Showing 111001 words to 114000 words out of 189984 words

Chapter 38 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15609

ya shigo hadaddiyar unguwar da gidannasa yake.


Bata Ankara da inda suka dinba sai data ji tsayawansu,cikin nutsuwarsa da kamewa irin wadda ba za ka taba fahimtar tafarfasan da zuciyarsa ke yi ba ya sa hannu ya bude bangarenta ya janyo hannunta kai tsaye kuma ya nufi cikin gidan da ita,kasa yi masa musu ta yi saboda bata da zarrar yin hakan,kaf tunaninta yana irin kalar dizgin da rabi ta yi mata,tana jin zuciiyarta babu dad'i sosai akan abinda ya farun.


Jin sanyi da ƙamshinsa da ya kama dakin tamkar kullum din yana rayuwa cikinsa ne,yasa ta Ankara da cewa har sun shigo dakin,dan dawowa hankalinta ta yi tana bin dakin da kallo,ko mai nasa a nutsu a tsaftace kuma abirgance,haka kuma na musamman wani abinda take gani tare da shi din duk kudinsu sam bata sani se ya zamana tamkar ko mai nasa yi masa ake yi.


Zaunar da ita gefan hadaddiyar gadonsa da taji shimfida ta alfarma ya yi,ji ta yi tamkar yau ne ta fara shigowa dakin saboda yau din ne ta dan yi masa kallon nutsuwa.sanyin tafin tattusan hannunsa da ya sauka kan fuskarta shi ya dawo da ita gayyacinta,se kuma alokacin wasu hawayen masu zafi suka ci gaba da sauka tana kara tunawa da duk zantukan na rabi,zuba mata idanunsa da suke matukar rikitata ta jefa ta cikin halin da take kasa tantance waye ita yayi yana yi mata kallonnnan nashi na kai tsaye me shigewa kanta ba tare da wani shamaki ba.rikicewa ta fara kokarin yi ,cikin sanyi ta yi kasa da kanta tana ci gaba da jin dukkan idanunshi da zuciiyarsa a cikin jikinta dan kame jikinta ta yi saboda rawar da ya soma saboda kusancinsu yar ta zarar dake tsakaninsu kuwa tuni ya haɗeta,a hankali yasa hannu shi ya dago fiskartta wadda har yanzu ba ta daina danshin hawayen da suka yi tsayawa ba,cikin wani irin sanyin jiki ya haɗeta da jikinshi yana sakin siririyar ɓoyayyiyar ajiyar zuciya,da sauri yake jin zuciyarshi na bugawa da wani irin tururin zafinso wanda ya dade da yi masa illa ba tare da yasan shi din ba ne,se kuma a yanzunne yake gane komai ta yadda yake kasa control din kanshi da zuciyarshi akan duk abinda ya rabi Raihan ɗin bare kuma ya shafi ita da kanta,sosai yake jin takaicin rabi da tsanarta dake son mamaye zuciyarshi.


Itama ce kin tsanantar bugun zuciya tare da sanyin jiki da kasala ta shige jikinshi tana shaƙar ƙamahinsa da bayanshi bata taɓa jinsa a tare da wani ba duk tsawon rayuwar da ta yi cikin maza ya'yan manya yan gata masu ji da Naira ko a wannan bangaren tasan shi din na dabanne,ji take tana mantawa da wata rabi bare kuma kalamanta,bata jin ko mi bata ganin komi sai dan Ammi da Abbu jikan innawuro da CHIBADO,wani kasala take ji da sanyin kaunarshi dake bin duk wani loko da sako na jikinta da zuciyarta kai dama duniyarta gaba ɗaya,dago fuskarta ya yi yana mai zuba mata lulu eyes dinshi masu kashe jiki da sakata taji kamar ba a duniyar mutane take ba,maganar shi ta ido da gira yayi mata sarai ta fahimci me yake nufi ita bata iya shurunnan ba shi yasa ta bude bakinta da niyar bashi amsa,amma se me? Sanyin harshenshi da kamshin mauth fesh na kamfanin mint bon ya shige mata kai har can can ga taushin harshensa da ya nemi zautata kamar yau dinne ya fara kissin ɗinta,samun kanta ta yi da maida masa martani ta hanyar bashi wani irin fationality kisses da ya nemi tsatse ruwan kan Chibado,se yake ji tamkar ba a duniyar yake ba,bai taba kisin wata mace a rayuwanshi ba saboda haka bai san ya ake ji idan mace na maida martani kisses din ba,shi dai ya ji a duniyar shi babu baki irin na Raihan babu harshe irin na Raihan kai harda haƙoran ma babu ya nata,a hankali ya fara shafe jikinta da wani irin sanyi kamar wanda ke taba kwai ,jin inda hannunshi ya sauka ya sashi manta kanshi da tuna shi din waye a ego,ya manta waye shi bare jin kanshi da wani kiskilancin shi,duk da cewa da bra a jikinta irin wadda take sawa dan tieting din jikinta ta saje as a male,cikin nutsuwarshi da sam baka gane yana kokarin ficewa hayyaci ne ya dago ta jikinshi kan kafafunshi suka kuma hadewa sosai,sosai ya fara dan cakudata yan son kai hannunsa inda ya ke muradi ta hanyar son jinsu a asalinsu ba cikin kaya ba, kokarin zame rigar cot din da take masa shamaki da naked asalin fatar Raihan ɗin yake,wayarshi ce fara haske wanda ba na farko ba ne,a hankali cikin kasala da jin dan ciwon kai na son mamayarsa ya bude gajiyayyun idanunsa da suka shige ciki ya dan kallo fuskar wayar sai kawai yayi katari da sunan Amminsa baro baro saman screen da din wayar.




Dan furzar da iska ya yi yana dauke idanunshi daga kan wayar,dago fuskar Raihan ya ya yi sai yaga har ta yi bacci, wani irin bacci me cike da nutsuwar zuciya take yi dan haka cikin tattashi da kallaɓawa kamar wata jaririya ya zame cot din jikinta da head scap din da yake rufe asalin kyakkyawar sumarta me tsayi da yawa ga baki kamar rinin dayin yana cire hular gashin ya baje saboda irin me santsin nanne da gazar gazar kamar gashin gira,shafa kan yayi cikin wata lallaɓawan ya cire duka nannauyan kayan jikinnata bai bar mata komai ba sai fara sol din singlet da tiet bra din jikinta gyara mata kwanciya yayi tare da ja mata tattusan doved dinsa da yake ta zuba ƙamahinsa,


Cikin nutsuwarsa ya dawo ya dauki wayar ya fita danyin waya da Ammintasa.




*Ruby*


Ruby kasa zama ta yi a buldin din, ji take kanta yana wani hayaki kamar tana bukatar wani abu,fita ta yi ta nufi Motanta dan komawa gida,karon da suka ci da Surry shine yasa ta ja da baya, take mummunan mafarkinta na jiyan ya shiga dawo mata, ji tayi kamar zata fita a hayyacinta hakan yasa ta yi saurin yin gaba Surry ta biyota a baya a tare suka bar buldin din zuwa can chibado's,haka suka taho kamar kurame, Surry ba ko mai yasa tayi shiru ba sai mamakin yadda rabi bata nemeta ba sannan kuma yanzun bata ga wani alamun tashin hankali a tare da ita ba.


A haka suka isa chibado's ko wacce ta dauki jakarta sannan suka rankaya zuwa bangaren rabin.


Koda suka shiga zama Surry ta yi tana ci gaba da yiwa rabi kallon mamaki ganin yadda take komanta kai tsaye kamar babu wani damuwa cikin rayuwarta,kasa shiru ta yi ta dubi rabin lokacin da take zama kujerar dake fuskantar Surry tana buɗe bottle din ruwan da ta dauko a Fringe,da kyar Surry ta ce", wai ruby lafiyanki kuwa naga babu wani abu da ya nuna kina cikin damuwar abinda ya faru jiya akan labarin Raihan da na kawo miki?karfa ki manta mijinki take aur.........wani irin mugun tari ne ya sarke ruby ruwan da ta sha suna dawowa ta hanci ta baki.......✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page40 ```




Sosai take tari saboda kwarewar da maganar Surry tasa ta yi,da sauri Surry ta taimaka mata har ta samu tarin ya lafa.dago idanunta da suka yi jajur ta yi ta kalli Surry kafin cikin dashewar murya ta ce", Surry ya akayi kikasan mummunan mafarkin da nayi jiya ba tare da na sanar dake ba? Wani mugun kallo Surry ta bi ruby da shi kafin cikin takaici ta ce", No wonder naga kina harkanki kamar me nutsuwa,to bari na kuma tabbatar miki abinda ya faru jiya ba mafarki ba ne zahiri ne kuma da gaske idan zaki nutsu mu sami mafita ki nutsu, dan wallahi idan baki maida hankalinki jikinki ba to kina ruwa tsundum cikin bakin kada idan baki tashi tsaye kan Raihan ba tas zata tsigeki daga dan matsayin da kika samu na aurensa.




Wani irin ja idanunta su kayi tamkar wadda aka zubawa barkono,jin zuciyarta take na wuta dan abinda take ji yafi karfin zafi sai dai wuta,wani irin tsanar Raihan na ninninkuwa a zuciyarta,ko sunan Raihan bata son ji ko me sunan bata so, lallai Raihan ta shammaceta,to me yasa ta boye kanta take amsa sunan namiji? Shin da sanin iyayenta?to ya akayi wazer yasan cewa ita din macece? Ji ta yi kanta na neman bugawa hauka take neman yi dan kanta ba zai iya dauka ba,cikin sauri Surry ta fito da guzurin da ta yo na kwalaben magani har ma da wasu kwayoyin,mikawa ruby ta yi tana cewa karbi wannan kisha zaki samu salama idan baki sha ba zaki iya haukacewa da wannan kalar tashin hankali....kafin Surry ta gama fada ta finciki bottle din maganin ta afa zuwa bakinta ba tare da wani tunani ba, haka kwayoyin ma ta bata su ta shanye tana faman sakin ajiyar zuciya.


A hankali ta fara lumshe idanunta tana ganin Surry bibbiyu,ganin haka yasa Surry ta taimaka mata ta kai ta dakinta,dawowa ta yi ta kwashe ko mai domin ba yanzu ne take son wazer yasan rabi na shaye shaye ba ,da sauran lokaci lokacin da ya zo daidai da cika nata burin bayan ta gama dasu duka.




_________




Tunda ya dawo gida yake faman kaiwa da kawowa, hankalinsa tashe yake akan dawowar yaran abbu don karbar ragamar comfanis,to amma yanzu me ya kamata ya yi ? Tabbas idan ya yi shiru ya zuba ido zai yi asarar tsawon shekarun da ya jima yana son cika burinsa ,wallahi ba zai yuwu ba,wayarshi ya janyo ya daddanna wasu nombobi jim kadan aka daga,ba tare da ya saurari gaisuwar da ake masa ba ya ce", lallai ina son a saka min ido akan iyalan Alh Chibado ina so ranar da zasu dawo kafin su ƙaraso gida gaba dayansu a gama min dasu duk wanda ya rabe su shima a hada da shi", ok sir aka fada ta can ɓangaren,kashe wayar ya yi yana huci kamar wani mayunwancin zaki,shi sam bai ga amfanin sako matar nan cikin tafiyarsa ba,se yanzu ne yayi tunanin hakan,to amma yasan tabbas watarana zata yi masa rana,ko dan kusancin da suke dashi da matar WAZEER.




_______


Cikin fushi tsohuwa ta nuna shuda da sandar tsafin dake hannunta bakinta na wani irin fitar da huci me tsananin zafi ta ce", shuda tabbas badan karin da ka kawo mana ba da yanzu hukuncin jini ya hau kanka saboda bamu taba aiki me tsauri wanda yaja mana lokaci irin naka ba,da ace a iya mulki abin naka ya tsaya da yanzu an wuce gurin to amma wannan tsinannan ahlin da ka sako a ciki shine abinda yake tokare duk wata sa'armu,dan haka dole yanzu mu fara shan jinin daya daga cikin alhlin Alhaji Muhammad nuur saboda shine matakin nasararka akan komai kuma shine zai yaye duhun da ya lullube idanunmu muka kasa ganin ko mai akan al'amarin gidan, dan haka kaje mune za muyi zaɓin wanda zamu dauka cikin yaran matansa guda biyu ", daga haka komai ya shafe tamkar ba ayi ruwansu a gurin ba.




*Shugaban jam'iya*




Duk da ya samu tabbacin babu wata damuwa a bayan sakin abokansa hakan baisa ya kwantar da hankalinsa dari bisa dari ba,shi dai yana ji ajikinsa ba shike nan ba dole akwai wata ɓoyayyiyar manufa a bayan sakin su da akayi,dan haka a ƁOYE ya shiga nazari da binciken ta inda aka haihu a ragaya.




Abangaren su Alh ja'e da su sanater kuwa kwantar da hankalin su su kayi sukanci gaba da sharholiyarsu.ba komai ne yasa su hakan ba sai kawai tabbacin da suka samu ta ɓoyayyiyar wasikar email akan cewa su kwantar da hankalinsu akan wannan video domin tuni an riga da anbatar da videon babu shi,duk da cewa sun so rudewa da wannan lamari to amma da su kayi wani nazari akan yadda Rahim ya kasa fitar da videon tuni suka watsar da tunanin komai,saboda acewarsu da ace Rahim yana da video nan to tabbas da yanzu ya tona musu asari ko dan ganin yadda aka kamasu kuma aka sake su ba tare da anyi musu ko wace irin tuhuma ba,sun tabbatar da cewa lallai akwai wani a cikinsu da yake da babbar alfarma,shi kuma wanda ke yi musu duk wannan gatan sun ƙaddara cewa yana daga cikin manyan mutanen da ba zaiso a sanshi da daurewa irinsu kugu ba, wannan ke nan.




__________




Mama murja ce zaune a falo kana ganinta zaka tabbatar da cewa hankalinta ba a wani kwance yake ba,tunda ta san cewa akwai me bibiyar rayuwar yaranta shike nan bacci ya gagara idanunta,gashi ta kasa gayawa Abbie tana tsoran kar allura ta tono garma tunda suma ba gaskiyar suke kullawa ba,sai yanzu ta gane a she karyar son kudi take tunda gashi wata yar barazana ta na neman hanata bacci da kwanciyar hankali,ita yanzu ji take ta hakura da komai in dai za a bar mata yaranta sanyin idaniyarta,karar wayarta ce ta katse mata tunaninta, a dan zabure ta kalli wayartata dake gefanta zubawa wayar ido ta yi tana mai jin wani irin bugun zuciya ga wani irin rawa da jikinta ya fara kamar wadda ake bugawa ganga.


Saida wayar ta yi ringing sau uku kafin ta kai hannunta dake rawa ta daga tana karawa a kunnenta Affan yana shigowa,ganin yanayinsa yasa jikinta ya kara tsananta rawa kafin affan yayi magana taji wani irin kuka na tashin hankali daga cikin wayar,bakinta na rawa ta ce", waye? Zainab matar rufa'i dake kan wayar ta kuma saka wani mahaukacin kuka tana cewa mama shike nan ya mutu rufa'i Faisal ya zama Maraya na zama me takaba", wayar ce ta zame daga hannun mama idanunta na kallon affan bibbiyu Muryar Zainab nayi mata amsa kuwa cikin kunnuwanta,kafin affan ya Ankara ta zube kamar matacciya.




*Wazir*




A hankali take bude idanunta,har ta bude su gaba daya,bin dakin ta shiga yi da kallo sai kuma abinda ya faru ya shiga dawo mata,da sauri ta yaye duvet din da ya rufe ta dashi tana duba jikinta da babu kaya,dafe kirjinta ta yi tana fidda manyan idanunta waje sai kuma ta shiga duba dakin tana neman inda zata Ganshi,ganin baya dakin yasa ta ɗan saki ajiyar zuciya amma ba wai ta gamsu cewa bai ganta ba,tunda alamu sun nuna shine ya cire mata kaya.




A hankali ta sauko daga gadon tana kara kallon jikinta tana ƙunkuni da jin takaici har cikin ranta,sai da tazo tsakiyar dakin dan shigewa toilet kawai taji bude kofa da shigowarsa duk alokaci daya yana fidda sallama can ƙasar makoshinsa,da sauri ta juyo tana mai saka hannayenta duka tana kalmashe kirjinta,ƙunkuni ta shiga yi tana hade fararen ƙafafunta guri daya,haka kawai an samu ancirewa mutum kaya dan anga yana bacci," wani tunanine yazo ranta wanda take ta kuma zaro ido tare da karasawa inda yake tun shigowarsa a tsaye yana kallon yadda take yi din,plz Hamma wazir me kayi min? Ka kalleni ko? Ka taba Ni ko? Ina ka taba dan Allah? Ta faɗa tana fashewa da kukan tsoro, wani munafikin Murmushi ya sake yana mai riko hannuwanta duka biyun kafin cikin deep voice dinsa ya ce", haba ke kam wannan fa kawai na gani da wannan ya fada yana kai hannunsa saman kirjinta kamar zai taba,ai cikin zafin nama ta manne da kirjinsa dan hana shi wannan damar,sai kuma cikin rishin kukan sakalci ta ce", Ni kam me yasa kayi hakan? Ta faɗa tana dan bugun kirjinsa", rike hannun da take bugunsa dashi yayi sannan a hankali ya kai bakinsa kunnenta sai da ya fara sakin mata hucin numfashinsa sannan cikin deep voice dinshi me tsinka jinin jikinta ya ce", saboda halalne a gare Ni,oh wai sai yanzu kike tunawa da baki so bayan tun ɗazu kin gama tsotsewa Ammi danta baki bar masa ko miyan haɗiya ba", ai da wani irin sauri ta fizge daga jikinshi ta faɗa bath da gudu tana sharbar hawayen kunyar da wazir ya gama bata.




Murmushin dake kara masa kyau da kwarjini ya sake yana tsirawa bayanta ido har ta shige bath din,shafa sumar kanshi me kyalli da taushi yayi kafin ya dawo da hannun saitin zuciyarshi yana saurarar bugun da take yi da dan sauri,cije lips din shi yayi yana mai ambatan sunanta a hankali can kasan makoshinsa cikin wani salo na jan hankali kai ka ce RAIHAN ɗin na gefansa.




Fuskanta yayi idan ba fita yayi ba to baza ta shirya ba,har zai fita sai kuma ya koma jikin kofar bath din ya dan yi knock kafin ya ce", fitowarki da wuri shine komawarki gida idan baki fito nan da minti ɗaya ba wlh sai dai ki kwana",daga haka ya bar kofar ya fita daga dakin gaba ɗaya.




Aiko ko rufe kofa bai gama yi ba sai gata ta fito tana ɗigar ruwa dan ko rigar bath bata saka ba sai guntun showel din da ta fizgo ta dan daura shi iya saman kirjinta dan da alama ma dai na tsane kai ne.




Yana jinta dan haka ya dan saki Murmushi kawai yana mai karasa ficewa dan bata damar shiryawa a nutse.




Cikin mitunan da basu wuce goma ba ta fito bayan ta maida kayanta da tazo da su ba dan ranta ya so ba,kallo daya ya yi mata ya mike fuskar nan babu yabo babu fallasa yayi gaba,dan tura karamin bakinta ta yi tana harararshi kasa_kasa,binsa ta yi a lokacin har ya shige mota hakan yasa itama tayi saurin shiga ya tayar suka bar unguwar gaba daya.




Muhammad nur..Hause...




Da gudu Affan ya tarairayota yana kiran sunanta kamar makoshinsa zai tsage,sai dai babu alamun tasan yanayi,da karfi ya shiga kwalawa me aikinta kira,wanda kiran ya jawo hankalin momy Hanne da ta kasa samun nutsuwar zuciya kullum a firgice take tana jiran jin ta inda masifar da ake son jefa su bullowa,a zabure ta tashi daga kujerar falonta dake bangarenta kasancewar sunfi kusa da mama murjar shi yasa iska ta debo Muryar Affan ta kawo mata kuma dama hankalinta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login