Showing 45001 words to 48000 words out of 232912 words
Chapter 16 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
Allah sai munyi waya anjima."
"Ok muje nayiwa su Mum sallama."
Suka karasa sukai musu sallama sannan sukaje wajen Momy Rukayya sukai sallama ta juyo ta dawo kowa ya shiga mota. Motar Yaa Alkasim suka shiga, shi da Yaa Fadima a gaba, Ita da Yaa Aliyu a baya. Su Ammi da Ummah da sauran yayyane nata a mota daya masu aikin su a dayar motar.
Kai ta jingina a jikin kujera tace
"My Hayyat!"
"Na'am Ma'ul Ayn!"
"Na gaji!"
"Na sani Bae taho in miki tausa!"
Kallon sa tayi ta make kafada murmushi yayi ya matso da kan sa wajen kunnen ta yai mata rada, da sauri ta matsa tana rufe fuskar ta da hannunta dan ya bata kunya sosai. Shima murmushin yayi ya dan cije lips dinsa na kasa yace
"Kika shigo hannu na ko?"
Kanta, ta kwantar a jikin kujera tana fadin
"Ni dai ka bari."
Ta fada tana lumshe ido, kallon ta yake yana murmushi wanda kan suje gida har tayi bacci suna zuwa gida Yaa Alkasim da Yaya Fadima suka fita. Kallon ta ya tsaya yi Ido ya kura mata sai yai saurin dauke idon sa dan wani abu da yaji yana taso masa.
"Ma'ul Ayn!"
Ya kira sunan ta. Kara gyara kwanciyya tayi. Yace
" *Matar Haiydar!* "
"My Hayyat Bayana, kuguna kamar zai balle nagaji matsa mi...."
Sai kuma tai sauri ta bude idon ta.
Aliyu kuwa ido ya lumshe dan a yadda tai maganar cikin magagin bacci muryarta, ta saukar masa da wani irin kasala.
Janyo ta yayi jikin sa yace
" *Matar Haiydar* "
"Uhmm!"
Ta fada tana kara kwantowa jikin sa. Bakin sa ya kai dai dai kunnen ta ya farai mata rada wanda hakan yasa duk jikin ta kara yin sanyi dan yadda yake mata maganar ga numfashin sa dake sauka a cikin kunnen ta.
Fuskarta, ta kife a kirjin sa tana jujjuya kan ta. Murmushin da baya taba barin fuskar sa ya saki sannan yace
"Bae kar mu makara sallah fa 6:30pm gashi kinsa sai nayi wanka."
"Wankan me?"
Ido daya ya kanne mata yace
"Kema kin sani in har ina tare dake sai naji...."
Da sauri ta mike a jikin sa tana rufe fuskarta. Da hannu daya dayan hannun ta daura akan bakin sa.
Hannun ta ya zame, Kansa ya matso dashi kusa da kunnen sa yace
"Wai ni kike jin kunya?"
Kai ta gyada yace
"Oh really?"
Hannu ta sa zata bude kofa yai sauri ya kamo hannun nata, yace
"Dan lokacin sallah ya kusa ne amman da sai..."
Ya matsar da bakin sa kan nata ya fara tsotsar lips din nata kamar ya samu alawa. Kokarin janyewa take yace
"Ba kyau fa."
Barin shi tayi sai da yai kissing nata na kusan minti biyar sannan ya sake ta, yana sakin ta tai sauri ta bude mota ta fice a guje.
Katon compound ne wanda a kalla zai dauki motoci sama da ashirin gefe daya babban masallacin Malam Muhammad Jabeer ne wanda yake limanci sannan duk bayan sallah magariba yake karatu a wajen. Daya gefen kuma bangaren gidan sa ne wanda yake katon gaske bangaren maza daban sai dayan bangaren da yake na ya'yan sa ne masu aure.
A guje ta shiga cikin gida, da kallo Yaa Alkasim ya bita wanda ya fito daga cikin gida. Yaa Aliyu ne ya fito a motar kallon sa Alkasim ya tsaya yi. Karasowa yayi kusa dashi yace
"Menene ne?"
"Kafini sani."
"Ko?"
"Kaga ana kira muje masallaci."
"Sai nayi wanka."
"Wanka kuma?"
"Yes!"
Ya fada yana yin cikin gidan.
Murmushi Alkasim yayi yace
"Abun ne ya motsa ni wallahi da Abbi zai yadda da ya daura auren before next week!"
"Ai ni tarewa kawai nake bukata."
Ya fada yana yin ciki.
Dariya Alkasim yayi yace
"Aliyu kenan."
Yaa Muhammad ne ya fito yace
"Me ka tsaya yi?"
Kai ya shafa yace
"Ba komai!"
Suka wuce masallaci. Yana shiga ya tube ya shiga yai wanka ya fito ya zura jallabiya kawai ya nufi masallacin. Raka'a biyu ya samu sannan suka zauna daukar karatu sai da sukai isha'i suka koma cikin gida.
Maryam na shiga bata tsaya ko ina ba sai dakin ta. Falo ne da bedroom da toilet da wani dan store. Tana shiga ta lumshe ido dan kamshin da yai mata sallama. Komai tsaf kamar tana nan dan duk sati ake gyarawa bama yanzu da aka san za ta dawo. Bedroom ta shige kawai ta wuce bandaki a can ta cire kaya tayi wanka ta fita daure da towel doguwar riga ta saka jin an tada sallah ta hau kan sallaya ta tada sallah tana idarwa ta dauko alkur'ani ta fara karantawa kan a yi isha'i. Ana tayar wa ta mike ta tada sallah. Bayan ta idar tayi shafa'i da wuturi sannan ta mike ba tare da ta cire hijab din ta ba ta nufo Babban falon su.
Babban falo ta fito inda ta Fara jiyo hayaniyar yan gidan su. Fuska dauke da murmushi ta yi sallama duk a tare suka amsa.
Yaa Muhammad, Yaa Ibrahim, da Yaa Abdullahi da matan su da yaran su duk da suka dawo anan suka zauna sai Yaya Fadima, Yaya Ummulkusum a cikin Yan gidan mutum biyu ne babu daga Yaya Zainab sai Yaa Alkasim da basu shigo ba.
Yaran ne duk suka taho wajen ta a guje durkusawa tayi ta bude musu hannayen ta tana fadin
"My sweet family I miss you!"
Dai dai lokacin da Yaa Alkasim da Yaa Aliyu suka shigo dakin bakin su dauke da sallama, Amsawa sukai gaba daya Yaa Aliyu ya shigo Yaa Alkasim na biye dashi a baya, idon sa na kan Maryam dake rike da 'yar gidan Yaya Fadima, Iham karasawa yayi ya zauna a kasa ya dan tabo ta, ta juyo suka sakarwa junan su murmushi ya dago suka hada ido da Yaya Ummulkusum kai yai kasa dashi, Yaya Ummulkusum tace
"Aliyu da Amaryar sa."
"Amaren wani satin!"
Yaya Fadima ta fada.
Matar Yaa Muhammad Rabi'a tace
"Iyayen soyayya ba ma huta ba."
"Ku huta da me Anty Rabi?"
Aliyu ya fada yana murmushi
"In kun tafi gidan ku mana."
"Ai Ma'ul Ayn tace zata fadawa Abbi a bamu part muma ko?"
Ya fada Yana cilla wa Maryam tambayar.
Kai ta gyada tana shafa kan Iham tace
"Eh mana mu anan zamu zauna tinda kowa ma Yana nan."
Yaya Fadima tace
"Tab wallahi Aliyu zaka sha fama har yanzu Maryam fa bata girma ba."
Da sauri ta dago ta kalli Yaa Aliyu tace
"Wai haka My Hayyat?"
Hannun ta ya kamo ya dan murza yace
"Kyalle Fadima, ai kowa yasan Matata ta girma."
Ya fada yana yin kasa da murya yace
"Ko ba haka ba sai ma mun haifo Baby mai kama da ke ko?"
Kasa tayi da Kai tana girgiza Kai yace
"Me? Bakya so?"
"Ina so amman ka bari kana ganin su Yaa Muhammad fa."
"Me nayi naga matata ce kuma bayan ba abinda nayi ma."
Ammi ce ta fito tana fadin
"Kunga ki tashi kuje kuci abinci kan mazan ku su zo su tsaya jira."
"Ammi Yaya Fadima kwana zatai."
Maryam ta fada. Ammi ta kalle ta tace
"Saboda me?"
Fuska ta shagwabe tace
"Sai bayan biki zata koma."
"Ba anan ba tayi maza ma ta kira sa in lokacin bikin yazo tazo tai kwana daya ma ya isa ke in ta tawa ne ma tai zaman ta a gidan ta tana zuwa tana komawa."
"Kai Ammi bikin autar guda."
"Sai ta bar mijin ta. Tasan Abbin Kuma ba bari zai ba tai maza ta kira sa ko su Aliyu ku kai ta gida."
"An gama Ammi daman ni ban ga amfanin tahowa ta kwana ba "
"Kai Yaa Haidar kai da zaka bata baki."
Fadima ta fada. Fuska ya dan hade yace
"Ni yaron ki ne ko? Tashi kuje kuci mu kai ki gida."
Yaya Ummulkusum ce ta mike tayi dining ta zubawa yaran sannan ta zubo musu mata a plate daya mazan kowa ya zuba. Bayan sun gama ci suka kintsa. Sukaje wajen Abbi sukai masa sallama, nan ya karai musu nasiha sannan ya saka musu albarka suka tafi Yaya Fadima ta shigo ta samu Yaa Aliyu da Maryam da Ammi.
"To ka taso ka kai ni!"
Ta fada tana kallon Aliyu. Ammi ya kalla yace
"Ammi bari mu kai ta gida."
Ya fada yana kallon Maryam. Da sauri ta mike tace
"Muje to."
Suka fita ya budewa Maryam gaba ta shiga, sannan ta zagaya ya shiga. Yaya Fadima da Iham suka shiga baya tana fadin
"Yaa Aliyu nifa yayar ka ce."
"Tayaya?"
"Saboda Maryam mana."
"Lallai yarinyar nan to ita ce zata zama Antyn ki."
Murmushi Maryam tayi a haka suka karasa gida ta dake jan bulo.
Har ciki suka rakata sannan suka mata sallama suka tafi. Shi ya kara bude mata mota ta shiga tana fadin
"My Hayyat kana sangartani da yawa fa."
"To Baby in ban sangartaki ba wa zan sangarta."
Ya fada yana rufe motar.
Kai ta jingina da jikin kujera tana mai lumshe idon ta. Shiga yayi ya kalle ta sannan ya tada motar. Hannun ta ya kamo wanda hakan yasa ta bude idon ta. Murmushi ya sakar Mata yace
"Ina kaunar ki Ma"ul Ayn! *Matar Haiydar* "
Hannunta take son janyewa amman yaki ta dan kalle shi tace
"Ba kyau fa My Hayyat!"
"Me din? A da kenan a yanzu fa kin zama tawa sauran kwana nawa ne mu kasance tare?"
Murmushi tayi ta jinginar da kan ta a kujera tare da lumshe Ido, tace
"Allah kaimu!"
"Amin ni wallahi ji nake kamar lokacin bai gudu. Allah ya nunan lokacin nan yana daya daga cikin lokacin da nake da burin gani a rayuwa ta. Ban san irin son da nake miki ba, kece kadai rayuwa ta Habibty."
Ido ta kara lumshe wa tana murmushi, parking yayi wanda hakan yasa ta bude ido ta juya taga ba gida suka zo ba da sauri ta kalle shi yace
"Me zan siyo miki?"
"My Hayyat ni bana jin yunwa fa muje gida kawai."
"No har ice cream din?"
Fuska ta rufe da hannun ta. Kissing hannun yayi sannan ya fita a motar ta bishi da kallo. Har ya bacewa ganin ta sannan ta dawo da kan ta, ta jingina a jikin kujera tare da lumshe idon ta.
Wani bacci take ji wanda ya zamar mata jiki a ko da yaushe da ta kwanta sai bacci anya kuwa ba sleeping sickness take ba.
Ta fada tana gyara kwanciyyar ta a jikin kujerar. Kan ya dawo har baccin ya dauke ta. Ledar ya ajiye a baya sannan ya gyara mata zaman kujerar yadda zataji dadin kwanciyya motar ya tayar suka nufi gida a lokacin tara ta gota.
Yana parking ya juyo yaga tana bacci murmushi ya saki ya shafa kan sa dake cike da suma mai kyau da taushi.
"Ina ma su ban Matata na huta."
Ya sa hannu ya daura akan goshin ta, wanda ta bude idon ta a hankali, murmushi ya sakar mata yace
"Mun iso gida fa."
Gidan ta kallah ta fara kokarin mikewa zaune ta daura hannun ta a baki tare da salati ta fara hamma. Kofa ta bude tace
"Dr Ina jin fa sai ka duba ni kwana biyu na zama kamar kasa nayi ta bacci duk inda na samu waje."
Fita yayi yana murmushi yace
"Kema kinsan gajiya ce da karatun dare da kuka dinga."
Hamma ta kuma yi tace
"Bari naje na kwanta sai da safe!"
Ledar ya dauko ya bi bayan ta. Ba kowa a babban falo dan haka ta kalle shi tace
"Kaga duk sun kwanta kenan."
Ledar ya mika mata dai dai fitowar Ammi dan rufe kofar babban falo, ganin su tace
"Sai yanzu kuka dawo?"
"Eh Ammi!"
Ta amshi ledar tace
"Nagode!"
Ya juya ya fita Ammi ta rufe kofa Maryam ta wuce dakin ta. Hijab din jikinta, ta cire sannan ta shiga tai alwala tazo ta canja kaya zuwa na bacci ta dawo ta dauki ice cream din ta saka a firij ta dauki roba daya ta fara sha.
Dakin Alkasim ya tafi ya same shi kwance yana waya. Baki ya tabe yace
"Tab wai nan soyayya kuke."
Yai dariya ya ajiye wayar sa ya nufi bandaki ya watsa ruwa ya fito ya saka kayan bacci kan gadon ya hau yana jawo wayar sa.
Number Ahmad ya fara nema ta can kasar da yake yana bugawa ya daga yace
"Ango Ango! *Mijin Maryam* "
Murmushi yayi yace
"Wannan haka yake Angon Maryama."
"To tana Ina?"
"Yanzu muka rabu yaushe zaka dawo ne?"
"Ina son na dawo kan bikin ku Amman ban sani ba ko zan samu dama."
"Ahmad kada kace haka man."
Dariya yayi yace
"Kada ka manta dani fa akai wancan wannan shagali ne fa kawai."
"Ni dai kazo."
Alkasim da ya gama waya ne ya zare wayar yana fadin
"Dan Allah kazo Ahmad, kaga yadda Aliyu ya koma marar kunya matar shi kawai yake so ayi a shafa ya dauke. Kazo muyi masa wa'azi dan naga kan sa na rawa da yawa."
Wayar sa ya zare ya kashe yana fadin
"Ba da kudin waya ta ba, matata zan kira. Kira da wayar ka."
Ya mike ya fita, layin ta ya fara nema.
Har ta fara bacci taji karar wayar ta hannu ta sa ta janyo dan tasan wa yake kira daga jin karar tasan Yaa Aliyu ne, ba tare da ta duba ba ta kai kunnen ta. Tace
"Assalamu alaikum!"
Tai maganar cikin muryar bacci.
"Wa'alaikum salam. My har kin kwanta ne?"
"Na fara bacci My, bana fada maka ba kwana biyu nai ta bacci ni bana so ka ban magani."
Kan sa ya shafa yana murmushi yace
"To shikenan, ki kwanta zan tashe ki, anjima ki sallah."
Hamma tayi tana mika hade da salati tace
"Sai da safe My!"
"Allah bamu alheri I miss you."
Ya kashe wayar ya koma daki ya samu Ahmad da Alkasim na waya duk akan bikin nasu ne.
*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*
*Antty*
💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 15
By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Washe gari, tin asuba da ta tashi bata koma ba saboda bata sababa dan ba kyau ma. Zaune take akan sallaya tana azkhar, Ash kalar hijab ne a jikin ta wanda yai mata kyau ya fito da aihin kyan ta dan ba karamin kyau hijab yake mata ba. wayar ta dake kan madubi ce tayi kara, karasa azkhar tayi wanda kan ta dauko ta katse, wani kiran ne ya kara shigowa.
Hannu ta sa ta dauko ta duba sunan taga an saka *My* Ido ta lumshe ta danna received, ta kai kunnen ta tana fadin
"Assalamu alaikum!"
Aliyu dake zaune a kan three sitter sanye da wando three quarters sai riga marar nauyi a jikin sa. Gashin kan sa ya kara bakikirin sai sheki yake, jin sautin muryar ta yasa ya lumshe idon sa yana mai shafa sumar kan sa hadi da sakin murmushi, a hankali yace
"Wa'alaikum salam My princess! Da fatan kin tashi cikin koshin lafiya?"
"Alhandulillah Yaya na, kaifa ya ka tashi ya daren ka?"
Numfashi ya sauke yace
"Yadda yake kullum My love, kullum dake nake kwana dake nake tashi kullum in ta mafarkin ki, Baby ina kewar ki sosai da sosai fa."
"Nima haka Yaya nah!"
"A'ah fa Baby bai kai nawa ba, Baby ni dumin jikin ki ma kawai nake so na dan ji a nawa."
"Yaya nahhh!"
Taja sunan wanda yasa abinda yake ji ya kara daduwa duk jikin sa yai sanyi. Kasa magana yayi sai lasar leben sa na kasa tare da lumshe manyan idon sa.
"My Hayyattt!"
"Uhmm!"
Kawai ya iya fada. Murmushi tayi ta mike ta koma kan gado tace
"Ya dai?"
Murya ya shagwabe Kamar zai kuka yace
"Ba kece ba!"
"Me nayi My?"
"Uhmm uhmm Baby I need you."
Murmushi tayi tace
"Haba Miji nah kwana nawa ya rage yau friday kaga remain one week a daura na kasance da kai sai abinda kake so zan maka."
"Why not now Baby!"
"Please Yaya nah kayi hakuri seven days ne."
"Wallahi gani nake Kamar seven years ne."
Murmushi tayi, yace
"Oh dariya ma kike min ko?"
"No no kawai dai."
"Shikenan ba ruwa na dake!"
Ya fada a shagwabe sannan ya kashe wayar. Dariya tayi ta fara neman layin nasa, kin dauka yayi ta kuma kira sai da ta kira sau uku sannan ya dauka, tana jin ya dauka ta saki kukan wasa, ai nan da nan hankalin sa ya tashi, ya hau tambayar
"Menene Baby? Meya faru? Dan Allah ki daina kukan nan, fada min menene?"
Kukan ta kuma saki tana fadin
"Ba kai bane!"
"Ni kuna Baby me nayi?"
"Fushi kake yi dani!"
"Ni na isa, ba zan taba fushi da Matata ba, please stop crying kinji da wasa nake fa na kashe ne dan ki dan kwanta ki huta kinga safiyya tayi ko?"
Dariya tayi tace
"I love you My! Sai anjima!"
Ta fada ta kashe wayar daga shi har ita murmushi suke wanda su kadai suka san ma'anar sa.
Kwanciyya yayi yana karatun Alkur'ani ita kuma mikewa tayi ta nufi kitchen. Ammi ta gani da me taya ta aiki, har kasa ta durkusa tana gaishe da Ammi ta amsa tana fadin
"Har kin tashi ko baki koma ba?"
Kai ta gyada mata ta gaishe da Baba Ramma Mai aikin su ta amsa tana kara taya ta murnar kammala karatu ta amsa tana godiya.
Baba Ramma tace
"Kinga Maryam je ki kwanta nasan tinda kuka fara jarabawa ba wani baccin kirki kikai ba ai Ina jin kin ma daina shiga kitchen sai na gidan ki."
Kasa tayi da kanta, Baba Ramma tace
"Jeki abinki ki huta kinji!"
Kai ta gyada ta juya ta fita, gidan sai kamshi yake dan an share anyi mopping an saka turaren wuta sai kamshi. Ido ta lumshe ta nufi bangaren Abbi.
Shima ko Ina fes sai kamshi ke tashi a dakin da sallama ta shiga falon nasa yana ciki inda yake zama yayi ibada.
Amsawa yayi ya bata izinin shigowa sannan ya dago yana kallon kofar dakin. Shiga tayi ta karasa ta zauna a gefen sa. Murmushi ya saki yana fadin
"Mamanah!"
"Na'am Abbi barka da asuba!"
"Barka ka dai! Da fatan kin tashi lafiya?"
"Alhandulillah!"
"Masha Allah, Allah yayi albarka yayi jagora ya bada sakamako mai kyau. Hakika Ina alfahari dake uwata duk cikin ya'ya na kece kika fita daban ta fannin son karatu sosai bama na addini da kuma dagewa, daga ke sai Aliyu shi da bama 'dana ba amman ina zaton shi zai gajen a wannan fanin nan gaba Allah muku albarka!'
"Amin Abbi!"
"A cikin waccan satin Alkasim da Aliyu suka zo da zancen shagalin bikin ku!"
Kai tayi kasa dashi, yace
"Alkasim yaso a kwashe sati ana biki amman ni da Aliyu muka ce a'ah ayi kamu, yini da walima Friday a daura aure yafi. Kinsan Yayan naki wai shi ba party ko daya, Aliyu yace ba za ai ba shine yace shi ya dauki nauyi, ni ba zance a'ah ba amman nace ayi a tsarin addini banda kide kiden nan dan albarka muke nemar muku me kika ce ke?"
Kan ta a 'kasa, kamar 'kasa ta bude ta shiga dan kunya tace
"Abbi duk yadda ka yanke yayi mungode!"
Sallamar Aliyu sukaji a kofar dakin. Suka amsa tare ita da Abbi dakin ya shigo ya