Showing 141001 words to 144000 words out of 189984 words
Chapter 48 - BOYAYYIYAR RAIHAN..! By Fatima Y Adam.-1.txt
kama matar ba.da gudu securitys suka shigo saboda jin karar da Aunty Amarya ta yi,suna shigowa suka tarar da ita kwance tana taga tagan tashi hannunta na nuna kofar shigowa, da sauri nos suka dagata suka dora akan gado cikin kankanin lokaci suka fara bata taimakon gaggawa,Dr Sabo ne ya shiga musu fada akan abinda ya faru duk da basu san komai ba,dakin cc camara ya nufa bayan ya tabbatar da tsaron dakin tare da gargadi me girma ga Saken da securitys din sukayi,lokacin da cc camara ta shiga nuna abinda ya faru kasake ya yi yana kallo cike da mamakin wayo irin na matar,baya yasa aka dawo maana tun shigowar matar,a nan yaga yadda ta yi ta shiga wato wasu ta fara turowa bakuwar fuskar da ba a sansu ba suka nemi shigowa nan securitys din suka hana shigar ta su wanda hakan ya janyo cece kuce tsakanin mutane biyun da securitys din,wanda ita kuma da wannan damar ta yi amfani ta shige reseption din har ta shiga dakin ba tare da hankalinsu ya kai kanta ba.
Hankalin Dr Sabo ba karamin tashi ya yi ba,da sauri ya koma ya kira sauran likitocin da alhakin kula da Abbie yake hannunsu suka rufu akansa dan duba lafiyarsa,cikin ikon Allah suka ga bata yi nasarar karasashi ba amma fa tabbas Abbie yana cikin critical condition sai dai kawai mu bi shi da addu'ar samun sauki,tunda rayuwar ba a hannunmu take ba.
Sosai take aje numfashi bayan fitowarta daga asibitin Allah ne ya taimaketa duka securitys din duk yawansu basu kula da ita ba amma tabbas da sai sun biyota kuma sai sun kamata,har yanzu ƙirjinta bai daina bugu ba dan kuwa hakika ta tsorata,kallon mai nafef din nata ta yi tana cewa maza maidani inda ka dauko Ni", ok Hajiy... Bai karasa fada ba yaga mutum ya zauna gefan nafef din yana cewa muje fuskarshi sanye da facemask shima", cikin razana ta ce", kamar ya muje babu inda zaije sai ka sauka inda zaka ba nan muka nufa ba", ke da ba mashin ɗinki ba Hajiya ina ruwanki", ya fada yana juyawa tare da yin kasa da facemask dinsa,wani irin dafe kirji ta yi kafin cikin rawar baki ta ambaci sunansa Yusuf meya kawoka nan? Abinda ya kawo ki shi ya kawoni", ya bata amsa yana maida facemask dinsa,kar ki tsoarata ba tona miki asiri ne ya kawoni gareki ba,kawai ina so mu hada hannu ne,dan da ace tun farko nasan me yasa aka boye RAIHAN da tuni na nemo makashiyar RAIHAN ɗin dan hada hannu da ita kuma da baki riski kanki a tashin hankali irin na yau ba,dan haka kai me dan sahu muje waje mafi sirri inda za muyi ɓoyayyiyar ganawar sirri tsakanin masu son kama abu guda,ba dan ta gamsu da abinda ya fada ba ta amince sai dan kawai tana tunanin ko da da wata manufar yazo ita tafi shi wayo da sanin duniya dan haka tasan yadda zata fidda kanta ta barshi.
Tun fitowar su Khalid ABBAN rabi yake tsaye yana kallonsu jin zuciyarsa yake tamkar zata buga saboda tsananin tsana da kyashi da hassada,tunda suka dawo wazer ya dora su akan harkar Companys ya tsara musu komai dan haka suka bi suka dabaibaye komai,ya zamana bashi da wani babban matsayi duk abinda zai shiga ko ya fita sai da saninsu,gashi kuma bayan su din har wasu ma'aikatan wazer ya kuma diba masu tsananin kaf_kaf ko mai a tsare yake tafiya yanzu sabanin da,gashi yanzu cikin kwanakin da basu fi goma ba abubuwa sun fara daidaita a Companys din,shi yasa ABBAN rabi yake cikin wata irin takura gashi duk wata hanya da zaibi dan ganin ya kawar da wazer hakan ya ci tura,wata irin kwafa ya yi yana jin ba zai iya ci gaba da kallon kayan takaici ba a gurin shi,dan haka a maimakon ya shiga gidan kawai sai ya koma cikin motarsa ya bata wuta ya kwashe ta a tsiyace", duban juna salim da Khalid su kayi kafin suka kwashe da dariya dan su din shakiyai ne na kin karawa ba kamar yayansu suke ba,duk tsayuwar da abban rabin yake suna kallonsa kawai sun dauke kansu ne a zuwan basu Ganshi ba dan duk hakan yana daga cikin tarkon da suke son yi masa.
Cikin bakin ciki ya shiga falon gidansa a nan kuma ya yi katari da rabi a gaban mahaifiyarta tana rusa mata kuka", turus ya yi yana kallonta kafin cikin tsawa da son huce haushin kaza kan dami ya ce", ke kuma sakarya me aka yi miki kike mana kukan jan mutuwa? Rarrafawa ta yi gaban shi ta rike kafafunshi tana cewa Abba wazer ne baya sona yau kusan kwana goma ban sashi a idona ba wai kuma a matsayin muna gida daya,idan na kai karar sa gurin innawuro sai ta hauni da fada wai bani da aji su kuma iyayensa ba ganin laifinsa suke ba,Abba tunda aka yi auren mu sau daya ya yi kwanciyar aure da Ni," zama ABBAN rabi ya yi ba tare da fuskarshi ta nuna alamun rashin dacewar maganarta ta karshe ba,saima cewa da ya yi rabi har yanzu kina son Wazer? Abba a da ina son wazer amma tunda ya ci amanata ya auri waccan yar daudun shike nan na ji ya ficen a rai wallahi Abba yanzu ko kasheshi zan iya yi,amma fa da zai dawo gareni ina son shi ba zan iya rayuwa babu shi ba", kai kaji sakarya da wani zance inji mamanta da duk zancan bai wani shigeta ba,shike nan yi shiru kisha kuruminki ba dai waccan aljanar yarinyarce ta hanashi kallonki matsayin mace ba? Jinjina kanta ta yi kamar wata yarinya,yauwa to kisha kuruminki dan waccan aljanar bana ji zata kai labari saboda gaba daya kewaye take da makiya na gida dana waje kinga kuwa wannan ba abinda zai dame ki ba ne kina zaune cikin inuwa zaki ji mummunan labari akanta,Ni dai fatana ki samu ki jawo hankalinsa ki samu ciki dashi a yanzu wannan shine babban burina ", ya fada yana sake wani lissafin da tun abaya bai yi shi ba sai yanzu lallai lokaci yayi da zai amfani da rabi a domin samun cikar burinsa,da zarar rabi'a ta samu ciki da wazer zai kashe shi idan ya kashe wazer kuwa dukiyarsa dole ta rabi a da dan dake cikinta ne,wani bushashshan murmushi ya yi yana dan jin salama a ransa.
Kebabban gurine da ba kowa ne yasan da gurin a cikin yalwataccen birnin na Yola ba,sai daidaikun mutane basu cika son shiga jama a ba,zaune suke a kan kujerun gurin sai tebur dake tsakaninsu,har yanzu bata bayyana masa fuskarta ba domin bata gama yadda da shi ba,numfashi ya aje kafin ya ce", duk da cewa na bibiyi labarin abinda ke faruwa da Raihan kuma ta haka ne na nemo ki amma ba shine yake nufin cewa nasan ko ke wacece ba,nasan dai kina cikin gidan nan amma ban san wacece daga cikin gidan ke son daukar ran Raihan da mahaifinta ba,tunanin da nayi kuma yasa na biyo ki shine na son abu guda da mu kayi tarayya a ciki,duk kuwa da cewa mahaifina ya so yin hakan sai dai bai kai ga ci ba asirinsa ya tonu,yanzu ina so na dora daga inda mahaifina gwamna ya tsaya dan haka zanso sanin ko ke wacece saboda amanata da zan baki",kuma ki sani cewa wannan abun da za mu yi kusan kece da ribar fiye dani", wani makirin murmushi ta yi kafin ta numfasa ta ce", Yusuf karka sake ka yaudare Ni domin fada dani babu abinda zai jawo maka sai karewa a fanko", shima murmushin ya yi Sannan ya dauko jakar da take makale a wuyanshi ya budeta,takardu ya shiga zarowa har sai da ya zarosu duka sannan ya dubeta kana ya dubi takardun,mika mata su ya yi gaba daya yana cewa ki duba wannan kadan daga cikin kadarorin RAIHAN ne dake wajen mahaifina", tirkashi cikin rawar jiki ta karba hannunta na rawa ta shiga dubawa,iya dubawarta bata ga alamar fake ba, tabbas wadannan takardun na gaske ne,dagowa ta yi tana kallonshi da idanunta da suka nuna tsananin mamaki ta ce", ya akayi ka samesu? Dage kafada ya yi kafin ya ce", wannan ba abin mamaki ba ne a wajena tunda kinsan dai waye mahaifina a wajen Abbie kuma kinsan cewa komai na RAIHAN yana gunsa idan kika cire biyun da Abbie ya bawa yan uwanta dan sukula mata dashi", tabbas a yanzu na yadda da kai to amma me yasa tunda ka samesu ka biyo ta gurina ? Gyara zamanshi ya yi tare da cewa kinyi tambaya mai kyau,na farko dai dole ne na samu mataimakin da zai dinga share min hanyar bi", na biyu kuma dole ana bukatar sa hannun mallakar wannan dukiyar Kinga ke nan dole muna bukatar sa hannun RAIHAN,kuma ba kowa ne zai yi wannan aikin ba sai ke,tunda a gidansu kike tunda kike cikin gidan kuwa dole kina da kusanci da RAIHAN dan haka ke zaki yi duk dabarar da zaki yi Raihan ta sa mana hannu da zarar tasa hannu shike nan komai ya zama namu", ya fada yana kallon fuskarta", wata irin dariya ta sheke da ita babu kakkautawa,har zuciyar Yusuf ta fara rawa da shiga fargaba sai kuma ya ji ta tsagaita da dariyar tana cewa ban taba shiga yanayi na farinciki irin yau ba tabbas Yusuf ban san abinda zan saka maka dashi ba,sai yanzu na kuma yarda da kai da nayi wani tunani barewa ba za ta yi rarrafe danta ya kasa ba dan haka na amince za muyi tafiyarnan tare,amma duk da haka ba zaka ga fuskata ba sai ranar da komai ya daidaita na karbi sa hannun RAIHAN ", wannan ba damuwa ba ne danni ban damu da nasan koke wacece ba kawai fatana shine ki rike amana kalas", daga haka ya tashi ya barta zaune bayan ya karbe takardun a zuwan idan ya gama tattara su gaba daya zai dawo mata dasu.
WAZEER RAIHAN....
Sosai wazer ya yi nisa gun bawa kansa nutsuwa ta hanyar romance din Raihan,yadda yake fada zai cinye ta din ko tabbas ya kusa cinye tan,saboda yadda yake lashe komai nata bakinta kuwa tamkar zai tsinkeshi saboda tsotsa har yana jin ba zai iya barin Raihan ɗin ba duk da zuciyarshi na mashi rawa da tuna yadda ya samu rabi a,to amma yasan zuciya ce kawai Raihan dinsa da ta yi rayuwa a matsayin namiji killatacciyar matar da Ubangiji ya yi masa,shi kansa yasan idan zuciyarsa tayi shakku akan Raihan to lallai shedan ke son hanashi samun nutsuwar da bai sameta akan rabi a ba,yaso samun nutsuwarsa da Raihan amma tausayinta da sonta sun hanashi karasa kaiwa inda yake son zuwa," cikin maida numfashi ya jawota jikinshi sosai ya rungume yana jin ɗimin jikinta na ratsashi ga wani kamshi da bai taba jinsa a ko ina ba yana shigewa hancinsa yana kuma bashi nutsuwa.
Ita kuwa Raihan tsananin kunyar cinyetan da wazer ya yi yasa ta kasa ko kwakwkwaran motsi dan har ga Allah kunyar haɗa ido take yi dashi,a hankali yasa hannunshi saman lallasar fatar bayanta yana shafawa kamar me shafa kwai,cikinta da ya shafa yasa ta ɗan motsawa,a hankali cikin kamammiyar Muryarshi ya ce", kina son zuwa gida"? tura baki ta yi idanunta har sun kawo ruwa saboda tunanin abinda zata cewa maminta,zata yi magana kenan wayar shi ta fara fidda wani sauti me sanyi,kamar ba zai dauka ba sai dai tuni Raihan da tafi kusa da bedside drower da wayar ke aje ta janyota, a hannunta yaga me kiran hakan ya sa ya karba wayar yana mai komawa asalin wazer Chibado ba wazer ɗin dake gaban Raihan ba.assalamu alaikum ya fada cikin dakakkiyar Muryarshi ta mazan da suka san kansu,Yusuf ya akayi ina fatan ansamu cigaba?.........😨wane yusuf din kuma jama a ku taya Ni ji....✍🏽
53
ƁOYAYYIYAR RAIHAN
Ina fatan dai kai kadaine? Yusuf ya fada daga can bangaren", umm um wazer ya fada yana kallon RAIHAN da ta zura masa ido", to ka dan matsa maganar tana da dan tsawo",
A hankali wazer ya zare Raihan dake kanannade a jikin shi,kana ya sauka daga gadon ya fida daga dakin gaba daya wayar na a kange a kunnenshi.
Wani irin kallo Raihan ta bishi da shi haka nan zuciyarta take saka mata cewa da budurwa zaiyi waya shi yasa ya kebe kansa dan kar taji,ji ta yi ƙwallah sun cika idanunta,ta shi ta yi ta faɗa toilet ta wanke jikinta sannan ta fito ta zura doguwar rigarta,gaban mirror da yake cike da manyan turaruka ta tsaya tana kallon turaren duk saninta da turare sai taga wasu da yawa bata sansu ba,dan tabe baki ta yi tare da daukar daya daga ciki nanfa ta samu abinyi dan duk yawan turarukan da suke gurin sai da ta yi wanka da su,dan ma suna da sanyin kanshi da ita kanta sai sun dameta.
A hankali ya samu daya daga cikin kujerun da suka kuma ƙawata dan kyakkyawan lambu ln wanda yake cike da shukar kayan marmari ga wani dan sweeming pool wanda baifi ya ci mutum uku ba a wadace shima ya kuma kawata lambun,zama ya yi tare da harde kafafuwanshi waje guda sannan cikin deep voice dinshi ya ce", Yusuf ina jinka, dariya Yusuf ya yi kafin cikin shaƙiyanci ya ce", ai na dauka ka koma ruwa ne ka cigaba da gurzar yar mutanen,mutum a haka kamar ba zai aikata ba,nan kuwa SOYAYYA ce fal cikinsa", ban san iskanci ka sanar dani abinda ya faru ko na kashe wayata", cikin komawa serious Yusuf ya ce", ok gaskiya wazer tunaninka me kyau ne duk da cewa kafin na kama matar nan nasha hawala amma gashi daga karshe munyi nasara", ka gano fuskarta? Wazer ya tambaya Yusuf cikin kara maida hankali kan batun,a'a gaskiya ban samu ganin fuskarta ba saboda tana da matukar wayo,duk bibiyar da nake mata dan mu samu haduwa banci nasara ba sai a yau da ta shiga asibiti dan karasa Abbie",runtse ido Wazer ya yi yana hadiye jin zafinsa,bai yi magana ba shima yusuf din yasan ba maganar zaiyi ba dan haka ya cigaba da cewa, wallahi wazer na so matar nan ta nuna fuskarta saboda mukawo karshen makircinta ita da irirenta,sai dai ban samu hakan ba,amma duk da hakan munyi nasara tunda har ta yarda dani daga karshe ma nuna mata nayi bana bukatar ganinta aiki ne ya hada mu dan haka mu yi abinda yake gabanmu kawai,da wannan na kawar da tunaninta har ta yi min alkawarin duk ranar da Raihan ta sa hannu a takardun nan zata bayyana min kanta,kaga ke nan ya zama dole mu sanar da Raihan iya abinda ya sauwaka dan ta bamu hadin kai gurin gano matar ta hanyar sa hannunta", na gode Yusuf ina fata dai bata samu nasara akan Abbie ba ? Yusuf ya bashi amsa da cewa ey bata samu ba amma gaskiya a yadda na saurari bayanin Dr Sabo tabbas yana cikin condition din da sai dai mu taya shi da addu'a ,sai ita kuma mami matar ta Yar da ita dan haka ita ma an bata gado amma itama lafiya in sha Allah rauni ne kawai a goshinta saboda buguwar da ta yi", ajiyar zuciya wazer ya dan saki kafin ya ce", da Yusuf na gode Yusuf", wazer ba kaine zaka min godiya ba nine zanyi godiya hakika ba dan kai ba ba za mu taba Ankara da abinda ke faruwa ba daga Ni har Abbana,jin jina kai wazer ya yi kana ya ce", shima haidar muna kan bibiyar lamarin za mu samu abinda muke so very soon his excellency zai fita daga kullin da a kayi masa", daga nan sallama su kayi.
Yusuf yana aje wayar ya dawo da kallonshi kan mahaifiyarsa da baya boye mata komai,sannan a ganinshi dole itama tana da hakkin sanin saboda mijinta a garkame a matsayin me laifi,Hajiyata wallahi wazer aminin kwarai ne shi yasa bana fatan abinda zaisa na juya masa baya ko na ha ince shi", jinjina kai Hajiya Turai ta yi kafin cikin sanyin jikin da ya sarketa tun bayan kama mijinta da hukuma ta yi ta ce", yanzu yusiwa kuke tunani da wannan kullin? Hajiyata har yanzu akan bincike muke,amma yanzu da ace za mu samu haidar to tabbas kamar mun gano mai laifi ne,kaf gidan suna cikin zargi shi yasa ba mu tsaya akan mutum biyu da muka fi zargi ba,hatta da matansa bincike muke akansu dan acikin wannan kullin babu wanda zamu bari kowa abin zargi ne in kika cire baffa Ali da mahaifiyarsu,ita kuma Hajiyar agadex wazer yasanar dani cewa yana zargin kamar ta san wani abu da ya shafi abinda ya faru da Abbana,dan haka itama Binta muke sannu a hankali,in sha Allah gaskiya zata bayyana.allah yasa ta faɗa tare da cewa to batun jaridar bayyana RAIHAN fa? Dariya Yusuf ya yi sannan ya ce", Hajiya baki san waye wazer ba,jinsa kawai kike, wannan batun tun a ranar ya gama da shi cikin awa daya ya gano matarsa ce rabi a", dalilin da yasa bai dauki wani mataki ba shine ita kanta rabi'ar bai yadda da wannan kawar Tata ba ya ce itama yana zargin wani takewa aiki akan Raihan ɗin shi yasa ya kyale su ai talala ya yi musu kawai", to alhamdulillah Allah Ubangiji ya da da kare mu, Ni wallahi tausayin ramla duk yafi damuna gashi nan duk abinda ta yi na boye RAIHAN ɗin babu abinda ya kara mata,umm um Hajiyata ya kara mata mana akwai hikima da kaddarar Allah a cikin abinda Aunty amarya ta yi,dan haka mu jira muga abinda Allah zai yi gaba.
WAZEER RAIHAN........
Tashi ya yi cikin nutsuwa,ya fita daga lambun ya koma cikin falonshi ta wata kofar da ban ba wadda ya shigo ba,
Da RAIHAN ɗin ya ci karo a tsaye a falo ta cika ta yi fam idanunta har sun gaji da zubar ruwan hawaye,cikin takunshi na cikakkun maza masu ji da kansu ya ƙaraso inda ta kafe tana son fashewa,Mrs WAZER CHIBADO me kuma ya faru? Kwabe fuskar ta yi hawayen na sake gangarowa,cikin wani salo ya fidda idanunshi waje ganin hawayennata kana