Showing 69001 words to 72000 words out of 189984 words

Chapter 24 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15605

kamala irin ta dattijon kwarai ,ya gama kallon fuskar kowa ya kuma karance su tsaf,duk da cewa ba wai ya karanci zuciyon su ba ne,kawai dai ya karanto tsoro sosai a cikin idanun su,sai da ya yi gyaran murya kana cikin nutsuwarsa ya fara magana da cewa,ya kamata ace zuwa yanzu ko mai yazo karshe ,ina so ku sani cewa mulki ba hauka ba ne,dan haka ya kamata a cikin mu nan idan da wanda yake da hannu a cikin wannan lamari to ya mika kansa ga jami ai,tun kafin wannan mutumin ya gano ko su waye,ina tabbatar muku da cewa idan haka ta faru wlh kashin kowa ya bushe daga masu ruwan har marasa ruwan,dan fa al'umma ba zata bar su ba",shugan jam'iya ya ɗora da cewa wannan haka.yake ranka ya dade domin kuwa kafin jam'i ai su yi wani abu jama ar gari sun babbakawa gidajen mu wuta,dan haka dan Allah idan muna da su a cikin mu to su yi kokarin fidda kansu tun kafin abin ya zama wani iri".




Abba yahya dake zaune gefan da dufuty yake ,ya zubawa Alhji Garba ur exsellency ido,kallo ne da shi kadai yasan manufarsa,gyaran murya ya yi kana ya ce",tabbas ur exsellency maganar ka haka take,dan ko Ni nan na samu wanda yake aikata wannan abun wlh sai na sare masa kai ko waye shi.




Nan da nan fa hayaniya ta barke har baka jin abinda wani ke cewa,kowa fada yake da rantsuwa akan bai san wannan lamari ba,da haka taron ya watse babu wani ci gaba.




TSOHUWA.......


Wani irin huci ne ke fitowa daga bakinta tare da wani irin hayaki wanda ke turnuke ilahirin dakin tsafin,cikin hucin bakin ciki ta ce",kai dudu zuwanka gare mu babu alheri me yasa haka bata faru a baya ba sai Yanzu?


Me yasa na kasa ganin wannan hatsabibin yaron?
Ta yaya akai ya gano wannan sirrin da muka riga muka binne da kuma tabbacin wanda ya tono shi sai jini ya sha jinin sa?




Tabbas akwai ƙura ta faɗa tana wata irin girgiza me cike da tsananin bacin rai,su kansu yan kungiyar sun ga bacin ran tsohuwa wanda basu taba gani ba iya kafuwar kungiyar,bude idanunta da su kayi jajur kamar jini ta yi tare da nuna shuda, ta ce"lallai ya kamata ka yi wani abun a bangaren mutane lallai muna son sanin wannan dan jaridar,zan yi bincike iya bincike ba za ku kara jina ba har sai na gano waye wannan matsiyacin dan jaridar, dif suka watse daga gurin kamar yadda ta bace ,duk zuciyoyin su cike da damuwa,dan abin da ya fi karfin tsohuwa ba karamin babba bane.........✍🏽


[12/21, 12:40] : *Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page23 ```






Abba yahya yana kan hanyar shi ta komawa gida wayar ur exsellency ta shigo masa,dagawa ya yi tare da yin sallama cikin girmamawa kamar yadda suka saba yiwa junansu,daga daya bangaren ur exsellency ya ce da Abba yahya,idan ya samu lokaci zuwa anjima da dare ya dawo akwai maganar da zasu yi iya su uku kawai wato shi da dufuty yake son gani.ok Allah ya kaimu ya fada suna aje wayar lokaci ɗaya.




Jinjina kai kawai Abba yahya yake zuciyarshi cike da kuma da mugun takaicin dan uwansa da ya kasa gane waye amininsa,to amma dai ko meye shine zai zama sanadin binne ur exsellency din da ransa domin har ya tabbatar da zargin da yake masa akan cin amanar dan uwansa da kuma cin amanar jiharsa, tabbas ba zai barshi ba.da wannan tunanin ya karasa gida.


..............


Haka nan aunty amarya ta tsinci kanta cikin faduwar gaba,hakan yasa take ta gwada kiran wayar Raihan amma ba a daga ba,hankalin tane ya kuma tashi cikin rawar jiki ta kuma sake gwada kiran,ajiyar zuciya ta sauke jin an daga sai dai kuma a maimakon ta ji Muryar Raihan sai taji Muryar namiji, innalillahiwa'inna ilaihi raji'un ta shiga maimaitawa zuciyarta na wani bugu na tsananin tashin hankali cikin rawar baki ta ce",ina me wayar?


A maimakon amsa sai kawai ta ji ansheke da wata muguwar dariya kafin daga bisani a tsagaita da
dariyar,cikin Muryar dake nuna ko waye yana cikin
nishadi ya ce"lamratu ina fatan kin shiryawa zuciyar ki akan rashin gudan jinin ki? Da karfi zuciyar Tata ta yi wani irin bugu har sai da ta dafe saitin zuciyarta,ya Allah ta ta fada tana mai runtse idanunta da take Ji tamkar za su fado saboda yaji,ya dai kin kasa magana ne? To babu damuwa yanzu dai gamu ga RAIHAN sai ki gaya mana abin da ya yi saura?wani mummunan jiri ne ya debeta badan tana zaune ba tabbas sai ya yi mata mummunan illah.


Da kyar ta samu bakinta ya iya furta ,wacece RAIHAN?


Cikin gatsali ya maida mata da cewa oh Rahim zan ce miki ba Raihan ba,tun da kema kin maida kanki kidahuma kamar yadda kika maida mutane,idan kuma har yanzu baki gane ba,to ina nufin kyakkyawar 'yarki da kika maida namiji Saboda son tsira da rayuwarta. wanda kuma hakan da kika yi Ni a gare Ni ya fi komai dadi a wajena,domin kin kawar min da hankalin sauran masu bibiyarta ,kin ga zanyi shagali na Ni kadai ke nan ba tare da sauran masu hari sun batan lissafi ba,kar ki dauka cewa zan tona wannan sirrin,a'a ba zan tona ba saboda nima yana min amfani,yanzu dai ga Raihan nan zan sake ta taho gida duk da cewa na fahimci ba Ni kadai nake bibiyar ta ba,amma dai ina da tabbacin cewa wani abu ne daban ba akan Ni wanda nake nema ba ne,na barki lafiya auntyn RAIHAN...daga haka kit ya kashe wayar yana mai kyalkyalewa da dariya,wayar ya mikawa wata budurwa yana cewa ku maida ita inda kuka dauko ta kar ku bude mata ido bare ku bari taga inda aka kawo ta",Yes oga ta fada tare da fita daga dakin.




Tana zuwa ta kama Raihan da bata ma san inda hankalinta yake ba,dan tuni ta dade da sumewa.




Wani irin kakkauran miyau aunty amarya ta hadiye tana mai jin wani irin tashin hankali da bata taba ji ba a rayuwarta,to ke nan ya kayi suka gano? Wane wannan ɗin? Shin wa zata zarga?




Tana shirin sakin wani azababban kuka aka turo kofar aka shigo,kutt ta hadiye kukan lokaci daya ta nemo nutsuwarta da ta kasa zama akan fuskarta,zuba mata ido abbie ya yi kafin ya taka zuwa bakin madubi yana cewa ,duk lissafin me lissafi sai ya samu Wanda ya fi shi iyawa sannan shi buwayi gagara misali ba a yi masa wayo don duk dabarar ka akan kar ya jarrabe ka idan ya so sai ya yi ikon sa akan ka.dan haka damuwa ba ita ce mafita ba tuba da komawa turbar gaskiya shine daidai,wata kila hakan yasa Allah ya dubi bawansa da bai ji ba bai kuma gani ba ya taimake shi ya ƙare shi daga mummunan ƙaddara", yana zuwa anan amaganarsa ya dauki abinda zai dauka ya fice ya bar aunty amarya cikin wani sabon tashin hankalin da ruɗani me birkita ƙwaƙwalwa.




Shin me maganganun abul Rahim suke nufi?


Wane sako yake son isar min?


Dan kuwa tabbas duk wanda ya ji maganganun nan zai tabbatar da cewa akwai gugar zana.


Wata zuciyar ta ce",kawai ya fahimci kwana biyu kina cikin damuwa shi yasa yake miki nasiha ta wani sigar dan tayi saurin fahimta, ta gamsu da wannan tunanin dan haka sai ta shiga tunanin mafita da inda zata gano Raihan ba tare da kowa ya sani ba.




Lokacin da Abbie ya koma falon baffa inda suke tare da wazir tun zuwansa tambayar da baffa ya yi masa na cewar ina Rahim shi ya sare masa gwiwa.duk da yasan cewa ba lallai ne baffan yasan Rahim ya dawo ba in dai ba shigowa sashen nasa ya yi ba, wannan dan nazarin da ya yi ne ya bashi kwarin gwiwar cewa ai Rahim ya riga shi zuwa gidan.abbie ya tashi ne dan ɗaukowa wazir katin daurin aurensa da Abbu ya kawo masa,a cewarsa ya bawa rahim ya rabawa ma aikata, tunda shi wazir din ba zai yi ba,shi kuma Abbie ya ce dole a bawa wazir din dan ba zai rasa wadan da zai bawa katin ba.shi yasa ya karba ya ce "shi zai bashi da hannun sa yasan ba zaiki karba ba.


Wajen dauko masa katin ne ya tarar da yanayin da aunty amarya ke ciki,shine har ya tsaya ya danyi mata nasiha.






Zama ya yi yana cewa wani abu ya dauke mun hankali ban duba Rahim din ba,amma bari na kira shi a waya ko zan same shi, shuru wazir ya yi ba tare da ya dakatar da Abbie din ba,tun da shi ya kira wayar wajen sau goma a kashe.


Wayar bata shiga ba cewar abbie yana duban wazir da ya ke zaune a nutsen shi,fuskar nan a kame babu alamun wani abu na taba zuciyar shi.




Baffa ya dan yi gyaran murya ya ce"ko ya kashe wayar? kasan haka yake da son kashe waya lokaci lokaci",shi dai wazir bai iya cewa komai ba ,amma tabbas ba zai bar gidan ba har sai yaga dawowar RAIHAN.




A nan shima Abba yahya ya dawo ya same su zama ya yi yana amsa gaisuuwar A wazir cikin nutsuwa da mutumtawa.




Tun suna jira a nutse har hankalinsu ya fara tashi, Abba yahya ya kira inna maimuna a waya ya tambayeta ko Rahim yana bangarensu,ta ce baya nan,daga nan itama tasan abinda ke faruwa, sai gata a falon Baffa hankali tashe kamar ance ba za a ga Rahim din ba.




A nan suka ci gaba da zaman jiran tsammani har aunty amarya ma da ƙaraso yanzu,fuska jajir alamun taci kuka ta koshi.


.................




Fitowar shugaban jam'iya daga wajen taro,kai tsaye gidan haɗuwar su na sirri ya nufa,a can ya tarar da su Dr sanate tare da alhaji sale,nan suka shiga tattauna abin da yake cizon ransu,tashin hankalin su bai wuce ace an dora wannan zargin akansu ba to amma idan suka tuna cewa dole sai anyi bincike sai hankalin su ya dan kwanta,duk da kuwa sun san cewa suma suna ruwa.




Ya zamu yi da batun kashe wannan yaron?,


Cewar Dr da rahim ya fi tsaya masa a rai, Alh sale ya ce"Ni ina ganin kawai mu kashe shi ko ma huta da ɗaya",shugaban jam'iya ya ce" babu yadda za ayi mu kashe shi ba tare da mun karbi video nan ba,fitar da video nan tamkar tashin alkiyamar mu ne,saboda duk alhakin abinda yake faruwa mu za mu dauka,Dr ya ce",yanzu goje ya tabbatar min da cewa suna gab da kama shi ,sai dai kuma wasu sun riga su dauke shi,sun yi niyar binsu gidan ,amma sai na hana su na ce su dakata idan suka ga basu sake shi nan da wasu mintoci ba,su shiga kawai su dauko shi ko tataya",wayar shi ce ta yi kara ya daga yana cewa goje kun taho da shi?yes hakan ya yi sai kun karaso",dariya ya yi bayan ya kashe wayar yana cewa,wadan da suka dauke shi sun fito da shi a sume ,sun kuma mayar da shi inda suka dauko shi,suna tafiya su kuma su goje suka dauko shi.




Lokacin da su goje suka saka Rahim a mota akan idanun sury ne dan haka ta yi amfani da wannan damar wajen kara kusanta kanta da Rahim ɗin,dan alamu dai sun nuna cewa ba hannun mutanen kirki ya shiga ba.dabarar kiran 'yan sanda ne ya zo kanta,dan haka cikin sauri ta yi kiran bayan ta hau mashin ɗin a daidaita.




Kasancewar yan sanda suna kewaye da ko ina na lungu da sakon garin,shi yasa Surry na fadar nomber motar suka gane cikin lokaci kankani suka kama su goje,da sauri suryy ta fito daga a daidaita tare dsp Haidar suka saka Rahim a cikin nafef su ka wuce har Haidar ɗin.




A hankali wazir ya mike ya na duba agogon dake saƙale jikin tsintsiyar hannunsa,ɗan duban Abbie ya yi cikin nutsuwarsa ya ce"ya kamata mu fita tun da har yanzu babu wani labari",tun dazu dama kawai hakuri yake saboda abbie dake dakatar da shi,amma yanzu kam ba ya jin zai iya tsayawa jira,su ba sa ganewa ne amma sam hankalinsa ba a kwance yake ba.


Aunty amarya ma da take jinta tamkar akan kaya tayi saurin miƙewa tare da cewa gaskiya zama bai ganmu ba,Rahim fa har yanzu yaro ne sannan ga irin aikin sa wanda yake cike da haɗari,dukan su miƙewa su kayi su ka fita har Hajiya goggo da ta fara daga musu hankali tun dazun.sai gashi gaba daya mutanen gidan sun fito ,abin da ya yi matukar bawa aunty amarya mamaki,mutanen da kome za ayi in dai akan batunta da na Rahim ne ba za ka ga kafar ko dayansu ba,daga su har surukan su idan ka ɗauke matar hamma idi,kallon su kawai ta dinga yi cike da nazarin su.




Wazir yana kokarin shiga mota shida Abba yahya da hamma idi da dawowar sa ke nan,sai ga shigowar dan sahu nan har cikin gate ,hatta da securityn gidan gaba dayan su sun fita neman Rahim din da lokaci daya suka ji maganar batannashi.




Kusan dukansu suka nufi a daidaita da suka fahimci Rahim ne a ciki,suryy bata da matsala ko da ace wazir ya ganta tunda tasan bai santa ba,dan ko lokutan da suke haduwa a gidansu tana gaida shi ba amsawa yake ba bare ya kalle ta,shi yasa kai tsaye ta fito a matsayin wadda ta taimakawa Rahim.




Dsp Haidar ya bawa A wazir hannu tare da dukawa ya gaida Abba yahya da Baffa da Abbie,daga nan ya shiga basu bayanai akan komai kamar yadda Surry ta faɗa yadda abin ya faru,harma da machine din sa da aka taho da shi.


Shi wazir ma bai saurari bayanan ba,tuni ya dauki Raihan cak ya yi sashen aunty amarya da ita.


A hankali ya kwantar da ita saman lallausar katifarta,dan zuba mata ido ya yi har Saida yaji motsin antyy amarya da ta shigo da ruwa,Hajiya goggo da Inna maimuna na bayanta fuskokinsu cike da jimami akan abinda ya faru,Hajiya goggo kam faɗa take akan ita fa sai Rahim ya daina wannan aikin kar ake a kashe mata jika babu gaira ba sabar.




Da kyar Abba yahya ya rarrashi Hajiya daga mitar da take yi,ya ce"da hamma idi ya rakata bangarenta,shi dama baffa bai cika fitowa ba saboda matsalar kafa.




Ba dan Allah ba sai dan Abbie,su mama murja da surukansu ,suka zo duba Raihan ɗin,wadda ke sume har yanzu bata farfaɗo ba.




Sai da kowa ya fice ,saura wazir da suryy da taƙi tafiya,sai kuma Abbie da aunty amarya,abbie ne ya ce" da suryy yarinya kema ki tafi gida kar a nemeki,mun gode Sosai da taimakonki", sunkuyar da kai ta yi kamar wata mutuniyar kirki,ta ce"shi ke nan Abba in sha Allah
Gobe zan dawo na duba jikin nasa, Allah ya kiyaye gaba,"da Amin suka amsa amma bakin abbie da aunty amarya kawai ta ji,shi kuwa uban yan wulakacin har yanzu bata jin ya yi mata cikakken kallo daya kai tun shigowarta gidanma bata ji ko da tarinsa ba bare yayi magana.ƙwafa ta yi can kasan zuciyarta kafin ta mike tana mai yiwa Rahim fatan samun lafiya har waje aunty amarya ta rakata.




Wlh sai na gano ko ma meye kuke boyewa,sai na cikawa Ruby alkawarinta,ta faɗa dai dai lokacin da security ya bude mata kofar sashen ta fita.


A hankali Abbie ya dawo da dubansa kan wazir da ke tsaye saman kan Raihan idanun shi akanta,tamkar wanda a aka bawa gadinta.


Abi ya ce" ya kamata ace ya farka yanzu, ko za a gwada zuba masa ruwa?


Da sauri aunty amarya ta kawo ruwan robar da ke hannunta,karba wazir din ya yi,ya dan zuba a hannun sa kana ya sunkuya a hankali ya shafa mata a fuskar,bai sauke hannunshi ba,har sai da yaji ta kawo nannauyan numfashi ta ajiye,kafin kuma a hankali ta shiga bude idanunta da suka dan shige ciki. akansa idanunta suka fara sauka,saurin rufe idon ta yi tana tunanin ko mafarki ta ke,tunani ta shiga yi,sai dai ta gagara tuna komai bayan abinda ya faru a office da fitowar da ta yi sai haɗuwar ta da suryy,bayan haka ta kasa tuna komai.




Maida kallonta ta yi kan Abi dinta,cikin raunin murya wanda ke nuni da halin da zuciyarta ke ciki, ta ce "Abi me ya faru da Ni ne?.




Kama hannunta ya yi yana mai jin wani a bu har cikin ranshi,ya ce"babu komai Rahim ,amma dai yanzu ina so ka tabbatar min babu abin da yake damunka,"jin jina kai ta yi tana mai ɗan lumshe idanunta da take jin sunyi mata nauyi,aunty amarya za ta yi magana,abbie ya yi mata alamun ta yi shiru dan haka nan ya ji baya son duk wani abu da zata furta a wajen.


Cikin kamewarshi ya dan dubi a gogon hannunshi ya ce"Abbie Ni zan wuce Allah ya bashi lafiya",Amin duka suka amsa, Abbie ya ce" ina so kayi saurin raba katin daurin auren nan,saboda ba mu da lokaci masu yawa kaji ko,in sha Allah Abbie zanyi yadda ka ce",daga haka ya fita daga dakin sai dai yana jin yadda idanun RAIHAN suke kanshi.






Yana fita ta lumshe idanunta da suke kan bayanshi,tana binshi da kallon da ita kanta ba tace ga ma'anarsa ba.


Samun kanta ta yi da Jefawa Abbie tambaya,ABBIE.daurin auren waye za ayi?


Kai tsaye ya bata amsa da cewa daurin auren abokinka kuma ubangidanka,ko baka sani ba? Abbie ya kare ba shi amsar da tambaya,bata ce komai ba sai rufe idanunta da ta yi tana kokawa da zuciyarta da numfashinta kai da duk wani abu ma dake motsi a jikinta,aunty amarya ta ce" Rahim ka ta shi ka yi wanka ka yi salla zanje na kawo maka abinci kaji,sam Raihan bata gane abinda auntyyn ke fada,har suka fita daga dakin ma bata sani ba,kuma bata yi yunkurin yin wani abu daga cikin abinda auntyyn ta lissafa mata ba.




Karshe dai har sai da auntyyn ta dawo ta taimaka mata da kanta ta kimtsa,ita kanta auntyyn bata da wata mutsuwa shi yasa ta kasa tantance halin da Raihan din ke ciki.




Sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login