Showing 144001 words to 147000 words out of 189984 words
Chapter 49 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
ya kuma cewa haba Queen of tears ya haka da kuka? Janyo hannunta yayi ya haɗe da nashi kafin ya fara leken idanunta da ta ki bari ya kalla,umm waye ya taba ki yanzu na bulale shi? Jin batun bulala yasa ta yi saurin Dagowa tare da nuna shi da yatsanta manuniya,kawar da fuskarshi ya yi yana ɗan sakin murmushinsa me sanyi,kafin cikin nutsuwarsa ya kuma cewa me nayi to Kinga ba a yin hukunci saida dalili ", cikin san fashewa da kukan da take ta makaleshi ta ce",kaine saboda zaka yi waya da budurwarka ka tashi kabarni a daki Ni daya ba,ta kare maganar cikin kukanta me karamin sauti,sosai murmushi ya kwace masa amma dan kar ya kuma yin laifi yasa ya haɗe jikinsu ya cusa fuskarsa cikin wuyanta yana cewa sorry ba da budurwa nayi waya ba,ai kin san wazer bashi da budurwa bashi da kawa,ko na baki wayar ki duba? Shiru ta yi bata bashi amsa ba,numfashi ya sakar mata me dumi yana cewa Raihan kina nufin da wannan turaren zaki fita ?wa ya ce ma ki saka ? Baki san ke matar aure ba ce? Yadda yake maganar kasa_kasa yana feso mata hucin bakinshi da yake hade da kamshin strawberry shi yasa ta ji tsigar jikinta na wani irin tashi,dago fuskarta ya yi suna fuskantar juna fuskarta cikin tafukan hannayenshi,bakinshi ya kai a hankali ya tsotsi tsinin hancinta sannan ya lashe hawayen kafin cikin Muryarshi dake fita kasa kasa ya ce", kina min asarar hawaye da yawa idan na shanye wasu nasan dole wasu zasu zuba yadda kike Sarkin hawayen nan", sauke kanta ta yi murmushi na fita daga kyakkyawar fuskarta, zuba mata ido ya yi yana jin kamar su yi ta zama ahaka,kaf rayuwarshi bai san da akwai abinda zai kaunata bayan mahaifiyarshi ba,bai taba sanin zai so wata mace kwatankwacin son da yake yiwa Raihan ba, Raihan wata tsokace me haɗe da jini a cikin jikinshi,ba zai misalta ba ,ko da a aikace ne sai dai ya kwatanta, gangar jikinshi da zuciyarshi sunyi kadan su iyakance kaunar da yake wa yarinyar nan,
Jin shiru ya sa ta dago kanta aiko idanunta da nashi suka yi arangama, da sauri ta yi kokarin kawar da fuskarta shi kuma yayi zafin naman rike fuskar, kafin a hankali ya kaiwa idanunta sumba yana cewa i lake dis eyes and dis ya fada yana dawo da bakinshi kan hancinta shima ya bashi sumba ɗaya, sannan ya dawo kan bakinta yana cewa i lake dis cute mauth so much", ya karasa fada yana hade bakin su waje guda, sumbatar bakin yake idanunshi akanta,sam baya jin zai gundura da yarinyar na. Sosai fa ta yi masa mamaya,yana so ya hakura ya Kaita gida amma mayen sonta ya na hanashi yin nesa da ita,shi bai da tabbas Raihan na sonshi amma ya na da tabbacin zai iya zama da ita ko bata sonshi ya kare rayuwarshi cikin bautawa SOYAYYArta.
Sassanyan Muryarta ce ta dawo dashi daga duniyar soyayyar da yake ji babu kamar tasa,Hamma gida ina tsoran mami ta rigani dawowa kasan ita fa har yanzu haushinka take ji", kina so ta daina jin haushina? Ya tambayeta alokaci daya yana zama da ita akan kushun din dake daf dasu,bata bashi amsa ba sai kokarin tashi dake yi,maida ta ya yi bisa cinyarshi a maimakon da take kusa dashi,yar harara ta bashi shi kuma yaja dogon hancinta yana cewa yarinya naso tana kaiwa kasuwa", turbine fuska ta yi tana kai mishi karamin duka a kirji,rungumeta ya yi sosai yana shakar kamshinta da ta bulbula kusan mintuna goma suna a haka kafin ya sake ta dan kanshi yana cewa ki zauna na shirya na kaiki muga mami sai mu dauketa mu wuce gida", ta ce tana asibiti ne har yanzu? Ta tambaye shi tana duban hadaddiyar agogon dake rataye a bangon falon", shafa fuskarta dake da matukar kaushi ya yi yana cewa in sha Allah tana nan", daga haka ya shige bedroom.
Maida idanunta ta yi ta lumshe su tana jin wani abu me girman dala da gauran dutse a cikin ranta,tunawa ta yi ta ce", da baffa Ali bata son wazer idan komai ya daidaita za a raba auren", wani irin tashi ta yi zaune daga kashingiden da take,hannunta dafe saman ƙirjinta,to ke Raihan me ye hakan ai kin san dama dole zaku rabu tunda shi dama yana na da matarsa azabbiyar mata kuwa,mele bakinta ta yi tare da kaiwa kofar bedroom dinshi kallon harara tana cewa Ni kam ba zan zauna da wannan mahaukaciyar ba,Gara a rabu,a rabu fa,duk sanda ta ambaci kalmar sai ta ji faduwar gaba,girgiza kai ta yi tana kuma cewa a'a ba wannyne me muhimmanci ba sanin inda haidar yake shine me muhimmanci duk inda muka samu haidar na tabbata za mu samu videon nan daga nan dole a kama su shugaban jam'iyya da Dr sanater,dama hujja kawai muke nema",ta gumi ta yi da hannayenta biyu tana tunanin ta yadda za su samo HAIDAR,
Tree full y trues in sha Allah sai na samoka ko namiji kake ko mace nasan kai kadai zaka yi min wannan taimakon", waye kuma tree full y trues? Wazer ya tambayeta yana fitowa daga dakin cikin shigar kananan kaya da suka yi matukar amsar jikinsa da yake shan geming ,tashi ta yi tsaye dan bata bukatar su kara bata lokaci ba tare da sunje asibitin ba, Sannan ta dubeshi cikin irin basarwar da ta koya a gurinshi ta ce", ai kasan ko waye, ina son samo shi saboda ya taya Ni neman haidar da inda videon su shugaban jam'iyya yake dan shine kadai abinda zan tabbatar a samu a kamasu ba tare da anyi wata makarƙashiya an sakesu ba,da ace iya shaidata ta baki zata gamsar da kotu tabbas da tuni an shafe babinsu an wuce gun", ana ta gagga wa yake ta wasu kananan kwari", ya fada yana jan hannunta,su waye manyan kwarin to? Bai bata amsa ba har suka fita ya bude mata gaban motar ta shiga,kallonshi kawai take tana jiran amsarshi sai dai shi din uban yan miskilanci ya fiske tamkar bashi ya yi maganar ba,ganin haka yasa itama ta yi shiru har suka fita daga gidan babu wanda ya kuma tankawa dan uwansa.
Wazer na yin fakin a harabar asibitin hamma Idris ma ya yi fakin, a tare suka fito suna nufar juna", hamma Idris ne ya fara bashi hannu suka yi masabaha yana cewa ashe kana tare da mutuniyar", ya tambaya idanunshi akan RAIHAN da ta yi kicin kicin saboda amsar da wazer ya ki bata,wazer bai bawa Idris amsar tambayarsa ba saima wucewa da ya yi cikin reseption din kai tsaye, sosai securitys din suka bincika su kafin su barsu su shiga duk kuwa da cewa sun san dangantakar dake tsakaninsu da me jinyar,amma wannan umarni ne me zafi daga ogansu me asibitin wato Dr Sabo akan cewa ko waye ya zo su tabbatar da sunyi bincike me kyau kafin barin sa ya shiga, Idris ne ma yaso yin gaddama acewarsa yana ɗan Abbie amma ace sai an bincike shi bincike me zafi kafin ya shiga wajensa, Raihan ce ta rarrasheshi sannan ya hakura yabarsu su kayi aikinsu.
Turus Raihan ta yi ganin bandeji a kan maminta,sai kuma ta karasa da gudu ta rungumeta cikin rudewa ta fara tabata tana cewa me ya sameki Mami ? Waye ya miki haka? Rike RAIHAN ɗin Aunty Amarya ta yi ganin yadda duk ta rude har ta fara halinnata wato kuka", calm down Raihan ki nutsu babu abinda ya same Ni faduwa na yi a bathroom shine a ka yi min dressing", kwanciya ta yi ajikinta cikin damuwa tana cewa to Mami amma babu zafi ko? Babu zafi Raihan gida ma nake shirin tafiya na kira Idris ya kaini,ey na Ganshi tare muka shigo ya tsaya duba wani abokinsa ne, Raihan ta faɗa tana dago fuskarta daga jikin mamin tare da kallon inda wazer yake ", karasowa ya yi cikin nutsuwa yana gaida Aunty Amarya da yi mata sannu da fatan Allah ya kiyaye,ganin yadda Raihan ta zuba mata ido idanunta cike da kwallar da take jiran kiris ta zubo yasa ta amsawa babu yabo babu fallasa,daga haka ta mike ta shiga hada kulolin abincin da suka kare tana cewa Raihan ki sallame shi ya wuce mu zamu tafi da Idris", kallon Wazer ɗin Raihan ta yi fuskarta a marairaice kafin ta yi magana ya sa hannu ya yafitota,kana ya juya ya fita,duban mamin ta yi sannan ta ce", to Mami bari na gaya masa na dawo", ina jiran ki ta faɗa tana ci gaba da gyarawa Abbie mayafinsa, zuciyarta kuwa babu dad'i dan ba a san ranta zata tafi ta barshi ba,dan kawai Dr Sabo ya bata baki ne kuma ya tabbatar mata da cewa Abbie yana cikin tsaro me kyau in sha Allah babu abinda zai kuma faruwa.
Tana fitowa ta sameshi a mota ya kwantar da kansa jikin sitiyarin idanunsa a lumshe kamar me bacci,shiga ta yi motar tare da dan taba kafadarshi tana cewa yaya wazer kayi hakuri ka ta fi za mu tafi da mam.....kafin ta larasa fadar abinda ke bakinta ya tashi motar tare da rigarta duk alokaci guda cikin zafin namanshi, wayyo dan Allah ka bari za mu tafi da mami", ba za ta same ki a gidan ba inda kika fito zaki koma,yanzu sai ki fada min wanda ya fi iko tsakanin Mami da mijinki? Ya karasa fada yana dage mata girarshi guda so very gentle.zata fara halin ya dora yatsanshi kan bakinta tare da cewa kar ki sake ki fara bana bukatar zubarsu a kasa ko bari idan munje gidan sai kiyi Nima a nan ne zanfi shanye sh dakyau", aiko mukut ta hadiye su ta kuma kame bakinta ta yi tsit kamar wata yar babyn dake tsoran bulala.........✍🏽
TOFA WAI YA HAKA NE INJI GWANJA,
KALLO DAI DA ALAMA ZAI KOMA SAMA
TABBAS DAI BAYA CE ZATA HAIHU
MAKIRA KIN KUSA ZUWA HANNUN MAZA.
HIS EXCELLENCY WAI ME YE A KASA NE....IDAN BA KAI BA NE WAYE?
ABBAN RABI KIFI FA NA GANINKA ME JAR KOMA
HAJIYAR AGADEX WAI YA TAKE NE MUNA SON SANI NI DA MASOYAN RAIHAN......
KU BULBULO MIN COMMENTS NI KUMA NA BULBULO MUKU AMSOSAHINKU
IDAN BA KUYI COMMENTS BA ZAN TAFI YAJIN AIKIN KWANA GOMA KO NA MAIDA SHI FAIN NA TAFI AREWABOOKS NA SAMU YAN CANJI NA😂
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivat the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page54 ```
54
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
Aunty Amarya tana gama hada kayan ta fito dan tarar Raihan a waje sai su wuce,
Duban HAMMA IDRES ta yi tana cewa wai ina Raihan dinne? Dariya Idris ya yi yana cewa aunty Amarya kawai kizo mu wuce dan ita Raihan akan idona tabi mijinta suka tafi", ɗan jim ta yi kafin ta yi kwafa ta shige motar, shima Idris din shiga ya yi yana kunshe dariyarsa, dan kuwa abin ya bashi dariya lallai Aunty Amarya ta hadu da sirikin zamani.
Suna zuwa gidan HAMMA IDRES ya yi mata sallama ya wuce bangaren mahaifiyarshi,lokacin da ta shiga falon babu kowa dan haka kai tsaye dakin Raihan ta nufa,wayam babu ita har bathroom saida ta leka amma babu Raihan babu dalilinta,fita ta yi ta shiga dakin hajiyar agadex in da ta samu HAJIYAR AGADEX na lazumi,katsewa ta yi tana duban Aunty Amarya ta ce", ke kuma lafiya ruɗadɗa gaba daya kin kasa kwantar da hankalinki sai ka ce akanki a kafara jarabta,ganin HAJIYAR ta fara fada yasa ta ɗan nutsu sanan ta tambayeta ko Raihan ta dawo? Bata dawo ba wani abu ya kuma faruwa ne? Girgiza kai Aunty Amarya ta yi kana ta ce" wazer ne ya ce ze kawota gida ni kuma mun taho tare da Idris shi yasa nake tambaya ko sun ƙaraso" to basu ƙaraso ba wata kila suna hanya,to wai ke meye damuwarki da haka wazer fa mijin Raihan ne duniya ta shaida hakan dan haka ki bar wani rawar jiki nan kusa kusa zata tare a gidanta dan munyi magana da shi Baffan harda iyayen wazer ɗin dan haka sai ki fara shiri ", Hajiya tarewa fa kika ce? A haf zancan kike so ,Ni a ganina hakan shine maslaha kuma Raihan sai tafi samun tsaro idan tana gidanta tare da mijinta,yau muka yi maganar shi yasa ban samu gaya miki ba,itama raihan din daina fita ko ina za ta yi saboda gyara za a fara yi mata", ko mai Aunty Amarya bata ce ba,dan tasan cewa ko da son ranta ko babu tunda suka yi niya sai sun Kaita,yo a kayi auren ma ba da saninta ba bare kuma tariya,fita ta yi daga dakin zuciyarta cike da wasiwasi akan wazer ɗin, to amma fa maganar hajiyar su tana kan hanya tabbas Raihan sai tafi samun nutsuwa a gidan aurenta gidan aurenma gidan WAZER.
Cikin nutsuwa baffa Ali ya dubi Abba yahya kafin ya dan yi gyaran murya ya ce", yahya abinda yasa nace duk dare idan ka shigo ka biyo nan ina son magana shine a ɗazu da yamma munyi wata shawara nida iyayenka mata hajiyarku ta nan da ta can agadex akan cewa mu sanar da iyayen wazer da shi kansa Raihan ta tare nan da sati daya hakan sai yafi kwantar mana da hankali akan duk wani tashin hankali da muke ciki, Allah ne me kiyaye bayinsa amma duk da haka idan tare sai ta fi killatuwa da samun tsaro a gidanta",a hankali Abba yahya yasa hannu ya dan share zufar da ta fara tsatstsafowa akan goshinsa sannan ya dubi baffa Ali cikin fitar da murmushin yake ya ce", haka ne Baffa amma Ni a ganina a dan dakata zuwa sati biyu domin muga yadda jikin Nura zai kasance idan so samune Raihan ta tare bayan warkewar mahaifinta saboda ita kanta sai ta fi samun nutsuwar da muke yi mata fata,nifa a tawa shawarar",ya karasa fada idanunsa akan baffa Ali domin ganin yadda zai karbi zancannasa, jinjina kai baffa Ali ya yi sannan ya ce", kazo da magana kaima,amma ai kaima uba ne ba shawara ya kamata ka bayar ba umarni za ka bayar tunda da kai da kaya duka mallakar wuya ne dan haka zamu bari zuwa nan da sati biyun idan har Allah bai sa Nura ya farka ba to TABBAS RAIHAN zata tare a dakinta,sai dai cikin ikon Allah muna fatan farkawar nur in sha Allah", na gode baffa hakika babu abinda zance da kai sai dai na ci gaba da yi maka addu'a har kashen rayuwarka abinda ka yi min ko mahaifina ne sai haka,ina alfahari da kai ta yadda ka samar min da dan uwa na gari wanda duniya ke alfahari da shi,tunda gashi har zuwa yau babu wanda yasan cewa ba kaine ka haifeni ba hatta da matata bata san cewa ba kaine mahaifina ba", ya karasa maganar yana zubar da hawayen nuna tsananin kaunararsa ga wannan bawan Allah", murmushi baffa Ali ya yi kafin ya dafa kan Abba yahya ya ce", bana son kana damun ka ko ka dinga taso maganar da muka binne ta iya mu imu Allah shine shaida ban daukeka a dan mata ba sai dana na cikina", na gode baffa", daga haka ya mike tare da yiasa sallama ya fita daga falon.
Kamar walkiya haka ya ganta a gabansa ta na binshi da kallon mamaki ta cikin hasken da ya dallare farfajiyar katafaren gidan", cikin mamaki shima yake kallonta kafin ya bude baki ya yi magana ta rigashi ta hanyar daga masa hannu fuskarta na fidda wani irin haske me kyalli ta ce", Yahya dama kai ba dan cikin Ali ba ne? Bata saurari amsarsa ba ta cigaba da cewa tabbas buri yayi kama da mutum", HAJIYAR AGADEX me kike nufi da biri ya yi kama da mutum? Dariya ta yi matsakaiciya sannan ta ce", Yahya saboda kai na cire kunya na dawo gidan suruki da zama shin kai hakan bai baka mamaki ba asa ilin da ka tsinci mace mai alkunya da kawaici cikin gidan surukinta a matsayin mazauniya ba,? Tabbas Yahya jinnu ba karya ba ne sai dai ba komai suke sani kamar yadda mutane suke zato ba ,suma basu san gaibuba duk abinda kafa sun sani to tabbas ya wanzu ne a lokacin da suke kusa da gurin saboda su su kasance iska shi yasa suke finmu sanin abinda yake ɓoye,amma ba ko mai ne Allah yake basu damar sani ba Allah shi kadai yake da sani a kan komai kuma shine yasan gaibu, shi yasa Nima ban gama sanin komai akan ka ba sai a hankali ta hanyar bincike na da bin kokofina Allah ya ke nuna min daya bayan daya,dan haka ka daina bacci da sanin cewa babu wanda yasan abinda kake shukawa kuma ka daina bacci da tunanin cewa asirin boye ba zai bankaɗa ba,dan haka ka zauna cikin shirin ka domin maza suna nan bisa kanka saura kadan dan hakin da ka raina ya tsole maka duka idanunka", ba tare da ta bashi damar yin magana ba ta yi gaba ta barshi a wajen tamkar wani status.
________raihanwazer.......
Bata san me yasa ya sauya tunani ba dan har sun kusa karasawa gidannasa sai kuma.ya juyo ba tare da ya tanka mata ba,ajiyar zuciya ta sauke ganin ya dawo da ita gida,yana yin fakin ba tare da ya dubeta ba ya ce", ina so ki min wani aiki amma bana bukatar tambayar ki ko guda kawai kiyi abinda zan umarce ki", bata ce komai ba amma dai tana saurarenshi, dan cije labbanshi ya yi yana kewaye gidan da idanunshi sannan ya ce", ina so ki samun ido akan fuskar duk wadda ta baki wasu takardu dan saka hannu ko ta wace irin siga ce,ki rike min fuskarta ko ita wacece a gidannan da kuma matsayinta ", daga haka ya ce", muje na raka ki", duk da cewa zuciyarta cike take da wasiwasi da dinbin tambayoyi akan abinda yake kira da suna aiki,haka nan ta fito ba tare da ta furta