Showing 132001 words to 135000 words out of 189984 words
Chapter 45 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
kokarin kawar da Yahya ina kawar dashi zan karasa Muhammad nur daga nan sai RAIHAN daga nan sai ramla,kafin cikin basira da hikimata dukiyar ta dawo hannuna.
*WASHE GARI*
Da sassafiyar yau mutane suka tashi da al'amarin da suka kwana dashi suka kuma tashi dashi.
Kamar yadda baffa Ali ya umarci surukansa da yayansa da jikokinsa taron tattaunawar cikin falonsa, to haka ce takasance,karfe takwas duk sun hallara a babban falonnasa wanda yakasance kamar nanne waje duk wata mitin da za su yi a gidan.
Ba tare da wani bata lokaci ba yayi musu addu'a tare da fatan samun lafiyar bangonsu wato Alh Muhammad nur,kafin cikin tsanaki ta kuma sigar da zasu fahimta ya yi musu bayani akan rayuwar RAIHAN da mafarin dalilin da yasa mahaifiyarta ta boyeta a matsayin mace ta bayyanata a matsayin namiji,cikin ikon Allah kuma Allah ya rufe sirrin har zuwa yanzu da yaga shine lokacin bayyanuwarta.
Ba karamin firgici suka shiga da jin wannan hikima ta Ubangiji ba,gaba daya. Sai aka shiga kallon kallo a tsakanin matan,ko wacce nason ta gani ko zata gano me wannan aika aikar,shi kansa baffa da Abba yahya zuba musu ido ya yi yana son ganin motsin kowa,haka Aunty Amarya da RAIHAN da kuma hajiyar agadex.
Shiru falon ya dauka na tsawon mintuna goma kowa yana tunani a ransa,sai dai duk yadda kowa yaso gane wata alama da zai nuna matar tana cikinsu hakan ya faskara", anan Aunty Amarya ta kuma tabbatar da cewa ko wacece wannan bakaramar shuuma ce da iya taku ba",
Baffa Ali tsoho me ran karfe shi ya kore shirun da cewa, ba zance ko wacece kar ta fasa yin abinda ta yi niya tun haihuwar RAIHAN ba,amma ina so ta sani cewa Allah da ya halicci RAIHAN shine ka dai yake da ikon daukar ranta,dan da ace ita din tana da iko to tabbas da alokacin da taso kasheta ta samu dama,daga karshe muna rokon ALLAH da ya bayyana mana makiyan mu na boye, Allah kuma ya tashi kafadar Muhammad nur ", gaba daya da Amin suka amsa, ita kuwa Raihan babu abinda ya dame ta sai halin da Abbie yike ciki, dan tun da baffa yasanar da ita komai da ya faru take kuka, tana son Abbie matuka son da ba zai musaltuba domin kuwa shima yana sonta,dan kuwa son da yake mata ne ma yajawo duk wannan halin da suke cikin daga shi har ita.baffan ne da kansa ya dinga rarrashinta,dakyar ya samu ta yi shiru saboda ya ce", idan bata yi. Shiru ba zai hana ta zuwa ganinsa.
____________
Za mu iya cewa mutane da yawa sun samu salama da nutsuwar zuciya akan kama shugabansu da ya zama maci amana kuma baragurbi acikin al'umma, Abba yahya dai yasha addu'a da fatan gamawa da duniya lafiya,sai kuma babban al'amarin da talakawa su ka fara zuwa da shi a safiyar ta yau,akan su kam sunyi mubaya'a lallai suna so a maida Abba Yahya kan kujerar Gwamna a matsayin me rikon kwarya,har zuwa lokacin da za ayi zaben gwamnoni, kuma suna rokon jam'iyar su da su tsayar musu dashi a matsayin dan takarar da zai maye musu gurbin gwamna,zasu zabe shi a matsayin gwamnansu na gobe in sha Allah.
Kafin kace wani abu an fara hawa teburin shawara da tafka muhawara tsakanin jam iyu da kuma manyan yan takarar da suke cikin jam'iyar dake ci a yanzu,kai ya dau zafi an kasa samun matsaya, talakawa kuma sun hura musu wuta akan su fa lallai ga wanda suke so a matsayin gwamna idan ba haka ba ba za su bawa Kowa kuriar su ba.
RUBY
Itama da nata burin ta tashi a yau, shi yasa ta shirya da wuri ta fice dan kawai tasan halin da ake ciki, a kuma ina makircinta ya kwana......✍🏽
Pls ayi comments kaina ya dau zafi ina bukatar kwarin gwiwar ku😀
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page49 ```
*Typing*
💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕
*NA*
*FATIMA Y. ADAM*
_____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*_____________________________________*
```Page49 ```
49
Abba yahya da su baffa kai kaf dinsu ma basu san abinda yake faruwa ba sai da suka fito daga gidan dan zuwa asibiti suka ga yadda yan jarida da al'umma suka yanyamesu,duk kokarinsu na son kaucewa tambayoyin yan jaridar amma hakan yaci tura ,sune rakiya a kafa har zuwa asibitin da Alh Muhammad nur yake kwance.
Yadda mutane su kayi cincirindo a jikin motocinsu babu ma hanyar da zasu wuce yasa,baffa Ali ya ce su tsaya su saurari yan jaridar ko dan Aunty amarya ta samu damar wanke kanta daga zargin da ake yi mata.
Ita dai Raihan gaba daya ta kasa sakewa saboda yau jinta take wata daban,bata taba shiga cikin mutane da shigarta ta ainahin mace ba,bata taɓa tsayawa gaban mutane a matsayinta Na mace ba,abu daya ne ya rage mata armashi shine halin da suka tsinci kansu,ga Abbie babu lafiya ga tarkon makiya dake zagaye da su.
Sanye take cikin wata hadaddiyar doguwar rigar Kuwait wadda ta zauna ajikinta ta fidda ainahin dirarriyar surarta ta cikakkiyar matashiya me dauke da sirrin kyau me tsayawa a zuciyar mutum,yadda ta yafa mayafin a rashin iyawa sai ya bada wani sitayal na daban, babu komai a fuskarta sai kwallin da Hajiya goggo ta zizara mata, a cewarta kwalli shi zai kara banbantata da namiji,duk da cewa Hajiya goggo na fushi da RAIHAN da kowa ma da ya boye mata wannan babban al'amari amma hakan bai hanata nunawa RAIHAN ɗin wata irin soyayya ba,a cewarta ita ce kadai jikanyarta mace,sai dai duk motsi sai ta zabgawa Aunty Amarya harara tana cewa cutata kawai a kayi Allah ya bani jika mace kamar wannan zankadediyar balarabiyar amma a kasa gayan duk da cewa nayi miki uzuri to amma me yasa lokacin Da kowa ya sani a ka ki sanar dani? Ita dai Aunty Amarya hakuri ne nata domin yanzu bata da wani power komai yinsa take a sanyaye gani take kamar lokacin rabuwar ta da RAIHAN ɗin ta ne ya zo.
Da yawan yan jaridan ba komai ne ya sa suke son hira da RAIHAN ba sai dan kawai suna son ganinta a ainahinta na RAIHAN.
Abba yahya ne ya fara fitowa daga mota ai take guri ya dau sowar talakawa ana sai kayi da yardar Allah,hannu ya daga musu fuskarshi cike da murmushi,dan jaridar dake kusa da shi ya yi saurin yi masa tambaya da cewa, yallabai ka dai ji abinda mutane suke fada akan ko nace talakawanku shin me zaka iya cewa a game da ra ayin su na son tsayawa dan takararsu dan ci gaba da jagorantar su? Dan gyaran murya ya yi kafin cikin kyakkyawan kalami ya ce", alhamdulillah babu abinda zance da jama a sai godiya,game da abinda suke fada Ni a yanzu bani da ta cewa har sai mun kai da tattaunawa a zauran majalisa", wani dan jaridar ya kuma wulloasa tambaya da cewa", yallabai shin dama kana da ra ayin tsayawa takarar gwamnan jahar nanne ko kuma dai za ka bi ra ayin yan jahar? A'a bani da wannan ra ayin a yanzu dan mu ra ayin mu shine gwamna ya cigaba da rike kujerarsa ya karasa shekara hudu idan Allah yasa muna da rai", wanda ya fara yi masa tambaya da farko ya kuma watsa masa wata tambayar, yallabai wannan abun da kayi na ceton dan uwanka da sauran talaka shin kayi ne dan Allah ko kuma kayi ne dama dan kasan talakawa zasu ce suna muradin ka?.
Ɗuf wuta ta daukewa mutane har masu kallo kai har su RAIHAN dake cikin mota",
Murmushi Abba yahya ya yi yana kuma fuskantar dan jaridar tare da kare masa kallo kafin cikin nustuwa ya ce", banyi wannan jihadin dan kowa yasoni ko yace a tsaudani takara ba, nayi ne domin Allah da dan uwana da kuma talakawan da suke cikin halin kakanikayi da cutar da su da akayi ta hanyar kashe ƴaƴansu da matansu",
Baffa Ali dake cikin mota daya da su Hamma Idris ya dubi Hamma Idris din ya ce", maza ka ce ", da su RAIHAN su fito daga mota nasan ganinsu zaisa yan jaridar nan su rabu da Yahya ", wannan tambaya haka ai duk gaskiyar mutum sai su sa ya mozanta", da sauri IDRES ya fita dan cika umarnin kakannasu,dakyar shima ya samu ya kai ga motar su Aunty Amarya.lokacin da ya fada mata sakon sakalo ta yi tana kallon dubban jama'ar dake wajen tana tunanin ta yadda za ayi ta fara magana da su," Raihan ce ta riko hannunta sannan cikin taushin murya ta ce", Mami karki damu ki zauna ba zaki iya magana da su ba saboda baki taba yi ba,dan haka zan fanshe ki zan basu duk wata amsa da suke bukata in sha Allah ", ajiyar zuciya Mamin ta sauke tana kallon RAIHAN ɗin da ta saki hannunta tana kokarin fita daga motar,inna maimuna ce ta dafa ta tana cewa kar ki damu Raihan zata yi komai tun da ita aikinta ne babu abinda zai gagareta.
*KALLO YA KOMA SAMA*
Bude murfin kofar motar da a kayi yasa mutane da yan jarida maida hankalinsu kan motar,kafarta ta fara zurowa wadda ke sanye cikin wani haddadan takalmi flat me madauri baƙi wanda ya matukar haska farar kafarta da tamkar bata taka kasa da da ita,kafin a hankali ta zuro gangar jikinta zuwa ƙayatacciyar fuskarta da take ta sheki da walwali duk kuwa da cewa tana cikin alhinin abinda ke faruwa,tsayuwar ta a gurin yasa gaba daya muntane suka jiyo kanta, yayin da maganganu suka fara tashi a gurin kowa da abinda yake fada wasu Masha Allah tubarakalla,wasu wowww wannan halittarfa, Allah kadai yasan manufarsa ta boye RAIHAN domin wannan ba dabarar mahaifiyarta ba ce,cewar wasu dattijai.
Take yan jaridar suka fara wawason son hira da ita harma ta fara rasa tambayar da zata amsa, idanunta ne suka sauka kan salim abokin aikinta a Chibado FM hakan yasa ta yafitoshi,da sauri ya matsa yana saita abin maganarsa,sannan ya fara da cewa ", Hajiya RAIHAN ko za ki bamu hadin kai mu gayyatoki gidan. Rediyon mu dan tattaunawa akan abinda ya shafi rayuwarki?wani aikin sai gidan rediyon Chibado tabbas wannan dabara ta salim ta yi mata hakanne zai bata damar fedewa al umma buri har wutsiya,dan haka cikin taushin muryarta da a da ake kiranta da Muryar mata ta ce", in sha Allah zan baku wannan damar duk sanda kuka nemeni zan amsa kiranku", wani dan jaridar ne ya yi mata tambaya da cewa ", shin me zaki iya cewa a game da sabon yanayin da kika tsinci kanki a ciki ma ana da kina fitowa cikin mutane a matsayin namiji yau kuma gashi kin fito a matsayin mace? Duban dan jaridar ta yi sannan cikin kamewarta ta nutsatstsiyar budurwa me cike da aji wanda a da sam basu bayyana ba Bama tasan tana da su ba,ta ce", ey naji wani iri naji kamar ba Ni ba,ummm a takaice dai ji nake kamar an sauyani", zai kuma yin wata tambayar ta dakatar da shi da cewa pls duk abinda kuke so kuji daga gare Ni zaku ji shi amma yanzu ku danyi excuse Dina ina son duba mahaifina bana cin mood din da zan iya fada muku abinda kuke sonji",
Tana gama fadar haka sai ga yan sanda wanda aka turosu musamman dan tsaron lafiyar Abba yahya sune suka kore mutanen da suka hana su wucewa,tare da yan jarida, duk da haka dakyar suka samu suka shige cikin asibitin.
Wasu irin ƙwallah ne suka cika idanun ruby da komai ya faru akan idonta ,me ta yi haka ne ? Ita da ta yi wannan abu dan tozarta RAIHAN da ahlinta amma shine yake nema zama silar ɗaukakarta,wata zuciyar ta ce", da ita ke banza ce ai ba dan wannan ka dai kika yi ba ,babban abinda kika yi danshi ai ya yiwu tunda gashi babu wazer a gurin yanzu haka ma sunyi tsiya_tsiya tun jiya ke baki sani ba",to amma tozarcin da RAIHAN zata yi shine zaisa su ji zafin wazer ɗin matuka anya kuwa bata haka rami ta zuma kanta ba?to dai ga wazer baizo wajen ba to dukkan alamu ta yi nasara", wannan tunanin da ta yi yasa ta ɗan sauke ajiyar zuciya.sai dai me juyawar da zata yi sai ganin sabuwar motar da wazer ya yi oder su a cikin satinnan ta yi, kafin ta gama tabbatarwa shidinne ko ba shi bane,tuni ya yi fakin kusa da motarta kafin ya fito kuwa tuni kamshinsa ya gama baibayye wajen,wani irin kakkauran yauwu ta hadiye kirjinta kuwa babu abinda yake sai sama da ƙasa, a hankali aka bude motar dake bayanshi wani kakkarfan body gard ya fito ya zo ya bude mishi kofa.
A hankali ya zuro kafarshi dake sanye cikin wani arnan coversue yana ta zuba kyalli,kafin a sannu gangar jikinshi ta biyo baya,kamshinsa kuwa tuni har kewaye rabin faffadan filin harabar aje motocin dake a sibitin,sanye yake cikin kayanshi na kullum ash din cot sai sunglasses da ya kara bawa gewayayyen sajenshi damar fitowa kasancewar glas din fari sai yasa kake hango kwayar idonshi tar a cikinsa.bai san meye kalle _ kalle ba dan haka bai lura da motar rabi a ba,kai tsaye ya wuce cikin hospital din gard din da Abbu ya kawo mashi sabbi wadanda suka san aikinsu na take mishi baya wasu kuma sun kame wajen motarshi saboda tsaron lafiyar shi,a hankali yake takunshi me cike da nutsuwa, kallo daya za kayi masa ka kasa yin na biyu saboda kwarjini da haiba tare da ilhamar da rabbi ya hore masa namiji ne iya namiji da duk wata mace mai suna mace zata yi burin mallakar sa matsayin miji uba zaiso ya same shi matsayin ɗa haka uwa zata so a ce danta ne", Masha Allah abinda mutanen da yake giftawa suke faɗa ke nan.
Wani irin ihu me tafe da kuka rabi a ta saka tana mai dukan sityarin motar,ji take tamkar zata yi hauka,wai me yake shirin faruwa ne ? Anya abinda Surry ta sa nayi hanya ce me bullewa? Ina ba zai yiwu ba wallahi,in dai a wannan lokacin banci nasara akan RAIHAN ba to wallahi sai dai kowa ya rasa zan kashe wazer ɗin kowa ya huta wallahi ba zan yadda ina ji ina gani ya zama nata ba bazai yiwu ba", ita kadai ke ta mannawa kanta hauka a cikin mota tamkar dai ta zare din da gaske.da sauri ta goge fuskarta ta fito daga motar to nufi cikin asibitin, dan bata jin zata iya tafiya ba tare da ta ga sakamakon da zai kwantar mata da hankali ba,dole ta bishi taga yadda zata kaya idan hakanta bai cimma ruwa ba sai ta san irin shirin da zata yi a gaba.
_____________
Hankalin yan takarkaru fa ya tashi da wannan hukunci da to lakawa suka yanke,dan haka babu shiri shugaban jam iya ya haɗa mittin din gaggawa,yan majalisu da sauran masu mukamai tuni a aka halla dan yanke hukunci,akan wannan zaɓin da talakawa su kayi.
Anyi muhawa an tafka gumurzu anyi kace nace daga karshe a ka tsaya a matsaya daya a shawarar shugaban jam'iyya", acewarsa idan har suka ki yadda da abinda suke so na tsayar musu da Abba yahya to tabbas zasu shiga cikin zargin mutane akan cewa da hadin makinsu tsohon gwamna yake aikata duk ta asar da yake yi,amma idan suka tsayar dashi dantakara to tabbas talakawa zasu yadda dasu za kuma aciresu daga zargi a matsayinsu na yan jam iya daya da gwamnan kuma wadanda suke karkashinsa,sai dai fa sunce ba su yadda da rikon kwarya a ba saboda a yanzu dufuty ne kawai ya cancanta da yayi rikon kwarya har zuwa lokacin zabe,shima kuma wannan dama ce a gare shi ta tsayawa yayi jinyar dan uwanshi a nutse,kowa ya yi na an da hakan ƙalilan ne basu amince ba sai dan basu da yadda za su yi, wannan muhawa da aka tafka babu Abba yahya a ciki kasancewar sunyi masa uzuri akan rashin lafiyar dan uwansa.
Bayan fitowa daga wannan tattauwarne suka zanta da yan jarida in da shugaban jam'iya ya basu tabbacin cewa sun tsaida Alhji Yahya matsayin dan takarar gwamnan gobe,amma fa ba zai yi rikon kwarya Ba saboda bashi ya cancanta ba matemakin gwanane kawai yake da wannan damar, ya dora da cewa a ganina shima zai samu nutsuwar fuskartar abinda yake gaban shi wato jinyar Muhammad nur,idan yaso sai ya tsaya a matsayin dufuty.
Talakawa sun gamsu da jawabin shugaban jam'iyya dan haka kowa ya shiga yiwa Abbie fatan samun lafiya da fatan zuwan zabe lafiya domin su cika burinsu na bawa Abba Yahya kuri'arsu wanda suke ganin ita kadaice hanyar saka mishi akan jihadin tsamosu daga hannun baragurbi da ya yi.
_________
Cikin tashin hankali Dr sanater ya dubi shugaban jam'iya bayan dawowarsa daga mitin din da suka yi da tattaunawarsa da yan jarida,ya ce", haba shugaban me kake nufi da yin hakan,kasan cewa idan har kuka tsaida mutumin nan takara tabbas babu makawa sai ya ci", idan kuma ya ci tabbas mune a ruwa saboda duk wata hanyar samun arzikinmu sai ya tosheta", Alh ja'e ya dora da cewa wannan maganar haka taka haka take Dr dan haka kai shugaban jam'iya sai ka yi mana bayanin da zamu gamsu",dan jan numfashi ya yi kafin ya ce,tabbas abinda kuka fada haka ne to amma Ni nayi hangen da ku kuka kasa yinsa,kun san dai kuma da tabo gurin yansandar jahar nan, a wancan karon ba dabarar ku ce ta fidda ku ba,dan haka dole muyi takatdantsan gudun tonon asirinmu,mu dai kunga iya kar Musa akashe mana,mu wawashi kudin talakawa mu zuba a susunmu,kunga kenan harsabibancinmu bai kai na wancan shahararren gwamnan ba,to asirinsa ya tonu mu kuma su waye da asirinmu ba zai tonu ba,dan