Showing 51001 words to 54000 words out of 189984 words

Chapter 18 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15614

dai daga karshe yadda abin ya kasance dole dai ya dawo gidan da baya so kuma ya rike kamfanin abin da dai baya so ɗin,ko meye dalilin kun hakan oho sai a gaba za mu iya ji ,to ko kuma yanzu ya saduda ne tun da takardun nashi sunki bashi abin da yake so ɗin oho.




Wazir a cikin masallacin ya bar su ya fito dan ya danyi bukatunshi kafin lokacin Isha i,tunda yau din bai samu dawowa da wuri ba,




Sannu kawai ya ce"da innawuro ya haye samansa cikin kara tsuke tsukakkiyar fuskar shi da babu alamun fara a ko ta kwabo,gyatsine fuska innawuro ta yi tana bin shi da kallon banza ta ce,wlh aure ne kamar anyi angama fushinka babu abin da zai tsinana"yaji ta sarai amma sai bai nuna hakan ba ya yi shigewarshi koridon da zai kaishi asalin falon shi,


Wanka ya yi tare da yin alwala ,cikin dan gaggawa ya goga turaren shi na gabbon ya taje lallausar suman shi ta asalin Fulani,blue din jallabiya ya saka mai tsantsi sai ƙyalli take zubawa ,ta kwanta luf a jikin shi ta fidda kirar shi ta karfaffan namiji me cikakken zati,silifas ya saka me taushi a kafarshi da kamar baya taka ta akan kasa,da sauri ya fice daga dakin jin ana ƙoƙarin tada sallar Isha'i.




Muhammad nurr hause.....




Zaune suke gaba dayansu a dining table,Dan sun kuma samun karin Hamma idi,duk kuwa irin fadan da mama ke mishi akan shishshigewar da yake yiwa aunty amarya da ahlin nata,amma shi ko ajikin sa,kansa tsaye yake yin komai nashi,dan wani sakewar da yake a ɓangare antyy amarya ko avangaren nasu ne iya haka zaiyi.




Sai da suka gama cin lafiyayyan girkin Aunty amarya,kana suka dawo falo gaba dayan su, Raihan ce ta tsaya taya sahura kwashe kayan da su kayi amfani da shi dan kaiwa kiching.




Kamar daga sama RAIHAN taji tambayar da Abbie yake yiwa aunty amarya,ya ce"Ramla wai me yasa kike son dawo min da yarona dan daudu"wata irin zabura Anty amarya ta yi tare da duban inda Raihan ta yi tsayuwar yan sanda,sai ta samu kanta da rikicewa da wadannan tambayoyin da abbie ya tsiri yi mata su daga jiya zuwa yau,bayan bai san halin da yake sa ta aciki ba duk lokacin da ya yi mata tambaya makamanciyar wannan,a hankali Raihan ta sulale tabar wajen,abin da kawai ta yankewa kanta shine daina zama tare da Abbie tun da hakan yana neman sawa Ummin ta hawan jini,dan ta tabbata cewa wadannan tambayoyin yana yin sune saboda kula da almuranta domin cike gurbin nesa ta kansa da su a baya haka kuma tasan tambayoyin suna taba zuciyar auntynta ta matuka da gaske,shigewa ta yi dakin ta tana cewa Hamma idi sai da safe a kwai wani dan aiki da za ta yi kafin gobe,jinjina kanshi ya yi a hankali.dan hankalinshi gaba daya yana kan kallon kwallon da ya sa a tashar aljazira.


Juyawa ta yi gun abbie cikin basarwa ta ce" abbie good night idan kuma na fito shike nan,haka ta yiwa aunty tana karasa shigewa dakinta ,tare da sakin ajiyar zuciya.


Zama ta yi a bakin gadon ta saitin madubi tana ƙara kallon kanta kamar kullum tun kafin tasan kanta a matsayin mace,idanuntane suka cika da kwalla, idan tace bata damuwa akan yanayin da rayuwarta ke ciki tabbas ta yi karya,sai dai tana matuƙar ƙoƙari gurin ganin ta yakice al'amuran da suke damun ranta,ba dan komai ba sai dan auntynta da tayiwa alkawari,share hawayen fuskarta ta yi tana jin wani abu na taso mata mai karfi da sanya gwiwa sacewa,shin yaya zata yi da abin da yake neman fin karfin ta,haka nan zata ci gaba da rayuwa a matsayin namiji ke nan Dan kawai kar aka sheta ??




Anya kuwa zata iya ci gaba da boye kanta??


Shin ƙaddararta ce zama a matsayin namiji ko kuma kaddarar mutuwar ce akan zaman ta a matsayin mace??


Anya kuwa babu sabon Allah akan wannan lamarin???


Hannu tasa ta goge fuskarta da ta yi ja saboda damuwa,




Ita ka dai tasan yawan damuwar ta,ita kadai tasan yawan dafin dake cikin zuciyarta..




Raihan kiyi addu'a kawai akan duk abin da zai zama alkhairi a rayuwar ki Allah ya tabbatar miki da shi, wannan shine amma damuwa da tunani ba na ki bane ,kina yarinyar ki dake damuwa ta rugurguza rayuwar ki, dalla share komai ki manta ki ci gaba da walwalar ki ,ki kuma zubawa sarautar Allah idanu duk yadda ya yi dake shine alkhairi,wata ɓangare na ingantacciyar zuciyar ta ne ke bata wannan shawarar,miƙewa ta yi tana mai jin kwarin gwiwa akan komai na rayuwar ta.




A bangaren abi da aunty amarya kuwa,zuba mata ido ya yi bayan shigewar Raihan daki,ganin bata ce mishi komai ba ya dan juya ya dubi , Idris wanda gaba daya hankalin shi da nutsuwar shi suke kan kallon boll,dawo da duban shi kan aunty amarya ya yi tare da dan yin gyaran murya,hakanne yasa ta juyowa ta kalle shi fuskarta babu alamun walwala,ɗage mata gira yayi tare da cewa ,to me kuma nayi ake wannan hade ran daga tambaya kawai,dan hararar shi ta yi tana cewa me kake nufi dan Rahim yana namiji bazan sashi aiki ba?




A'a Ni ba haka nake nufi ba,amma a yi hakuri a maida wukar" ya fada cikin son maida abin wasa,itama Murmushin ta yi tana dan satar kallon Idris,daga nan suka ci gaba da yar hirar su,har zuwa lokacin da Hamma idi ya yi musu sallama ya wuce gidan su.








A bangaren Abba yahya kuwa,tun bayan da Baffa ya sanar da shi wannan batu na dukiyar Raihan dake hannun aminin ƙaninnashi kuma gwamnansa shugabansa a wajen aiki,ya kasa zaune da tsaye, sam hankalinsa bai kwanta da wannan gurbin tunanin na ƙaninshi ba.wai Abban Bashir lafiyar ka kuwa?ka kasa cin abincin kirki sannan yanzu ka kasa zuwa ka kwanta dare sai yi yake anya kuwa lafiyar ka kalau? Cewar inna maimuna ke nan da fitowarta daga daki ta kusan hudu ke nan tana ganinshi a yanayin da ta shi,zama ya yi yana fidda wani numfashi ta hanyar fesar da iskar bakinshi,sai da ya yi ɗan jim,kana ya ce"maimuna wani abu ne yake damuna,a nan ya sanar mata da abinda ke faruwa,inna maimuna ta yi Murmushi tana cewa to kai meye naka na damuwa meye abun tashin hankali acikin wannan lamarin? maimuna ba zaki gane ba,me zai hana kuwa na gane idan ka fahimtar dani"juyowa Abba yahya ya yi yana duban inna maimuna cike da son ta fahimceshi,ya ce"Nura yayi wawtar dankawa Alh Garba dukiyarshi,har yanzu Nura bashi da wayo bai san masoyinsa ba,damuwata akan wannan al'amari bai wuce kar Alh Garba ya cutar min da dan uwa akan dukiya ba,ina matukar jin tsoran abinda zai biyo baya,saboda ɗan zaman da nayi da gwamna tsaf na karanci waye shi na karanci cewa shi ɗin akkuya ne da fatar kura mayaudari ne, cin amanar ƙasar bai zama komai share shi ba,bare kuma cin amanar amininsa cin amanar aminta da aka jima ana gina ta cin amanar wanda ya aminta da shi,tabbas ina tsoro ina tsoron wani al'amari ",cikin tashin hankalin kalamansa inna maimuna ta ce",me yasa ba zaka sanar da shi nuran ko Baffa ba?in dai har kana irin wannan tunanin kuma kasan wani abu akan Alhji Garba ka yi shiru daga baya wani abu yazo ya faru tabbas baka da fita kuma ɗan uwanka da mahaifinsa ba za su taba yafe maka ba,dan haka ina mai nusar da kai kayi wani abu kafin me faruwa ta faru".




Mainuna ba za ki gane abinda nake hangowaba,yanzu idan nace zan sanar da su kai tsaye ba za su yadda ba karshe ma reshene zai juye da mujiya nine zan zama abin zargi za su ce ina bakin ciki ne dan ba abani riko ba an bawa bare,tabbas kaima kana da hujja ,to amma yanzu me kake tunanin yi akan taimakon nuran?inna maimuna ta tambayeshi idanunta akansa,dole zanyi wani abu zan taimaki dan uwana kamar yadda ya tallafi rayuwata,duk da nadan cewa ba zan iya biyansa dinbin alkhairin da ya yi min ba,amma dai zan kwatanta, Allah ya taimakeka akan niyarka Nima idan da taimakon da kake bukata daga gare ni zanyi koda shawarace.




____________________




Darene sosai ,wanda alokacin ko wane bawa ya sauke hakarkarin shi dan hutawa,masu dabara kuwa suna can suna bautawa Allah da neman biyan bukata ta hanyar salloli da karatun Alqur'ani,




Da yawa kuwa daga cikin mabiya shedan,wadan da zuciyar su ta ƙone ƙurmus,kuma ta ƙeƙashe,suna can cikin wani dogon tsauni inda tsohuwa me jini ke zaune da mabiyanta wanɗanda suke nema a gare ta..




Jajayen idanunta ta ɗago ta ta kalli ɗaya daga cikin mutane goma dake durƙushe gabanta,kawunan su duk a kasa,ta buɗe bakinta me tsananin wari kato kamar kofar yin bahaya,ta ce"ina mai tabbatar maka da cewa shigowar ka wannan ƙungiya Tamkar samun nasarar ka ce ta rayuwa,juyar da fuskarta me dauke da ƙwalaƙwalan idanu ta yi kan na kusa da shi ta ce",kai kuma tun da ka kawo mana shi cikinmu nasarar ka yanzu ta fara,mu dai kawai mu na so ka ci gaba da aikata duk ta asar da muka sa ka aikatawa,duk inda ka sa kafar ka ya zamana cewa an zubar mana da jini domin jini shine muradin ya'yan tsohuwa mai jini,idan ka ci gaba da yin haka ina tabbatar maka da cewa siyasa da yin nasara ba ka fara ko mai ba,za ka ci gaba da nasara akan dukkan wani kudurinka,siyasa kuwa yanzu ta fara zama a hannunka sai kayi mulkin da babu wanda ya taba yin irinsa a cikin ƙasar nan,za ka samu ɗaukaka inndai har kana tare da mu,kuma idan ka ɗiba zaka dinga zubawa,to kuwa tabbas za kana kwashewa"...hahhhhhhhhh....ta saki wata shiɗaniyar dariya wadda ta sa gaba daya tsaunin ya shiga girgiza da kansa,bai tsaya ba har sai dai ta rufe bakin ta kai kace ba wajen ne yake girgiza ba,haka kuma kamar ba ita ce ta yi dariyar ba.




Duban wanda aka kawo din ta yi tare da nuna shi da wata sandar tsafi,nan take kanshi yayi tas kamar Allah bai yi tsiron gashi akan ba,wanda ya kawo shi ta umarta da ya dauki kwaryar dake gabansa ya zuba masa akansa,babu musu ya dauki kwaryar ya zuba masa jinin dake ciki, ragowar kuma ta ce"ya bashi ya shanye.


Sai da ya shanye jinin nan tas,yana faman runtse ido,kana tsohuwa ta kuma bushewa da wata mahaukaciyar dariya,wanda a wannan karon harsu kansu sai da jikin su ya dinga girgiza ba tare da sun girgiza da hakan ba,




Daga yanzu ka zama namu,kuma zamu canja maka suna wanda a hankali zai bika sunanka na asali zai bace domin wannan shine muradinmu.


Jin jina kansa ya yi ba tare da ya ɗago ba har yanzu ,dan wannan doka ce ta nuna ladabi ga tsohuwa.


Duban wanda ya kawo shi ta yi ta ce" shuda daga yanzu sunan yaron ka,dunan duniya saboda yana tare da Aljani dunan duniya,dan haka za mu dinga kiran shi da dudu,gaba dayan su kawunan su na a sunkuye su ka hada hannayen su biyu tare da jinjina a gareta,..




Kai kuma duduu ka tabbata daga yau zaka fara cimma nasara a kan abin da ka dosa, sannan daga gobe muke son ka fara aikata manyan zunuban da muka umarce ka da yin su".........


____________


Washe gari tsaf Raihan ta shirya ba tare da ta jira Hamma idi ba ta fito tana kiran driver,sai dai kuma fitowar Hamma din ya sa ta dakata da ga kiran drivern,karasowa ya yi yana cewa lil broth yadda mu kayi da kai ke nan? Wato na fahimci dai baka so na samu ladan kaika gurin aiki ko? Dan murmushi Raihan ta yi kafin cikin siririyar muryar ta ta ce" ba haka bane Hamma idi kawai bana son takura maka" girgiza kai ya yi yana mai kama hannun ta ya ce" ai Ni nace ka dinga kirana ina kaika da ɗaukoka kafin zuwa Monday Nima na fara zuwa nawa,idan kuma mun cigaba da tafiya tare shike nan duk hakan ba damuwa bane" bude gaban motar ya yi,tare da yi mata nuni da ta shiga,shiga ta yi tana cewa Hamma na gaskiya kana ji dani" to idan ban ji da kai ba dawa zanji? Ya fada bayan ya shiga wajen zamansa yana mai kokarin tada motar.




Hira Hamma Idris yake yi da dan uwan nashi wadda ke cike da nuna kulawa tare da soyayya, Raihan din ma amsa shi take da kulawar dan har ji take kamar ya cancanta da ya san wacece ita a matsayin sa na ɗan uwanta me kaunar ta,to amma babu damar yin hakan saboda alkawari ne da ta ɗaukarwa auntyyn akan bayan wazir babu wanda zai kuma sanin asalin jinsin ta.




Rahim motar nan kuwa ba mu take bi ba?Hamma idi ya tambayi Raihan bayan ya fara rage karfin gudun da yake dan son tabbatar da abin da yake hasashe,duban bayan su Raihan ta yi ta hanyar duba mirror din gefanta,tabbas kuwa mota ce baka me bakin gilashi a bayan nasu sai dai kuma kamar yadda ya fada basu da tabbacin su take bi.




Ganin ya rage gudun da yake yi motar bata daina binsu ba,yasa shi ƙoƙarin sauka kan hanya dan yin parking cikin sauri da kokarin ƁOYE razanar da ta yi ta ce", a'a Hamma kar mu tsaya ba mu sani ba ko masu cutarwa ne,duban ta Hamma idi ya yi na ɗan wasu sakanni kamar yana son gano halin tsoran da Rahim din ya shiga, sai kuma ya ɗauke kansa tare da bawa motar wuta ya fice da mugun gudu,wanda hakan ya basu damar bacewa waccan motar.




Tana kokarin fita Hamma idi ya dubeta kana ya dan furzar da numfashi ya ce"Rahim me kayi musu suke bin ka? Da sauri Raihan ta shiga girgiza kanta tare da cewa wlh ban sani ba kuma ai bani suke bi ba"ok shike nan,amma ina so ka dinga kula kasan irin binciken da zaka dingayi Rahim bana son wani abu ya same ka ta sanadin aikin nan,domin kuwa hakan ce take faruwa akan da yawan yan jarida masu gaskiya,dan haka ka kiyaye",jin jina kai Raihan ta yi kana ta fice jikin ta a sanyaye da al'amarin da ya faru yanzu kuma ta tabbatar da cewa ita din ake bi,gaban ta ne ya fadi lokacin da tayi wa kanta tambaya akan abin da suke shirin yi mata.






Cike da mamaki Hamma idi yake kallon motar da suka baro tana bin bayan su,bai nuna ya ganta ba sai kawai ya juya ya koma cikin ma aikatar ya yi fakin tare da kwantar da motar kujerar ya kwanta,yana kallon masu shige da fice dan tabbatar da tsaron kanin nashi....




Hello sir aikin nan fa ya jike,cewar tk,da yake waya da Dr sanater,me ya faru ke nan baku samu damar dauko shi ba? Duk ya jera musu tambayoyin a ɗan rikice,tk ya ce"oga wani dan uwansa ne ya Ankara da bin su da muke a yanzu haka da ya ganmu ya koma cikin ma'aikatar yana gadin sa"ok to maza ku bar gurin kar ku bari kowa ya gane me kuka je yi" da wannan umarni suka bar bakin tafkeken buldin din chibaɗo FM din..




__________________




A hankali Dr ya sa hannu ya share zufar da ta karyo.mishi ,yana cewa na fi kowa shiga matsala ,saboda Ni komai nawa na sa ka gurin neman takarar senator, idan asirina ya tonu na shiga tara ya zamana bani da tsuntsu bani da tarko ma ana ba dukiya ba mutunci"ya karasa maganar da mikewa tsaye yana jin kamar ya je har inda rahim yake ya bindige shi kowa ya huta........ ✍🏽


Fyadams.........✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page17 ```




Shugaban jam'iya ya ce"ai idan ma iya mutuncin ne zai zube to da sauki,karfa ku manta batu ake na kisa ta zahiri da ta boye,kuma duk akan mu,to dan me zai sa ku dinga yin tunanin zubewar mutunci ai ana kama mu Kuma kunsan meye makomar mu daurin rai ne kawai",numfashi Alh sale yaja ya fesar kana ya dauki kwalbar barasa ya dan zuka kana ya dubesu ɗaya bayan ɗaya mu,sai da yaja wasu yan sakanni kana ya ce"kai fa takarar senate ne nifa gwamnan kasa nake son karba idan baka manta ba,dan haka duk cikin mu shugaban jam'iya ne kawai Gara tun da shi bai kashe komai ba,duk a cikin kudin gwamnati yake facaka,shugaban jam'iya ya zabura yana cewa haba Alh sale duk kudin da nake facaka da su ɗin ba tare muke ci ba,kar fa ku manta a idon mutanene muke yan adawa amma a badini mudin aminan junane,kuma duk kudin da nake dannewa ba tare da sanin gwamna da yan kungiyar sa ba,ai tare muke ci,duk wata cuwa cuwa da za muyi da sauran masu muƙamin gidan gwamnati rabi ku nake kawowa ba tare da su na basu kasonsu ba,shine yanzu dan son kai zaku ce na fi ku kwanciyar hankali,a ganina ma ai sai nafi kowa tozarta",shike nan yanzu dai mafita ya kamata mu nema duk wannan batun mu ajiye shi,cewar Dr da kamar yafi su damuwa da lamarin, Alh sale ya ce" Ni ina da shawara,duk zuba masa ido sukayi cike da so da dokin jin abinda zaice" ƙasa ya yi da murya tare da ya fito su da hannun shi,aiko da sauri suka matsa kusa da shi suka sashi a tsakiya,raɗa ya yi musu wanda duk ƙwaƙwata na kasa jin abin da ya fada musu,dariya suka sheƙe da ita suna tafawa tare cike da farin ciki da alamu dai shawarar ba karamin dad'i da karɓuwa ta yi a gurinsu ba,nan suka ci gaba da tattaunawa kan yadda za su yi komai a tsare batare da asirin su ya tonu ta hanyar camarar nan ba.




__________________




Jiki a sanyaye tasa kafar ta a cikin office din ya,zuciyarta ba karamin nisa ta yi akan lamarin wadannan mutane da har yanzu bata san ko su waye ba,kokarin ya kice abin ta yi dan sam Raihan bata barin damuwa ta yi tasiri a jiki da zuciyarta,ko

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login