Showing 114001 words to 117000 words out of 189984 words

Chapter 39 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15611

yana kan murjar da ahlinta saboda tana tunanin komai zai iya faruwa ta bangaren mama murjar.




Da gudun kafafu dana zuciya ta fita daga sashenta ta nufi na mama murjar inda har alokacin tana jin Muryar Affan dake ta kiran maman tana dan marin fuskarta,dai dai lokacin da ta shiga suma su Hajiya goggo da su hajiyar agadex har su Anty amarya da kafutanen gidan suka ƙaraso saboda kiran da salame me aiki tayi musu,cikin tashin hankali suke tambayar abinda ya faru,cikin kuka Affan ya shiga basu labarin mutuwar rufa'i,salati suka tafka aunty amarya kuwa kuka ta saka harma da momy Hanne dasu inna maimuna da sauran surukan gidan,inna maimuna ce ta yi karfin kiran Dr Sabo ( karki manta Dr Sabo shine likitan family din Alhji Muhammad nuur) cikin lokaci kankani gida ya rikice da koke koke har zuwan Dr Sabo da su Abba yahya, mutuwar rufa'i ta daki Abbie da duk wani namiji dake gidan dan Baffa ma duk dauriyarsa sai da ya share hawaye,Hamma idi da sauran kannensa kuka suka dinga yi kashirban.


Da kyar aka samu mama murja ta farfaɗo da taimakon Allah dana Dr Sabo,sai dai kukan da take yi shi ya kuma karyawa duk wanda ke gurin zuciya.




Daidai lokacin masu gadi suka budewa wazer tangamemen gate din gidan, sai da ya samu guri yayi fakin sannan ya juyo yana kallon RAIHAN da taki yadda su haɗa ido,hannu ya kai ya dan tsunkuleta wanda hakan yasata zabura har ta juyo gare shi idanu cike da ruwan hawaye,bude baki tayi zata yi magana sai dai bata samu damar hakanba wannan maganaɗisun dake jan zuciyarsa gareta yaja shi ya haɗe bakinsa da nata tare da tarairayota jikinsa gaba daya,wani irin tsinkewa zuciyar Raihan ta yi wani tsoro ne ya kamata na kar wani ya gansu duk da cewa glas din motar tintank ne......




More comments and share 🙏..........✍🏽


Pg 41


Baisan ya akai ba shi dai kawai ya samu kanshi da kasa rike kanshi akan RAIHAN wani salon kisses yake mata me matukar tsayawa a rai da zuciya,tun zuciyarta na bugawa da tunanin kar wani ya gansu har taji tunaninta ya tsaya akansa bata jin komai sai ruwan sanyin harshensa a duk wata gaba me amsa sunan gaba dake jikinta,duk da cewa rigar dake jikinta tana takurashi amma hakan bai hana shi cakudata da salonshi da shi kansa baisan ya iya ba sai akan RAIHAN din.




Tunda ta fito daga ɓangaren mama murja taga shigowar motar family din wazer tasan cewa shine,zubawa motar ido ta yi tun tana irga sakonni ta koma mintina sosai abin ya tsaya mata a rai ganin babu wanda yayi kokarin fitowa daga motar,wani tunani da ya shiga ranta yasa zuciyarta fara bugu da sauri sauri, me RAIHAN take yi tare da wazeer a mota? Dan tasan tabbas ita ya kawo gida,numfashi aunty amarya ta saki tana kokarin daidaita kanta daga tashin hankalin da take son shiga da wasi_wasi akan yartata da kuma amintaccen maigidan RAIHAN ɗin wazer.




Da kyar RAIHAN ta samu ta zame daga rikon gudun kar ki barni da wazer ya yi mata,sosai ta haɗa fuska saboda tunawa da abinda yace mata ɗazu," wai ta tsotseshi,cikin kasalalliyar murya ta ce da shi yanzu waye yake tsotse wani? Bata jira abinda zaice ba tayi saurin bude motar ta fice tana jin sanyi a ranta akan ramuwar da ta yi", maida kansa ya yi ya kwantar yana mai tsirawa hanyar da tabi ido, shi ka dai yasan azabar da yake ji da radadin da zuciyar shi ke yi akan RAIHAN,da kyar ya saita kansa yaja motar ya fita bayan masu gadi sun bude masa kofar.




Yana fita aunty amarya ta yi saurin bin bayan Raihan wadda tuni ta kai falonsu da yayi tsit babu motsin kowa saboda duk suna can bangaren mama murja,tana shirin shigewa dakinta dan kimtsa kanta saboda bata so aunty amarya ta ganta a birkice haka,bata kai ga shiga ba aunty amarya da ta shigo cikin wani irin fushi da sassarfa ta cafko hannunta, a tsorace RAIHAN ta juyo ganin aunty amarya yasa ta Dan ja ajiyar zuciya sai dai yanayin da taga auntyn ya tayar mata da hankali,dan haka cikin rawar baki ta ce", Mami me yake faruwa ne? Wani kallo ta jefa mata kafin taja ta su yi dakin RAIHAN ɗin, Abbie da komai ya faru akan idonsa har zai rabu da su sai kuma ya bisu dakin,ganinsa yasa aunty amarya duk ta daburce ta rasa ta ya za tayiwa Raihan tambayar dake cin ranta,ganin haka yasa Abbie ya dan saki Murmushi me ciwo dan har ga Allah mutuwar dansa ta dake shi,ya ce", me kike son sani ramla? A dan rikice ta dube shi sai dai kafin ta yi wata magana ya tari numfashinta da cewa dan Allah ramla ki bar yarinyar nan ta samu salama ko yaya ne ɓoyan ya isa haka, idan kina zargi akan ita da wazer ne to ki daina saboda tuni aka ratayawa Raihan igiyoyin auren WAZER", daga haka ya fice daga dakin ya bar aunty tsaye da alama ko mai nata ya daina aiki na wucin gadi,tsoro razani firgici mamaki duk su ne suka hadu su kayi dabaibayi a kwakwalwarta. sai kuma tarin tambayoyin da babu wanda zai iya amsa mata su sai Abbie din da kansa sai kuma RAIHAN da wata ƙil ta san wani abu akan hakan saboda ganin yadda bata firgita ko shiga shock akan maganar Abbie ba.




Shigowar hajiyar agadex yasa Dukansu suka zuba mata ido,me ye hakan kuka tsaya ciki cirko kamar wasu sassake?ke Raihan baki san me yake faruwa a gidan ba ne? Da sauri RAIHAN ɗin da aunty amarya da ta kuma shiga ruɗani da tsananin mamakin yadda hajiyar agadex ta kira sunan RAIHAN kai tsaye ,ita kuma Raihan abinda ke faruwa din da Hajiyar agadex ta ambata shine yaja hankalinta.




Da sauri aunty amarya ta matsa gaban hajiyar tare da kama hannunta cikin rawar jiki da ta baki ta ce", Hajiya ke ka kin sani? Tayaya kuma yaushe? Ashe Ni kallon mahaukaciya kuke min kowa ya san sirrin da na binne nake ta kunbiya_kunbiya akansa amma kuka barni ina takurawa zuciyata data da hana rayuwata sakat duk gurin ɓoye RAIHAN?wani kallo hajiyar agadex ta yiwa aunty amarya kafin ta ce", kece kika maida kanki mahaukaciyar tunda a kullum ta Allah sai wani daga cikinmu ya nuna miki alama amma saboda zuciyarki da idanunki a rufe suke sun kasa gano miki ko mai,amma tunda yanzu kin warke daga makanta zauna na gaya miki abinda kike son sani", cikin sanyin jiki ta zauna gefan gadon RAIHAN ita kuwa hajiyar agadex kan sofar dake dakin ta zauna, Raihan ɗin kuma toilet ta shige jikinta sanyi kalau duk da cewa tana jin wani sakayau nakasanxewar maminta zata san ko mai kamar yadda Abbie ya sani akanta.




Bathroom ta shige ba tare da ta tsaya sauraren labarin da Hajiyar agadex zata bawa maminta ba.




Dan numfashi Hajiyar agadex ta sauke kafin cikin nutsuwa ta fara da cewa ramla kafin nace da ke komai ya kamata na fara nusar dake abinda kika manta tunda dai_dai gwargwado kina da ilimin addini me zurfi,to amma idan mu kayi la'akari da kaddarar da ta rigayi fata sai muce ita ce ta zama sanadi.




Dan muskutawa ta kuma yi sannan ta cigaba da cewa", ramla abinda kika yi ya sabawa Shari'a dan me ya sa zaki lullube abinda Allah ya bude sam baki da wannan damar dan haka ki yi istigfari dan kuwa kin shiga hurumin Ubangiji ,shi yasa ya jarrabeki da rashin kwanciyar hankali da tashin hankali rashin nutsuwa, daga karshe kuma duk abinda kike boyan ya ki boyuwa a gurin wanda kike boyan dansu,tunda makiyan dai suna nan kuma baki sansu ba har yau da ko mai yake son fallasa ga kowa,cikin nutsuwa Hajiyar agadex ta sanar da ita dukan abinda ya faru da yadda akayi Abbie ya sani har zuwa kan auren RAIHAN da WAZER.......




Kuka aunty amarya ta saka tana jin wani irin tsoro na kuma shigarta har yanzu bata jin cewa tayi kuskure akan abinda tayi,kallonsu kawai take a dan basu suka haifi Raihan ba basu san irin son da take mata ba,kuma har yanzu bata jin zata amince a tonawa duniya wacece RAIHAN.




Cikin kukan aunty amarya ta ce", bayanku waye na waje ya san da wannan sirrin? Girgiza kai hajiyar agadex ta yi tana bantarar goranta kana ta ce", ai bayan shi Ahmad Chibado wato baban wazeer da kuma dan uwansa babu wani da ya sani a waje kuma ina da tabbacin yadda muka rufe maganar a cikin gidannan ta rufu babu wanda zai kuma sani idan har hakan kike so,(Hajiyar agadex ta boyewa aunty amarya ur exsellency yasan da maganar saboda bata san batun dukiyar Raihan tana gurinsa ba,shi yasa taki sanar da ita saboda wannan ba hurumin ta ba ne)




RAIHAN tana jinsu bata ce komai ba karewa ma tuni tayi shirin bacci,dan kallon RAIHAN ɗin aunty amarya ta yi kafin ta dubi Hajiyar agadex ta ce", zanje na roki Abbie kar ya bari kowa ya sani saboda yanzu mun hau matakin nasara akan gano makiyanmu bana so sai da muke gaf da cimma burinmu komai ya lalace zanso sirrinnan ya cigaba da ɓoyuwa zuwa nan da ɗan wani lokaci,wallahi Hajiya duk wanda ya ce ", zai bankaɗa sirrinnan wa duniya zan iya raba rayuwa da shi zan kuma yi mishi tsana mafi muni dan haka mu ci gaba da killace RAIHAN dani da ku gaba daya har mu cimma nasara", jinjina kai kawai Hajiyar agadex ta yi tana ci gaba da tauna goronta kafin ta ce", shike nan nima dai a yanzu ina bayan hakan tunda an riga an fara dole a daure a karasa fata dai shine Allah ya bamu nasara,ajiyar zuciya aunty amarya ta sauke jin kalaman Hajiya sai taji ta ɗan samu sauƙi, tashi ta yi tana kallon RAIHAN da ta dunƙule kanta tana jinsu, RAIHAN ki yi hakuri ki ci gaba da yi min Alfarma akan ɓoye kanki,kuma ki toshe duk wata hanya da kika san asirinmu zai iya tonuwa dan Allah RAIHAN ",ta karasa fada tana haɗe hannayenta alamar roƙo", da sauri RAIHAN ta girgiza kanta hawaye na tsatstsafowa daga idanunta,ta ce", mamina ki daina roƙona a kan abinda ya zamar min dole duk abinda kike so shi nake so kuma na miki alƙawarin kiyayewa da toshe duk wata hanyar da nasan asirinmu zai iya tonuwa", murmushi aunty amarya ta yi tana cewa karki manta daga ciki har da kiyaye mu'amalarki da WAZER", dummm RAIHAN ta ji kamar jinta ya dauke tana kallo mamin ta fita daga dakin Hajiyar agadex ma tashi ta yi tana mata bankwana,sai dai ita Raihan ta kasa motsa koda yatsunta,haka nan maganar aunty ta shigeta ta kuma tsaya mata a rai,shin me take nufi da maganarta ta karshe? Saurin kawar da tunanin ta yi tare da kwanciya tana kokarin yakice komai saboda bata son zuciyarta ta tabbatar mata da manufar maganar aunty amarya akan hasashen da take yi.






A wannan dare da yawan rayuka da zuciyoyi basu kwana cikin jin dadi ba ta bangaren ahlin Alh Muhammad nuurr,mama murja ta yi kuka tayi sambatun har an kasa gane inda ta nufa sai tofi da mahaifiyarta da ta ƙaraso a daran take mata, tuni yan uwanta sun cika gidan kafin washe gari a ƙaraso da gawar a shiryata anan.




Tabangaren momy Hanne ma hankalinta bakaramin tashi ya yi ba,tunani biyu ne yake kuma daga mata hankali shine murja zata iya zarginta sannan kuma duk wanda ya kashe rufa'i tabbas zai juyo ne kan nata ya'yan tunda itama anyi mata wannan barazanar, koda yake wannan yafi karfin barazana tunda gashi kowane ya tabbatar da abinda ya fada ya aikata,a ranar dai a tafe ta kusan kwana saboda sunturin zuwa sashen surukanta dan duba lafiyar yaranta.




A bangaren Affan ma dai kusan haka ne, saboda shi yasan komai akan mutuwar dan uwansa, ga tashin hankalin rasa dan uwansa ga kuma tunanin shima da harinsa ake wanda a iya tunaninsa yasan cewa shine za aka she sai kuma mutuwar ta faɗa kan dan uwansa,to fa shi dinma yasan ba sha ya yi ba,dan haka shima idanunsa bai ga bacci ba duk da yake barawo.




_____________________




Lokacin da dare ya tsala, alokacinne su kuma ranarsu take haskawa saboda a wannan lokacinne suke nasu kasuwancin.




Yadda garin yayi shiru su kuma a wajensu ba haka bane,saboda wata iriyar dariya da tsohuwa me jini ke yi tamkar zata tsaga dajin da abinda ke cikinsa,komai girgiza yake wani abinma saboda tururin bakinta wuta yake kamawa da shi,su kuwa su shuda suna tsugunne akan gwiwoyinsu kawunansu duka a kasa,ko wanne sanye yake da jar riga iya gwaiya sai jan kyalle ɗaure a goshinansu,hannayensu kuwa dauke da ƙokuna wanda ke dauke da jinin rufa'i.




Sai da kowanne ya shanye sannan suma suka fara sheka wata muguwar dariya tamkar da yawansu ba musulmi ba ne,bayan mintina uku gurin yayi tsitt tamkar babu wata halitta a gurin.




Maganar tsohuwa ce ta karaɗe dajin cikin wani irin amo da sauti mara dadin sauraro, ta ce", shuda a wannan karonma kayi nasara dan haka zaka yi ta ganin nasara babu wanda ya isa hanaka kujerar mulki sannan babu wanda ya isa yi maka shamaki da dukiyar da kake nema, sunan ka zai ta fita yana linkaya cikin duniya baki daya, sirrin nasarar arzikinka yana jikin ahlin Alh Muhammad nuur,yanzu nasara ta fara zuwa zamu yi ta daukar ahlinsa har zuwa kan wadda muka fi buƙata,duhun da ya lullube idanunmu ya yaye jini yaga abinda ke boye," hahhhhhhh
Ta kuma babbakewa da wata muguwar dariya,kaje kaje kaje shuda nasararka na tare da kai da duk wanda ka kawo ko ya rabeka.




Washe gari tuni gida ya cika makil da manyan mutane, tuni gawar rufa'i ta iso tare da ahlinsa.




Lokacin da RAIHAN ta tashi ta ci karo da wannan tashin hankali ba karamin kuka tasha ba,duk da cewa ba kaunarta su rufa'i keyi ba, amma hakan baisa ta kasa jin radadin mutuwarsa ba.




Wazer ma sammako su kayi shida su Abbu da Abba rabi,


Cikin lokaci aka gabatar da salla aka mikashi makwancinsa sai dai halinsa na gari ya bishi, daga nan aka ci gaba da karbar gaisuwa,har zuwa kwana uku...........✍🏽




Comments and share 🙏
Pg42






Sosai yake son ganinta dan tabbas yasan tana cikin damuwa,tun ranar da abin ya faru bai karasata a idanunsa ba,wani irin damuwa yake ji akan rashin ganinnata,dan haka yasawa ranshi ganin nata a yau da akayi sadakar uku.




Rabi'a kuwa rabuwa ta yi dashi bata kuma gigin shiga sabgarsa ba,domin ta riga ta shirya makamanta na tarwatsasu daga shi har yar sonnashi,tuni suryy ta dorata akan shirinsu na gaba wanda take saran shine bom na karshe da zai tarwatsa dukkan wata muamala dake tsakanin RAIHAN da shi da kuma yar karerentasu wato Ruby.




Tunda yayi gaisuwa yake zaune guri daya a kamenshi ,fuskarnan babu yabo babu fallasa,Hamma ido dake kusanshi ne ya dann matso saitin kunnenshi ya ce ", wazer shiru baya takuraka kuwa naga tunda ka fara zuwa zaman makokinnan a takure kake baka iya hira da kowa,shi kuma wanda ka saba dashi matsoracine,ya cigaba da cewa na rasa me yasa duk wata sabga ta mutane Rahim baya son shigarta,kamar daurin auren gidannan duk yadda muke dashi fa ko leke bai leka ba,sannan baya son zuwa Masallaci duk da dai yace min kuna zuwa tare,sannan ga mutuwar dan uwanshi ko sau daya ya kasa zuwa ya zauna dan a karbi gaisuwa dashi,gaskiya wazer kayiwa kaninka fada ,duk da cewa ina yi mishi uzuri saboda tun farko an sanar mishi da irin wannan rayuwarne wato rayuwar killace kai da kadaici,shi yasa nake mamakin yadda ya iya yin aikin media SANA'AR hulda da mutane maza da mata.




Tunda Hamma Idris ya fara surutunsa wazer bai dago ya yi masa cikakken kallo ba bare yasa ran zai bashi wata gamsashshiyar amsa,shiru na kusan minti ɗaya har Idris ya cire ran tankawartasa sai kuma daga can kamar tsinkayi deep voice dinsa yana cewa,ina son ganin Rahim din ", ba wai dan yasan me dame ye ne Idris ya fada ba kuma bawai dan zaiyi wani abu akan abinda ya fada din ba ne yasa ya nemi yin magana da Rahim din ba,a'a sai dai kawai dabarar da ya samu zai fake da ita yaga RAIHAN ɗin.




Idiris da yayi tunanin karar da ya kawo ta Rahim ce yasa wazer ɗin ya bukaci ganin Rahim ya sa shi saurin tashi yana cewa taso muje na rakaka har dakin sa", wazer bai tanka ba ya mike ya zura saucikinsa da yake ta daukar ido tamkar alokacin ya fito daga kamfani,bin bayan idiris din yayi yana jin zuciyarshi na dan yi mishi nauyi akan damuwar rayuwar da Raihan ke ciki,wanda take fuskantar kalubalen rayuwa iri_iri.




Ur exsellency dake can gefe inda suke tare da su Abbie ya ɗan zubawa su wazer da Idris da suka tashi ido,Abba Yahya da shi kuma hankalinsa yana kan ur exsellency ɗin da duk wani motsinsa ya yi tsai da tunaninsa yana kallonsa tare da son gano manufar kallon da ur exsellency yakewa su wazer ɗin. wanda acikinsu bazaka tantance wanda yake kallan ba,sosai ur exsellency yayi zurfi cikin tunani tabashin da Abbie yayi ne yasa shi dawowa hayyacinsa a dan firgice, Abbie ya ce",dan Allah ur exsellency ka daina wannan dogon tunanin komai fa da kake ganinsa yana da karshe,idan cuta ta kwantar da kai fa su babu ruwansu mu da iyalanka da kuma talakawa abun zai shafa dan Allah ka daina kaji", Abbie ya karasa maganar cikin yanayin tsantsar tausayawa.




Jinjina kai ur exsellency yayi yana ɗan sakin murmushin da na kasa bashi ma'ana.




Abba yahya kuwa da ya gama sauraren nasihar da dan uwanshi kewa amininsa,kwafa ya yi yana jin taisayin dan uwannashi da ninkaya cikin tunanin hanyar da zai samu ya tseratar da ahlinsu daga hannun mugun aboki.






Suna saka kai falon da karadin Hajiya goggo suka fara cin karo ita dinma dai fada take akan halin RAHIM,na son kadaice kansa.haka kawai yaro ka maida kanka mace" babu yadda za ayi a ganka cikin taron maza kowa yana waje yana amsar gaisuwa kai kuwa kana daka,duk wanda ya zo maka gaosuwa sai dai ya shigo gida a kira masa kai,yo wannan wace irin rayuwace,ko da yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login