Showing 174001 words to 177000 words out of 189984 words

Chapter 59 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15612

yake wajen furta na shiga uku Ni surayya", daga karshe dai dole sury ta amince da bukatar boka saboda bata da wata mafita tunda ta riga tazo,tana ji tana gani wani katon tsohon kauye me wari da warin baki ya haye mata,da kuka ta bar wajen saboda tsabar ta kaici ko fahimtar yadda zata yi da maganin bata tsaya tayi ba,barin garin ta yi tana jin kamar zata yi nadama....




ABBAN RABI........




Cikin tsawa ya ce", da ciska maza ina so kafin sha biyu na rana a batar min da abu Huraira,shi kuma Wazer ku tabbatar min cewa ku din killers ne na karshe gurin kawo karshen rayuwarsa,dan tabbas idan na bari a ka gama da wannan hargitsin ban kawo karshensa ba to Ni ne target dinsa na gaba dan haka maza ku bace min ba zan fita daga gida ba har sai Naji an fasa kukan mutuwarsa,


Karaf sai a kunnen Rabia da ta sawo kai dan sanar dashi sakon innawuro kuma ta jaddada masa ya maida ta gidan mijinta zata zauna da ko wace a matsayin kishiya,cak ta tsaya tana karewa samudawan samarin majiya karfi da suke fitowa daga falon Abbanta kallo,




Shiga ta yi falon idanunta akan Abbanta da yake kaiwa yana kawowa hannayenshi biyu goye a bayanshi,me kuma ya faru ya tambayi Rabia yana tsareta da idanunsa da suka canja kala", durkushewa ta yi a gabansa tare da rike kafafunsa idanunta cike da hawayen nadama ta ce", Abba dan Allah ka dakatar da duk wata mugunta da ka shiryawa hamma wazer in dai saboda nine wallahi na hakura yanzu ma zuwa nayi na gaya maka ka maidani gidan mijina kamar yadda ka daukoni,saboda naje gurin innawuro ta ce", ba za ta karbeni ba sai tare da kai",wata muguwar bankaɗa ya yi mata kafin cikin masifa da kumfar baki ya ce ", kin gani ko wato ma koroki ta yi to wallahi in dai ina raye kin gama zama a wannan gidan saboda an riga an gama nuna mana matsayinmu,Ni kam yanzu tantama nake akan anya innawuro ita ce ta haifeni kai da walakin tabbas akwai lauje cikin naɗi, dan Allah Abba kayi hakuri wallahi ina son wazer kamar raina ba zan iya rayuwa babu shi ba", ki mutu nace ki mutu in dai akan wazer ne wallahi sai dai ki mutu," daga wannan magana ya bangajeta ya bar mata gurin tana faman rusa kuka,kamar ranta zai fito.




12:00AM.....




Duk wanda ka kalla zaka Ganshi da waya a hannu baki sake idanu a waje,kasancewar waya ta zama abincinmu ko da yaushe tana tare da mu,shi yasa mujallun tree full y trues suke saurin zaga duniya,cikin kankanin lokaci videon ta addancin Abba yahya ya kewaya kasa,saboda tsananin al'ajabi garin shiru ya yi saboda masu magana sun rasa abin cewa.




Tuni jiniyar yan sanda ta cika anguwannin da suke kusa da gidan Alhaji Muhammad nur,kan kace kobo jami'an tsaro sun kewaye gidan ko wanne dauke da bindiga me cin alburusai,idanunsu da fuskarsu babu alamun Rahma ko tausai ga munafiki.




A daidai lokacin mutanen ABBAN rabi suka karaso suka shige cikin mutane, saboda suna da yakinin cewa zasu iya farmakar wazer ta wannan hanyar.






A can cikin gida kuwa hajiyar agadex ce kan gaba dan zuwa fito da Abba yahya wanda har yau babu wanda yasan inda yake sai ita,sosai mamaki ya cika mutan gidan lokacin da suka tabbatar da cewa duk budurin da ake yana cikin gidan dakin da hajiyar agadex ta boyeshi,zuba ido suka yi suna kallon kofar da securitys suke kokarin budewa.




Kwance yake a wajen kai baka ce shine ba,babu abinda dakin yake sai wari saboda yadda yayi faca_faca da kashi duk saboda tsananin tsoro da razanar dashi da ake yi,yayi wani zuru zuru ya yankwane alokaci daya fatarshi ta kwakkwaile kamar tsohon da ya shekara dari,idanunshi kuwa dakyar yake iya budesu saboda yaji da ciwon da suke masa saboda kukan da yasha.




Kukan Bashir suka tsinkaya wanda basu san lokacin da ya zo gurin ba,zubewa ya yi gaban Abbie tare da rike kafafunshi yana cewa dan Allah Abbie kayi hakuri kar ka bari yan sanda su tafi da Abbana ,duba ka ga wannan wahalar da yasha ma kadai ta isheshi ishara dan Allah Abbie ka taimakawa rayuwata kar na shiga cikin maraici,baffa ne ya katse shi da cewa Bashir ka tashi kuma kabar wannan batun dan kasan babu yadda za ayi mu kubutar da Yahya saboda bamu yayiwa laifi ba dan haka dole ne a hukuntashi bisa laifin da ya aikata,idan da ace laifinsa iya wanda ya yiwa nur ne tabbas zamu yafe masa tunda a halin yanzu ma yana tare da yafiyar mune,kayi hakuri kawai ita dai mahaifiyarka in sha Allah za a fito da ita", kuka ya kuma rushewa da shi yana fadin kaiconmu wallahi kaiconmu da irin wannan mummunan sonzuciya wanda bai diremu a ko ina ba sai tashar nadamar da bata da amfani ba zan iya jurar ganin masifar da nake ciki ba Gara Nima a tafi dani a yanke min hukuncin laifin da na aikata,tabbas mun tafka kuskure wanda ba zai taba gyaruwa ba,baffa Nima ina cikin kungiyar Abbana ko mai tare muke aikatawa banbancin kawai shi a nan yake Ni kuma a can nake yin nawa saboda dodon tsafinmu ya ce", nasararmu ba zata tafi yadda ake so ba dole sai mun hada da shan jinin jar fata, wannan shine dalilin da yasa Abbana ya hanani dawowa ku kuma ya yi muku karyar cewa ina can ina kasuwanci da auren da nayi wanda nayi shine ba dan radin kaina ba sai dan umarni ne daga tsohuwa me jini,munyi abubuwa masu tarin yawa wanda a baki ba zasu lissafu ba,dan haka Nima dole a yi min hukunci tare da Abbana.




Ya kare maganar yana kuma sakin kukan da bashi da wani amfani a yanzu,tuni Salim da Raihan ta kirashi Ya shigo ta can kofar baya ya kuma gyara zaman abin daukar maganarshi tare da maidashi kan Abba yahya da yake fidda numfashi a hankali saboda shaƙar Ni imtacciyar iska da yayi,gyaran murya Salim ya yi sannan ya ce", Alh Yahya shin abinda danka ya fada gaskiya ne ko kuma kana da ja? Girgiza kai Abba yahya ya yi yana fitar da ruwan hawayen nadama da tsananin wahala dan shi kadai yasan irin azabar da yake sha, Alh Yahya muna bukatar jin muryarka domin bamu tabbaci idan hakan zai samu", cikin wata irin murya me zurfi da rashin dadin sauraro Abba yahya ya ce", wannan abinda Bashir ya fada babu dad'i a ciki sai ma ragi da yayi akan wasu munanan aiyukan da muka aikata daga ciki har da sallamawa tsohuwa jinin dan dan uwana da ya rasu wato marigayi rufa'i."


Wani irin kuka ne ya ƙwacewa mama murja,yayin da gaba daya gurin aka kaure da salati cikin wani sabon tu ajjibin,baba karami dan gidan momy Hanne shi ne yayi wani irin kukan kura yayi kan Abba yahya saboda duk yafi su zuciya, Abbie ne ya tare shi yana girgiza masa kai,hamma Hassan ne ya rike shi yana cewa barshi me sunan baffa baka gani ba tun kan aje ko ina duniya ta fara koya musu hankali ba, Affan kam bai ce komai ba sai share hawaye da yake haka Hamma Jamil ma dan wani tashin hankalin yafi karfin magana.




Raihan kuwa kara lafewa ta yi a jikin Hajiya goggo tana jin wani irin tsoran duniya na kuma shigarta gani take kamar wannan abun duk ba zai wuce ba.




Wazer ma kallonsu kawai yake hannunwanshi cikin aljihun cot dinsa,nazari yake akan mutanen duniya tare da hararo nasu maci amanan da yake gab da zuwa hannu ba tare da ya cimma burinsa akansu ba.




Dady da shima ya samu damar shigowa ya saita abin maganarsa ya kuma watsawa Abba yahya tambaya akan abinda kowa yake son sanin ya akayi kuma ta yaya? Yahya shin ko zaka gayawa masu sauraro yadda akayi HIS EXCELLENCY ya shiga cikin wannan al'amarin har aka kamashi dumu_dumu da zubawa amininsa guba a abinci?


Garin ne ya yi tsit kowa ya zubawa waya da tv idanu,hatta da HIS EXCELLENCY da yake cikin gidansa tare da iyalansa bayan ya samu nutsuwa zubawa tv ido su kayi gaba dayansu suna jiran wannan amsa da za ta iya bawa Kowa mamaki saboda shi kansa his excellency ɗin bai san ya akai hakan ta faru ba.




Hatta da jam'i an tsaro da suka yiwa gidan dafifi sun yi tsit ne tare da wayoyinsu a hannu suna jiran wannan amsa daga bakin Abba yahya.






Surrya dake kwance kan katifarta tana fama da kaikayin da ya fara mata yawa tun bayan dawowarta daga gurin boka,zubawa tv ido ta yi idanunta,na zubda hawaye ashe dama mutumin nan da yake shirin aurenta matsafi ne? Ey lallai biri yayi kama da mutum,ashe da yanzu tana can ana watanda da jininta,runtse ido ta yi tana jin tsigar jikiinta na tashi kamar dai ana yanka tan,hamdala take ga Allah da bai bashi dama akanta ba,to idan shi bai samu dama akanki ba ai kin kai kanki da kanki inda aka samu damar a kanki,wata zuciyar ke yi mata wannan jawabin da take ya kuma karyar mata da zuciya.




A gidansu wazer kuwa innawuro kuka ta saka da ganin wannan ta addancin baranma da ta ji labarin Raihan da dalilin da yasa mahaifiyarta ta boyeta,wanda Abbu ya sanar da ita,wata irin kaunar Raihan taji tana shigarta tana mai nadamar abinda taso yi na raba aurensu da wazer,yau din dama gaba daya suna gida hatta Ummu rumana tana gidan ita da mijinta,hajiyar Kano ma kanwarsu wadda ABBAN rabi ke bi tazo,gidan dai ya gama zama completely,wazer ne kawai ba ya nan sai ABBAN rabi da ahlinsa.




Inna maimuna dake sel itama fito da ita aka yi dan ta gani,saboda wannan al'amari ne da ya kamata kowa ya gani saboda ya zama darasi ga masu son aikata makamancinsa ko wadanda suke aikatawar dan su san cewa ba fa zasuyi ta yi ne ba tare da karshensu ya zo ba, wannan izna ce.




Lokacin da taji abinda danta yake fada ba karamin kuka ta yi ba,nadamar da ba tayi ba sai yanzu ta fara yinta da ta tabbatar da cewa wadanda su kafita ma Allah ya Kawo karshensu bare ita,wai kuma duka ahlinta wannan abu shi yake saka ta kuka har ta yi shi ta ba uku lada,saurarawa ta yi da kukan daidai lokacin da ta ji Muryar mijinta ABBAN Bashir ya fara magana da cewa.




Sunana Yahya kamar yadda kowa ya sani,sannan Ni yaya ne ga Muhammad nur uwa Daya amma ba uba daya ba",


Take kallo ya koma sama mutane suka fara surutu,saboda babu wanda yasan ba uwa daya uba daya suke ba,hatta su Raihan zaro ido su kayi suna kallon baffa da alama shima suna son jin tabbaci daga bakinsa,hakan yasa shi jinjina musu kai,ba tare da ya iya furta komai ba.




Ci gaba da magana da Abba yahya ya yi ne yasa kowa ya gimtse mamakinsa yaci gaba da sauraronsa.




A agola mahaifiyata tazo dani,amma tun da ta shigo dani gidan baffa Ali yace bai san wannan Magana ba sunana ya tashi daga agola ya koma dan me gida,dan kuwa baffa Ali ya karbeni ya rikeni tamkar shi ya haifeni har sai da aka haifi dan uwana Muhammad nur,duk da haka bai banbantamu dan ya samu nasa ba wani abun da yake min baya yiwa nur shi,kai hatta kai da cewa jikokinsa ma basu san cewa Ni ba dansa ba ne haka yarona da matata har zuwa kan duniya , kowa da dan cikinsa yake kallona", na fara zama butulu me son zuciya da hassada ne lokacin da Muhammad nur ya fara mallakar dukiya da ilimin da Allah ya bashi ya samu kudi ba na wasa ba,wanda take zuciyata ta fara kitsa min hanyar da zan kwace komai daga gareshi, Muhammad nur ya yi suna duniya ta sanshi dan haka Nima nake so duniya ta Sanni ta ko wane hali,karfa ku yi zaton Muhammad nur da mahaifinsa ba sa jikani da irin arzikin da Allah ya basu ,a'a sam duk wani abu da kuka san me kudi zaiyi shi nake yi saboda ya mallaka min kadarorin da Ni ma zan tsaya da kafafuna amma hakan baisa Naji a raina zan hakura da iya kyautatawarsu gareni ba.




Alhji Garba me fata Asalin mahaifiyarsa yar Gombe ce Mahaifinsa shine bafulatani,ban taba sanin Nura da wani amini da ya aminta dashi ba sama da Garba,kuma ban taba sanin cewa akwai sirri me girma tsakaninsu ba sai a wani lokaci da na tsinkayi hirarsu bayan haihuwar RAIHAN da ake kira Rahim a lokacin ba,ba komai na ji ba sai maganar dukiyar da yake bawa Raihan wanda kowa yasan wacece RAIHAN ,ashe duk abinda ya bawa Raihan suma yan uwanta sai ya kwashi na su ya bawa baffa Ali a jiya saboda gudun hakki,yayin da ita kuma Raihan yake mikawa amininshi nata yana juyawa a maimakon ajiya wanda wannan juyawar da akeyi shine dalilin habbaka dukiyar ta shahara ta zama wani abu da har ake son mallakarta,sosai nayi bakin ciki da jin takaicin wai aboki ya fini a wajen Nura,to amma sai ban nuna komai ba na cigaba da binsa a yadda muka saba,katsaham kuma sai mutane suka nemi da Muhammad nur ya tsaya takarar gwamna wanda shi kuma baya da sha'awar siyasa hakan yasa ya maida Garba a matsayinsa ya tsaya masa har ya ci gwamna dan acewarsa shi kadai ne mutumin da ya yadda zaiwa talakawa fiye da abin da shi zaiyi musu, wannan ma ya kuma tunzura zuciyata akan kiyayyar Garba hakan yasa naci alwashi akansu su duka biyun.


A lokacinne farkon shugata kungiyar matsafa,dan duk na samu sanara akan burina da nasa a gaba,ko matata bata san na shiga ba sai dana wan da shi sai daga baya na kaishi a matsayin tagomashin da zan bawa kungiya.dake kusan burinmu daya da Bashir sai kawai ya amince ba tare da na yi masa wani dogon turanci ba.....✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page66 ```




Numfashi ya ajiye yana goge hawayen da suka ki dakatawa daga zubar da suke daga cikin idanunsa. Sanan ya dora da cewa.




A lokacin da Garba ya samu kujerar Gwamna yaso a ce Muhammad nur ya karbi mukami amma sai ya yi fur ya ce", baya so,abu na farko da ya faranta min shine yadda Muhammad nur ya bukaci da a bani wannan kujerar a madadinsa hakan kuwa a kayi ba tare da wani jan magana akan cewa bani da ilimi ba,mataki na farko ke nan da na fara takawa sai nake jin a cewa lallai fa wannan ƙungiya ta tsafi ita ce ta sa na fara samun wannan nasarar kamar yadda suma suke fada,hakan yasa na kuma jajircewa da yin dukkan abinda kungiya ta bukaci nayi.




Dama ta farko da na fara samu akan his excellency shine yadda talakawa suka fara zarginsa da kashe kashen da ya fara yawaita bayan hawa kujerarsa ta gwamna bayan kowa yasan cewa a baya ba haka ce take faruwa ba duk da cewa basu ji dadin mulkin gwamnatin da ta sauka ba, wannan abu ne ya sa muka kara kaimi wajen kwamushe ya'yan mutane muna amfani da wasu sassa na jikinsu dan cimma manufofinmu,haka kuma wani lokacin tsohuwa me jini zata bukaci a tada tarzoma a gari dan Musa yaranmu su yi kashe kashe mu kuma mu yi amfani da ga warwakin shi yasa wani lokacin ko gawar yan uwanku bakwa samu.




Haka dai mu ke aikata duk abinda muka ga dama muna shigewa rigar gwamnati hakan yasa ko lissafi ake yi babu wanda yake kawo mu ciki,


A bangaren su shugaban jam'iyya kuwa tabbas suna da nasu laifin amma basu da laifi akan kashe kashen da ake yi,ko da suna yi na su kadanne akan nawa kuma sai an shiga gonarsu,a garin hakane halima ma aikaciya a gidan jaridar Chibado ta bibiyesu har ta gano sirrinsu na kamo maza yara ƙanana da samari suna amfani dasu kamar dai yadda kuka gani a wannan videon nasu da nasan dole yanzu an sake shi,kuma ta gansu lokacin da suke kashe wani yaro da shima sirrinsu ya gano wannan dalilin ne yasa suka kasheta ba tare da sun san ta riga ta yi musu videon ba har sai bayan da suka kasheta.




A nan labari ya tafi kan yadda su shugaban jam'iyya suka daga hankalinsu kan neman videon da wanda ta turawa.....




Ya ci gaba da cewa duk lokacin da aka kamasu nine nake sawa a fitar da su saboda suma ina jin dadin yadda nake aikata barna ana canki waye tsakanin su da HIS EXCELLENCY.wannan shine dalilin da yasa nake bin wasu hanyoyi dan a sake su.




Lokaci na farko da na fara muzanta HIS EXCELLENCY shine lokacin da aka yi hira da shi a Chibado FM,idan mutane zasu tuna a lokacin an yi kira dan yiwa his excellency tambayoyi,to Nima da wannan damar na yi amfani wajen sa daya daga cikin yarana su yi min wannan aikin,wanda hakan ya yi matukar tasiri saboda na bankaɗa abinda mutane basu sani ba kuma na kara saka zarginsa a zuciyar mutane wanda ko da a gaba nasan duk abinda aka ce yayiwa Muhammad nur ba za a Musa ba kamar dai yadda ta farun.




Mataki na karshe shine dabarun da na yi amfani dasu wajen sakawa Muhammad nur guba,dama na gama tsara yadda komai zai tafi,daga cikin wadanda na samu hadin kansu a kwai kukun HIS EXCELLENCY,ta kansa na fara bi amma kafin na je masa da maganar sai da tsohuwa ta rufe masa baki ta yadda ba zai iya musu akan bukatar da naje masa da ita,dan haka kai tsaye bashi gubar nayi nace duk runtsi ya zuba a cikin abincin da Muhammad nur zaici,daga haka na shiga tunanin dabarar da zanyi dan Muhammad nur yaje gidan his excellency,har kusan karfe biyar na yamma ban samu mafita ba,sai daga can dabara ta fado min,wajen tsohuwa na nufa na kai mata kukana,a nanne ta bani wata laya ta ce", na makalata a bakina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login