Showing 120001 words to 123000 words out of 189984 words

Chapter 41 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15633

dan ji take idan ta kara minti ɗaya komai zai iya faruwa,yadda ta ja motar ma a sukwane da ace da yawan jama a a gurin sai ta jawo hankalinsu.






Suryy da taga fitowarta ita da oganta tuni ya yi mata alama da tabi bayanta ,aiko cikin sauri ta ja motar da ya sai mata ta bi bayan rabi a,binsu da kallo ya yi yana wata banzar dariya kafin ya dawo da kallonsa kan gidan ji yake tamkar ya shiga cikin gidan ya shake Raihan,sai dai kuma bashi da wannan ikon saboda a komai na dukiyar Raihan ana bukatar saka hannunta shi yasa yake bin komai a hankali mataki kan mataki duk dan ya samu burinshi ya cika ya je can ya bude rayuwa sabuwa.




Acan falo kuma Hajiya goggo ta dubi inna maimuna ta ce", amma naga yarinyar nan kamar bata ji dadin abinda akayi mata ba,hmm inna maimuna ta ce", to ai mijinta ne ya yi mata dan haka ita su,daga haka itama ta koma wajen su hajiyar agadex dan ta tabbatar dai yanzu Rahim ya samu tsaro.






A can bangaren Abban rabi kuwa zubawa juna ido su kayi shida Abba yahya da ya zago wajen dan amsa waya,zuciyarshi kuwa har wani dinlin_dinlin take fatanshi dai ace Yahya bai ji abinda yake fada ba,to fatan nashi ya karbu dan kuwa Abba yahya nuna masa ta yi baiji ko mai ba,se ma ce masa da ya yi kai ma wayar ka zago ka yi? Ey ey cikin dan in ina ya fada alamun rashin gaskiya duk sun bayyana a tare da shi, murmushi Abba yahya ya yi sannan ya ce", ai kasan idan ana hayaniya ko yaya take waya bata yiwuwa dan ma Allah yasa daga yau an gama zama sai kuma bakwai shima addu'a za ayi a masallaci Allah dai ya jikansa da Rahma mu kuma ya kyauta namu karshen", da sauri ABBAn rabi ya kama da Amin ya Allah Amin ya Allah,cikin sauri ya bar gurin jikinshi har rawa yake yi,da kallon mamaki Abba yahya ya bishi yana jinjina halin dan Adam wato dai shi mutum duk inda ka ganshi kalleshi kawai sanin zuciyar mutum sai Allah, Allah dai ya raba mu da sharrin zuciya ka tsare imaninmu da hangenmu,daga haka bar wajen dan ya ma manta amsa waya yazo yi wajen..........




______________




*HAIDAR*




A hankali yake bude idanunsa da suka kumbura su kayi wani irin taruwar jini bakin shi kuwa ko buɗuwa ba yayi saboda tsananin kumburin da yayi jikinshi kuwa gaba daya shatin bulalane da kwantaccen jini,kai duk wanda yasan haidar ringim idan ya Ganshi a yanzu da wuya ya ganeshi,duk da ya bude idon ma dai duhun yake gani don yasa ba da duhun saboda tun ranar da aka kawoshi gurin bai ga kowa ba sai dai duka da yake ji ta ko ina da naunshi baya jin Muryar kowa abinci kuwa a duhu ake tsayawa a bashi shima dan kar ya mutu ne saboda ba mutuwar tasa ake bukata a yanzu ba........✍🏽✍🏽




More comments and share 🙏
*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page44 ```Pg44






Allah ne yasan manufarsa da baisa rabi a tayi hatsari ta samu mummunan ranuni ko rasa ranta ba,saboda irin tukuin da tayi ya kawota gida,ko Surry dake bin bayanta cike take da fargaba gani take kafin su karasa me afkuwa ta afku,sai dai cikin hukuncin Allah tazo gidan ba tare da ko bugawa wani mota ta yi ba.shigowa gidan ma baisata ta nutsu ba haka nan ta ake motar a waskace ta fice ba tare da ta dau ko wayarta ba,shukra dake kokarin shiga bangaren kakarsu ta tsaya tana dubanta cike da mamaki,sai dai ganin yadda rabin tayi kamar bata ganta ba yasa ta tabe baki ta yi shigewarta.




Surry kuwa tana can tun gate din farko securitys sun hanata shigowa da mota,barinnata ma da su kayi dan sun santa tare da rabinne,aiko kafin ta shigo ko ƙurar rabi bata gani ba,hakan yasa tayi azamar Binta can sashenta.






Shukra tana kaiwa innawuro sakonta, to koma bangarensu ,tana shiga ta samu Ammi a kiching kamar yadda ta barta,dubanta Ammin ta yi tana ci gaba da kwaba fulawar da zata yi fankaso,ta ce",yana ga har kin dawo nasan dai ba dawowa kikayi dan tayani ba?dan tura baki shukra da bata wuce sa ar RAIHAN ba ta yi, Sannan ta ce",wlh Amma gaba daya banji dadin wannan auren na yaya da aunty rabi a ba,saboda bata da hali kinsan boye halayyarta take yi a nan amma wlh sam bata da kamun kai",ba shiri Ammi ta bar abinda take yi ta juya tana kallon shukra cike da tuhuma kafin ta ce",shurka ina kika samo wannan halin? Meye ruwanki da abinda me shafeki ba,bana son irin wannan wannan abinda kika yi babu kyau tunda ba taba gani kika yi ba",wlh Amm......kallon da Ammin ta yi mata ne yasa ta maida bakinta ta rufe tare da hadiye yawunta sum_sum ta fice daga kiching din amma dai bata ji dadin yadda ammin ta ki fahimtarta ba.




*HAIDAR*




Ci gaba ya yi da kallon gurin ko da dai baya ganin komai sai tsananin duhu,wajen sakon ashirin da farkawarsa yaji alamun shigowa shifa ko inda kofar take ba a bashi damar sani ba,bai san ta inda aka shigo dashi ba bare ta inda zai fita,alamun aje kujera da zama duk alokaci daya yaji daf dashi har hakan yasa shi shaƙar ƙamshin dake tare da mutumin.




Saukar murya kawai yaji cikin isa da takama yana cewa,mu zo lokacin da zaka iya magana a tunanina wahalar da kasha ba zata bari kayi min haddama ba,ina ainahin Flash din da kake da shi akan duk binciken da kuka yi kaida tree full y trues, sannan kuma ina so ka gaya min waye tree full y trues wannan kawai zaka yi min na Barka ka fita da ranka",


Wani irin Murmushi dake fita dakyar HAIDAR ya yi kafin ya tofar da miyan bakinsa da yasan jinine,a hankali ya bude bakinsa bai kula da zugin da fuskarsa da duk wani abu dake fuskar ke masa ba ya ce",au dama kaine kasa a ka kwamusoni?to bari kaji na gaya maka duk abinda zaka yi min bazan taba baka Flash din nan ko gaya maka inda yake ba,sannan a bakina bazaka ji ko wanene tree full y trues ba,da kake maganar kasheni to ai na san cewa ko da na fada maka ba zaka kyale Ni ba domin ba dabiar ka ce wannan ba,nama bai taba shiga hannunka ba tare da ka cinye shi ba...bai gama kai aya ba yaji wani irin barin makauniya wanda har sai da jini yayi tsartuwa daga hanci da bakinsa,duk da haka bai yi shiru ba cikin jan numfashin wahala ya ce",idan kana da iko kaje tsafinka da tsohuwar mashrikarku ta bayyana maka abinda baka sani ba,"wani irin naushi aka kuma kai masa ta gefen cikinsa wanda har sai da ya saki ƙarar azaba, mutumin bai ce ko mai ba har sai da ya kai hanyar fita daga akurkin dakin sannan ya ce",tabbas ka fadi gaskiya babu wanda ya taba shigowa gonata ya fita da ransa dan haka kaima ba zaka fita ba sai dai gawarka amma ina tabbatar maka da cewa sai ka fadi duk abinda nake son ji daga gare ka Sannan kayi wulakantacciyar mutuwa,ƙarya kake kaine za ka yi wulakantacciyar mutuwa mugu tsohon mushriki mayaudari azzalumi ko ban fada ba karshenka ba zaiyi kyau ba,haidar ya fada yana fitar da maganganun dakyar cikin azaba, well-done jarumi shima daya jaruminnaka yana nan tafe dan nasan mace bazata zama ita ce tree full y trues ba",kafin ka bankadosu su zasu fara bankadoka", cak mutumin ya tsaya daga shirin fita da yake yi,dariya ya yi tare da cewa kaga tun kafin ake ko ina ka fara bani satar amsa ashe ma ba mutum daya ba ne? Ba mutum daya ba ne amma ka sani cewa duk cikinsu babu wanda zaka iya kamawa su din kamasu ba abune me sauki ba", da alamu dai maganganun haidar sun soki mutumin dan bai kuma cewa komai ba ya fice daga duhuwar dakin.




______________




Surry na shiga ta yi saurin fitowa da guzurin kayan mayen da ta tahowa ruby su,mika mata kawai ta yi, da sauri ruby ta karba ta bude ta afa , dan yanzu abun ya fara shiga kanta ta fara jin dadin sabuwar halayyarta,lumshe idanunta ta fara yi dan har yanzu ba su yi mata shigar da zasu kasa sara maye ba,da sauri ruby ta taimaka mata ta shigar da ita daki Sannan ta juyo ta fita ta rufi mata gidan,fuskarta dauke da murmushin nasarar da take tunkarota.




ABBAN rabi dai bai samu yadda yake so na sanin lokacin dawowar su Khalil ba dole ya hakura dan kar ya sawa zuciyar dan uwanshi zargin wani abu,sai dai ya koma ta bangaren securitys din da ya kawowa Wazer dan ya bincika masa ya kuma sa masa ido akan duk wata waya da WAZER ɗin zai yi daga yau din nan.




Har yanzu mama murja ta kasa sakewa gani take kamar za a kuma cewa wani daga cikin yaranta ya mutu shi yasa take a firgice goggonta ce da yayarta lantana suke tare da ita.




Itama dai momy Hanne ba ta cikin nutsuwa kullum cikin taraddadi take da tsananin fargaba da tsoron halin da zata tsinci kanta a ciki take.






Sosai inna maimuna ta ji zuciyarta ta kasa yardar mata da Hajiya goggo,to amma idan bata yarda da ita ba me take nufi da hakan tabbas akwai sittin da ake boyewa a cikin gidan dan ta ga gaba daya jama'ar gidan basu da nutsuwa.




Wazer tunda ya fita office ya wuce Ya gabatar da wasu muhimman aiyuka cikin awa daya ya fice ya nufi gidansa da yake kai Raihan,yana zuwa kofar gidan ya samu securitynsa a wajen,cikin boye mamakinsa ya dube shi kafin a hankali ya bude baki ya ce", lafiya dai? Sosa kansa ya shiga yi cikin dan daburcewa ya ce", oga ya ce", mu daina bari kana yawo kai ɗaya saboda akwai risk a cikin hakan", ɗan zuba mishi ido Wazer ya yi sannan ya gyada kanshi cikin yanayinshi na basarwa ya ce", ok zaku hana min mutuwa ko kuma faruwar abinda yaso zai faru dani ko? Wani iri secuerityn ya yi duk sai ya daburce kana kallonsa zaka sancewa akwai rashin gaskiya tare da shi,murmushin gefan baki Wazer ya yi kafin ya dan motsa motar kamar zai wuce sai kuma ya tsaya ba tare da ya dubeshi ba ya ce", na baka hutun sati guda saboda ina son privency bana son damuwa", daga haka ya wuce cikin gidan,sakalo secuerityn ya yi duk sai ya ji tsoran Wazer ɗin ya karu a ransa, shi kan dama sai da ya ce, ba zai iya wannan aikin ba dan babu wanda baisan halin Wazer ba yasan duk ranar da ya sameshi da rashin gaskiya sai ya gayawa yan garinsu.






Yana shiga dakinsa ya wuce, kai tsaye ya fada toilet ya sakarwa kansa shaya sai da ruwa ya zuba ajikinsa na kusan mintina goma kafin ya yi wanka ya tsaftace ko mai nashi ya fito yana jin jikinshi na sakewa,zama ya yi yana dan furzar da iskar bakinshi yana ɗan taune lips dinsa duk a lokaci guda saboda yadda yake ji RAIHAN na yawo a cikin jininshi,tamkar wani mace haka ya shirya kansa kafin ya dan hada copy yasha,bai nemi cin komai ba ya kwanta ya shige bargonsa da yake ta ƙamshin RAIHAN,janyo wayarshi ya yi ya buga video call saboda yadda yake jin bukatar ganinta na hawansa kamar wani karamin yaro dake neman uwarshi dan ta ciyar dashi.






A dai dai lokacin RAIHAN ɗin ta kwanta bayan gama shirinta na bacci ta kashe fitila ke nan wayarta ta hau karkarwar.




A dai-dai lokacinnan da kowa ke kokarin kwantar da hakarkarinsa dan ya huta su kuma lokacinne kasuwancinsu ya bude,lissafi suke akan haidar da kuma babban kamunsu na gaba wanda suke fata daga kanshi ko mai ya kawo karshe zasu bude sabuwar rayuwar jindadi.






A hankali ta daga wayar tare da kaiwa kunne, kafin cikin kasalar dake tare da ita ta yi sallama cikin sanyin muryarta da ta kuma kashe masa jiki,lumshe idanunsa ya yi kafin ya ce", reihann baki bacci ba? Wani irin abu taji har zuwa tafin ƙafafunta har wani runtse ido ta yi tare da ƙamkame jikinta,tabbas sunan da ya kirata da shi da yadda ya fadi din ba karamin tasiri ya yi a tare da ita ba,ki kwanta ki bacci kiyi addu'a kinji", ya fada cikin wani murya kamar me rada ,jinjina kai kawai ta yi tare da zame wayar daga kunnenta tana jin wani sanyi na ratsata wanda bata ji shi ba sai yanzu,yadda jikinta ya yi yasa ta kamar ciwo gabobinta suke ,sauka ta yi daga gadon tare da ficewa daga dakin ,yanzu sam bata da matsalar yawo a bangarensu baranma a wannan lokacin da tasan cewa iya su kadaine a cikin gidan,dakin hajiyar agadex ta nufa dan ta karbo man zafi tunda tasan itama tana amfani da shi.




Har ta zata Murda kofar dakin ta ji kamar motsi a kiching har zata share sai kuma taji kamar magana ake ƙasa_ƙasa hakan yasa ta fasa shiga dakin hajiyar agadex ɗin ta dumfari hanyar shiga kiching ɗin.






Ruby kuwa yau bata yi dogon bacci ba, cikin dare ta farka ta haɗa sallolin da ake binta ta yi su cikin hanzarin da rashin nutsuwa, tana idarwa ta janyo wayarta ta danna kiran Surry,kamar jira take kira daya ta daga tare da cewa ya dai kawata kin wartsake? Na wartsake daga bacci amma zuciyata bata da ranar wartsakewa sai ranar da na tabbatar da cewa na gama da Raihan na kassara rayuwarta shike nan sai na samu nutsuwa ", Surry ta yi dariya kafin ta ce", hakan zata faru kawata ke dai ki ci gaba da yin abinda ya kamata kuma ki tabbatar kinyi komai cikin nutsuwa yadda ba za mu samu wata matsala ba",suryy ba zan iya bari na kai sati Daya ban watsa rayuwar Rahim ba wallahi bazan iya ba goben nan zan watsa labarai da jaridu na fallasa rayuwarta tare da ƙagen da har abada ba zata taba mantawa ba duniya ma ba zata manta ba,shi yasa ma na kira ki saboda kar kice ban sanar dake ba", ajiyar zuciya Surry ta yi tana jin zuciyarta na yadda da hakan itama Gara ayi komai a wuce gurin,dan haka kawai ta ce", shike nan ruby amma ina kara jaddada miki akan kiyi taka tsantsan kar ki bari a gano ki idan ki bar hanyar da Wazer zaisan cewa ke kika yi abinnan to fa biyu babu zaki dan wallahi sai ya rabu dake tare da horan da baki taba zato ko tsammani ba", na sani suryy jiya na ga hakan na tabbatar da cewa Wazer zai iya yin komai akan Raihan na ga wani irin so me zafi wanda ban taba gani ba ban kuma taba ji ba,dan nasan shi kansa baisan irin son da yake mata ba,shi yasa naji ba zan iya hakuri ba suryy",shike nan ruby kinyi dai-dai ina miki fatan nasara,daga haka suka yanke wayar.




_____________




A hankali ta kai kunnen ta jikin kofar dai-dai kafar key wanda shine zai bata damar jin abinda ake yi a kiching din.


Wani irin duka ƙirjinta ya yi lokacin da ta ji Muryar Hajiyar agadex tana cewa,ba zan bari haka ta faru ba dole nayi wani abu,to me zaki yi ta ji muryar kakanta baban agadex wanda a tunaninta ya tafi yau din bayan share sadakar uku duk da cewa a ranar yazo ba kwana ya yi ba,cikin kuka hajiyar agadex ta ce", wallahi bazan bari a cutar min da yarinya ba zan fasa kwai na gaji da boyewa ,tabbas idan aka taba Raihan ramla zuciyarta bugawa zata yi, nasan kuma tunda aka fara daukar yaran nan to tabbas Raihan ita ce ta gaba",haba me kike yi haka meye tabbacinki kar da ki manta ba komai aljanunnaki suke fada miki dai-dai ba dan suma ba komai suka sani ba", wani kallo ta watsa masa tamkar ba ita ba sannan ta ce",tun da haka ka ce shike nan amma ina tabbatar maka da cewa idan wani abu ya samu RAIHAN ko lamra bazan taba yarda ba dan wallahi har kai ba zan bari ba,bata saurari cewar shi ba yana kiranta ta yi hanyar barin kiching din,dan haka RAIHAN ta yi saurin labewa kasan dininng, bata dago ba sai da ta ji shigar Hajiyar agadex daki sai kuma baba buzu da ya fita ta can hanyar kofar kiching wadda zata bulla da shi manyan dakunan bakin da suke sauka a ciki idan sun zo.




A hankali ta fito tana goge zufar da ta jiƙa mata jiki numfashi take maidawa tamkar wadda ta yi gudun awa Biyar,to wai me ke faruwa a gidan haka,dama hamma rufa'i kashe shi akai? To waye ya kashe shi? Me yasa kuma ya kashe shi? Kai ko dai saboda ita ne tunda taji hajiyar agadex na cewa bata son akashe ta,shin wa ye zai bata amsoshin tambayarta? Anya kuwa ba zata tun kari Hajiyar agadex ta nuna mata cewa taji tattaunawar da su kayi ba?




Dafe kanta ta yi saboda juyawar da ta ji yana yi kamar zai cire innalillahi kawai ta shiga ambata akan harshenta domin shine kawai zaisa taji sauƙin abinda take ji........✍🏽
*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page45 ```






Da bin bango ta lalubi hanyar dakinta ta faɗa,tunda ta kwantar da jikinta saman gadon take fidda wani wahalallan numfashi,rufe idanunta ta yi tana son bacci yazo ta karfi amma hakan ya gagara,jin komai ya tsaya mata yasa ta kuma tashi tana layi ta shige toilet, kyakkyawar alwala ta daura sannan ta dawo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login