Showing 42001 words to 45000 words out of 189984 words
Chapter 15 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
boye shi take kamar kayan tsafi ,innarshi maimuna ita kadai ke ganin shi duk sanda taso ba dole yayi ja kamar jan kosai ba"mama murja ta amshe da wata muguwar dariya har da tafa hannaye a hayye , dan ma bakuga da yadda ta bari yayi karatu har yake aiki ba,saboda kar a taba shi tun da kayan kudi ne shi ɗin,Hajiya goggo ce ta dakatar da su ta hanyar watsa musu harara ,ta ce "babu wadda ta isa ta zo gaba na tana aibata min jika,ku babu wanda ya aibata muku yara dan haka kar ku sake wannan banzayen surutan ehe"Raihan kuwa ta cika ta Batse kiris take jira ta fashe ,dan fa ita a rayuwar ta duk abin da zaka yi mata bata damuwa amma kar ka taba mata auntyn ta da innar ta,wannan a jinin duk wani dan halak yake me son gamawa da duniya lafiya,zata yi hakuri akan komai amma banda ciwa,auntynta mutumci,shi yasa sam basa ga maciji ita da kishiyoyin auntyn ,dan sun yi mata shedar mara kunya,akan tana tarewa auntynta cin mutumcin da suke mata,ko shashensu bata zuwa dama can bare kuma yanzu da ta san ciwon kanta,ko ada auntyn bata hana ta saboda wan can dalilin,to ita dama ta hana kanta saboda gujewa zagin da suke wa auntyn Tata.
Taka musu burkin da Hajiya goggo ta yi shi ya hana Raihan tanka musu kamar yarda ta saba,a duk sanda a kayi irin haka,kuma dawowar ya'yan su ba zai sa idan sun ciwa mahaifiyar ta mutunci ta kasa ramawa ba,ta shi ta yi fuu cikin fushi ta bar falon tana kunkuni,momy hanne ta ce" kin ga Ni dai hajiya yadda yaron nan ya yi kamar zai buge Ni ga kuma zagin mu da bai fasa yi ba kamar yadda ya.saba,cikin mamaki Affan ya ce" zagi kuma? Ey mana kana mamaki ne cewar mama murja da take ji kamar ta janyo Rahim ta murɗe masa wuya ko sa huta da bakin cikin sa,ƙwafa rufa i ya yi yana cewa Allah ya bashi sa a akan zagin naku ya ga asalin yadda ake kwallo dan wlh sai na karya shi gida biyu na watsar".
Salati Hajiya goggo ta sa tana mai tafa hannayen ta,ikon Allah yanzu ku dan Allah baku ji kunya ba,ga fa yadda kuke shirin batawa yara zumunci daga dawowar su,har kin fara saka musu mummunan akida na yan ubanci,( tab Hajiya goggo ai sai dai kar a kuma wannan abun ya dade da zama a zukatan su tun suna yara).ganin fadan Hajiya goggo yaki karewa yasa suka dinga barin sashen nata da ɗaddaya.
Ko da Raihan ta isa sashensu haka ta dinga ƙunci har ta gama abin da take yi,ta dawo wajen aunty amarya da tun shigowarta taƙi tanka mata bare tambayar ta abin da ya faru,dan ta san dai tatsuniyar gizo bai wuce koki tun da taga fitowar ta daga ɓangaren kakar ta su,kuma tasan duk suna can,tun da itama basu jima da dawowa ba ita da inna maimuna,basu isa shigowa su gaidasuba sai sune sukaje musu sannu da zuwa,dan tabbas idan zasu shekara da dawowa baza su taba zuwa sashenta ita da inna maimuna ba,iyayen su sun koya musu raini dan ma Abba yahya yana ƙoƙarin taka musu birki da batun sai yafi haka.
Zama ta yi gefan auntyn tana tura baki dan har yanzu fushin bai sake ta ba,saboda bata samu ta maida musu maganar ba, murmushi auntyn ta yi tana mai janyo ta jikin ta,da cewa haba autar aunty da Abbie 'yar lelen inna maimuna da Abba yahya ga kuma Hajiya goggo, duk wannan fushin fa,ke yanzu ai bake ba fushi gobe ne fa Abbie ɗinki zai dawo" ai kuwa da sauri ta washe baki kyawawan haƙoranta farare tas suka baiyana,ta ce" haka ne fa aunty natuna dan haka na yafe"yauwa autar aunty.
Fatima y Adam ..............✍🏽
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page13 ```
Da misalin karfe tara na dare bayan sun kammala cin abinci,dukan su suka had'e a sashen mama murja dan son tattauna babbar matsalar su,wanda suke ganin cewa yanzu ne lokacin fara babban yak'in ,saboda yaran su gaba daya sun girma sun mallaki hankalin kan su,kuma basu da matsala ta wajen fahimtar da su ,tun da sun jima da yin wannan yakin,kuma sun yi nasara,dukkan su a yanzu sun dawo ne da shirin ko ta kwana.
Mama murja ce ta ɗan yi gyaran murya bayan dubawar da su kayi suka tabbatar da cewa babu me yi musu labe,ta ce"to alhamdulillah mun gode Allah da ya kawo mu wannan rana damuka daɗe muna jiran ta,duk da cewa ba ku haɗu dukan ku ba,to amma jinkirin tattaunawar zai iya kawo mana matsala a cikin yakin da muke son farawa da zafizafi,da farko dai kun san da cewa dukan ku munyi muku matan aure wadan da mukasan cewa ba za su cutar da ku ba,kuma ba za su saka mana ido akan yakin kwatar dukiyar mu wadda aka rike da sunan gaibu ba,kuma kun amince da hakan,saboda a yanzu dukan ku kun kai minzalin ajiye mata, ba ku ba har ma kannen ku,dan haka mun gama da wannan babin dama jiran dawowarku ake yi a kai kudin aure da sa rana,kamar yadda mahaifin ku da wancan dan ƙadafin(Abba yahya) suka tsara.
Sai kuma abu na gaba shine shirin yadda zamu karbi dukiyar mu da aka dankarawa gaibu kai harma da wannan shegen Rahim ɗin me fuska kamar ta Aljani,dan haka kuje kuyi tunani akan yadda zamu mullowa lamarin dan wannan yaki ne wanda yake bukatar nazari,ta karasa fada tana sakin wani Marayan murmushi me cike da ma anoni,momy hanne ce ta dauka da cewa kuje kuyi tunani kafin dawowar yan uwan ku yadda idan sun dawo zamu ɗora da tasu shawarar" jin jina kai su kai fuskar su cike da shedar tabon tsanar dan uwan nasu Rahim da kuma babban matsalar ta su da suke kira da gaibu.
Washe gari Raihan kin zuwa office ta yi saboda dawowar Abbie dinta,kasancewar wannan dawowar idan ya dawo ya dawo ke nan kamar yadda ya fada,duk wani dukiyar shi ya tattara guri daya,a cewar shi shima so yake ya samu nutsuwa da iyalan shi,kuma tun da yaran shi sun gama karatun su bashi da matsala ,duk zasu dawo ne su ci gaba daga in da ya tsaya ,duk da cewa shima din ba wai zama zai yi ba,kawai dai zai dawo da harkokin shi cikin ƙasar shi ne dan samun nutsuwa daga yawan zirga zirga.
Tun da suka tashi suka fara shirye shiryen tarban sa,ita da auntyn nata ,harma da jiddo da ta shigo dan taya su,suna yi jiddo na wa Rahim dariya wai sun samu kuku,harararta Raihan kawai ke yi,cikin tsokana jiddo ta kuma cewa wlh aunty amarya ko acikin mata wadan da suka kware da girki ba za a samu wadda zata nunawa Rahim iya girki ba,gaskiya matar ka ta huta" aunty amarya murmushi ta yi ta ce" kin gan ki ko jiddo ai dai Rahim din yana jinki babu ruwa na idan ya kama ki" ɗan duban shi jiddo ta yi tana kunshe dariyar dake son kufce mata.
Shigowar inna maimuna ce ta katse musu hirar su,inda ta jonasu suka cigaba da aikin tare.
Tun da A Wazir ya zo office yaga Raihan bata zo ba duk sai yaji hankalin shi na neman ta shi,sai dai kuma miskilanci da kokarin ƁOYE abin da yake ji din ya hana shi ko da tambayar ta a wajen abokan aikin ta,bare kuma ya kai ga yi mata waya,haka nan yake jin wannan damuwar akan Raihan wanda ya rasa ta me cece bare kuma ainahin dalilin jin hakan,haka ya dinga gabatar da aiyukan shi cikin jarumta da son ya kice tunanin ta a ranshi,gizagon shi da tsananin kamewarshi ya da ɗa tasiri wajen boye yanayinshi, hirar da zata gabatar a ranar ma sai Allah yasa itama hajiyar tafiya ta taso mata wanda ya sa dole ta bada uzurin a bar hirar sai ta dawo,su kuwa a bokan aikin ta duk sun san dalilin rashin zuwan Rahim ɗin,ba su dai kawo cewar oga bai sani ba,to ko bai sani ba ma waye yake da zarran yi masa shishshigi wajen sanar da shi ba tare da ya tambaya ba,hakan ya sa babu wanda ya yi masa koda alamun maganar Rahim.
Da misalin ƙarfe hudu,gwamna tare da Abba yahya suka wuce dan dauko amininshi da yake matukar ji da shi yawa tsoka daya amiya,cikin madaukakin farinciki suka rungume juna, Alh Garba gwamna ya rike hannun amininnasa bakinsa yawa gonar auduga ya ce", alhamdulillah naji dadin dawowarka kusa damu",shima Abba yahya cike da kaunar ɗan uwannasa ya rungumeshi yana nuna tsananin farin cikin dawowarsa gida,daga nan suka ɗunguma su da tarin motocin gwamna da suka yo musu rakiya suka raka shi har gida.
.........
Lokacin da Raihan ta yi ido hudu da sanyin idaniyar ta Abbien ta me son ta tun kafin a san za a haifota,sai kawai ta rungume shi tare da saka kukan farincikin dawowar sa kusa da ita,cike da farinciki ya shafa kanta yana cewa to me haka da kuka kuma Rahim, bayan gani na dawo har ma da yan uwan ka da suka yi nesa da kai,ya. Fada yana janyo hannun jiddo kusa da shi,maza jeka tari dan uwan ka ga shi nan yana kallon ka kana kukan tabbara"da sauri Raihan ta juya inda Hamma Idris yake tsaye hannuwan shi soke jikin aljihun rigar shi babu abin da ke dauke a fuskanr shi sai murmushi wanda kana gani kasan na farincikin dawowar sa cikin ahlin sa ne,da gudu Raihan ta karasa gefan sa ta rike hannun shi tare da dan rungeme shi cikin farin ciki da shagwabar da ta saba yi masa tun kafin ya bar ƙasar ta ce"Hamma ido na na yi kewar ka sosai(kasance War a baya haka take fada masa Hamma ido maimakon Hamma idi saboda bata iya fada ba, a kwai shakuwa me girma tsakanin Idris da Rahim dan ko can baya shi kadai ya fita Zakka a cikin yan uwan sa,saboda shi kadai ne baya daukar hudu bar iyayen su akan aunty amarya da Rahim kai harma da gaibun Raihan,shi yasa ta su ta fi zuwa daya)ware idanun shi ya yi tare da dan bude baki irin na mamakin nan,ya ce"kai auta haka ka zama ƙato idan mun zauna sai kafada min abin da Hajiya goggo da aunty amarya da inna maimuna suke baka"juyawa yayi inda jiddo take kusa da Abbie suna kallon su cike da sha'awa,ya ce",jiddo babu magana bare sannu da zuwa? Abbie ya yi saurin tare mata da cewa ina ka bata dama kana can ka hadu da dan uwanka, murmusawa ya yi yana shafa sumar sa kana ya ce"sorry jiddo kin san dai halin abokin fadan ki idan ban gama da shi ba yanzu sai ya sa mana rigima anan gurin"babu komai Hamma ai nasan halin tabarar Rahim,gaisawa su kayi tayi masa Barka da zuwa,daga nan suka shige bangaren Baffa Ali dama tun da gwamna ya sauke su ,suka juya acewarsa ya samu ya gana da iyalansa kafin su zauna shima su gana,
Sosai Baffa ya yi farin cikin dawowar dannasa tare da jikokinsa,yanzu saura Yamma Bashirne kawai baya tare da su, goggo kuwa kamar ta zuba ruwa akasa ta sha gida ya kammala yanzu za su fara kirankan su da cikakkun family.
Tabbas inna maimuna da Abba yahya sunso ace Bashirma ya dawo gida,to amma ba yadda za su yi da shi kasancewar ya dage sai ya zauna a can Dubai ɗin matar da zai aura ma yar Cance,dole suka hakura ba dan sunso ba.
Da ciwon kai ya dawo gida,gashi yana zuwa ya tarar da taron iyayen sa da innawuro ta haɗa duk akan sa,tun da ya gaida Abbu da Abban rabi a,ya wuce saman shi ko kallon inda innawuro take baiyi ba,idan ka kimtsa ka fito muna jiran ka cewar Abbu kenan,ok kawai wazir din ya fada tare da shigewa falon shi.
Harara innawuro ta bishi da ita tare da mele baki ta bantari goron ta tana cewa, duk wani nunƙufurcinka kayi ka gama muna nan muna jiran ka aure ne dai sai kayi shi ehe,Abban rabi ya ce"innawuro a yi dai mana hakuri abi abun a sannu dan Allah, hmmm kawai ta ce"ta na ci gaba da hararar inda wazir ya bi kamar shi take gani a wajen.
A bangaren su RAIHAN kuwa,kowa ya kammala shirin sa,kaf din su suna bangaren kakan su baffa Ali,idan ka cire Hassan da jami'lu da Bashir wanda sai wani satin zasu dawo gida banda Bashir da shi sai an ganshi kawai.
Bayan bude taro da addu a ,baffa Ali yayi gyaran murya kafin ya ɗora da cewa,to alhamdulillah na gode Allah da ya kawo Ni har zuwa wannan lokacin dana hada zuri a masu albarka,ina fatan Allah ya yi muku albarka ya ci gaba da dafa muku,abu na farko da zamu tattauna shine maganar auren su Affan wanda idan Allah ya kaimu sati me zuwa za aje a gama komai tun da Allah yasa duk yaran na gida ne ,iyayen ku ne mata suka zaba muku su daga cikin dangin su,kuma yadda da tarbiyyar su ne yasa har suka yi muku sha'awar su ,dan haka binciken da za muyi ba zai bamu wahala ba,Ni dai iya abin da nake da shi a bakina ke nan"duban Hajiya goggo ya yi ya ce"idan kina da abin fada Bismillah"sosai Hajiya goggo ta hade fuskarta alamun dai abin da zata fada mai muhimmanci ne, cikin nuna bacin ranta akan abin da ya fara faruwa akan idanun ta ta ce"Ni ba wani dogon zance zanyi ba kawai dai maganar da zanyi tana da matukar muhimmanci,gyara zaman ta ta kuma yi tana mai sa idanun ta a cikin na Affan, ta ce"wallahi tun wuri ku kawar da abin da kuke kokarin sawa kanku wato yan ubanci da iyayen ku suke son koya muku,idan kuma ba haka ba tsaf zan sa mutum ya bar cikin ahlina dan bana son fitina ,hadin kai da zumunci nake bukata a cikin zuri'a ta,kashedi ne haɗe da umarni duk wanda ya ga kuma zai gwada bata mana zumunci to Bismillah ban hana shi ba"daga haka ta yi gum da bakin ta tana mai ci gaba da taunar goranta.
Ajiyar numfashi Baffa Ali yayi sai kuma ya fara musu nasiha mai ratsa jiki akan zumunci,daga karshe shima ya kuma yi musu gargadi da akan duk wanda ya samu da tsiro da fitina acikin su tabbas shima zai dauki babban mataki a akan sa,dan haka su kiyaye, Abba yahya ma nasiha ya yi musu akan muhimmancin hadin kai,harma misali ya yi musu da kansu da suka hada kansu tamkar wasu yan biyu,hakuri suka basu tare da cewa insha Allah zasu kiyaye,su dai su mama murja ba su ce komai ba kuma basu nuna komai ba,sai dai kuma Allah kaɗai yasan irin ƙunar da zuciyar su ke yi,
Baffa Ali ya bawa Abbie damar gabatarwa da iyalin shi abin da yake son sanar da su,cikin biyayya ya amsa umarnin baffa Ali,shima addu a yayi ,kafin cikin nutsuwa ya fara da cewa, da farko dai ina so nasanar da ku cewa,na dawo gida bani ba kara fita waje sai dai ziyara in sha Allah,abu na biyu kuma shine dukkan ku kowa yasan cewa acikin tarin arzikin da Allah ya bani akwai wanda ba nawa ba,wato na dukiyar RAIHAN,,,,,gaba dayan su suka zabura cikin dinbin mamaki,har hada baki suke mama murja da momy hanne wajen cewa ,wai har yanzu kana nan akan bakan ka na bawa gaibu dukiyar ya'yan ka to ko dai da akwai RAIHAN dinne mu bamu sani ba?wani mummunan duka kirjin aunty amarya yayi ,take itama ta zubawa Abbien idanu kamar yadda kowa na wajen yayi don son jin amsar da zai bayar.
CHIBADO' s hause...........
Fuskar nan tam haka ya zauna kai kace bai taba murmushi ba duk da cewa murmushin ma ba ga kowa ba ne,gyaran murya Abban rabi ya yi tare da cewa,to wazirin gida kaji dai karar ka da innawuro ta kawo akan kaki yadda kayi aure,yanzu kuma an kawo lokacin da ba za ta daga maka kafa ba,dan haka ka gaya mana wadda ka fitar a matsayin mata sai aje a nema maka auren ta mu huta da korafin innawuro "ya sauke maganar da murmushi akan fuskarsa,hararar sa innawuro ta yi kafin ta ce"ai dama bakin ku daya wai kai me d'a ko?to wlh anan zai fada mana wadda yake so idan ba haka ba kuwa sati me zuwa za ayi masa baiko da rabi"wani kallo wazirrrrrr ya ɗago rikitattun idanun sa da suke cike fal da gajiya da kuma damuwar da take son kara masa,ya wurga mata,ey ko wane irin kallon ka Ni ba zai firgita Ni ba,idan ma kayi ne saboda na ji tsoranka"shi dai Abbu har yanzu bai ce komai ba,Abban rabi ne ya kuma tambayar sa a karo na biyu, girgiza kai kawai wazir ya yi,Abbu da sai a lokacin ya yi magana ya ce"kayi mana magana yadda zamu gane dan bana gane wannan Yaren bebayen naka,a hankali cikin cunkushewar murya ya ce"Abbu Ni bani da wata duk yadda kuka yi shike nan,daga haka ya mike ya bar falon,ko kallon inda yake innawuro bata yi ba,sai Abban rabi da ta kalla ta ce" shike nan sati me zuwa za a kawo kudin na gani ina so,zai yi magana ta katse shi tana mai kara tsuke kyakkyawar fuskarta irin ta wazir din ta.dole yaja baki ya tsuke dan fa innawuro nan ba sauki ce, addu'ar alkhairi kawai su kayi daga nan suka ci gaba da tattauna yadda ko mai zai kasance.
________________
Gaba dayan su su uku ne a dakin sai dai kuma yau an samu karuwar wasu mutanen biyu,wanda ga dukkan alamu yaran su ne,daya daga cikin yaran ya ce" yallabai an gama komai kuma munyi nasarar gano lambar da aka turawa sako lokaci da rana duk gashi a rubuce,saurayin ya fada yana mikawa shugaban jam'iya takardun da bayanan