Showing 27001 words to 30000 words out of 189984 words

Chapter 10 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15657

mamakin ganin sa ba,fa ce,Alhaji rabi'u me kwangila,wanda ya kasance shugaban jam'iyyar su Alhaji Garba me fata,wanda kuma kowa ya san cewa ba jam'iyar su daya da su Alhaji sale me shanu ba,hasali ma abokan adawa ne na bugawa a jarida,kuma a fili kowa yasan basa shiri da shugaban jam'iyyar wato Alhaji Rabi'u kwangila,abu na biyu kuwa kowa yasan wadan nan mutanen basu da wata lamba ko wani hali da zaka bigi kirji ka ce idan ka gansu a wannan yanayi ba zaka yi mamaki ba.




Saurin barin wancan tunanin ta yi don fuskantar abin da suke shirya wa,shugaban jam'iya ne ya dubi alhaji sale ya ce" ya dai me kuke jira da wannan baku bazar da shi ba,ai irin su ba su da wani amfani a cikin irin mu,dan haka ya dubi ƙwaro ya ce" ƙwaro maza sashi baccin da ba zai farkaba kuma ka tattara shi ka kai tsohuwar rijiyar a jiya" an gama shugaba" ƙwaro ya fada yana nufar wannan saurayi da aka datsewa baki da salatif,take saurayin ya fara mutsutsu da daga hannayen sa da suke a haɗe wanda tunanin halima ya bata cewa lallai amota bayan yayi masa barazana da bindiga sun shiga ya yi masa wannan daurin,kafin halima ta kai ga dire tunanin ta ,ta tsinkayi karar harbi har cikin tsakiyar kunnen ta,a tunanin ta ma ita aka harba sai da ta bude idanun ta da ta rintse su bayan jin Harbin sai taga ashe saurayin nan ƙwaro ya zubawa bullet har biyu a tsakiyar kirji.




Burin mu shine duk abin da muke aikatawa ya koma kan gwamna da wannan dankanzagin nasa Alhaji Yahya,dan naga alamu ya ma fi defity samun guri a gurin sa, Alh sale ya ce",duk ba dan Allah yake yi ba saboda kawai yana yayan Amininsa ne Alh Muhammad nuurr,kasan shine komai nasa kai dukiyar ma da yake takama da ita duk ta Alh Muhammad nuurr ce,a yadda naji ma cewa a kayi ta wata yarshi ce Raihan da ba a haifa ba ya bashi yake juya masa saboda yaddar da ya yi da shi",rike baki shugaban jam'iya ya yi yana cewa kai duk a ina kasan wannan maganar? murmushi kawai ya yi tare da kawar da maganar ta hanyar cewa,ku fita da gawar akai ta ma ajiyar".


Bata san lokacin da ta saki wata siririyar ƙara ba,wanda karaf sai a kunnen su shugaba,cikin tashin hankali ta bar jikin window ta fara kurɗawa cikin ciyayi da mugun gudu tana yi tana turawa Rahim sako ta WhatsApp,wani tunani ta yi sai kawai ta yi saurin goge lambar Rahim da sakon video da na test bayan ta tabbatar sun shiga.




Ka kira duka yaran ku bita kar ku sake ku dawo ba tare da gawaarta ba,Dr sanate ya fada cikin tashin hankali,shugaba kuwa kaiwa yake da kawowa burin shi da fatan shi bai wuce a ce an kamo wannan tsinanniyar yarinyar ba.




Sosai suka bazu dan neman halima,ita kuwa a cikin wannan ciyayi ta samu ta binne camarar,tana gama binnewa ta cigaba da gudu numfashinta har daukewa yake ,amma ta yi yakinin Allah zai bata lada ko bayan ranta tana da tabbacin Rahim zai karasa aikin da ta dauko koma fiye da yadda ta so yi.kamar daga sama taji saukar bullet a tsakiyar bayan ta,take kuwa ta fadi ko shurawa ba ta yi ba.allahu akbar Allahu ya karbi shahadarki halima.




Tsugunawa ya yi a gaban gawar yana kallon ta na tsawon lokaci kafin ya ɗago idanun sa da su kayi jajur ya ce" meyesa ƙwaro me yasa baku yi tunanin kawo min ita a raye ba,idanuwa na sun rufe na baku umarnin kashe ta bayan kuma kashe ta ba shi ne mafita ba,kamata ya yi mu fara tambayar ta su waye su ka turo ta kafin mu aiwatar da nufin Mu akan ta" duk shuru su kayi cike da jimamin katoɓarar da su kayi,Dr sanate ne ya ce" shugaba ai ina ganin tun da munyi nasarar karbar wayar ai bamu da matsala da wanda suka turo ta" kai ku dakata" alhaji sale ya fada yana wani dan nazari kafin da sauri ya tashi tsaye yana cewa kai yarinyar nan fa har da camara a hannun ta wannan video ba iya wayarta ya tsaya ba akwai camara a hannun ta tabbas,take hankalin su ya kuma ta shi,Dr ya dakawa yaran tsawa to me kuma kuke jira maza kuje inda kuka harbeta ku lalubo camarar" ko rufe baki bai gama yi ba su ka fita cikin mugun hanzari.




Sai dai kuma babu duban da ba suyi ba amma babu camara sama ko kasa ,haka suka haƙura suka dawo, amma sun ji babu dadi a wajen shuqagabannin su,haka su ka tattara gawar su ka fita da ita,shugaban jam'iyya ya ce" ita kar ku Kaita tsohuwar rijiya ku je ku jefar da ita a gefan hanya ta yadda yan uwanta zasu ganta,ina tunanin ta wannan hanyar ce kawai zamu san su waye suka turota" wannan shawarar ta yi cewar Dr.




Ganin da Raihan da su salim su kayi halima bata dawo ba ,har aka gama shirin siyasarmu a yau,sai su kayi zaton ta wuce gida,dan haka su ma suka ta shi ,amma ko wannen su kokarin kiranta ya shiga yi dan tabbatar da cewar tana gidan.




Cike da gajiya da yar damuwa Raihan ta koma gida,ba tare da ta iya aikata komai ba ta zube akan lafiyayyan gadonta,tana maida numfashin damuwa da gajiya.




Koda Anty amarya ta shigo taga Raihan bata yi mamaki ba, sannan bata tsaya tambayar ta damuwarta ba,dan ta san tatsuniyar gizo ba zai wuce ƙoƙi ba,sai dab da magriba RAIHAN ta tashi ta dauro alwala, duk da cewa ba sallar zata yi ba,to amma bata sake ta zauna babu alwala,damuwar dai bata sake ta ba ,to amma yanzu sai take jin wata irin fargaba da faduwar gaba wanda ta rasa daga ina ne,sai kawai ta shiga jan innalillahiwa'inna ilaihi raji'un,da haka ta samu sassaucin fargaba da faduwar gaban da ya same ta gab da magribar.




Tun bayan tashin sa daga office,yake gwada nomber ta amma a kashe, bangaren su ya shiga dan ganin yadda komai yake kamar yadda ya saba duk lokacin tashin sa daga aiki,dole zai shiga dan ganin wadan da zasu karbi aikin dare, salim ya tambaya ina halima ko ta tafi? Ishaq ya ce" ai rabona da halima tun karfe hadu saura ta ce" min zata shiga shopping moll ta dawo,ina ga dai wuce wa gida ta yi" ok Wazir ya fada yana kiran nomber halima ,ita ma din dai a kashe ,kawai sai ya hakura amma ya ce da su salim anjima su kuma gwada kiran wayarta saboda su tabbatar da lafiyarta.




Haka nan ya kasa bacci ya tasa wayarsa a gaba ,daga ya kira Rahim sai ya kira halima,amma har zuwa wajen goma babu wani labari,dole ya hakura ya danne zuciyarshi.




A gidan su halima kuwa ,mahaifinta ya riga ya san irin aikin da take yi shi yasa bai damuwa da yin daren ta,to amma fa duk da haka ya a damu a yau saboda duk yadda aiki ya riski halima bata haura tara na dare,to yau kuma gashi har goma ta gota,mahaifiyarta wadda suke kira da umma ta ce" Ni dai malam ka kira ogan nasu a ji ko lafiya ina ga sai hankalin mu ya fi kwanciya" da shawarar ta ya yi amfani ya danno kiran yayan haliman ya fara sanar da shi,daga nan shi kuma yaya Usman din ya danna kiran A Wazir.




Kamar almara haka ya ji batun na yayan halima, cikin hanzari ya tashi ya fito yana sanar da shi duk abin da ya faru kamar yadda Ishaq ya sanar da shi.




Kafin wani lokaci su Ishaq da salim ma sun fito an baza neman halima 'yan sanda kuwa ko wane lungu da sako bi suke dan binciko inda Halima take,har lokacin wayar Rahim a kashe take ,kuma koda a kunne take ya sanar da kowa kar wanda ya gaya masa, saboda yasan halin sa haka yake kamar mace nan da nan sai ya ruɗe ya fara koke koke,duk kuwa da jarumtar da yake da ita.




Misalin karfe goma sha biyu na dare a ka tsinto gawar Halima a can bakin wani katon kwalbati in da mafi aksari a can aka fi tsintar gawarwakin da ake yawan kashewa.




Tashin hankali an shige shi a wannan dare, dan ma ba kowa ya san Halima a matsayin yar jarida ba,kasancewarta yar jaridar da take aiki a sirrince,to Halima dai ta yi shahada Allah ya jikanta da Rahma.




A ranar nan sam bacci bai ga idanun Ahmad wazir chibado ba, innawuro babu lallashin da bata yi masa ba amma ko duban inda take baiyi ba,zuciyarsa a cinkushe take da tunani iri daban daban ,shin meye silar mutuwar Halima ? Su waye suka kashe ta? Me ta yi musu ? Wadan nan tambayoyin su suka hana shi rintsawa, tare da wata irin fargaba da hangen rayuwar Rahim da ya ɗauka ya saka a cikin irin wannan aiki mai matukar haɗari.




Sai karfe bakwai Raihan ta farka,a gurguje ta shiga bathroom ta yi wanka tare da brush,sai da ta shirya tsaf sannan ta fito dan ta karya ta wuce office,tun da ta fito take latsa kiran Halima amma sai taji wayar a kashe,dole ta ajiye wayar ta fara karyawa, daidai lokacin taga antyy amarya ta fito cikin shigar dogon hijab har kasa,antyy amarya Barka da safiya" Barka dai Raihan ta faɗa ba tare da ta dubeta ba,antyy amarya ina zuwa haka da sassafe? Zan raka Hajiya goggo ganin likita ne,inna maimuna ma zata ga likita dan haka ki zauna mu dawo sai ki tafi aikin"ok shike nan sai kun dawo"har antyy amarya ta bude kofar fita , Raihan ta jefo mata tambaya da cewa antyy me yake faruwa ne kamar kina cikin damuwa? Ba tare da ta juyo ba ta ce" babu abin da yake faruwa ke dai ki zauna muje mu dawo" Tom sai kun dawo ta faɗa tana kara gwada lambar halima,kafin ta ɗago har antyy amarya ta fice, tana fita wazir ya kirata ,dagawa ta yi bayan sun gaisa tare da yi masa gaisuwa ,ta ɗora da cewa zaka iya karasowa gidan yanzu. Mu mun tafi gidan gaisuwar" ok antyy amarya ganinan amma dai kin hana shi kunna tv ko dan yanzu haka a na kan baza labaran tare da hotunan gawar Halima da kuma wanda take raye"wallahi wazir ban hana shi ba kawai dai kayi sauri nasan ba Lallai ne ya kunna ba tun da nace mishi yanzu zamu dawo" daga nan su kayi sallama.




Mintina goma da fitar antyy amarya Raihan ta shige dakinta,ganin ba kowa yasa ba ta rufe dakin ba sai kawai ta cire kayan da suke matuƙar takura mata ta dawo Raihan dinta ta asali,Masha Allah abin da zamu iya cewa ke nan,ban taba kallon surar Raihan ba sai yanzu saboda bata bada damar hakan, Raihan gata dai yarinya karama wadda har yanzu ko shekaru sha tara bata cika ba,amma sai kira,ko da ike zamu iya cewa Allah ne ya nuna ikon sa ta hanyar ƙawata budurcin Raihan,wanda ko antyy amarya ta na da niyar ci gaba da boye Raihan to kuwa nan gaba kadan tabbas ba zata boyu ba,dan ba kankanuwar sura Ubangiji ya yi mata ba,kai hatta da booms din Raihan abin kallo ne domin kuwa a cike suke kuma masu kyau wadan da baza su taba lalacewa ba,sai dai muce tubarakallah.




Zama ta yi kawai sai hankalinta ya kai kan tv,daukar rimot ta yi tana jin Gara ta kunna taragewa kanta damuwa,tana kunna wa ta dauki wayarta dan sake gwada kiran Halima wanda har yanzu mamakin kashe wayar na Halima take yi.


Fatima y Adam ✍🏽
*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page9 ```






Ɗan tsaki ta yi tare da maida wayar ta ajiye,tunanin buɗe chat din ta yazo kanta hakan yasa ta maida hannu dan daukar wayar,sai kuma labaran da ake watsowa a tashar c nn tv yasa ta fasa daukar wayar tare da zubawa tv din ido zuciyarta na wani irin bugu da sauri kamar wadda ake doka guduma,zaraf ta mike tsaye ganin an nuno hotan Halima lokacin da tana raye da wanda take a mace , jikinta duk jini da alamun harbi,wata irin kara ta saka wanda yayi daidai da shigowar wazir falon ,kuma karar tata ce ta alamta masa inda dakin nata yake,dan haka kai tsaye ya saka kansa zuwa ainahin dakin Rahim wadda a daidai wannan lokaci tuni ta koma asalin RAIHAN dinta.


.....................




Abba yahya da defity gomner tuni suka sanarwa da gwamna abinda ke faruwa,alokacin ma tuni ya riga ya gani a labarai,hankalin su ya yi matukar ta shi ,wanda hakan ya sa suka hada tarin gaggawa,duk wannan abin da yake faruwa sun san cewa daga makiya ne so kawai ake a yi musu sarƙa.


RAIHAN.......


Kuka take yi tun karfin ta tana kuma yin watsi da duk abinda taci karo da shi,cak wazir ya tsaya zuciyar shi na wani irin bugu,zubawa Raihan ido ya yi cike da mamakin kammannin da su kayi da Rahim dan sam zuciyar shi ba ta bashi Rahim din ne ba,kawai dai ya yi tunanin yar uwar antyy amarya ce wadda su ke kama ta sosai da Rahim,ko kuma su din 'yan biyu ne,sai dai bai gama tunanin da yake kan yi ba,su kayi ido hudu da Raihan wadda har ta fara fita a hayyacinta,da wani mugun gudu ta nufoshi tsayawa ta yi a gabanshi tare da kama hannunshi, da gaske Halima ta tafi ta barni da gaske mutuwa ta yi? Da gaske ne wasu ne marasa imani suka kashe mana ita?jin shuru yasa ta fara dawowa hayyacinta wanda take ta fahimci halin shock din da wazir ya shiga,sakin hannunshi ta yi tana mai saurin tattare gashinta da yake ta faman lilo a gadan bayanta,to me yay saura kuma ya riga ya ganta to me zata ƁOYE mai? Cikin sarkewar harshe ya yi dauriyar bude baki ya yi mata tambaya da cewa ina Rahim shi nake NEMA? Matsowa ta yi kusa da shi idanunta na sake cikowa da hawayen dalili biyu,ta ce" Hamma wazir babu Rahim Rahim gaibu ne RAIHAN ita ce gaskiya,duba yake mata me cike da tashin hankali da ruɗu duk da cewa ba zaka taba gane hakan ba,domin kuwa wazir jarumi ne kuma dakakken namiji me cike da tarin nutsuwa da ilhama,dan haka da wuya ka gane rudewar shi,cikin yanayin nasa na kamewa ya ce"ban fahimta ba?ey abin da nake nufi shine Rahim din da kake tunanin akwai shi to babu shi sai dai RAIHAN, Raihan ce kake tare da ita a matsayin RAHIM" .




Jin kamar kafafun shi zasu kasa daukar shi su kuma fallasa halin da yake ciki yasa shi takawa a hankali ya isa bakin gadon ta ya zauna yana mai ci gaba da bin RAIHAN da kallon tuhuma da mamaki,itama cikin sanyin jiki da mutuwar Halima ta saukar mata ta karaso gaban sa tare da durkushewa a gaban sa,ba tare da ta saurare shi ba ta fara bashi labari kamar yadda antyy amarya da Dr suka sanar mata ko mai bata ƁOYE masa ba har zuwa yau da ta riski ta shin hankalin mutuwar Halima.




Zuba mata ido ya yi zuciyar shi cike da mamakin dama Rahim namiji ne tsawan lokacin da yasan shi ,amma bai taba ganewa ba? Ko da yake a kwai wasu lokuta da dama da yake yin wasu abubuwan da yake sawa ya fada zuzzurfan tunani,to amma bai taba kawo cewa ai Rahim din ba namiji ba ne.


Kukan RAIHAN dinne ya dawo da shi tunanin sa, da Allah Hamma wazir kar ka gayawa kowa wlh kai ma na gaya maka ne saboda babu yadda zanyi ka riga ka ganni,kuma nayiwa antyna alkawarin cigaba da boye kaina"cikin tarin nutsuwar shi ya dube ta kana ya ce" kar ki damu Raihan Nima nayi miki alkawarin zan ci gaba da boye sirrin ki ,zan ci gaba da kallon ki a matsayin Rahim har zuwa lokacin da kaddarar ki zata sauya"na gode Wazir su kaji Muryar antyy ta ratso kunnuwan su,gaba daya suka maida hankalin su kan kofar shigowa inda anan antyy amarya take tsaye duk da cewa a lamu sun nuna bata jima da shigowa ba, karasowa tsakiyar dakin ta yi tare da jan Stoll din madubi ta zauna ,kana cikin damuwa ta ce" wazir ka riga kasan sirrin mu,sirrin da babu wani abin yarda ta da ya taba sanin sa,da muna mu biyu muka dawo mu uku gashi yanzu mun dawo mu hudu,ban san kuma waye zai zama cikon na biyar din ba,ina matukar jin tsoran fitowar sirrin nan ba tare da mun shirya ba,nasan cewa Raihan bazata taba dauwama a matsayin da take kai a yanzu ba,to amma ba yanzu nake bukatar hakan ba,wazir ina son RAIHAN,,,,ta faɗa Muryar ta na rawa zuciyarta kuma na son karyewa,da kyar ta daidaita kanta ta ci gaba da cewa ,ji nake kamar zan rasa Raihan wannan abin da ya faru da Halima ya kuma tayar min da hankali matuka da gaske,ina ji kamar ko nets target din mugayen nan Raihan ce"da sauri wazir ya dakatar da ita cikin nutsuwa da son kwantar mata da hankali ya ce"antyy ki dai na wannan batun dan Allah,Ni nayi miki alkawarin cewa babu wanda zai san wacece Raihan a bakina ko a bangarena ,kuma nayi miki alkawarin babu abin da zan bari ya samu Raihan insha Allah bazata wahala ba,zan yi iya yina da taimakon Ubangiji dan ganin na bata kariya,dan haka ki sawa zuciyarki nutsuwa RAIHAN tana tare da ke insha Allah,kuma ki sa aranki cewa babu wanda ya isa yiwa RAIHAN ko mai face da izinin Allah, Allah zai kare ta da ga dukkan me Binta da sharri".


Ajiyar zuciya antyy amarya ta yi kafin cikin samun nutsuwa da maganar wazir ta ce"na gode wazir kuma ina nan ina ci gaba da addu'a har malamai nasa suke taya mu da addu'a da karatun Alqur'ani ko mai zai zo mana da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login