Showing 63001 words to 66000 words out of 232912 words

Chapter 22 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1268

yafi wancan zafi Yaa Haidar ciki na ciwo yake min!"
Hannun sa ya daura akan cikin yana fadin
"Kiyi hakuri ba zan sake ba, tashi muje kiyi wanka ki sallah ki tafi gida kar Ammi ta neme ki!"

Kai ta gyada. Ya dauke ta suka shiga bandaki yai mata wanka bayan ya gama ya barta tayi na tsarki sannan ya nado ta cikin towel ya ajiye ta akan gado. Wardrobe ya bude ya dauko mata rigar sa ta saka under wear din ta da katon hijab ya bata ta saka ta mike a hankali ta tada sallah. Tana idarwa ta jingina kan ta a jikin gado.

Karasowa yayi yace
"Zo na duba ki kinji!"
Ya kamo hannun ta ya mikar ya dauke ta ya daura akan gado hijab din ya cire mata ya dage rigar ta yace
"Ina ne yake ciwo?"

"Jiya da kana min abun wani abu ya tare min a ciki na."
Murmushi ya saki yace
"Yaushe rabon da kiyi ciwon mara?"

"Tin wancan karon fa!"
"Wane karon?"
Ya tambaya yana shafa fatar cikin.

Fuska ta shagwabe tace
"Da ka dauken a makaranta mukai....."
Sai kuma tai shiru yana murmushi yace
"Mukai me?"

Hannun sa ta buge ta mike tace
"Ka ban magani Yaya!"
Janyo ta yayi yace
"Matata sirri nah, Matar Haidar, Farin cikin Haidar, Jigon Haidar, Hasken idaniyyar Haidar, Ruwan idaniyyar Haidar!......"

Hannuta ta daura akan bakin sa tace
"Yaa Haidarr!"
Kallon ta yayi yace
"Na gama gamsu cewa duk duniya, kece sirrina Maryam! Dole ki zamo suturata, kamar yadda nima zan zama suturarki, kamar yadda Allah (S.W.A) ya fadi."

Ya ƙarashe maganar yana manna bakinshi da nata, lips ɗin ta duka biyu ya ɗan kamo ya tsotsa a hankali. sannan ya sake, kiss ya manna mata a goshi kana ya manna mata a tsakanin wuyanta da kafaɗarta, harshensa ya zaro ya manna bisa wuyanta yana ɗan lasawa. Hannun sa ta kamo tace
"Yaa Haidarrr!"

"Uhmm *Matar Haidar* !"
Ya fada yana shinshinar wuyan ta, sannan yace
" *Matar Haidar* yau duniya zata 'kara tabbatar wa da nine sirrin ki nine mijin ki."

"Yauwah ina son muyi magana Miji nah!"
"Uhmm ina jinki!"

"Yaa Haidar menene hukuncin auren da zamuyi bayan...."
Sai tayi shiru, hannunta ya kamo yace
"Hmmm menene hukuncin auren mu, to yanzu ya za ayi me kike ganin za ayi?"

"Yaa Haidar mu sanarwa iyayen mu halin da muke ciki!"
"Kina ganin ba matsala?"

"Insha Allahu babu Yaya."
"Ok shikenan anjima zan fadawa Mamah ki fadawa Ammi ko Abbi zaki fadawa?"

"No Ammin dai!"
"Ok ki fada mata."
Ya fada yana kai kunnen sa cikin ta, shiru yayi can ya dago ya kalle ta yana murmushi yace
" *Matar Haidar* Uwar ya'yan Haidar Ina son ki, ina kaunar ki, ki yadda da son da nake miki, ki tayani raino da bawa ya'yan mu tarbiyya, ki fada musu Dadyn su yana son su, ki fada musu ina kaunar Momyn su dasu dukkan su. Ina kaunar ki Maryam, ina kaunar ki Maryam, ina kaunar ki Maryam!"

"Nima ina kaunar ka Yaa Haidarr!"
Rumgume ta yayi yace
"Zanyi kewar ki *Matar Haidar* "
Ido ta lumshe sai kuma ta bude a hankali.

Da sauri ta mike Aliyu ma ya mike yana fadin
"Kina yi a hankali fa."
Fuska ta shagwabe tace
"In Ammi ta gane ba a gida na kwana bafa?"

"Dadin yadda zaki fada mata meke a tsakanin mu ma kenan."
Hararar sa tayi tace
"Kai Yaa Haidar ni dai na tafi."
Ta juya zata tafi yace
"Tsaya na rakaki mana."
"A'ah!"

Bayan ta yabi da sauri ta fice ta nufi gate yana tafe a bayan ta, har suka karasa bakin gate inda mai gadi yake, gaishe shi tayi ta fita Aliyu yabi bayan ta, tana shiga gida ta juyo ta daga masa hannu tayi cikin gida murmushi ya sakar mata ya juya ya fita.

Tana shiga ta nufi dakin ta, su Aisha duk suna kwance suna bacci da wasu yan matan. Kan resting chair ta zauna tana mai lumshe ido tino abinda ya faru jiya tayi take tsigar jikinta, ta tashi. Wayar ta taji tana kara ta dauko ta zauna tare dakaiwa kunnen ta Yaa Haidar ne kwanciyya tayi tace
"Yaya lafiya?"

"Gani kwance a kan gado ina shakar kamshin turaren ki, wallahi kewar ki ce ta fara damu na, ban gaji da jin dumin ki da Jin muryar ki mai zaki ba."
"Yaya Haidar kenan bana son kanasa damuwa da tunani aranka ka ba kada ka manta ni taka ce ba tin yau ba kawai dai yau zan dauwama taka, a karkashin kulawar ka mu kasance tare a ko da yaushe amman menene sabo, in doki ne nasan ba abinda zakai doki a waje na."

"Waya fada miki? Wallahi Allah kinji nace Allah ko nafi jin dokin akan before a yanzu nafi bukatarki ba abun haramci mukai ba da Allah zai saka mana tsanar juna. Ki sani ina sonki kuma ba zan taba daina sonki ba har abada. Ki yadda dani *Matar Haidar* ki yadda ko bana nan zan bar miki jigo wanda zai taimaka miki wajen cika burin ki i love you my wife!"
"Love you more Husband. Allah ya bamu zaman lafiya ya kade fitina ya hade kan mu ya kara mana fahimtar juna Amin!"

"Amin Amin *Matar Haidar* fada min me zaki tanadar min anjima!"
"Ni kuwa me zan tabadar maka bayan dan gyaran da akai duk ka shanye abinka"
"Ai nasan anjima za a kara baki wasu kuma ba dukka na shanye ba fa na rage na anjima."

"Kai Yaa Haidar!"
Murmushi yayi yace
"Da gaske man."

"Ni dai ba ruwa na."
"In fada miki wani abu da zaki sha ki kara...."
Wayar ta kashe tana dariya.

Kira ya kara, kamar ba zata dauka ba ta dauka,
"Saboda me zaki kashen waya, ni kai na nakewa fa dan bake zakiji bane da, da gudu zaki ce eh to ni ba zan sha abinda zai sa kijini so sweet ba."

"Yaa Allah yaushe Yaa Haidar ya koma haka ne?"
Dariya yayi yace
"Tin da nasan wacece Matata."

"Iyeee wacece ita to?"
"Itama jarababbiya ce kamar yadda Ahmad yake ce min jarababbe."

"Lah lalah wallahi ni ba ruwa"
"Oh ko zan mai daki da ruwan ki, indai kina tare dani. zan miki text din abinda zaki sha in babu kuma yanzu zan bayar akawo miki. Ko da yake Matata akwai sweet kin tina waccan karan bani da haufi akan ta nayi dace sosai ga ta kyakyawa ga ilimi ga tarbiyya ga ni'ima....."

"Ni dai ba ruwana."
Aisha ce ta tashi tace
"Oh ku wai tin safe har kun fara soyewa dan Allah Yaa Haidar yai hakuri anjima dai za a kaiki dakin sa mu huta."

"Kana jin ta ko Yaa Haidar?"
"Barni da ita zan kamata ne. Kuma ai matata tace."
Ta mike tace
"Bari naje na gaida Ammi!"

Ta fita ta nufi dakin Ammi, Ammi zaune ita kadai zama tayi a kasa tace
"Ina kwana?"
"Lafiya lou kin tashi lafiya?"

"Alhamdulillah!"
Shiru tayi Ammi ta kalle ta tace
"Lafiya?"

"Ammi daman ina son muyi wata magana ne!"
"Ina jin ki."

"Ammi daman ni da Yaa Haidar ne.....'
"Assalamu alaikum!"
Yaya Ummulkursum tai sallama. Amsawa Ammi tayi ta kalle ta.

"Ammi, Abbi ne ke kiran ki."
"To!"
Ta fada tana kallon Maryam tace
"Ina zuwa."

Yaya Ummulkursum tace
"Taso muje na karasa baki wancan hadin!"
Ta mike tabi bayan ta. Bangaren Yaa Muhammad suka nufa sai ga Yaa Abdullah nan da sauri ya shigo da leda a hannun sa. Mikawa Maryam yayi yace
"Inji Yaa Aliyu!"
"Nagode!"
Ta fada tabi bayan Yaya Ummulkursum. Suna shiga sukai wani daki mai mata gyara ce a ciki, tace
"Jiya ba ai ba yau ma ba za ai bane?"

Kai ta girgiza tace
"Gani ai!"
Yaya Ummulkursum ta amshi ledar hannun ta tace
"Menene wannan?"

Ledar ta mika mata ta amsa ta leka tace
"Wa ya baki wannan kayan arzikin bari na gyaro miki!"
Ta shiga kitchen tai blendung ta zuba madara ta kawo mata tana sha ana mata gyara har sha biyu sannan aka gama ta shiga tai wanka ta fito aka sa ta fara turare jikin ta. Sai daya saura sannan aka dauko mata kayan wani farin less mai adon golding ajiki ta saka wasu dan kunne da sarkar gold wanda yake har kan kirjin ta haka abin hannun ta da agogon ta duk na gold ne. Farin mayafi ta yafa mai golding kala ta saka golding half cover. Ba ai mata kwalliya ba amman tayi kyau har ta gaji da kyau.

Aliyu kuwa yana dakin sa ya fito da kayan da wani farar shadda wacce akai yar ciki da babbar riga ya ajiye akan gado yana zaune wayar sa a kunnen sa yana fadin
"Kun shirya dai ko dan yanzu zan fito saura rabin awa dan Allah ku shirya gani nan."

"Ok sai ka karaso."
Mamah ce ta shigo da sallama ya amsa yana dagowa ya kalle ta.
"Neman me kake min?"

"Mamah wata magana ce daman zamuyi!"
"Kuma sai dole yanzu Aliyu."

"Tana da mahimmanci ne yanzu!"
Wayar ta ce tayi kara tana dubawa taga Abbahn sa ne dauka tayi sai ta mike da sauri tana fadin
"Gani nan ranka ya dade."

Aliyu ta kalla tace
"Bari naje ina zuwa."
Ta juya ta fita komawa yai ya zauna cikin sa yaji yana masa ciwo mikewa yayi ya bude firij ya dauko maltina ya sha sannan ya dauko magamin sa ya sha. Kwanciyya yayi a hankali sai yaji cikin yana saki, mikewa yayi ya saka kayan wanda ya kara fitowa a ango yai kyau sosai. Ya shafa turare yana tsaye ya saka agogo Alkasim ya shigo yana binsa da kallo yace
"Ango kaga yadda kayi fresh da kai."

Tafawa sukai yace
"Ko?"
"Eh! Tare muke da su Ibrahim fa kazo mu tafi sauran minti goma a kira sallah fa."

"Muje!"
Ya fada yana neman layin Maryam tana zaune a dakin Anty Rabi ita da kawayen ta kiran ya shigo dauka tayi takai kunne yace
" *Matar Haidar* na shirya na fito zamu tafi fa ai mana addu'a."

"Adawo lafiya Allah bada sa'a."
"Amin nagode."

Ya kalli Alkasim da ya zuba masa ido yace
"Ya dai?"
"Zan zo ka koyan soyayya."

Dariya yayi yace
"Kai da Ahmad yan iska ne wallahi."
Suna fita suka hadu da Mama a compound dake cike da mutaneya karasa ya durkusa yace
"Mamah mun tafi."

"Allah tsare ya bada sa'a!"
"Amin nagode!"
Suka juya suka tafi a masallacin Abbi dake sallah juma'a akai sallah juma'a bayan an idar dubun nan jama'a dake wajen suka shaida daurin auren Aliyu Haidar Suleiman da Amaryar sa Maryam Muhammad Jabeer.

Waya ya zaro ya shiga text ya rubuta
"Alhamdulillah Finally duban jama'a sun shaida Maryam ta zama *Matar Haidar* ina miki fatan alheri Matata. Allah miki albarka."




*Allah ya jikan mu, yasa mu cika da kyau da imani, Allah yasa.muyi kyakyawan karshe, Allah ya jikan iyayen mu da kakkanin mu. Amin*



*Antty*
💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 22

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*


*
Maryam na zaune sakon ya shigo hawaye ta fara na farin ciki da sauri ta mike ta tada sallah godiya ga Allah ta idar ta jima tana addu'a su Aisha sai huto da vedio suke mata.

In kaga Aliyu bakin sa ya kasa rufuwa sai Allah sanya alheri ake masa yana ta washe baki a ka'ida sai 3pm za a tafi reception dan haka daga nan gidan su Maryam suka isa. Bangaren Ammi suka fara shiga suka gaisheta da godiya Yaya Fadima tai musu jagora bangaren Yaa Muhammad.

Suna shiga ya dinga baza ido dan ya gano Maryam a tsakiyar Aisha da Rukayya ya hango ta an rufe mata fuska da sauri ya karasa ya rumgume ta tsam a jikin sa yana fadin
"Alhamdulillah finally jama'a sun shaida abin boye, Maryam ta zama *Matar Haidar* farin cikina, hakika ko yau na mutu buri na ya cika mutane sun shaida ke din Matata ce."

Yan dakin suka hau Kabbara suna fadin
"Allahu Akbar Allah ya bada zaman lafiya ya bada zuri'a mai albarka."

Fuskar Maryam ya dago yaga hawaye hannu yasa ya goge mata yace
"Kice Alhamdulillah Maryam komai ya faru dake mai kyau ko akasin haka kice Alhamdulillah Allah zai kara miki sama da abinda kika sama."
"Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!!"
Ta furta tana jin wani sanyi a zuciyar ta.

Haka aka dinga daukar su picture masuyi nayi masu vedio nayi anan suka jima dan sai uku sannan suka tafi kamar kar su rabu ya tafi yana daga mata hannu itama haka. Wanda yana tafiya taji zuciyarta, ta tsinke gaban ta na faduwa.

Nan aka fara yinin gida inda Amarya ta shiga dan canja kaya ta saka wani less mai kyau sea green ta yafa babban mayafi batai makeup ba yan matan amarya suka sha ankon atamfa green and blue sunyi kyau sallah la'asar sukai sannan suka fito suka zauna a inda akai decoration aka fara raba abinci ana ci ana sha ana kida da rawa mata ne kadai ke yini kamar yadda gidan Mamah ma suke can suke yi.

Su Aliyu kuma suna can Meena event centre ana reception abokai sai abinci suke ci shi kuwa yana zaune a takure waje daya. Alkasim ne ya karasa yace
"Ya dai Angon Maryam?"

Hannun sa ya kamo suka fita a wajen yace
"Buden mota na kwanta ciki na ke ciwo."
Bude masa yai ya shiga baya yace
"Ko mu tafi asibiti ne?"

"A'ah kaje ka kula da sauran abokan mu kace musu bana jin dadi ne."
Kwanciyya yayi Alkasin yace
'Ba matsala?"

Kai ya gyada Alkasim ya juya ya tafi Aliyu ya rufe kofar motar ya kunna AC amman gumi yake dan haka ya mike ya zare Babbar rigar sa. Wayar sa ya dauko ya fara rubuta sako
" *Matar Haidar* ki yafewa Haidar, Haidar yana son ki burin sa ya rayu dake har karshen rayuwar sa."

Ya ajiye wayar yana dafe cikin sa dake juya masa wanda ya jike da gumi ya jingina kai yana fitar da numfashin sa da kyar.

Maryam dake wajen biki hankalinta gaba daya baya wajen dan yadda zuciyar ta ke bugawa sakon Aliyu ne ya shigo ta karanta ta kuma karantawa amman ta kasa daina karantawa kuma gaban ta bai daina bugawa ba.

Alkasim kuwa yana can yana fama da mutane wanda suke da yawa dan ka rantse lokacin aka daura aure kowa yana sha'anin gaban sa wasu na cin abinci wasu hira dan haka duk ba su lura da rashin Aliyu ba.

Wani juyi da cikin sa yayi wanda yasa ya saki salati tare da lumshe idon wanda nan take numfashin sa ya fara masa wuya dawowa, haka ya dinga jan sa da kyar wanda in yaja baya iya dawo da wanda ya shiga sai dai ya nemi wata iska, dan haka abun sai ya hadar masa goma da ishirin ga ciwon ciki ga numfashin sa dake neman daukewa. Hannun sa akan cikin sa yana juyi ba abinda yake sai ambaton Allah

Wanda a dai dai wannan lokacin Maryam ta fara fita daga hayacin ta dan wani irin haki take sai kace ita ce ke fama da ciwon nasa. Aisha ce ta lura da Maryam din na cikin wani hali ta karaso wajen ta hannunta ta kama ai kuwa Maryam ta damke hannun tana daura dayan hannun ta akan kirjin ta. Idon ta ya ciko da kwalla ganin haka ne yasa Aisha dago ta suka bar waje daki suka tafi ta zauna sai kuma ta fara neman layin Aliyu wanda yana kwance yana fama da ciwon ciki sam bai ma ji ringing din nata ba.

Ta kira shi sama da sau biyar amman bai dauka ba Aisha ta kalla tace
"Na kira Yaa Haidar but he did not pick!"

"Haba Besty kema kinsan yana tare da mutane kila bai ji bane."
"No Yaa Haidar ba zai dauki wannan tsawon lokacin bai kira ni ba and also har nai masa more than five missed call bai dauka ba. Aisha wallahi jiki na ba dadi, zuciya tin dazu take tsinkewa."

Ta kamo hannunta, ta daura akan kirjinta tace
'Kinji ko kinji yadda take buga min da karfi ko, i feel like something bad will happened, ina son nasan halin da Yaa Haidar yake....."
Ta kasa karasawa saboda yadda jikin ta yake rawa da kukan da ya kwace mata.

"Haba Maryam ki nutsu insha Allah nothing bad will happened insha Allah be reciting Innalillahi wainna illahir rajiun."
Amsa tayi ta dinga maimaitawa tana cigaba da kiran Aliyu.

Aisha na kusa da ita tana ta bata baki, Yaya Zainab ce ta shigo ta gansu a haka tace
"Me yake faruwa ne? Ke nake nema kije ki wanka magariba ta kusa."

Idonta ta dago ta kalle ta tace
"To ina Yaa Haidar?"
"Me zai miki bayan yanzu za a kai ki kwa hadu a gidan ku. Aisha rakata bangaren Anty Hauwa tai wanka na hada mata ruwa kayan da zata sa suna dakin kuyi sauri gani nan ma dai."

"To!"
Ta fada. Mikewa Aisha tayi ta kama hannunta da har yanzu jikin ta rawa yake. Dakin suka shiga ta cire kaya ta shiga dan yin wankan.


Karfe biyar da Rabi Alkasim ya fito jin shiru ba Aliyu ba alamun sa har lokacin ko cikin bai daina ba. Mota ya bude ya same shi cikin mawuyacin hali duk ya jigata da sauri ya dago sa yana kiran sunan sa amman bai san inda hankalin sa yake ba. Motar ya tayar ya fice ya nufi asibiti dashi ana zuwa aka amshe shi a emergency a bakin dakin ya tsaya yana zarya ya kasa zama kwata kwata. Tin shida saura amman har shida da arbain ba wanda ya fito a dakin domin jikin Aliyu ba karamin tashi yayi ba.

Maryam na fitowa Yaya Zainab ta shigo da kwaskon turaren wuta ta ajiye ta zuba aciki ta sa ta turare jikin ta da kasanta. Kayanta ta saka wata atamfa fara ce mai adon purple, purple din anyi shi nai sheki. Riga da zani ne ta saka farin mayafi da farin flat takalmi duk abinda take jikin ta rawa yake. Kallon ta Yaya Ummulkusum tayi da ta shigo tace
"Kinci abinci kuwa?"

Aisha tace
"Ba abinda taci."
"Ai ga jikin ta nan yana ta rawa. Me za a samo miki?"

Kai ta girgiza. Yaya Zainab tace
"Barta angon ta ya ciyar da abarsa."
Hawaye ne ya zubo a idon Maryam dan ita ta rasa a wane hali take ciki.

"Kuka kuma?"
Zama tayi gefen gado. Yaya Ummulkursum ta karaso ta kama hannun ta tace
"Ki kwantar da hankalin ki wajen Yaa Haidar fa za a kai ki menene na kuka ko yaushe kike son ganin Ammi zai kawo ki, ki daina kukan kinji."

Kai ta gyada tace
"Tashi kiyi sallah kan azo a tafi dake."
Kai ta gyada ta mike ta nufi kan sallaya dan tayo alwala ta tada sallah. Fita su Yaya Zainab da Yaya Ummulkursum sukai ya rage Aisha da ta shiga dan tayi alwala. Number Alkasim ta fara nema, yana dauka tace
"Kuna lafiya? Ina Yaa Haidar?"

Dakin da Aliyu yake ya kalla yace
"Lafiya lou. Yana nan kalou menene?"
"Maryam ta damu tana kira sa bai dauka ba ina fatan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login