Showing 177001 words to 180000 words out of 189984 words

Chapter 60 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt

27 Nov 2024

15605

naje gurin his excellency na fada mai bukatata zai amsa min.




To amma da naje gurinsa sai na samu kaina da jin tsoran fada masa,ban taba kokonto akan aikin tsohuwa ba sai a ranar, hakan yasa na yi yan kame kame na na tashi zan tafi,maganar da his excellency ya yi min ita ta dakatar dani daga fita daga falon da nake kokarin yi,kun san me ya ce min? Yahya kaji tsoran Allah ka sani cewa akwai ranar da Allah zai tsaidamu a gabansa,dan Allah Yahya ka daina kokarin cutar da dan uwanka,Ni ba zance kar ka cutar da Ni ba amma shi dai ina rokon alfarma kar ka cutar dashi domin zuciyarsa me kyau ce", ban taba sanin cewa Garba ya san abinda nake aikatawa ba sai ranar wato zuru ya yi min kuma bai tona min asiri ba,a maimakon naji shawararsa ko nace nasiha sai kawai hakan ya kara harzuka Ni na fice daga gidan fuuu ina kumfar baki da borin kunya,ranar banyi bacci ba ina ta saka abinda ya kamata nayi daga karshe na tsaya akan shawarar da zuciyata ta bani na samu karfin gwiwa sosai akan tunanin da nayi,ko da his excellency ya fadawa nur ba zai taba yadda ba idan har ba shaida ya bashi ta gani da ido ba,to suma shaidun a daren nasa aka kama minsu wato haidar wanda nake da tabbacin cewa Flash din da shaidar ke ciki tana hannunsa idan kuma na kama shi ai his excellency bashi da wuri aya shaida, wannan dalilin ne yasa na kama haidar wanda dama cikin shirin kama shi nake saboda bincikena da ya nuna min akwai shaidar da yake shirin gabatarwa a hannunsa.




Ban san ya akai ba washe gari na shiga bangaren nur dan ribatarshi zuwa gidan gwamnati sai kawai mamin Raihan take sanar dani ai tun sassafe ya fita his excellency ya kira shi yana nemansa da gaggawa,duk da cewa ban karaya ba amma tabbas na tsorata dan nariga na kwana da sanin cewa batuna zai sanar da nur.




Hakan yasa nayi azamar bin bayansa,ganin har lokacin his excellency bai sanar da nur ba sai hankalina ya dan fara kwanciya na samu window falonsa na musamman ta can baya na labe ina leke da kasa kunne,to amma abinda ya bani mamaki his excellency ya kasa sanar da Nura komai akaina har wani tsawon lokaci suna zaune babu wata hirar nishadi bare ta ɓacin rai tamkar dai masu zaman makoki, shi kuma Nura bai tambayi his excellency komai ba yana dai binsa da yadda yake so akan zaman shirun da ya ƙirƙirar musu.




Har lokacin Sallah ya yi suka tashi sukayi sallah wanda Ni kuma da wannan damar nayi amfani wajen zagawa kiching wajen kukun da na bawa wannan aikin na saka shi a gaba sai da na tabbatar da ya saka wannan gubar a karo biyu duk da cewa ya tabbatar min da ya saka a karin kumallonsu na safe,dake ba akan idona suka ci ba sai nake kokonto akan cin nasu shine dalilin da yasa na kuma zuba musu.




Cikin sauri na koma inda nake a tsaye ko gajiya banyi saboda na sakawa raina cewa yau sai Muhammad nur ya mutu his excellency kuma sai ya kwana a gidan yari kafin shima a yanke masa hukuncin kisa kunga na jefi tsuntsu biyu da dutse daya ke nan. Dan shiru ya yi kafin ya cigaba da cewa ba saina baku labarin abinda ya biyo baya ba nine na kira yan sanda suka tafi da his excellency.


Burina na hawa wani mataki a siyasa ya cika sannan burina na duniya ta Sanni ya cika duk a wannan lokacin,abu daya ne yazo min a tamgarda shine Muhammad nur bai mutu ba,kuma dole sai ya mutu ne za a yankewa his excellency hukunci tunda wadancan laifukan babu shaidar da ta tabbatar da cewa shine ya ke aikatasu hakan ya nuna min cewa tsugunne na bata kare ba.




Yana zuwa nan alabarinsa ya fashe da wani mahaukacin kuka wanda yake yinsa bil hakki da gaskiya,yana jin takaicin rayuwarsa da ta ahlinsa.




Take garin ya hargitse kowa da irin kalar tsinuwar da yake yiwa Abba yahya,wasu kuwa kuka suke na tunawa da yan uwansu da ya yi sanadinsu.




His excellency da iyalansa kuwa hamdala suka dinga yi ga Ubangiji, fuskokin su cike da farin ciki na wankesu da Allah ya ya yi ba tare da tsuminsu ko dabararsu ba.




Jami'an tsaron da suke kewaye da gidan dana cikin gidan kuwa basu yi wata_wata ba gurin kama Bashir da Abba yahya,su Hajiya goggo na gani a ka saka danta a motar da take da tabbacin baza ta taɓa dawo dashi ba,tana kallon lokacin da yake hade hannayensa biyu yana rokon gafararsu ita da baffa da Abbie,a hankali take jin zuciyarta na sosuwa,lallai na yadda cewa ɗa duk lalacewarsa ɗa ne kuma uwa sonshi take yi kamar yadda a wajen da uwa duk lalacewarta take uwa a wajensa,tabbas Hajiya goggo taji daci da bakincikin fitowar Yahya daga tsatsonta amma ya ta iya da wannan kauna da jin kan dake tsakanin ɗa da mahaifi,hannu tasa ta share hawayenta tana mai binsa da addu'a ba wai dan tana da tabbacin zai zama wankakke kuma me tsarki ba,




Hatta da Abbie sai da yayi kuka dan wallahi yana son dan uwanshi so na hakika shima dai daga karshe addu'ar ya raka Abba yahya da ita.




Jiki babu kwari suka rankaya suka koma cikin gida kowa da nasa ciwon zuciyar wanda basu san ranar warkewarsa ba,wazer yana kallo hajiyar agadex ta janye raihan su kayi ciki tana cewa muje kema ki ɗan samu nutsuwa", numfashi ya sauke tare da bude idanunsa sosai akanta cikin zuciyarshi yake cewa duk ki gama wayon naki daga karshe dai dole ki bani matata dan babu wata nutsuwa da zata samu a wajenki", motarsa ya shige securitys din da ya riga ya fara sabawa da bibiyarsa da suke suka take mishi baya.




A halin yanzu babu cikowar mutane a kofar gidan saboda an tafi da wanda suke son gani yan jarida kuma suke son tambaya, tunda a halin yanzu kowa ya samu amsar tambayar dake cizon zuciyarsa,hakanne yasa babu mutane sai yan tsirari suma yan cikin unguwar ne da suka tsaya maida magana.




Da wannan damar mutanen ABBAN rabi su kayi amfani wajen saita makamansu don cika umarnin ogansu,ko wanne yana labe a maboyarsa yana saita kibiyarsa ga abin harinnasu.




Tamkar wani waliyi haka wazer yaji a jikinsa akwai wani abu da aka shirya masa a wajenann,hakanne yasa yasa drivansa ya tsaida motar,sir lafiya dai ko? Drivannasa ya tambaya cikin ladabin da akasan ko wane mutum yana wa uban gidansa,ina ga fa akwai matsala maza kira min wayar motar su daniyal ok sir ya fada cikin sauri tare da cika umarnin ogannasa,bayan yaji alamar dagawa yayi saurin saka wayar a amsa kuwa,cikin nutsuwarshi dake bayyana a dukan aiyukansa ya ce", daniyal ina so ku fito cikin dabara ku duba wasu wurare a wajenann duk wanda kuka ga alamunsa da rashin gaskiya ko da makami a hannunsa ku kamashi is don daniyal ya fada cike da fatan cika umarni.




Ciska da suke can labe suna zura idon ganin wazer ya fito daga cikin mota,saboda a tunaninsu wannan tsayawar da yayi akwai wanda yake jira Wata kila ma matarsa yake jira sun san kuwa idan ita ce dole zai iya fitowa shi yasa basu harba kibiyar a jikin tayar motar Ba kamar yadda da farko suka tsara,sam dukkansu babu wanda yayi zato ko tsammani kamar daga sama haka suka ga garadan samudawan securitys din wazer akansu ko wannensu hannunsa rike da bindiga me rai wadda suke da lasisin riketa da yin harbi,zube makamansu su kayi tare da yin saranda domin duk rashin tsoranka ka haɗa hanya da wadannan mutanen dole zuciyarka ta girgiza,kaɗa ƙeyarsu su kayi gaba ɗayansu su biyar ɗin,.waya daniyal ya kira daga can headquarters dinsu akan a basu jami ai,cikin kankanin lokaci sai ga jami'ai na fararen kaya sun bayyana,ba tare da wani bata lokaci ba suka kaɗa keyarsu ciska zuwa gun wanda ya turosu,ba su yi gardama ba kuwa suka jagorancesu har zuwa gidan ABBAN rabi da ya basu tabbacin cewa babu inda zashi har sai sun kawo masa kyakkyawan sakamako akan wazer ɗin.






Tun bayan gama sauraron labarin da Abba yahya ya bayar sai kawai ya tashi ya shige dakinsa,yana ji kamar jikinsa zaiyi sanyi,zama ya yi bakin gadonsa ya zuba tagumi,tunani yake yi idan har irinsu Abba yahya zasu shuka irin wannan ta asar kuma asirinsu ya tonu to shi din karamin alhaki tayaya ne nasa ba zai tonu ba?tayaya Allah zai kawo karshen irinsu tsohuwa shi ba zai kawo nasa karshenba? Anya kuwa idan ya cigaba da haka ba zai iya samun kansa cikin katuwar nadama irintasu Abba yahya da inna maimuna ba? Kafin ya bawa kansa amsa ne wayarshi ta fara kara alamun kira na shigowa,dubawa ya yi yaga ciska ne,da sauri ya dauka yana fatan basu aikata aikin da ya sasu ba,ka fito muna waje", abinda ciska ya ce dashi ke nan wanda hakan umarni ne daga jami'in da ya bashi damar yin wayar.


Jiki na rawa abban rabi ya fito a tunaninshi ko basu samu nasara ba,wanda a Yanzu shine babban fatanshi,sai dai abinda ya gani shi yayi matukar razana shi da saka shi cikin tashin hankali wato dai abinda yake gudu din ya riga da ya faru,asirinsa ya tonu,ji yayi baya tsoran hukuncin da za ayi masa amma yana tsoran idanun mahaifiyarsa da dan uwansa shin ya Abbu zaiji idan yaji cewar dan uwanshi ciki daya yana son ganin bayan ahlinshi? Kafin ya ci gaba da tunanin da yake yaji an sakale hannunwanshi da sarka,ku bashi dama ya sanar da iyalansa", wani daga cikin mota ya fada da alama shine babbansu,tasa keyarshi mutum biyu su kayi har cikin falon gidan,inda suka sami rabi a da mamanta tana faman rarrashinta akan ta ci abinci kar yunwa ta kamata.




Da sauri suka mike tsaye jikinsu na rawar tashin hankali,abban rabin bai iya ce da su komai ba,sai daya daga cikin jami an ne ya basu shedar ko su su waye ta hanyar nuna mu ID dinsa,sanan ya juya suka fice da abban rabi,kuka rabi a da mama suka saka suna binsu akan su yi hakuri amma tamkar da dutse suke magana ,haka suna ji suna gani aka tafi dashi suka barsu a bakin gate suna kuka kamar ransu zai fito.




Biyu daga ciki ne suka wuce suka fito da abu Huraira wanda babu wani ja ya sanar dasu wanda ya sa shi ya zubawa wazer guba,basu da duwa da haka tunda shima a halin yanzu yana hannu,dan haka suka wuce da abu Huraira akan idon sauran staff da hakan ya matukar tsorata su shi yasa kowa ya shiga karkace zuciyarsa idan ma da wani abu makamancin Wannan a cikinta to sun kade shi, Allah Ubangiji ya raba mu da son zuciya.




Sai yanzu wazer yaji ya dan samu nutsuwa,ko da ya je gidan bai shiga bangarensa ba sai da ya tabbatar ya sanar dasu innawuro abinda ke faruwa iya wanda ya sani,daga haka ya kabe jikinsa ya wuce samasansa ya barsu cikin wani sabon tashin hankalin, innawuro kam tasha kuka baranma da su Khalid suka kara sanar da ita abubuwa da yawa da suka faru da irin tsallake tarkon abban rabin da yayansu yake yi,Abbu da hajiyar Kano ma sunyi kukan takaici da bakincikin rayuwar da dan uwansu ya saka kansa a ciki,daga karshe dai dole kowa ya hakura, innawuro da kanta ta ce", gobe Khalid zai Kaita gidansu Raihan dan tayi jaje sannan ta faɗa musu sati na gaba za ayi biki Raihan ta tare a gidanta, wannan maganar ita ce ta sanyaya musu rai daga kunar da suke ji,hadiyar Kano kuma ta kara da cewa zata karbi kudi wajen wazer su tafi Dubai ita da Ruma da shukra su hadowa RAIHAN lefe na kece raini,ba su tashi da ga wajen ba dai sai da suka tabbatar sun maye gurbin bakincikinsu da farinciki,duk da cewa ba wai abin ya bar ransu ba ne......✍🏽


*Typing*

💕
*BOYAYYIYAR RAIHAN* 💕


*NA*




*FATIMA Y. ADAM*










_____________________________________*


*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation


*_____________________________________*






```Page67 ```




"""""Komai yayi farko yana da karshe,duk a baya gani suke kamar zuciyarsu ba zata yi sanyi ba,gani suke kamar abin ba zai wuce ba,sai gashi yau da ake cinye sati daya da faruwar komai suna cikin walwala da farinciki,gashi duk inda ka duba gidan mutanene cike yan uwa na nesa da na kusa kowa yazo dan tayasu farincikin shagalin bikin yar gata yar so wato RAIHAN MUHAMMAD NUR,bikine aka shirya na manya da sarakuna wanda aka tsarashi cikin tsari me kyau da burgewa,ta bakin mutane da suke cewa saima ranar,jiddo ita ce aminiyar amarya tun da can wanda Raihan take shan shaƙiyanci a gurinta,wai ashe dama duk wannan abun da take yi akan wazer so ne wanda ya haifar da kishi, Raihan bata ce mata komai sai dai harara dan ita kadai tasan azabar da take sha na hanata ji da ganin wazer da aka yi sai wani uban gyaran jiki da ake ta yinsa wajen sati biyu,yanzu hatta kai da cewa ita kanta kamshin da take yi ya fara damunta dan duk inda ta motsa ko ta gifta sai kaji wannan sihirtaccen kamshin hadin turarukan da yar me duguri ta ke yi mata.




A Bangaren gidan su wazer ma yau hajiyar Kano ta dawo ita da shukra da Ruma,lefe suka hado na gani da bada labari,tabbas idan na tsaya gaya muku abinda lefennan ya kunsa za mu cinye lokaci ne ba tare da mun gama ba, komai classqui aka saka saboda wazer ya ce Raihan ta musamman ce dan haka komai nata dole ya kasance na musamman,to suma dai a bangarensu sai dai muce alhamdulillah dan kuwa kowa ya saki ransa yana walwala yadda ya kamata,sanann sun rufe komai iya su ba tare da sun bari dangi na waje sun san abinda abban rabin ya aikata ba, wannan ne yasa wasu yan uwan da yawa suke tambayarsa.




A bangaren Rabia kuwa za mu iya cewa abin ba sauki, dan sosai ta kwanta ciwo babu kowa tare da ita sai mahaifiyarta wadda take ci gaba da yi mata fadan bin rayuwa a sannu,ita dai bata da abincewa sai ruwan hawaye dan yanzu bata da wani buri illa ta bude idanunta ta ganta a dakin mijinta kai ita fa ko da wazer ba zai dinga kallonta ba zata iya zama dashi dan soyayyarsa ta zame mata ciwo me mugun muni.




Surry kuwa ta debowa kanta jaraba dan abin ya ci gaba tun tana tunanin warkewa daga karamar cutar da ta fara har abin ya fara bata tsoro,daga karshe dole iyayenta suka sani a ka shiga nema mata magani amma abin kamar kara mata shi ake yi,dan yanzu ta kai ga cewa ko fitsari bata iya yi saboda yadda gabanta ya koma,wasu irin kuraje ne masu wari suke fitowa a duk inda ta sosa daga nan kuma sai su kumbura wannan ne yasa gabanta gaba daya ya zama baya moruwa,a hankali dakin ya fara daina shiguwa saboda azabar wari,mahaifiyarta kanta bata iya shiga dakin.






Tsohuwa me jini ......




Tun lokacin da wannan mesar ta kanannadeta bata kuma barinta ta motsa ba,ga dai ta da ranta amma wannan mesar tana tare da ita babu abinda take sai azabtar da ita,a maimakon ta sareta a'a sai ya zamana cizonta kawai take duk sanda taso,daga baya kuma ta fara cinye wasu sassa na jikinta wanda tsohuwa tana ji tana gani sai dai ta yi kuka da iya idanunta da kuma zuciya,a hankali mesar nan take cinye tsohuwa tana kuma janyota daga cikin dajin zuwa cikin gari saboda al umma suga irin mutuwar wulakancin da zata yi ko hakan ya kuma zama izna ga al'ummarmu.




Su Abba yahya kuwa suna can a garkame babu wanda ya kuma waiwayarsu,hatta da lauyansu ya gujesu,shi yasa Bama su san ranar shiga kotun ba,yo wane lauya dama ya rage musu ai su yanzu sun san tasu ta kare.




Shima Idris Shari'arsu rana daya duka a kasa har da inna maimuna me yunkurin yin kisa har sau biyu,Dukansu cike suke da nadamar da bata da wani amfani garesu tunda sun riga sun aikata laifukansu.






A bangaren his excellency kuwa dakyar mutane suka bari yayi hutun kwana biyu sannan ya koma gidan gwamnati shida iyalansa tare da rakiyar dubban al'ummarsa da suke a karkashinsa,cikin kwanakin da ya dawo bakin aiki yayi abubuwa masu dama wa'danda sai dai muce sambarka.




Haidar ma ya samu sauki ya koma gida tare da ƙarin girma zuwa Kwamishinan yan sanda.




Abban rabi da su abu Huraira da yaransa duka tare aka kullesu aka saka ranar Shari'ar su bayan kwana ɗaya da yin shari'ar su Abba yahya,daga karshe dai yan sanda sun matsashi ya sanar dasu sawa ya yi a kashe Khalil,ciska da shi aka saka ya yi aikin ya bada tabbacin cewa bai kashe kalil din ba,fansar kansa ya yi ta hanyar bashi kudi masu yawa ,dan haka ya sake shi amma ya bashi damar barin kasar saboda kar abban rabin yasan bai kasheshi ba,jin haka yasa take kwamishina ya baza cikiyarsa tunda har iyayensa basa nan bare a nemi sanin inda yake ta hanyarsu.




_________




Biki buduri.....ranar Alhamis aka saka Raihan a lalle.




Ranar juma'a kuma akayi kamu,wani irin kamu na burgewa wanda aka yi shi da al'adun kamu biyu,kamun buzaye bangaren uwa ke nan,sai kamun Fulani wanda bangaren uba suka kamata daga nan a ka raba kayan al'adu na ko wane yare fillo da buzanci,idan nace muku kayatuwa da haduwa to na rage muku armashi,sai mu ce Masha Allah,a bangaren amarya kuwa duka shigar da ta yi babu batun tsayawa bada labari kunsan wacece RAIHAN dan haka kawai kuce Masha Allah domin kyaune ya taka rawarsa ranar.




A ranar kuma aka karbi lefen da ya gigita jama a da dama ya shiga bakunan mutane da dama,wasu alkhairi suke fada wasu kuwa sai hakuri dan mutum ba a iya masa.




Lokacin da wazer yayi arba da hotonta da yasa jiddo ta tura masa, sai

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login