Showing 231001 words to 232912 words out of 232912 words
Chapter 78 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
masu aikin su, Baba Ramma ta sama tana gyangyadi ta zauna tana fadin
"Baba kije ki kwanta mana, ina Salamatun?"
Baba da ta farka tace
"Tana ciki, banji duriyar ku ba shiyasa ban kwanta ba, kun dawo lafiya yasu Ummin?"
"Suna lafiya suna gaishe ku."
"Muna amsawa."
Ta mike tace
"Bari naje na kwanta sai da safe."
"Allah tashe mu lafiya."
"Amin."
Ta mike ta fita. Bangaren su ta shiga ta nufi dakin ta ta shiga tai wanka ta fito ta shirya cikin wata pink kalar rigar bacci tai mata kyau sosai ta shafa turare mai dadin kamshi, kofa ta nufa inda tana daura hannu taji an bude ta ja baya ya shigo yana binta da kallon so da tsantsar sha'awa, jikin sa ta shige tana sauke ajiyar zuciya tace
"Yaya nah!"
Ya kara rumgumo ta yana fadin
"Noor ina son ki bana son ki nesa dani."
"Nima haka Yaya."
Ta fada tana daura bakin ta akan wuyan sa, tana bashi wani kiss, dan janyewa yayi yace
"Ba wani nan gashi nan har da fadawa Ummi dan kinsan in tace dole ayi, ni nasan me zanyi tinda wahala nake in zaki gida aure zan kara yadda in kin tafi zan samu mai kula dani da kin dawo kuma shikenan."
Jikin shi ta shige tana sakin kukan shagwaba tace
"Ni dai ban yadda ba Allah in haka ne na fasa zuwa shikenan."
Ya daga ta ya ajiye akan katon gadon da ya sha sabon zanin gado sai kamshi ke tashi a kai, kissing nata ya fara a haka suka cigaba da faranta ran junan su, washe gari ma da yai maganar tafiya cewa tayi ta fasa amman yace ta shirya tinda yaiwa Ummi alkawari the next day suka daga Kano cike da kewar mijin nata, kwanan su daya akai suna gaba daya yan uwan ta sun zo yaran su suka hadu gaba dayan su, familyn Abbi ya hadu aka sada zumunci, tin bayan sunan ta fara jin sauyi a tare da ita da kanta tai wa kanta test ta gane shigar cikin dake jikin ta.
Murna tayi sosai tana fadin
"In Yaya ya gane ko yaya zai?"
Dan Aliyu yana son yara duk lokacin da ta samu cikin in kaga yadda yake murna kamar bata taba haihuwa ba, haka in ta haihu yadda yake mata kyauta da nuna musu kulawa kamar ya mai dasu cikin sa.
Kullun kuwa suna makale da waya da dare kusan kwana suke soyayya a waya a haka suka cinye sati biyun su suka tashi tafiya, shi ya dauko su, tin a hanya yake binta da kallon mai cike da so da kauna, ganin sun kar kata hanyar gidan Ummi tace
"Ina kuma zaka kaimu?"
"Su Haidar zan ajiye dan gaskiya ina son nima na huta da matata bana son kowa ya damen."
"Kai Honey waye zai dame kan?"
"Ga Sajida nan da bata son barin jikin ki kullum kuna makale da juna."
Dan hararar sa tayi ta shafa kan Sajida da zuro da kan ta ta baya tana wasa. A haka suka karasa gidan suna shiga suka bude kofa suka fita a guje, da kallo ta bisu tana mai fadin
"A tafi a hankali dai."
Ai ina sun fice har Sajida, hannu ta sa zata bude kofar taji ya saka lock juyowa tai ta kalle shi tace
"Ka bude min mana."
"Gida zamu tafi."
"Haba Yaya ai ma gaisa da Ummi ko?"
"Wallahi Baby a matse nake kawai muje."
Ya fada yana kunna motar, tare da ficewa a gidan.
Tin daga compound ya dauke ta kamar Baby suka shige ciki, a kan gado ya ajiye ta wanda yai dai dai da fara ringing din wayar ta dauka tayi tana ganin Ummi tace
"Kaga ko ni ban san me zan ce mata ba."
Wayar ce ta katse wani kiran ya kara shigowa amsar wayar yayi ya kai kune yace
"Ummi kinga su Haidar ko? Mun shige gida ne sai gobe zamu shigo."
"To a gaishe min da daugther."
"Zataji."
Ya kashe wayar yana fadin
"Ummi na ai wayayyiya ce ba ruwan ta."
Hararar sa tayi tace
"Bari na watsa ruwa."
Ta mike tana zuge zip, tana zare rigar taji ya rumgume ta ta baya ya fara kissing dukkan jikin ta, daga haka ya dauke ta suka haye gado suna shan soyayyar su.
Kwance yake akan gadon Maryam kwance a jikin sa idon ta a lumshe hannun sa na bayan ta yana massaging nata, saukar hannun sa akan hips din ta yasa ya dan bude ido yana fadin
"Noor let me check you."
"Me zaka duba?"
"You know what?"
Kai ta girgiza ya kai bakin sa kunnen ta yana mata rada, hannu ta daura akan bakin sa tana fadin
"To wa ya sani?"
"Please am i right?"
Fuska ta rufe da hannayen ta tace
"Na yadda kai Dr ne."
Ta fada tana murmushi, yai murmushi yace
"Da gaske dai Sajida zata samu 'kani ko 'kanwa?"
Kai ta gyada tana rufe kan ta a jikn sa, murmushi ya saki yana kara rumgume ta tare fadin
"Alhamdulillah, Allah nagode maka a baya nayi zaton ba zan kara aure ba bare har na ga jini na sai gashi yau ni ne da ya'ya har hudu ina shirin samun na biyar, Alhamdulillh, Allah nagode maka, Allah ya kara min ni'ima Allah ya yasa ki haifa min yan uku."
Ido ta zaro tana fadin
"Dan ba kai kake haihuwar ba ko?"
"Zan amshi wannan baki ga wannan cikin ba ruwan sa ba."
Bakin sa ta kama tana kissing, sannan ta saka ta dago tana kashe shi da wani kallon so da kauna, hannun ta yana wayo a jikin sa, idon sa a lumshe tace
"Wannan naga bukata ya dada min ni kadai nasan yadda naji a Kano lokacin da bama tare."
"Ai naga alama, tinda tin da kika zo kike tsotse ne."
"Kai Honey har da sharri kai ban ce ka tsotse ni ba sai kai."
Bakin ta yai kissing yana fadin
"Zo na kara tsotse kin."
Ya hade bakin su yana romancing nata daga nan suka cigaba da soyayyar su.
A haka suka cigaba da rainon cikin wanda bata da matsalar komai kulawa take samu daga Aliyu har yan uwan ta. Cikin watan ta tara ta haifi dan ta kyakyawa namiji mai kama sak da Abbin sa, sosai Yaa Aliyu yayi farin ciki inda ranar sunan yaron yaci sunan Abbin Maryam Muhammad.
Two years later
Zaune suke a cikin jirgi Maryam sai Aliyu dake gefe ta, kan ta ta daura akan kafadar sa tana mai lumshe ido, kan sa ya sunkuyo ya dan yi kissing bakin ta,
" 'Dan ka dai yana kallon ka."
Ta fada tana nuno masa Haidar dake zaune a kujerar dake opposite din su kunnen sa makale da earpease yana sauraron karatn Alkur'ani, yaron shekara goma sha shida wanda yana shekara sha biyar ya haddace Alkur'ani ya gama secondary school din sa har ya zana jamb addmission kawai yake jira.
Ya Haidar ya rumgumo ta yana fadin
"Ina ruwa na da shi, dan shi sai naki kula da matata?"
Murmushi ta saki ta rumgume shi tana fadin
"Miji na sirri na, Mijina abin alfahari na."
"Matata farin ciki na, matata abar alfahari na."
"Ina son ka mijin Maryam."
"Nima ina son ki *Matar Haidar,* Ummu Haidar, Humaira, Islam, Sajida, Aslam, and Sabir."
Dan dagowa tayi tace
"A ina Sabir din?"
"Coming soon."
Dariya tayi tace
"Gaskiya yanzu sai na huta Yaya."
"Haba Noor wane hutu kuma kin yaye Aslam uhmm."
"In dan sha soyayya wai da."
"Wannen cikin ne ya taba hanaki soyayya? Ai ke dai ki ta haifa min ya'yan so nake nan da shekara uku nagan mu da ya'ya bakwai ko takwas."
Ido ta zaro tana fadin
"Amman ba dani kadai ba ko?"
"Da wa kenan?"
"A'ah ban sani ba ko dai a gano wata yar baby."
"Lalalalah, Haidar mijin Maryam ne kawai, Maryam ce kadai *Matar Haidar* insha Allahu."
"Allah ya yadda Mijin Maryam i so much love you."
"Am eager to be with u at home Baby."
Narkewa ta karayi a jikin sa, tace
"Kano zan tafi muna sauka."
"Da izinin wa?"
"Izinin My."
"Ban yadda ba ki bari muje next week muyi two days ko?"
"An gama Ranka ya dade."
"I love you Honey."
"I love you more."
Ya rumgume matar sa suna 'kara keta hazo dan dawowa gida Nigeria daga 'kasa mai tsarki da sukeje sukai aikin hajj.
*Alhamdulillah!*
*Alhamdulillah!!*
*Alhamdulillah!!*
Alhamdulillah da Allah ya nuna min farkon da kuma karshen littafin *MATAR HAIDAR,* Allah ya yafe min kuraren da nai darasin dake ciki Allah ya ba mu ikon amfana da shi.
*Afwan ina neman yafiyarku mace ko namiji babba ko yaro wanda na sani da wanda ban sani ba wanda na tab'a magana dashi ko ita da wanda ban tab'a magana ba ni na yafewa kowa. Fatan alheri.*
*JAN HANKALI*
*BAN YADDA WANI KO WATA YA COPY KO YA JUYA MIN LABARI, KO YA KARANTA MIN A KO WANNE CHANNEL BA TARE DA IZINI NA BA. NAGODE*
_Na sadaukar da littafin nan ga My first and last love Ummi nah, Allah ya kara miki lafiya da nisan kwana Allah ya biya miki bukatun ki na alheri, Allah ya kara budi ya faranta miki duniya da lahira, Allah yai miki tukwici da gidan Aljanna madaukaki Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum. I so much love you My Mommy._
*Our Momy Hajiya Nafisa ina godiya da yadda kika kara min kwarin gwiwa tare da addu'a Allahu ya saka miki da gidan Aljanna, Allah ya biya miki bukatun ki na alheri Allah ya raya zuri'a Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum.*
_Mariya Kabir Bako (Bintu Sheihk), Fatima Muhammad Sani (Habibty), Sadiya Mohd (Barrister Sady) nagode da kauna da yadda kuke kara min kwarin gwiwa Allahu ya bar kauna Allah ya saka muku da gdn Aljanna. I so much love you Sisters._
*Ba zan manta daku ba makaranta *MATAR HAIDAR* ina godiya da yadda kuka bibiyi labarin nan tin daga farko har karshe nagode sosai da sosai.*
Godiya ga dukkan member na wandan nan groups din
*Indabawa Hausa Novels*
*Matar Haidar Fans Group*
*Hakuri da Juriyya Online writers*
*Maryan Salisu Maidala*
*Special Room Ummu Farisa*
*Marahmad Chatting forum*
*Sona Hausa Novel/ Qalbina comment group*
*Masarautar Zeedan*
*Romantic Hausa Novels*
*Khaleesat Haydar Novels*
*Kasaitattun Mata Group*
*Na'ikke Hausa Novels*
*RAZ Novella*
*Bakuwar Fuska Fans*
*Sirrin Zamantakewa*
*Bintu Sheihk Hausa Novel group*
*Hausa Novels*
Da sauran da ban lissafo ba dukka ina godiya.
I will not forget with my Facebook fans, the groups are many, but dukkan ku kuna raina na ina godiya da yadda kuke min comment da addu'a Allahu ya bar zumunci u all are the best thank you.
*My Wattpad Fans, you too i really appreciate with all your, vote, comment, i heart u all, especially Aishaummulkairi and BarakaJoda, MamanAlmeen da sauran gaba saya*
_Ba zan taba mantawa daku ba My whatsapp fans Amina Yar'adu'a, Samira Malami, Caramella Queen (Shaheedah), Nabila, Jamila, Zuwaira Zuzu, Ubaidah, Ummi Glomor, Kaltoom, Maryam Danlitti Sheshe, da sauran kuna da yawa sosai, nagode da yadda kuka kasance dani tin daga farko har karshen labari na nagode da yadda kuka dinga bani nishadi da addu'a tare da ban kwarin gwiwa i so much love you._
*Am so glad, i never know that MATAR HAIDAR will have such followers, Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!*
Sai kuma idan mun sake tarayya da ku a littafi na gaba, idan mai komai mai kowa ya yarje mana.
AM SAYING A GOOD BYE TO *MATAR HAIDAR FANS* I GONNA MISS YOU ALL THANK, YOU, THANK YOU, THANK YOU.
```Dan Allah duk wanda ya karanta wannan littafin nawa yanzu ko nan gaba yai min addu'ar gamawa lafiya in kuma na mutu yai min addu'a Allah min rahma ya jikai na. Amin nagode```
```Yaa Allah ka kawo mana dauki a cikan wannan rashin tsaron da muke fama dashi, Allah ka kare mu da duk al'ummar musulmai Allah ya daukaka musulunci da musulmai Allah ka karya karfici da kafirai Allah ka dadawa Annabi Muhammad SAW daraja Amin.```
_Allah ya jikan mu ya gafarta mana Allah ya mana rahma ya kyauta namu zuwan Allah yasa muyi kyakyawan karshe, Allah jikan dukkan musulmai ya kyautata namu zuwan Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum._
Fatan alheri daga taku har kullum *Maryam Suleiman Indabawa*
*Subhanakallahumma wabi hamdika, ashahadu an la'ilaha illa anta, astagfiruka wa'atubu ilaika*