Showing 54001 words to 57000 words out of 189984 words

Chapter 19 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15607

mai takan kokarin ɓoyewa sai dai idan abin ya taso ba karamin kokawa take da shi ba kafin ya sake ta na wani lokacin,cikin himmar ta na son kawar da komai ta fuskanci abin da ke gabanta ta fara gudanar da aikin ta kamar yadda ta saba..




_______________






Duk yau din baya jin dadi shi yasa tun da ya shigo office din bai leka ko ina ba,hasali ma ya hana shiga office din sa daga bakin sakatariyar sa,kuma ya soke schedules din sa da kowa,haka nan yake jin damuwar rashin Raihan a kusa da shi kwana biyu,ga kuma sa ranar sa da a kayi shida rabi sati Uku,duk sai yake jin sa a wani iri,duk da cewa ba a cika gane damuwar sa ba,amma idan ka dube shi kana dan yin nazarin sa zaka san akwai abin da ya dan taba shi,ko da ya fita sallah bai biya ko ina ba ya dawo office ya kuma rufe kansa saboda baya son abin da zai kara mai damuwa.




Sai da Hamma Idris ya tabbatar motar nan kome kama da ita ma babu a bakin buldin din chibaɗo FM, sannan ya tafi yana mai jin tsoron wannan aiki na Rahim.




A hankali cikin sanyin jiki ta fito daga dakin madaukar murya,salim ne a gefan ta, yana sanar da ita wani labari da suka samo akan Hajiya Turai wadda a baya zata yi hira da ita aka samu matsala,kuma Yar takarar sanata a jam'iyyar gwamnati me ci a yanzu,wato abokiyar takarar Dr.dan tsaki ta saki tana duban salim din,ta ce"salim kabar min batun matar nan bana jin yadda akanta haka nan"salim ya ce"shi yasa nake so mu dan yi bincike akanta,hmm kana gani taki zuwa a yi hirar da ita ko me take tsoro oho mata,dariya salim ya yi ya ce"haba Rahim kai din ne fa ba kyau ko mutum yana da gaskiya idan kayi hira da shi sai ya koma mara gaskiya saboda tsauraran tambayoyinka masu kada yan hanjin mara gaskiya"yauwa Gara da kace mara gaskiya,cewar RAIHAN tana nufar office din ta.




A bakin office dinta ta hadu da Khalid da wasu fayal a hannun sa da alama ya dan jima yana jiranta,ya akayi Khalid? cewar RAIHAN tana dubansa da kuma fayal din dake hannunsa,yauwa Rahim dan Allah wani taimako zaka yi min tun dazu nake zuwa office din oga sakateria na hanani shiga daga umarnin sa,wai baya jin dadi,to dole yau din ya kamata na yi submit din wadan nan fayals din dan Allah kaje ko kai zaka samu ya saurareka"ɗan jim Raihan ta yi kafin a hankali ta karbi fayal din ,shike nan bari na je na gani"yauwa Rahim na gode ya fada yana barin wajen shida Salim.




Sai da ta ajiye takardun dake hannun ta , sannan ta fito dan zuwa office ɗin,kai tsaye lifter ta bi dan ragewa kanta aiki,tana isa ba tare da ta saurari sakateria ba ta nufi kofar kai tsaye,da sauri sakateria ta mike tare da saurin shan gaban Raihan,wani irin kallo Raihan ta watsa mata kafin ta raba ta gefan ta ta wuce,har tasa hannu kan handle din kofar sakateria ta ce",umarni ya bada kan cewa kowaye yazo kar ya shiga saboda yana bukatar nutsuwa"juyowa Raihan ta yi ta ce"to ai idan nutsuwa yake bukata ba a nan ya kamata ya same ta ba sai ya bari sai yaje gida"daga haka tasa kai ta shige office ɗin,tana mai kara jin haushin sakateria,itama sakateria bin sa ta yi da harara tana cewa wannan shu'umin yaron na kasa gane abin da ya taka da kuma matsayin sa gurin oga? (He sakateria daina wahalar da kanki ba zaki gane ba tukunna,kar ku manta sakataria a matsayin namiji take kallon Raihan dan haka dole ta shiga rudani akan lamarin nasu).




A hankali ta yi sallama tana mai wara manyan idanunta a cikin ko wane loko da saƙo na office din,sai dai duk iya hangen ta bata hango shi ba,tsam ta yi da ranta tana kallon kofar toilet wanda budewar da akayi ne ya ja hankalinta,bin sa ta yi da kallo idanunta suna wani yin ƙasa ƙasa cike da rauni suna komawa kalar kuka da san zubda kwalla.




Cikin wata irin kasalalliyar Murya wadda ke tafe da wani irin amo me karya garkuwar jiki,ta ce" Hamma wazirrrrrr"yadda taja karshen sunan haka yaji zirrrr din har cikin kwanƙwalwar kanshi,dan rintse idanun shi ya yi ba tare da ya juyo ko amsa mata ba,sai ma ci gaba da takawa da ya yi cikin kamewar shi me tafiya da yan matan Yola harma da na wasu jiha,tura dan karamin bakinta ta yi,tare da saurin tarar gaban shi ,langabar da kai ta yi tana kallon shi cike da wani irin yanayi da sauyawar tafiyar numfashi,zuba mata ido ya yi yana son kallon cikin idanun ta,ko Allah zai sa ta fahimci halin da yake ciki,tun da shi ya kasa ganowa,wala Allah tunda akanta ne kome ma yake faruwa watakila ita din ta gane tayi mishi bayani.






Sai dai kuma taki bari su hada idanun kamar yadda ya so,saima lumshe idanun da tayi tana mai ɗora maganar ta da cewa me yake faruwa kwana biyu? Ka sauya duk da cewa ba a gane sauyinka bare ainahinka,amma Ni bakan kokarin gane ko wane irin sauyi naka ko yaya yake,akwai damuwa ne Hamma wazir,ta karasa fada idanunta na kara cikowa da kwalla har tana shirin zuba,sam bata jin daɗin yanayin saboda ba haka ya sabar mata ba,duk da cewa ita ma din ba tsira ta yi daga mugun miskilancinshi ba.




Ba tare da ya amsa mata ko daya daga cikin tambayoyinta ba, ya raba ta gefan ta ya wuce saman kujerarsa, ya hakimce tamkar wani sarki,fuskar nan har yanzu tana nan a yadda kowa ya santa,ita sauna gani ta yi kamar ta kara tsukewa fiye da kullum,duk da cewa ta san wannan basarwa da gizagon halinshi amma sai taji duk ta takura dan ko ba komai ita din yana ɗan ƙoƙarin sakar mata wani lokaci,to meye yake yi hakane?


Me yake tunani akan ta? Ko yana tunanin itama zata ce tana son shi ne kamar sauran yan mata?tabbas biri ya yi kama da mutum,tunda shi mutum ne da baya iya sakewa da mace, wannan tunanin da ta yi yasa ta yi saurin kama kanta tare da alkawarin kame kanta kamar yadda shima da yake namiji yake da tsananin kamewa,dole ne ta mutunta kanta a wajen sa ,a matsayin ta na mace.




Wannan tunani da tayi a cikin mintin da bai wuce daya ba,yasa ta yi saurin mika masa fayal din hannun ta ,tana cewa sorry na shigo ba akan daidai ba kayi hakuri,dama wannan Khalid ya ce na baka saboda muhimmancin baka akan lokacin"karba ya yi,kafin ya yi tunanin cewa wani abun da wulakacin sa da sai yanzun ta ƙara fahimta,ta yi saurin juyawa ta bar office ɗin,bin bayanta ya yi da kallo zuciyarsa na shiga cikin wani irin yanayi akan sauyawar lokaci guda da ya ga tayi,to amma shi ya zaiyi duk yadda yaso daidaita kansa ya kasa,wanda har da wata iriyar Fargaba dake ƙassara duk wata gaba da lakar jikin shi.




Lokacin tashinta na yi ,ta fito dan ko sake haduwa da shi bata yadda sunyi ba,daga ranar yau din ta dauki aniyar kaucewa duk wani abu da zai zubda darajarta ta mace a gurinsa, shima da yake namiji ya yi jan aji da kamewa bare kuma ita,ƙwafa ta yi abin yana dan cizon ranta,ganin Hamma Idris tayi a gaban ta ba tare da ta kira shi ba,yau ma tahowa kike shirin yi bayan kashedin da nayi miki harma da abin da yaso faruwa yau ɗin ko " girgiza kanta ta yi kana cikin kwantar da murya ta ce" kayi hakuri yanzu nake shirin kiranka sai kuma na ganka,ok sai ka wuce muje uban taurin kai" Hamma Idris ya faɗa yana hararar ta, murmushi ta yi wanda ya ƙara ƙawata kyakkyawar fuskarta ya fito da jerarrun fararen haƙoranta har da lobawar kumatunta.




Dai dai nan wazir ya fito shima cikin kamewar sa fuskar nan a kame kamar bai taba ko da murmushi ba, haɗa ido su kayi da Raihan amma sai tayi saurin kawar da nata idon,duk da cewa taga alamun son ya jefa kwayar idon sa cikin nata kamar yadda yaso ya yi dazun hakan ya gagara saboda kin bashi dama da ta yi,taku yake a nutse dan karasowa inda suke,sai kawai yaga Raihan din har ta shige motar ba tare da ta kara duban inda yake ba,shi ma din ba ita ya nufa ba,dan haka kawai sai ya mikawa Hamma Idris hannu suka gaisa,duk da cewa bai gama tabbatar da ko shi din waye a gurin Raihan ba,amma shi Hamma Idris din yasan wazir sosai ko ba a dalilin Raihan ba,tun da suna karanta jaridun su,da kuma kallon tashoshin su,ta hakan ne yasan shaharar da CHIBADO's din suke a fannin daukaka.




Duk da cewa Hamma idi yaso jansa da 'yar hira kafin su wuce to amma hakan bai samu ba,dan baiga fuska daga A Wazir ɗin ba,shi abin ma mamaki ya bashi da yaga yazo takanas dan su gaisa, to amma da ya yi wani tunani sai yaga kamar dan dalilin Rahim ne hakan ta faru, dan haka kawai sai ya share su kayi sallama shima ya shige motar sa da Raihan ke jiransa.




Bayan dawowar su affan abubuwa da dama sun faru,kamar tsaida ranar bikin su da akayi kamar yadda su baffa Ali da Abba yahya suka tsara tare da iyayen yaran,




Allah yana nasa shirin mutane su na nasu.




___________




Gurfane yake a gaban tsohuwa tamkar zai kwanta mata saboda tsananin biyayya da ƙan da kai, gaba dayan ta hayaki ne ke zagaye da ita,daga ita har shi babu wanda yake magana,sai can tsawon wani lokaci tsohuwa ta yi wata irin ƙara tare da zabura wanda hakan yasa gaba daya kogon da yake saman tsakiyar kogin can wata ƙasa nesa da mu,ya shiga girgiza idan a wajen kogon kake zaka zaci jirgin ruwa ne yake neman lumewa cikin kasan tafkeken ruwan,




Tana buɗe baki dan yin magana wani irin hayaki ya shiga fitowa tamkar wadda ke shan shisha,ta ce" shuda kada kayi sake ka samu matsala akan wannan karamin dan shilar,tabbas ina ganin wani duhu tattare da kusantar yaron nan da kake yi,sai dai nayi nayi na ga meye a cikin wannan duhu na gagara gani,amma tabbas ba abin daɗi ba ne a gare mu da kai,amma kuma jini ya tabbatar da cewa dole sai mun bibiyi rayuwar yaron saboda duhun da muke gani tare da shi hakan ya nuna muna da alaka da shi,a kwai boyayya lamarin da jini ya kasa nuna mana shi amma ba wai dan ya gare shi ko kuma bai sani ba ne,dan haka kuje ku fara aikin da zai kusanta mu da shi,,kuma ina tabbatar maka da cewa jini yana kokarin yin fushi saboda kwana biyu jini ya rage zuba"""dan haka sai kaje ku fara aikin da ya kamata hhhhhhhh,,,,,,ta shekar da wata irin dariya da lokaci daya ba zaka iya cewa dariya ba ce,dan tamkar karar injin markade me mugun kara haka take yin ta,lokaci daya kuma komai ya baje tamkar ba ayi ruwan ta a gurin ba,daga ita har shuda da tunda ta fara magana bai ɗago ba kuma bai ce kan zil ba,tun da bata nemi cewar tasa ba kamar yadda ƙa'idar su take................✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page18 ```






Haka kawai yau a ka tashi da wata iriyar hatsaniya wadda aka rasa daga inda ta bullo,yan sara suka ne kawai suke banna da zubda jini wani akashe wani a yi masa mummunan raunin da ba zai iya ta shiba,ba kajin komai sai ihu da karar rufe gidaje,a binda zai baka mamaki da tsoro shine baza ka samu wannan fitinar a manyan unguwannin masu kuɗi da mulki ba,duk abin da za su yi suna yin shi ne a unguwannin talakawa masu rangwamen karfi.




Lokacin da ake wannan tashin hankali , Raihan suna can ana shan bikin yayye duk da cewa ba wai ta zage ta shiga mutane ba ne,dan bata da wannan damar amatsayin da take kai na amsa sunan rahim,hasali ma shigewa ɗaki tayi ta rufe ta janyo computer wadda a cikin sati biyu ta karbi shedar zama cikakkiyar kuma kwararriya a fagen sarrafa computer,ta online ta yi wannan cos din ba kuma tare da sanin kowa ba,dan hatta da auntyyn ta bata sanar da ita ba, itama bata san dalilin yin hakan ba,amma tasan ko meye ma nan gaba zai amfane ta.




Tana cikin kurɗawa da shige shige dan kara fahimtar ilimin computer,wayarta dake kusa da ita ta fara kawo haske alamun kira,dubawa ta yi taga abu Huraira ne wato sabon ma aikacin da suka samu ya maye gurbin halima,bayan yasha interview masu zafi wanda Allah ya taimake shi ya tsallake su,ya samu damar zama a karkashin Rahim,tana ɗagawa ba tare da ya bari ta ce"komai ba ya ce"Rahim kasan abin da ke faruwa kuwa?ture computer da ke gabanta tayi cikin ɗan faduwar gaba ta ce" ban sani ba abu Huraira kasan dai yau din aka daura auren duka yayuna ko? Na sani Rahim amma fa abindake faruwa ya shafe mu, nan ya shiga bata labarin tashin hankalin da ake ta yi tun safiyar yau din ta Lahadi,cikin faduwar gaba da rawar jiki Raihan ta ce" abu Huraira kana ina ya zama dole mu ziyarci gurin nan, kafin wasu su riga mu yada karya da gaskiya barin ma gidan jaridar nasss"to amma Rahim gurin fa a rikice yake anya ba za mu ɗan bada ƙafa ba kar fa muje garin daukar rahoto ta rutsa da mu"tsaki Raihan ta yi kafin cikin yar fusata ta ce"haba Abu Huraira sai kace wanda aka canjaka dama mu ba mun ɗauki aikin jarida da yaki da duk abin da zai cutar da al'umma ba ne? Sorry Rahim mu haɗu a ja'e street bamu da lokaci" ok kawai ta faɗa ta tashi cikin hanzari ta yi shirin ta na kullum cikin bakar cot wadda ta fito da zahiran haskenta me sheki irin na yan itopia,kalar Raihan wata irin kala ce me matukar kyau ba fara ce irintas din nan ba sai dai kuma ta wuce ace mata coculate shi yasa ta bada wata kala me kyau da tsayawa mutum a rai,naɗe dogon gashinta ta yi ta cusa sa cikin irin hulunan da take sawar dan rufe gashin yadda ya kamata,tsaf dai ta kammala shirin ta duk cikin sauri wanda yake tafe da zallar nutsuwa da aji wanda tuni suka fara kamata a matsayinta Na mace me kamala,karamar wayar aiki ta dauka ,ta fice da sauri.




Zagawa ta yi ta ɗauki mashin ɗin da tun bayan fara zuwan Hamma Idris office,tasa abbie ya sai mata,tun da ita sam bata son tukui gashi tun jimawa ta hana kanta bin driver,da farko suna tafiya da Hamma idi kamar yadda ya bukata ,to amma daga baya sai ta zame saboda matsalar datake jawowa tsakanin sa da mama,akan tafiya da itan.


Ina kuma zaka je Rahim??




Muryar Hamma idi ta katsewa Raihan hanzarin da take na tada hadadden mashin din nata,sai dai kuma bata tsaya da abin da take kokarin yin ba ta bashi amsa da cewa sorry Hamma wani guri zanje yanzu zan dawo"haba Rahim ana wannan bikin auren na yayin ka amma zaka fita bayan ka kulle kanka kaki fitowa cikin mu"sorry Hamma idi idan na dawo ma yi magana" daga haka taja mashin din da gudu ta fita daga gidan ta baya wajen gate din gidan su Hamman nata.




Tana fita wayar shi ta yi kara,ɗagawa ya yi ,sai dai kafin yayi sallama ,abokin shi sagir ya fara sanar da shi halin da ake ciki dan haka a dakata da dinner din da a za Afita anjima dan garin babu lafiya,wata irin zabura Hamma idi ya yi yana mai bin mashin din Rahim da yasan cewa a yadda ya fita yanzu ko ƙyallinshi ba zai gani ba,dafe kanshi ya yi cike da tashin hankali,dan kuwa ya tabbatar da cewa kaninnashi aikin da ya tafi yi ke nan,da karfi ya ce" wlh ba zai yiwu ba,Rahim dole sai ka dawo gida kuma sai ka hakura da aikin nan,domin masifun shi sunyi yawa"sai ka hana shi uban shi"yaji an fada daga bayan shi,juyowa ta yi cike da mamakin abin da ya kawo maman gurin,mama me kike anan ke da kike cikin jama'ah Hamma Affan ne ya ce"Ni ne na kira ta,saboda tun da naki abin da ke faruwa nasan cewa zaka iya bin bayan sa shi yasa na kira wadda ta isa da kai"wani kallon banza ya bi yayan nasa da shi,mama ta ce"eh ai Ni yayi min daidai kake masa wani kallo kamar zaka bigeshi,to wlh ina mai tabbatar maka idan kasa kafa ka fita daga gidan nan ban yafe maka ba" Affan ya yi dariya yana cewa Ni da ace da 'yan sara sukan za su yi masa wani abu da sun rage mana aiki wlh,maman ta wuce tana mai ci gaba da yi masa mummunan gargadi akan Rahim din.




Sakaro ya yi kamar wani sakarai zuciyar shi na kuna akan halin 'yan uwanshi da maman shi,babu yadda ya iya dole ya hakura da bin bayan Rahim ya shiga yi masa addu'a'in fatan dawowa lafiya.




A can bangaren inna maimuna ma taji labarin abinda ke faruwa,zuwa ta yi tana neman Rahim ɗin sai sahura me aikinsu take ce mata ai Rahim din yana daki bacci yake yace kuma dan Allah kar wanda ya tashe shi,da wannan inna maimuna ta samu nutsuwa har ta samu karfin komawa cikin jama ai su ita da aunty amarya ba tare da ta sanar da auntyn ko mai ba.


_________________




Sassanyan ƙamshinsa kawai innawuro ta zuƙo ta yi saurin juyawa,shi dinne kuwa yake saukowa daga up stairs cikin wannan kamewar ta shi, ya yi kyau sosai cikin ash din suet da tayi matukar karbarshi,kamar wani Balarabe sumar nan sai ƙyalli take zabgawa,rabi dake kusa da innawuro zuba mishi ido tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login