Showing 39001 words to 42000 words out of 189984 words

Chapter 14 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15658

dafe kirjin ta tayi idanun ta na cikowa da hawaye,bata taɓa ganin sa a irin wannan yanayin ba,duk kuwa da cewa kullum fuskarsa a kame take babu wani sassauci amma ai ita yana rangwanta mata kai ita hasali ma ba ta taba sanin ainahin halin sa na miskilanci a kanta ba.




Kai tsaye dakinta ta wuce duk da taga alamun dawowar su antyy amarya,tana shiga ta ciro madaukar murya da ta shiga da ita,ba tare da shi kansa wazir ya sani ba,kuma duk binciken da akayi musu ba a gano tana jikin ta ba,wani dan murmushi ta yi me ciwo tana duban madaukar ta ce" ganganci ne shiga irin wannan wajen a haka ga mu yan jarida,kasancewar mu ba ma raina abun magana ko mai kankantarsa,bare kuma Ni da nake Binciken wanda suka kashe halima ido rufe,ko kai Hamma wazir ba zaka taba sanin komai ba har sai nayi na gama idan nayi nasara shi ke nan,idan kuma aka samu sabani na mutu kamar halima to hakika nasan na dace tun da na mutu ne akan hanyar binciko gaskiya,karasawa ta yi ta yi masa kyakkyawan boyo duk kuwa da cewa ba wai tana zargin gwamna da cin dunduniyar su ba ne ga kuma abin da haluma ta kuma faɗa, to amma ya kamata ace binciken su yabi takan kowa kamar yadda gwamnan ya fada da bakin sa.




Cikin sanyin jiki wadda damuwar halin da wazir yake ciki ya saka mata ,ta kammala shirin ta na bacci bayan ta gabatar da salla da cin abinci,wanda abincin ma dakyar antyy amarya ta takura mata ta ci kaɗan,antyy amarya bata takura mata da san jin damuwar ta ba ,dan a tunanin ta har yanzu batun mutuwar halima ne bai gama sakin ta ba.




Wazir kuwa ,yadda ya bar Raihan a fusace cikin fushin da shi kansa yake jin ya kasa control din kansa,haka ya karasa gida da shi,bai kula su Ammi dake falon innawuro ba,ya wuce saman sa kai tsaye ,cikin yanayin takun shi na karfafan maza wanda yake kuma nuna halin fushi da motsawar halinsa na miskilanci,duk bin shi suka yi da kallo,kafin innawuro ta tabe baki ta ce"Ni wlh duk aikin nan na wazirin gida ya gundure Ni,sam bana son sa"ta karasa maganar tana mai ɓantarar farin goron ta,shukrah ta ce"wlh Nima innawuro fargaba aikin nan yake saka Ni,dan da shi da aikin soja ba su da wata maraba"ke dai bari 'yar nan cewar innawuro,Ammi dai bata ce komai ba,amma fa tabbas maganganun innawuro da auta shukrah sun yi matukar tasiri a gare ta,to amma ya su ka iya da kafiya irin ta Abbu da ɗansa,da anyi magana yanzu za su fara wa azin da ba sa gajiya da yin shi in dai akan aikin su na taimakon al'umma ne.




Tun da ya shige bai ƙara lekowa falon ba sai da lokacin Sallah ya yi, sannan ya fito, a hakan ma babu wanda ya kula,to innawuro ma dai bata kula shi ba dan tasan idan wannan halin nashi ta motsa babu wanda baya nunawashi.




A bangaren Raihan kuwa,haka ta kwanta da saƙe saƙen dalilin fushin Hamma wazir a kanta,gefe daya kuma tana kara tariyo hirar su da gwamna tana sauraro ko Allah zai sa ta tsinci wani abu da zai bata haske akan kyakkyawar niyar ta.




Washe gari,tsaf ta fito cikin shirin ta na fara zuwa aiki tun bayan rasuwar halima ,wanda kusan dukan ma'aikatan sai yau din zasu koma sakamakon jimamin mutuwar ma aikaciyar su,driver ne ya dauke ta sam bata yi tunanin tsayawa jiran Hamma wazir ba,dan tasan abu nee me wuya yau din ya biyo,duk da cewa bata san takamaiman laifin da ta yi masa ba.




Shima Wazir din kai tsaye office ya nufa ba tare da ya biya gidan su Raihan ba,kuma har yanzu yana nan tare da bakin ran nasa na tun jiya wanda abin da ya kusan faruwa tsakanin gwamna da Raihan ya haifar masa,har yanzu yana jin ɗacin abin a can kasan makoshin sa,duk lokacin da ya rufe ido hannun RAIHAN yake gani tana mikawa gwamna a domin su gaisa ,ko yanzun da yake tunanin abun a hanyarsa ta kusan isa office ji yake tamkar zai yi aaman zuciyarsa,dafe goshin sa ya yi tare da dan lumshe lumsassun idanunsa wanda suke cike da baccin da bai samu yin sa ba a daren jiyan,shi kansa so yake yasan dalilin zuciyarsa na shiga wannan halin akan abin da ya farun,sai dai kuma hakan ya gagara a gareshi,amma dai yana kokarin jingina hakan da dalilin son kare mutumcin Raihan a matsayinta Na kanwar sa.da wannan tunanin ya isa chibado fm.




A daidai lokacin drivern raihan ya ajiye ta,tsayawa ta yi tana duban wazir din da yake rufe motar shi,yayi matukar kyau cikin shigar suet kwantacciyar sumar shi ta Fulani sai ƙyalli take tare da kayataccen sajen shi wanda ke kara mishi matukar kyau da kwarjini,ji tayi idanun ta sun kawo ruwa na rashin sanin cikakken dalilin da ya sa wazir din ya canja mata lokaci daya.


Duk da bai waiga in da take ba ,amma jikin shi da zuciyar shi sun bashi tabbaci akan tana kusa da shi haka kuma yaji kaifin kyawawan idanun ta akansa,a hankali ya fara takun shi me cike da nutsuwa,dan kaiwa ga lifter da zata kai shi ga office din shi,duk yadda yaso kauda tunanin jiyan hakan ya gagara hakan yasa ya kara karfin takun shi dan barin wajen.




Hannu tasa ta share hawayen da suka cika idanun ta ,tare da takawa cikin sanyin jiki dan wucewa bangaren office din su..........✍🏽


FATEEMAH Y ADAM
*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page12 ```






Dukkan su haka suka fara aiki cikin sanyin jiki,sai abokan aikin suka dinga tunanin ko mutuwar Halima ne har yanzu take dukan su.


...................




Inna maimuna ce zaune tana waya da Bashir faɗa take masa akan shashashancin da ya tsaya har ya samu matsala a jarrabawarsa yan uwansa duk zasu dawo amma ban dashi,Abba yahya yace", dole sai ya tsaya ya sake maimaita shekarunsa baya bukatar dawowarsa indai ba zaizo da abinda aka tura shi ya yi ba, inna maimuna duk hankalinta ya tashi bata san cewa shi hakan ya fiye masa ba domin zai samu karin lokaci da dama ta sheƙe a yarsa,sallamar Abba yahyan ce ta katse mata nasihun da take masa tare da kawo masa misalai akan kannensa,dan Allah ka maida hankali kaji ta faɗa tana kashe wayar tana maida hankalinta kan abban.duban sa ta yi cikin nutsuwa ta ce", Abban Bashir me kuma ya faru ne naganka haka ko har yanzu ɓacin ran Bashir dinne?zama ya yi yana dan sakin ajiyar zuciya sannan cikin damuwa ya ce",ba wannan ba ne, babu abinda zai sa na ci gaba da damun kaina akan Bashir yake kawai.ya yi rayuwarshi yadda yake so.to menene? ta tambaya duk da cewa bata ji dadin kalaminsa kan tilon ɗannata ba, haba maimuna kema kin san abin da yake damuna ba ya wuce maganar RAHIM tsakani da Allah bana son wannan aikinnasa kina dai kallo kullum da wanda za ace an kashe a cikin 'yanjarida,gashi shi kuma Nura ya ki dawowa bare mu sami mafita akan wannan lamarin gaba ɗaya ",numfashi inna maimuna taja kana cikin gasgata maganar Abba yahya ta ce",ko Ni dan ba yadda zanyi ne kullum maganata daya ce idan muka zauna da lamra, to amma yadda take bani kwarin gwiwa akan aikin yasa na hakura nake binsa da addu'a, Rahim yana son aikin nan dan haka mu yi hakuri mu barshi mucigaba da yi masa addu'a",Abba Yahya ya ce",haka ne amma dai nuran zai dawo dole a samu wani da zai dinga tsaronsa koda jami i ne ta haka ne kawai hankalinmu zai dan kwanta", wannan ma shawara ce me kyau Allah ya tsare mana su baki ɗaya,ta faɗa tana tashi dan samo masa ruwa me dan sanyi.


_________




Misalin karfe biyu na rana ,gari ya hargitse da faɗa sakamakon taron siyasa da aka gabatar a cikin unguwar jabbama,abun har ya kai ga kashe rai,tuni 'yan jarida masu nema a kusa suka garzaya inda abun yake,a cikin su har da su Rahim da basu saurari cewar ogansu ba suka garzayo,tun da ita dama tun bayan haɗuwar da su kayi yayin shigowa bata kuma bari sun hadu ba.




A can kuma gidan jarida na chibaɗo,sai bayan tafiyar su RAIHAN,wanda ba kowa ne ma ya Ankara da fitar ta su ba,ita da salim da Khalil da rufa'i da Ishaq ,sammani daya daga cikin ma aikatan su ne ya garzaya office din A wazirrrrrr dan kai masa rahoton abin da ke faruwa.




Zubawa sammanin ido A wazir ya yi bayan ya gama sauraron jawabinsa,sai da ya dan numfasa kana ya ce"sammani kuje ku dauki rahoto da kai da su salim da khalil amma ina mai shaida muku cewa kamar yadda muka saba,bana son sauyi ina son rubutu da jawabi akan daidai abin da ya faru bana buƙatar ƙari ko ragi, iya ku kaɗai nake bukatar kuje kar ku bari Rahim ya bi ku wannan umarni na ne"in sha Allah oga za mu yi kamar yadda ka ce"sai dai fa ina ga su salim din tuni Rahim ya ja su sun wuce tun kafin na karaso nan"cikin nutsuwarsa ya ɗago ya kafe sammani da idanun sa masu tsoratar da mara gaskiya,sam ba za ka gane bacin ransa ko damuwarsa ba,amma shi ka dai yasan ɗacin da ya ji a makoshinsa da wannan batu na sammani,jin jina kai kawai ya yi tare da yi masa nuni da kofa.




Sammani yana fita ya furzar da wani iska mai tsananin hucin zafi ,tare da maida kansa ya kwantar yana hango Raihan cikin dandazon maza ana kokawa da ita wajen son jin abin da ya faru wanda ba ayi a gaban su ba wanda kuma ya zama dole su sani dan fidda rahotansu yadda ya kamata.miƙewa ya yi tare da ɗaukar key din mota, fuskar nan ta shi kamar wanda aka aikowa da sakon mutuwar uwar shi,takunshi ma ka dai ka kalla kasan yan maza sun motsa,duk inda ya gifta sai takunshi ya bada wani irin sauti na alamun takun mazantaka, buɗe motar ya yi ya shiga mazaunin driver kana ya tada ita ,ya kuma figeta a tsiyace,wanda hakan yasa sai da jama'ar dake harabar wajen suka bishi da kallo.




Kamar yadda wazir ya lissafa to haka lissafin yake,dan kuwa RAIHAN na tsakiyar maza a na wawason daukar rahoto daga bakunan da suka ji suka gani,ga kuma gawarwakin wadan da aka kashe nan daga can gefe yan sanda na ta faman bincike da tutture mutanen da suke son ganewa idanun su ba wai a basu labari daga nesa ko gidan rediyo ba.RAIHAN dai sun sami cikakkun bayanai kamar yadda suke so,dan kuwa kamar ko yaushe labarin da suka samu babu wani gidan jarida da suka sami irinshi,saboda tsananin kwazon su da jajircewa akan aikin su,da kuma son tabbatar da gaskiya,akan idanun wazir wani dan sanda ya tura RAIHAN kan mazan da suke kokawar son ganin ƙwaf, saboda son aba su filin wajen,da kyar Raihan ta samu ta fito daga wajen da taimakon su salim da suma kusan rabin jikinta da hannun ta yana hannunsu saboda karancin karfin da take da shi ,ga kuma raunin ya mace a tare da ita,sai da suka fito fili sannan ta kwace hannun ta tare da daidaita abin maganarta ta fuskanci rufa i da ke haskata,cikin Muryar ta da mutane suke yawan cewa Muryar ɗan jarida Rahim irin ta mata ce,ta ce"to masu sauraren mu kamar yadda kuke gani kuma kuke sauraron mu,muna a tsakiyar wajen da yan bangar siyasa su kayi vannan babbar ɓarnar ta kashe rai,gashi nan yan uwan mamata suna kuka da fatan hukuma zata bi musu kadun hakkin ran yan uwan su,kai ba ma su ka ɗai ba har da sauran al umma saboda suna jin matukar ciwo akan abun da yake faruwa da al'umma,musamman kashe kashen da ake mana ba tare da mun ji mun gani ba,to masu sauraro ku ci gaba da bin mu cikin jaridar mu ta gobe me taken hakkin matattu yana kan yan siyasa" tana zuwa nan a labaran ta suka yi ido hudu da A.wazir wanda ya kafe ta da nasa idon da suke cike da bacin ran da ita kadai take iya gani da fuskanta,kafin ta yi wani motsi tuni ya tako cikin nutsuwa da kamalar sa da ta cike gurbin ɓacin ransa da ba kowa yake gani ba, hannunta ya kama ba tare da ya ce"ko mai ba,suka bar gurin, buɗe motar ya yi tun kafin ya ce"mata komai ta yi hanzarin shigewa motar kirjin ta na wani irin bugu saboda yadda ta ga tsantsar bacin rai da wutar bala'i a idon A. wazirrrrrr.




Duban su salim ya yi ya ce"ku wuce a motar da kuka zo a kwai inda zamu"ok sir suka fada a tare a lokaci daya suna tafiya dan isa gurin motar su.


.........…..………




Cikin tashin hankali inna maimuna ta nufi bangaren aunty amarya,sai ta tarar da aunty amarya ma kallon tashin hankalin da ake haskawa take,zama ta yi gefanta tana cewa yanzu lamra haka zamu zauna muna ji muna gani ana kashe 'ya'yanmu da 'yanuwanmu?nifa wannan lamarin ya fara fin karfin tunanina gaskiya",numfasawa aunty amarya ta yi tare da maida kallonta kan inna maimuna Macen da take da matukar kima a wajen ta,tasan cewa duk wannan rudewar da ta yi bai wuce akan Raihan,yasan cewa ita kadai ce a ranta ta saya ne kawai saboda yawan kwantar mata da hankali da take yi,sanin hakan yasa ta fuskanceta cikin nutsuwa da son kwantar mata hankali,ta ce",inna maimuna duk wannan abun da kike gani yana faruwa zai wuce ya zamo labari,babu abinda zai faru da Rahim ina ji ajikina Rahim zai iya zamowa silar daidaituwar al'amuran da suke faruwa,shi dan jariidane me kwazo gashi yana tare da A wazir,nasan cewa zasu tsaya tsayin daka dan ganin sun zakulo yantaaddan da suke wannan aika_aikar,duk da cewa su ba jami'an tsaro bane,amma mutanene da suke da muhimmanci wajen al'umma domin suna ƙoƙarin zakulo masu laifi wadanda ba asan da su ba, waɗanda suke boye suke aikata manyan zunubai,dan haka ki kwantar da hankalinki innar Bashir ".




Ajiyar zuciya Inna maimuna ta saki alamun gamsuwa da maganganun aunty amarya,daga nan suka ci gaba da tattaunawa akanatsalar dake faruwa.


______________




Tunda suka fara tafiya bai kalli inda take ba,ya yin da Raihan gaba daya ta tsargi kanta akan wane irin laifi ne mai girma ta yiwa Hamma wazir da ya sa shi wannan bacin ran haka,da wannan tunanin taji ya yi fakin,ɗaga manyan idanunta da suka sauya ta yi saboda ganin inda ya kawo su,sai ta ga ashe gida ya dawo da ita,kafin ta yi magana ya rigata ta hanyar mika mata tattausan hannushi cikin cunkushewar murya ya ce"bani madaukar bayanan"miƙa masa ta yi jikin ta yana matukar yin sanyi,yana karba ya kuma cewa kije gida ki huta bana bukatar ganin ki wajen aiki har sai na bukaci hakan"waro manyan idanunta tayi gami da dafe kirjinta,cikin rawar murya ta ce"Hamma wazir me nayi maka zaka yi min wannan baƙin hukuncin?dan Allah kayi haƙuri Ni dai ko me ye bazan sake ba wlh"ta faɗa tana mai rushewa da kukan da yasa wazir rintse idanun sa saboda yadda ya bugi zuciyarsa,dan Allah kayi hakuri Hamma Ahmad wlh bazan sake ba duk da ban san laifin da nayi maka ba,gobe da akwai aiki me muhimmanci da zanyi kuma kasani cewa dole wannan hirar da za ayi da Dr sanate dole Ni ya kamata nayi ,dan Allah kar ka mun haka hamma wazir"ta faɗa tana mai ci gaba da raira kukan da yake jin sa tamkar wuta saboda yadda ya ke sukan zuciyarsa,is ok,ya fada can kasan makoshin sa, ɗago kanta ta yi tare da dan tura bakin ta ta ce"Hamma Ahmad me nayi maka? Shuru ya yi saboda shi kansa bai san ta kamaiman abin da zai ce ta yi masa ba.


Dan haka sai kawai ya share tambayar da ɗan furzar da hucin bakinsa,tare da cewa shi ke nan jeki gida na yau dai ya wuce sai Allah ya kaimu goben ,sai kizo ki gabatar da hirar da kuma sauran rahotannin yau ɗin" ya fada yanayin fuskar shi na sauyawa da wani dan kara tsukewa saboda tuna abin da ya faru yau ɗin, Raihan dai ganin babu fuska yasa ta kaɗa mishi kai kawai tare da fita daga motar ,kai tsaye ta shige gida ba tare da ko waiwaye ba.




Kaɗan ya bi ta da lumsassun idanunsa,bai tashi motar ba sai da yaga me gadi ya bude mata ta shige gidan ,sannan ya saki ajiyar zuciya tare da tada motar ya fice daga layin.






Ko da Raihan ta shiga gida nan ta tarar da saukar su yaya Affan da yaya rufa'i sai kuma baba karami na wajen momy hanne,gidan duk ya cika.da murnar dawowar su ,wanda su sam basu san cewa yau din zasu dawo ba,duk da cewa sun san dawowar ta su a cikin satin,a nan dai Rahim ya shiga murnar dawowar yan uwan nashi,duban Hamma Affan ya yi ya ce" Hamma Affan su kuma su Hamma Hassan da Hamma jami'lu da Hamma Bashir da Hamma idi,yaushe zasu dawo? Affan da murmushi a fuskar sa ya dubi dan uwan nashi wanda yaga duk ya sauya masa ya girma sannan yayi kyau kamar ka taba shi jini ya fito,ya ce" Auta wani satin zasu dawo,shi kuma Idris gobe insha Allah yana hanya wani dan uzurine ya dakatar da shi shine ya tsaya su taho tare da Abbie" Allah ya kawo su lafiya cewar RAHIM (Raihan)Hamma rufa i ya ce" wai me aunty amarya take baka ne Rahim dan naga kafimu yin ja kamar kaine kaje kasar Wajen,dariya momy hanne ta yi kasancewar dukan su suna sashen Hajiya goggo, babu yadda za ayi su nuna bakin halin nasu harsu Affan din ma duk gimtsewa suke saboda Hajiya goggo,ta ce" dole kaga yafi ku samun jikin hutu tun da yafi ku komai da komai,kullum auntyynshi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login