da shi kuma ya tsaya ata bayanta yana kallon fuskarta tarwai a cikin madubin,ba tare da ya yi mata magana ba ya janyo man da ya tabbata shine take shafawa lakatowa ya yi ya murza cikin tafin hannunsa,a hankali ya shiga murtsika mata a saman kafadunta in da ya zame towel din da ta rufa, Raihan dai kawai kallonshi take tana mai kara jin mamakinsa a ranta,jin ya zame towel din dake daure a jikinta yasa ta wata irin zabura wanda hakan ya bawa towel din damar sauka gaba ɗaya,kara ta saka me karamin sauti tana mai fadawa jikinsa ta cukwikwiye shi tana sakin kwallar takaici da kunya.lumshe idanunsa ya yi yana jin sanyin jikinta na taba shi kasancewar jallabiya ce me kwanciya a jikinshi,a hankali ya dauki hannayenshi duka biyun ya dora bisa bayanta dake bude yana sheki da dan sanyin ruwan da bai gama bushewa ba,a nutse ya shiga shafa man dake hannunshi a bayanta yana yin sama da kasa da hannunshi.




Cikin kukan sakalci tasa hannunta a bayanshi tana bugunshi,Ni kam ka rabu dani ka tafi ban son wannan abun,haka nan sai Mami ta shigo tace muna iskanci....wata yar makalalliyar dariya ce ta kufce masa sai dai baiyi dariyar ba baya ga ƙayataccen Murmushin da ya saki wanda ya kara ƙawata kyakkyawar fuskarshi me cike da gwarjini yana ci gaba da shafa jikinta har yana zuro hannun ta cikinta dan kawai ya kuma tsokanarta,ai kuwa zabura ta yi idanunta na kuma cika da ƙwallah ta ce",meye ne hakan kake yi? Cikin son ta kalleshi ya dan hade labbanshi sannan ya ce", iskanci.....zaro ido ta yi kana cikin sauri ta kwaci kanta daga jikinshi ta sunkuya ta dauki towel dinta ta maida tana faman tura baki da kananun maganganun da bata san yana jinta ba,Ni kam ka tafi kar Mami tazo",da sharadi", ya fada yana leka fuskarta,meye sharadin? Ta tambaye shi tana tafiya zuwa bakin sip din kayanta ", zaki sha wani abu kafin ki kwanta", na yarda ta faɗa tana dauko rigar baccinta daga sip.




To zo muyi sallama", ya fada idon shi akanta yana mata wannan kallon dake kashe duk wata laka dake jikinta banza ta yi da shi kamar bata ji ba", hucin numfashinsa kawai taji a bayanta kafin ta yi wani yunkuri tuni ya haɗe tazarar dake tsakaninsu sannan a hankali ya juyo da ita ya karbi rigar daga hannunta, saka mata rigar ya yi ta yadda ba za su yi fada ko ta hanashi ba,tsayawa ya yi yana ganin yadda rigar ta yi matukar yi mata kyau da amsar dirarran jikinta,sai yake ganin kamar tafi ko wace mace kyau da tsari,wata ƙilma Allah ne ya dubeshi shi yasa kaddararta tazo a matsayin namiji domin killace masa ita ba tare da ko wane kato ya gane masa sirrin da Allah ya boye a jikinta ba, ɓoyayyiyar ajiyar zuciya ya saki kafin ya kai fuskarshi dai-dai da Tata ya haɗe goshinsa da nata sannan tsinin hancinsu na gugar juna,haka labbanshi da nata suna hade,a hankali ya bude bakinshi ya sumbaci labbanta daga nan ya sumbaci goshinta ido zuwa kuncinta,kafin cikin wata nutsatstsiyar murya ya ce", good night my angel", daga haka ya sake ta ya fita ba tare da ko waige ba,dan ya tabbata idan ya biye ta zuciyarshi da gangar jikinshi to tabbas zai iya kwana a dakin tare da tafka abin kunya a gidan surukai.




Sassanyan ajiyar zuciya ta sauke, tana mai takawa a hankali zuwa bakin window dan kawai taga fitar shi daga gidan.




Yaci sa a bai hadu da kowa a falon ba dan haka cikin kwanciyar hankali ya fice,har ya bude motar zai shiga sai kuma ya fasa ya dan tsaya jim yana kallon window raihidake ta can nesa sosai da shi ta cikin gadin din gidan,tabbas yaji a jikinshi tana kallonshi.




Da sauri tabar window tana dafe saitin zuciyarta,kafin ta yi sufa saman gadonta tana fidda numfashi a hankali,,




Murmushinnan nasa me tsada ya yi sannan ya shige motarsa ya fice daga karamin gate din.




Tunawa ta yi da alkawarin da ta yi masa akan cewa zata ci wani abun, hakan yasa ta mike da sauri ta fita zuwa kiching,shiru gidan da alama kowa ya nufi makwancinsa saboda rashin dadin zuciya da suke ciki,ita ma sai alokacin ta tuna da matar da ta gani a jiya,take komai ya shiga dawo mata ya kice abun ta fara kokarin yi duk dan saboda bata son zuciyarta ta yardar mata da wadda ta gani a matsayin makashiyarsu,da wannan shawara ta zuciyarta ta yi amfani har ta samu ta dan hada shayi me kauri ta dauko cake ta koma daki, sama sama ta ci ta mayar,sai kuma take jin wani irin kewar Abbie dinta saboda wunin ranar kaf bata sashi cikin idonta ba.


______


Kowa yana bacci wani kuma yana kusanta kanshi da Allah buwayi gagara misali,amma ita tana tsaye a cikin dakinta tana sunturi kamar me yin fareti,zuciyarta a dungunzume take ,gaba daya lissafinta so yake ya kwance kai zata iya cewa ma ya kwance din,wai me yasa duk fadi tashin da take yi dan ganin ta samu abinda take so hakan ya gagara,suna daukaka da alama dai bazata samu ba,ey ba zata samu ba mana tunda gashi wanda komai yake hannunsa ma abin yagagareshi daga karshe ma asirinsa ya tonu,anya itama Yahya ba zai gano ta ba kuwa? Kai ba zai yuwu ba Yahya dole na kawar da kai domin na fahimci kaima wani babbar katangane da zai hanani cikar burina,shi dai wancan an gama dashi tunda yaci guba babu tabbacin zai rayu,ko acan gadon asibitin zan iya karasa shi,shi kuma his excellency yana garkame,ɗan jim ta yi sai kuma can ta kyalkyale da dariya tana cewa idan haka ne kuwa ai an rage min aiki,yanzu babu abinda ya kamata nayi sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login