Showing 24001 words to 27000 words out of 232912 words

Chapter 9 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1223

banda yanzu da na fito?"

Abdul yace
"Kenan soyayya kuke?"
"No!"

"To menene tsakanin ku?"
"Kafin nan wacece ita?"

"Cousin din Najwa ce."
"Na taba taimaka mata amman kar ka damu da wannan, 'kawar Jawahir ce."

"Ah haba amman ta gane ka kuwa?"
Murmushi Muhammad yayi yace
"Ta gane ni bakaga yadda take ba ta kasa sakewa a wajen"

Abdul yayi dariya yace
"Ohh naga alama da akwai wani abu a kasa kenan"
Muhammad yace
"No at all "

Tin kan magariba Maryam take son tafiya amman Najwa taki barin ta wannan yasa tana idar da sallah ta mike tace
"Tafiya zanyi Sitti."
Najwa tace
"Da daren nan."

"Eh."
"Please ki kwana."

"A'ah gobe akwai abinda zanyi."
"To yanzu Yaya za ayi?"

"Zanje na samu napep "
Ido Najwa ta zaro tace
"Kinsan halin Yaa Aliyu bai son ana hawa motar haya gashi drivern Sitti bai dawo ba."

"Ke ni ko a kafa zan koma gida "
Dariya Najwa tayi tace
"Ah lallai sannu."

Ta mike Najwa tace
"Wai da gaske sai kin tafi?"
"Yes "

Sitti ta kalla tace
"To bari naje wajen su Abdul in sun gama cin abinci sai su ajiye ta ko?"

"Eh hakan yayi."
Zama Maryam tayi Najwa ta fita bata jima ba suka shigo ita da Abdul da Muhammad suka zauna sannan Abdul yace
"Sitti zamu tafi."

"To Abdul a gaida mutan gidan."
"Zasuji Sitti."

Muhammad ya durkusa cikin muryar sa mai sanyi yace
"Sitti zamu tafi sai wata rana."
"To Muhammad a gaida mutanen gidan."

"Zasuji."
"Nagode sosai."

Kudi Muhammad ya zaro ya ajiye mata sannan yace
"Mungode."
"Ah ah Muhammad meyasa haka?"

"Sitti ki sa mana albarka kawai."
"To Allah yayi albarka."

"Amin nagode "
Suka mike suka fita. Maryam ta kalli Sitti tace
"Ni kamar na kwana."

"Kuma dai"
Mikewa tai tace
"Sai da safe."

"Allah kaimu ki gaida mutanen gidan."
"Zasu ji."

Fita tayi taga Najwa da Abdul a tsaye, Muhammad zaune a driver seat, tsayawa tayi a gefen tana danna waya Abdul ne ya dago yace
"Ah kina tsaye ki shiga ki zauna mana."

Motar ta bude ta shiga baya ta cigaba da danna wayar ta. Sai da sukai sallama da Najwa da Abdul sannan ta leko tacw
"Sai kuma yaushe?"
"Sai kin ganni kawai."

"Uhmm daman ke! sai da safe ki gaida su Ammi kan nazo."
"Sai kinzo."
Sukai sallama


Hira Muhammad da Abdul suke tayi a motar, ita dai danna wayarta kawai take, amma da ta daga kai za su hada ido da Muhammad ta madubi, sai tayi maza ta sauke kanta, bayan tafiyar kusan minti goma ta ji Abdul yace
"Kaga Muhammad ajiye ni nan zan biya ta wajen Fu'ad mu hadu a gida in ka ajiye ta."
Parking Muhammad yayi, Abdul ya fita yana kallon Maryam yace
"Toh 'Kanwar ce ko Yayar?"

Tai murmushi tace
"In muna tare da Najwa ni Yaya ce in bama tare ni 'kanwar kace."
Yai murmushi yace
"To 'kanwata sai mun yi waya ki gaida Ummi, abokina zai ajiye ki gida"

Fuska ta shagwabe zatai magana yace
"Dare yayi ki barshi ya kai ki gidan nima akwai wanda zan gani in ban ganshi yanzu ba nasan da wuya na ganshi nan kusa please sorry kinji Muhammad babban aboki nane kuma dan uwa gareni zai kula dake kada ki damu."

Kai ta langwabar kawai yace
"Kar ki damu kinji?"
Kai ta gyada, ya kalli Muhammad yace
"Drive her carefully plss sai mun yi waya"

Daga haka Muhammad ya ja motar suka hau saman titi, Maryam dai sai wasa take da fingers dinta, bayan wani lokaci ta dago a hankali tana kallon gaba suka hada ido ta madubi, da sauri ta sunkuyar da kanta, yayi murmushi yace
"Kina tsoron kada in sace ki ko?"
Kin cewa komai tayi, bayan kusan minti biyu taji cikin cool voice dinsa yace
"I am Muhammad Auwal, mahaifi na haifaffen garin Kano ne kasuwanci, da siyasa su suka kawo mu Abuja da zama, a UK nai primary da secondary na, har sa University mun jima da Abdul dan tare mukai secondary har graduation, acan ma muna zuwa gaida Sitti sosai, am a doctor now."

Kallon sa kawai Maryam take ta madubi, yayi murmushi yace
"Kina kallo na, Jawahir kanwa tace dan mahaifin mu daya nine babba a wajen mahaifi na. So ki daina tsoro na ni bana yanke kan mutane."

Daga haka yayi shiru ya kalleta yana murmushi yace "Zan iya sanin ki?"
Shiru tayi da farko, can a hankali tace
"Sunana Maryam"

Ta kallesa don a hankali yake driving din kasancewar babu motoci sosai titin, ya gyada mata kai alamar yana ji, yana murmushi, murya can kasa tace
"Kasan gidan mu da yan uwa na so me kake son ka sani, Jawahir 'kawatace mun hadu shekaru hudu baya tin da muka zana waec har yanzu da muke karatu tare."

"Masha Allah Allah ya taimaka to."
Murmushi tayi murya can kasa tace
"Ameen"

"Samarin ki nawa?"
Ya jefo mata tambayar ba tare da ta shirya ba, ido ta zaro
"Samari kuma?"
Yace
"Yeah"

Ta girgiza kai tace
"Tabb, ni bani da Samari"
Yace
"Sai dai friends kenan?"
Ya fada yana kallon ta tare da wani murmushi.

"Uhmmm."
Ya fada ta bata fuska tace
"A school bani da male friends, ka tambayi Jawahir."

Dai dai lokacin da yai parking a kofar gidan su, da sauri tace
"Ajiye ni anan ba sai ka shiga ba."
Yai parking ta bude kofar motar tace
"Nagode"

"Kar ki damu ki gaida Ummi."
"Zataji."
Ta sauka ta rufe kofar ta nufi gate din su tsaye taga Aliyu rike da mukullin motar sa, kai tayi kasa dashi dan yaki bata hanya jikin ta sai rawa yake zuciyar ta na bugawa ciki yayi ta tsaya a wajen tana kallon yadda yake tafiya a hankali cikin nutsuwa, sanye yake da bakin wando da farar riga mai gayeren hannu, gashin dake kwance a hannun sa baki masu tsayi zara zara, ajiyar zuciya ta sauke sannan tabi bayan sa tana tafiya kamar ba zatai ba.

Tana shiga compound din su tai karo da abu da sauri tai baya a mugun tsorata wanda hakan yasa rumfashin ta ya tsaya cak, da sauri ya taro ta, ta fado jikin sa fuskar ta ya fara jijjigawa jin tai masa nauyi lekawa yai ya tabbatar da abinda yake zargi, janta yai zuwa bakin famfam dake wajen ya kunna ya debo ruwan ya shafa mata wata ajiyar zuciya ta sauke ya dauke ta ya karasa da ita kan wata ginnanniyar kujera dake wajen, a hankali ta bude ido tana ganin sa ta mike zaune da sauri tana kallon wajen, ya hade rai yace
"Waye ya ajiye ki a mota?"

Ta zaro ido sai kuma ta turo baki bata san duk yana kallonta ba, yace
"Ba tambayar ki nake ba"
kamar zata yi kuka murya can ciki tace
"Abdul ne fa"

Fuska ya kara hadewa yace
"Ni za ki ma karya?"

Shiru tayi yace
"Ba magana nake miki ba?"
"Me?"

"Nace wa ya ajiye ki?"
Ta rufe idonta tace
"Abdul ne"
yace
"Maryam."

Dagowa tai tana kallon sa, yanayin sa kadai ya canja ya kada mata kai kawai tai saurin yin kasa da kanta tace
"Yaya abokin Abdul ne fa, tare muke da Abdul shi sai ya sauka a wani anguwa zai ga wani shine abokin ya ajiye ni shi, ka kira Yaa Abdul din ma ka tambayesa wllh"

Yana gyada kai yace
"Akan me ya kawo ki to? Dan me kika hau motar Abdul din?"
Kasa tai da kan ta yace
"Ba magana nake ba?"

"Yaya to ba mai kawo ni ne, ni kuma ba zan kwana a can ba."
Wani kallo yake bin ta dashi yace
"Meyasa baki kirani ba ko ki kira Ummi ta turo driver."

Baki ta turo ya dauki hannu ya buge bakin yace
"Ina miki magana kina turon baki?"
Bakin ta dafe hawaye na taruwa a idon ta, yace
"Na sake ganin kin fita ba driver sai ranki ya baci, na hana fitar ma gaba daya kina ji na ko?"

Shiru tayi yace
"Ba magana nake ba?"
Kai tai saurin gyadawa yace
"Tashi ki ban waje."

Da sauri ta mike wani irin jiri taji tai saurin dukewa kasa tana dafe kan ta ya mike ya karaso yace
"Me ya faru?"
"Kaina jiri nake ji."

"Tashi ki koma ki zauna."
Mikewa tai tana runtse idon ta sai kuma ta bude tana kallon hanya a hankali tace
"Zan iya tafiya."

"Ok jeki."
Ta fara tafiya a hankali har ta karasa bakin kofa, juyowa tai ta kalle sa dan yana tsaye bai motsa ba sai kallo ta da yake dauke kai yayi itama ta juya ta bude kofar ta shiga. Komawa yayi ya zauna yana dafe kan sa.

Tana shiga Ummi tace
"Ah ai na zata kwana zaki."
Zama tayi tana dafe kan ta dake sara mata tace
"A'ah."

"To wa ya kawo ki?"
"Abokin Abdul ne ya kawo ni."

"Abokin Abdul kuma?"
"Eh tare muke da shi."

"Ok amman me yake damun ki?"
Kai ta nuna tace
"Kaina ke ciwo."

"To kije ki sha magani."
Fuska ta bata Ummi tace
"An fadi makiyin ki ko?"

Mikewa tayi tace
"Haidar fa?"
"Yana wajen Mamin ku."

"Yau kuma can akayi?"
"Mun shiga dazu shine ya zauna."
Sama tayi ta shiga tai wanka ta fito tai sallah isha'i ta kwanta dan kan ta dake ciwo.

Tin da ta shige ya koma inda suka tashi ya zauna, yafi minti goma yana zaune yaji ana kiran sallah mikewa yai ya tafi masallaci. Sai bayan yai sallah ya fito ya nufi sashen Ummi, a zaune ya same ta akan sallaya ya zauna yana fadin
"Haidar bai dawo ba?"

Ta gyada masa kai kallon sama yayi yace
"Maryam fa?"
"Ta shigo bayan fitar ka amman wai ciwon kai take."

"Ta sha magani?"
"A'ah kasan ta da magani ai."

Mikewa yai ya shiga daki ya dauko magani har da allura ya fito ya nufi sama tana kwance har bacci ya dauke ta taji ana buga kofa cikin muryar bacci tace
"A shigo"
Ta koma ta kwanta murda kofar yai ya shigo tsayawa yai a gefen gado jin kamshi turaren sa yasa tai saurin bude ido dake cike da bacci da ciwo kuma.

Kan sa yai saurin daukewa yace
"Tashi kisha magani."
"Yaya ya daina fa."

"Oh ba zaki sha ba ko?"
Shiru tayi ya ajiye ledar ya dauko siriji da ruwan allurar ya fara shirin zuka a firgice ta mike tace
"Yaya amman bani zakai wa allura ba?"

Bai dube ta ba ya fara zukar allurar, ta fashe da kuka tace
"Dan Allah Yaya kada kai min wallahi bana so."
"Zaki sha maganin?"

Kai tai saurin gyadawa, yace
"To dauki ki sha."
Ta mike ta balli maganin ta sha tana dafe kirji sai ta fara kokarin kuma ta shi da sauri yace
"Kika amayar sai nai miki allura."

Ai a guje ta shige bandaki ta dinga kwara amai, bakin kofar ya isa yana tsaye ta gama ta dauraye wajen ta raba ta gefen sa ta fito, kan gadon ta kwanta tana mai da numfashi yace
"Allurar fa."

Mikewa tai ta fara yarfa hannu tace
"Wayoo Ummi kizo Yaya zai min allura."
Hararar ta yayi yace
"Sai fa na miki tinda ke bakya son magani."

"Zan kara wallahi zan kara."
"A'ah ba zaki min asara ba."
Hawaya ta hau yi ya matso yace
"Tashi tsaye."

kin tashi tayi yana matsowa ta mike da sauri tana yarfe hannu tace
"Dan Allah Yaya kayi hakuri."

Janyo ta yai ta fada jikin sa wani abu yaji ya tsarga masa da sauri ya matse hannayen ta ya zura mata allurar ta saman wandon baccin ta kuka ta saki ya dure ruwan allurar sannan ya zare allurar hannun sa ya saka yana mulmula wajen sannan ya sake ta da sauri ya nufi kofa, kan gado ta fada tana kuka tare da kiran sunan Ummi, a haka bacci ya dauke ta sai ajiyar zuciya da take saukewa. Cikin dare da ta tashi ba ciwon kai dan tai sallah ta koma ta kwanta.

A haka ta cigaba da karatun ta, zaune take a dakin ta bayan ta dawo daga makaranta taci abinci tai wanka jakarta ta janyo ta zaro wayarta ta ajiye a gefe wani memo ta dauko ta bude tana karanta abinda ke ciki wayar ta ce tai kara tana dubawa taga Jawahir ce dauka tayi tace
"Ya akai?"

"Question dinan zaki turon yanzu zan nunawa Yaa Khalifa."
"To bari na turo miki."

Ta kashe wayar missed call har biyu ta gani da sabuwar number bakinta ta tabe ta shiga whatsapp ta tura mata sannan ta ajiye wayar ta sauka kasa.

Da dare ma tazo kwanciyya ta duba wayar ta kara ganin missed call din da thesame number dazu, agogo ta duba taga tara ta wuce to waye zai neme ta, kwanciyya tayi kawai.

Washe gari bayan ta dawo daga makaranta tana kan sallaya ta idar da sallah jakar ta ta janyo sai taga missed call, dailing number tayi har ta katse ba a dauka ba, few seconds later sai ga call din ya shigo wayarta, dagawa tayi ta kai kunne, sallama aka yi daga daya bangaren cikin cool voice, ta amsa tace
"Waye?"

"Ya kike?"
Aka tambaye ta, fuska ta dan hade tace
"Uhmm nace waye?"

"Ki amsa min mana yan mata."
"Wa kake nema please wrong number."
Zata katse taji yace
"Wait mana. Ki tsaya na fada miki waye to."
"Naga baka da niyya."

"Muhammad ne, tin ranar da na sauke ki naso naji ya kika shiga gida to sai jiya Abdul ya ban number ki."
Wani murmushi ta saki ta d'an bude ido da mamaki amma ta kasa cewa komai, yayi murmushi a hankali yace
"To ya kike?"

Murya can kasa cike da kunya tace
"Alhmdulillah"
Yace
"Ya school?"

"Alhamdulillah."
"Masha Allah."

Sukai shiru a hankali yace
"Nasan yanzu kika dawo bari na barki ki huta sai anjima."
"Nagode."

Tin daga ranar kullum sai ya kira ta da daddare sun gaisa duk da basa waya mai tsawo iyaka gaisuwa shikenan amma har wani murna take idan ya kirata, dan tana jin dadin yadda yake nuna mata kulawa yace taci abinci? Ya makaranta? Ko tana da wata matsala irin wadan nan abubuwan dai kullum yana kira su gaisa wani lokacin sai dai taga missed call dan ita ba ta wani damu da waya sosai ba sai dai ta kira in ta kira kuma bai dauka sai ta katse yake kira.


Ranan wata Wenesday Maryam da Jawahir suka fito daga library a gajiye suna jiran driver wata mota ce ta karaso tai parking acan gefe wayar Jawahir ce tai kara ta duba tace
"Yaa Khalifa."

Sai ta kai kunnen ta dagowa kai tana bin motar gefe tace
"Wallahi ban lura ba gani nan."
Maryam ta kalla tace
"Wai ashe Yaa Khalifa ne a motar can zo muje ku gaisa."

Muhammad dake cikin mota tunda yayi parking idonsa ke kan Maryam, wacce take sanye da wani cream kalar less anyi zane da purple kalar zare sosai yai mata kyau ta saka mayafi three in one purple kala fuskar ta ta kara fresh, suna hada ido gabanta ya fadi, Jawahir tace
"Yaya ga Maryam."

Ta kalli Maryam tace
"Kin gane shi ai?"
Maryam ta d'an yi murmushi kawai, Jawahir tace
"Yaya kai fa?"

Shima murmushin yayi yace
"Na gane ta ba bestyn ki ba?"
Kai ta gyada. Maryam ta sauke idonta kasa tace
"Ina yini?"
yace
"Lafiya lau, ya makarantar?"

Tace
"Alhamdulilalh"
Ta dan dago suka hada ido wani lallausan murmushi ya sakar mata ta dauke kai da sauri gabanta na faduwa, yace "Let drop u mana"
Ta girgiza kai tace "Aa yanzu driver dina zai zo"

Yace "Ohk"
Ta dago ta kalli Jawahir tace
"Sai gobe ki gaida Momy."
"Zataji."

Motar gidan su ce ta shigo, Jawahir tace
"Yauwah kinga sai mu tafi tare ma."







*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*




*Antty*
[10/23, 14:16] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 8

By
*MARYAM S INDABAWA*



*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Dis page is for both of you, *Jamila Yusuf, Khadija Salisu, Amina Muhd, Zainab Muhammad, Ubaida Abubakar Fari, Aisha Maman Fahad* from MATAR HAIDAR FANS GROUP, ina godiya mutanen Amana Allah ya bar kauna.



Bayan isha'i ta idar da sallah, ta mike ta nufi kofar fita wayar ta dake can kan mudubi ta fara ringing kan ta karasa ta katse, tana dauka taga Muhammad ne ya kirata, komawa tayi ta zauna tayi dialing, katsewa yayi ya kira cikin cool voice din sa yai mata sallama ta amsa tare da gaishe shi. Yace
"Ba zan amsa ba bayan dazu nunawa kikai baki sanni ba."

"Nima ai haka kai min."
Tai maganar a shagwabe, yai murmushi yace
"Nifa ba kuka nace ki min ba ko?"

"Uhmm to ina yini?"
"Lafiya lou ya gajiyar school?"

"Alhamdulillah."
"Masha Allah. Dazu kinyi kyau amman fa."

"Hmmm kaji ka."
"Allah da gaske ban gaji da kallon ki ba."

"Uhmm ina Abdul kwana biyu."
"Baku hadu ba?"

"Eh kwana biyu banje gidan Sitti ba."
"Yaushe zakije?"

"Ban dai sani ba."
"To ya shirye shiryen biki?"

"Alhamdulillah."
"Allah ya kaimu."

"Amin."
"To sai da safe."

"Allah tashe mu lafiya."
"Amin."
Ta kashe wayar ta mike ta fita.


*
Yau watan ta biyu kenan rabon ta da gidan Sitti ba wai zuwan ne batayi ba tayaya zata tambayi Yaa Aliyu zata take tunani tasan halin sa, da sauri ta mike tace
"Shi Yaa Aliyun nan in yasan wata bai san wata ba Abba zan tambaya tinda yana gari."

Ta mike ta nufi dakin Abba sallama tai yana zaune a falon sa ya amsa ta shiga ta zauna tare da marairaice fuska tace
"Abba zan je gidan Sitti nayi ko sati daya ne tinda mun samu hutu."

"To Maryam ki shirya ki tafi mana kin fadawa Maman taki?"
"A'ah haka nace bari na fara fada maka."

"Ok kije ki shirya to."
"Nagode Abba."

Ta mike ta shiga dakin Ummi a zaune ta same ta tana danna wayarta, ta zauna tace
"Ummi gidan Sitti zani nayi mata sati daya."

"To yaushe zaki tafi."
"Yanzu in na gama hada kaya na."

"To shikenan. Je ki hada kayan."
Ta mike ta fita tana murna, dakin ta ta shiga sai ga kiran Muhammad nan dauka tayi tin daga muryar ta ya gane tana cike da farin ciki yace
"Ya dai yar gida na?"

Tai murmushi tace
"Yau zani gidan Sitti."
"Da gaske ko na zo na kai ki?"
"A'ah."

"Why?"
"Ba komai."

"No ba dai ki yadda dani ba ko?"
"A'ah fa."

"To in ba haka ba zan zo na kai ki."
"To shikenan."

"Da karfe nawa."
"Yanzu."
Yai murmushi yace
"Gani nan."

Ba ai minti ashirin ba sai ga Muhammad ya kira ta wai yazo, jakar ta ta rufe ta mike ta fita a dakin wajen Ummi ta shiga tai mata sallama sannan taje wajen Abba ta fita taje wajen Sitti tana fitowa daga wajen Sitti ta hangi Aliyu na tahowa sanye da wando nude colour sai milk riga mai dogon hannu, kafar sa da sandal baki, kamar ta koma ciki haka taji amman saboda ya ganta sai kawai ta maze ta fara takowa.

Tinda ya hango ta yake kallonta, Maryam kuwa sai sunkuyar da kai take gabanta na faduwa, kallon sashin su yayi sannan ya kalleta yace
"Ina za ki?"

"Gidan Sitti"
"Wa kika tambaya?"

"Abba."
Ta bashi amsa kamar zatai kuka. Akwatin dake hannun ta ya kalla tai saurin yin kasa da ido yace
"Akwatin fa?"

"Kaya nane a ciki."
"Me zaki dasu?"
Ya tambaya yana tsare ta da idanun sa masu birkitata.
Da sauri ta dauke idon ta tace
"Kwana zan."
"Kwana?"

Ta gyada kai, kallonta ya tsaya yi sai kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login