Showing 207001 words to 210000 words out of 232912 words
Chapter 70 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
fa mun shirya zamu zo Yaya ya ganmu wai ina zamu, muka ce gidan ki wai a'ah mu bari sai wani lokacin yanzu shima zai koma. To kinga me zamu zo muyi shiyasa muka canja akala mukai gidan Aisha."
"Ai shikenan kun kyauta."
Ta kashe wayar, tana mai mikewa dan ta gyara gidan tin da ya tafi ya barta dakin sa ta shiga ta fara gyarawa ta canja zanin gado ta saka turaren wuta haka ta gyara dakin ta, da dayan dakin, dukka falon ma haka ta gyara ta saka turaren wuta, bayan ta gama ta kunna kayan kallo ko sa debe mata kewa.
*
Karfe uku da rabi da minti bakwai ya shigo unguwar wanda yai dai dai da kiran sallah da ake a massalacin dake kusa da gidan shi, parking motar sa yayi anan bakin gate ya fito ya nufi massalacin ya zauna yana tasbihi har aka tada sallah suka hada sahu sukai sallah, sai da ya idar da sallah ya fito motar sa ya shiga mai gadi da lokacin shima ya dawo daga massalaci ya bude masa gate take ya cinna hancin motar ta shiga cikin katon farfajiyar gudan nashi wanda zata dauki a kalla motoci sama da guda shida gashi an kawata farfajiyar da shuke shuke masu kyau wanda suka karawa wajen kyau da sanyi.
Maryam ma dake kallo kiran sallah yasa tai dakin ta bayan ta idar ta kara gyara fuskar ta wannan karan har da jan baki ta kara shafa turarukan ta masu dadin kamshi ta dawo falo ta kwanta akan kujera, bata jima da kwanciyya ba ya shigo bakin sa dauke da sallama, amsawa tai tana kallon sa, kayan hannun sa ya ajiye ya buda mata hannu, a hankali ta tashi, tana tafiyar ta mai daukar hankali ta karasa wajen sa ya rumgume ta yana daga ta sama sukayo cikin dakin, akan kujera ya ajiye ta yace
"Sannu da zuwa Yaya."
"Yauwah My Noor ya gida?"
Kukan shagwaba ta fara tace
"Shine ka gudu ka barni....."
Bai batar ta ta gama maganar ba ya hade bakin su yana aika mata da wani zafaffan kiss, wanda tini tai lukum da ita sai da ya mantar da ita batun sannan ya dago ta ya matse ta a faffadan kirjin sa, wanda kamshin junan su ke ratsa jikin su da ruhin su,
"Kina jin yunwa ko?"
Ya rada mata cikin kunnen ta, kamkameshi tayi jin yana sauke mata numfashi a cikin kunnen ta, kansa ya janye ya kwantar da ita ya dauko musu kayan da ya shigo dasu, abincin da Ummi ta bawa su Najwa su kawo mata ne sai fruits din da ya siyo musu a hanya bayan ya ajiye ta ya dauki ledar yai kitchen tare suka gyara friut din sannan suka dauko plate, a jikin sa ya zaunar da ita yana bata abincin shima yana ci har suka koshi suka fara shan fruit din da ta hada musu.
Bayan sun gama ta kwashe kwanunkan ta wanke su ta dawo falon zata zauna a gefen sa ya miko mata hannun sa ya saka ta a cikin jikin sa yana fadin
"Indai daga ni sai ke ne, nan ne wajen zaman ki kinji?"
Ya fada yana tura kan sa 'kansa wuyanta yana shakar kamshin turaren ta mai dadi wanda yake kara fuzgar shi yana kara masa wutar sha'awar kasancewa da ita.
"Baby wanne turare ne wannan?"
Gaban ta ne ya fadi, dan Yaya Fadima ce ta bata shi, murya a sanyaye tace
"Me turaren yayi?"
"Ya min dadi."
"Humra ce."
"Uhmm so sweet i like it."
Ya sakar mata kiss a wuyanta wanda take tsigar jikin ta ta tashi.
Haka suka wuni manne da juna yana bata wata irin kulawa tamkar zai maidata cikin cikinsa, Maryam kuwa sai kara shishige masa take tana sakar masa shagwab'a, wacce take kara masa shiga wani yanayi yana nan nan da ita, suna a wannan halin akai kiran sallah magariba, tare suka shiga daki yai alwala ya tafi massalaci ita kuma ta tada sallar ta a daki, bayan ta idar ta zauna tana azkhar da lazumi ta dan ya fada mata sai yayi isha'i sai shigo gidan.
Bayan ta idar da sallah isha'i ta mike ta shiga tai wanka ta fito daure da towel, bangaren da aka ajiye mata yan kananun kayan ta ta nufa dan dauko wanda zata saka, dan duk da an mayar wa da Muhammad lefe sunce ta rike amman Abbi yace sam ba zasu amsa ba, to wannan yasa Ummi ta shiga kasuwa da kanta ta siyo mata kananun kaya masu kyau da tsada haka, daman lokacin bikin sun mata dinkuna masu yawa.
Rasa wanda zata dauka tayi, sam bataji sallamar sa ba sai ji tayi an rumgume ta ta baya, firgita tayi, ya saka kansa a tsakanin wuyan ta yace
"Ya dai My Noor."
"Ka ban tsoro Yaya."
"Tsoro kuma? Duk sallamar da nayi tunanin me kika tafiyi?"
"Na rasa kayan da zan dan saka ne."
Tai maganar cikin shagwaba, Kamo hannun ta yayi ya ajiye ta akan gado ya juya ya nufi gaban wardrobe din kayan ya dinga dauka yana kallon sitikan kayan dake jere a haka idon sa ya sauka akan wasu wanda ya kasance mini siket ne da yar karamar riga red colour ne, su ya dauko ya karaso ya ajiye ya dauko mata pant da bra duk ya kawo yace
"To na zabo miki."
Ta dago tana kallon kayan wata kunya taji ta kamata tace
"Nifa basu zan sa ba Yaya."
"To ni su nake so ki sa min."
Ya dauko pant din nata yace
"Tashi ki saka."
"Uhmm Uhmm Yaya ni bani zan saka da kai na."
Kai ya girgiza yace
"Ni zan shirya matata."
Dan dole ta hakura ya saka mata, haka a wajen saka bra ma, tana ganin yadda yake kallon kirjin ta har sai da ya tsotsa ya samu yar nutsuwa ya saka mata kayan wanda ba karamin kyau sukai mata ba, gashin kan ta ya zare wa ribom din ya sake shi ya sauko har bayan ta, yana fadin
"My Baby u look so take away, wallahi da zan iya hadiye ki da na hadiye ki."
Jikin sa ta fada tana rufe fuskar ta, dan wata kunyar sa taji gani take kamar ba Yaa Haudar din nan bane mai tsare gida wai shi ke mata wadan nan abubuwan, dago ta yayi yace
"Dago na kara kallon ki My property!"
Ya dago ta yana kallon ta tin daga sama wacce rigar iyakar ta cibiya ta sai siket din da kungun ta ya bayyana sosai iyakar sa cinyar ta dogayen fararen cinyoin ta duk a waje, gaban mirrow yayi yana fadin
"Ina turaren nan yake?"
Kwalbar da yake ta nuna masa kwalbar ma kanta abar kalla ce ya dauko ya zuba a hannun sa ya fara shafa mata a wuyan ta zuwa cikin ta da cinyoyin ta, daga baya ya dauke ta suka fita falo, TV ya kunna mata ya juya yace
"Five minute."
Ya shiga daki wanka yayi shima ya shirya cikin three quartern wando da riga armless yayi barin turare, yana fitowa ana knocking karasawa yayi wajen ta yai kissing nata a kumatu sannan ya nufi babban falo, yana budewa yaga Farouk ne,
"Ranka ya dade Yaya Angon Anty Maryam."
"Farouk wai yaushe na fara wasa da kai ne?"
"A'ah Yaya nifa auren nan nake so, dan dana san da kai za ayi da tini nima zance ayi."
"Tinda ga sa'an ka ko?"
"Ah haba ni na isa Yaya, ina Auntyn tawa?"
"Bacci take."
"Shikenan agaishe min da ita kan nazo cin abincin amarya."
Juyawa Aliyu yayi yace
"Sai da safe."
"Allah tashe mu lafiya."
Ya juya yana dariya kasa kasa. Yana shiga ya ajiye kayan abincin ya nufi wajen Maryam ya dago ta ya rumgume yana bata wani kiss sai da suka dade a haka sannan ya zuba musu gashin kazar da Ummi tai musu da kayan ta wanda taji kayan hadi sai kamshi take, ita kadai suka ci, sannan suka shiga suka wanke kwanukan, falo suka koma suka kara makalewa juna Yaa Haidar na kara rikirkita Maryan da salon sa.
*Allah ya jikan mu yai mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe Amin.*
*Antty*
[12/11, 09:46] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 83
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Kwanan su Yaya Fadima biyar suka zo gidan Maryam, ranar Aliyu yini yayi a takure sai ta kai masa abinci ko wani abu yake samu ya dan rike ta ya dan tsotsotse ta sannan ya bar ta da kyar, sai yamma suka tafi wanda washe gari suka daga Kano ta dabo ko da mai kazo an fika.
A haka suka kwashe sati biyu suna shan amarcin su, a cikin sati biyun nan ba karamin kulawa da tarairaya Maryam ta samu a wajen Yaa Haidar ba, dole ta sake take biyewa Yaa Haidar suke shan soyayyar su, soyayya suke mai tsafta da fahintar juna kowa na son kowa kowa na son faranta ran junan su, yadda suke soyewa sam baki bazai fad'i irinta ba, dan wata irin soyayya sukewa junansu, kamar zasu cinye junansu soyayyace mai cike da kulawa da tattalin juna.
A haka suka cinye sati biyun hutun sa, ranar Monday tin asuba bata koma ba dan tasan ranar zai fara zuwa aiki itama kuma zataje makaranta, tsaye take a kitchen sanye da wani wando iyakar sa cinya sai yar vest wacce bata da hannu, kanta sanye da hula fara tas, tana ta hada-hadar musu breakfast, wanda shi kuma Yaa Haidar shigowar sa kenan daga massalaci sanye da jallabiya milk kala ya ji ta a kitchen, kitchen din ya karasa ya shiga da sallama, ta amsa tana fadin
"Welcome Honey."
Ya karasa ya rumgumo ta ta baya yace
"Morning Noor ya aiki? Yau na barki da aiki ko?"
"To ya za'ai tinda fita zamuyi."
Suyar ya amsa yace
"Kawo na karasa aiki na."
Ta sakar masa tana komawa bayan sa ta saka hannunta ta zagaye kugun sa, ta saka kanta a bayansa,
"My Noor ni dai ji nake kamar na bar aikin na mu cigaba da zaman mu a gida."
Sakin sa tayi tana dariya tace
"Kai Yaya kaga daga nan nima sai kace na ajiye karatun ko?"
"Allah Baby da ace karatun ki yafi shakara daya da hakura zaki dashi."
Ido ta zaro tace
"Kai Honey."
"Allah da gaske nake."
"To yanzu dai a barni na karasa ko dan na cika burin Yaya da ni kaina ko?"
Ya juyo yana binta da wani kallo, da sauri tai kofa tana dariya hadi da fadin
"Karasa bari na gyaro daku nan kada ka makara."
Sam Maryam bata da nawa kuma daman dakin ba wani datti yayi ba tana shiga ta gyara ta turare shi ta fito tana gyara falon da shima ba dattin da yayi, tana cikin mopping taji ya daga cak yayi hanyar bedroom din su da ita,
"Yaya ban gama aikin ba fa."
"Muje kiyi wanda yafi shi samun lada, Allah yau ni kadai nasan irin missing din ki da zanyi."
"Haba Yaya awa nawa ne?"
"Ke kike ganin haka."
Ya fada yana dire ta akan gadon tare da hayewa kanta.
8:30am
Tsaye take yana saka mata kaya sai turo baki take ya dago ya kamo bakin yana kissing nasa, wanda ya dauki minti wajen uku yana kissing bakin nata kafin ya saki, tace
"Uhmm ina fushi ka makarar damu shine kake son kara wani laifin ko?"
"Allah My Noor bana gajiya dake, kiyi hakuri danasa kika makara kinji?"
"Kai Honey nifa da wasa nake in kana son ka dada mu koma mana."
Riko hannun sa tayi zata jasa, ya janyo ta yana murmushi yace
"A'ah zo muje mu karya sai mu tafi."
Suka fita falo a cinyar sa ya daura ta suka karya ta kwashe kayan ta wanke sannan ta fito ta dauko mayafin ta kato mai dubu ta fito, Aliyu dake zaune ya dinga bin ta da kallon har ta karaso tace
"Yaya ya dai?"
"Ina zaki a haka?"
Kallon kanta tayi, cikin kamilar shigar ta doguwar riga ce ta atamfa sai babban mayafin ta da jakar ta, kansa ta fada tace
"Me shigar tayi?"
"Hijab zaki saka."
Ya janye ta a jikin sa yai cikin daki bai jima ba ya fito rike da brown kalar hijab din ta kalar atamfar ta, ya mikar da ita ya zare mayafin ta ya ninke ya saka mata hijab, wani kyau yaga ta kara, mayafin ya dauka ya shigar dashi daki sai gashi rike da ba'kin abu, kallon sa take har ya karaso ya daura mata nikaf din tace
"Oh Honey har da nikaf?"
"Kinga yadda kike ne? Haka kurum ana kallon kaya na."
Tai murmushi tace
"Ba mai kallar maka fa ba Honey."
"Yanzu ba da nai maganin abun."
Ya kamo hannun ta ya dauki jakar ta da tashi suka fita shi ya bude mata sashen ta ta shiga tana sakin murmushi tare da fadin
"Ina godiya Jarumi na."
Murmushi ya sakar mata sannan ya rufe ya zagaya ya shiga ya tada motar suka fita a gidan, suna hanya ta kira Jawahir amman da yake suna lecture bata dauka ba sai text tai mata, a haka suka karasa makarantar yai parking ya kamo hannun ta tare da dage nikaf din fuskar ta, murmushi ya sakar mata yace
"Give me bye bye kiss."
Kan cinyar sa ta haye ta hade kansu ta kama lips din sa tana tsotsa, sam sun manta a inda suke karar da wayar Maryam tayi ita ta dawo dashi hayacin su, ya saki lips din nata ta lafe a jikin sa yana shafa bayan ta, wayar tata ce ta kara kara ta dauko shi kuma ya hau zuge mata zip din rigar ta tare da gyara mata zaman hijab din ta, wayar ta kai kunne, cikin kasallaliyar murya tace
"Gamu a mota ki karaso."
Ta kashe wayar tana kallon Yaa Aliyu da shima ke kallon ta cike da so da kauna, light kiss ta sakar masa a kan lips din sa tare da sauka a cinyar shi tana fadin
"Ya dai Honey."
"Kema kin sani."
Tai murnushi dai dai zuwan Jawahir yadda su suka ganta tinda tint glass ne, ya sauke glass din, Jawahir ta gaishe dashi ya amsa yana fadin
"Ga amanar Matata nan."
Tana murmushi tace
"Baka da matsala."
Ya dauko jakar ta tare da zuba mata kudi a ciki yace
"Baby sai munyi waya ko?"
"Eh Yaya Allah ya tsare ya bada sa'a Allah ya kiyaye min kai, ka kula da kan ka."
Hannun ta ya kamo yai kissing sannan ya saki ta kamo nasa itama tai kissing sannan ta bude kofar ta fita tana daga masa hannu, har sai da ya daina gano su sannan ya bar wajen, lecture goma suka shiga, goma da rabi taji karar shigowar sakon sa, ta duba tana murmushi ta mai da masa reply, basu fito ba sai da suka dauki awa uku sannan suka fito lokacin daya saura, material din karatu Jawahir ta bata ta fara koya mata abubuwan da akai na sati uku bata nan wanda karfe daya da rabi sukaje sukai sallah, bayan sun idar ta fito ta fara neman layin sa
"Honeyyy!"
Ta fada kamar zatai kuka.
"Matar Haidar menene fadawa Haidar din ki uhmm"
"Honey na gaji."
"Sannu kinji dear sannu, ko nazo nai miki tausa?"
"Uhmmm!"
"Da gaske?"
"A'ah Yaya muna da lecture biyu yanzu mukai sallah, sai hudu zamu fito."
"Shikenan zan san yadda za ai na karaso kan hudu."
"Yaya ba sai biyar kake dawowa ba."
"Da da yanzu ai ba daya bane."
Tai murmushi tace
"To ya aikin?"
"Ba dadi babu Baby na a jiki na i so much miss you."
"I miss you more Honey."
"Take care ki samu kici wani abun kinji?"
Kai ta gyada ya kashe wayar, Jawahir tace
"Wai yaushe kuka zama masoya haka ne?"
"Idon matambayi."
Tai dariya tace
"Muje muci abinci."
"Ke ni lemo kawai zan sha."
"An dawo za a cigaba da rashin cin abinci ko? To wallahi Yaya Haidar zan fadawa."
Tai dariya tace
"Ina Yaa Muhammad kuwa?"
Yana nan jiya yake tambayar ki nace baki dawo school ba."
"Ina matar tasa?"
"Suna na lafiya."
Ta fada tana tabe baki. A haka suka gama suka shiga lecture sai karfe hudu da rabi suka fito, wanda yai dai dai da zuwan Yaa Haidar, waya yai mata ta fito, tare da Jawahir, mota ta shiga ta zauna yace
"Jawahir kizo mu ajiye ki man."
"Yaa Haidar hanyar ai ta baude nasan yanzu za a zo dauka ta."
"Zo mu tafi ma hadu a hanya."
Ta shiga motar suka dauki hanya sai da suka kusa gida sannan suka hadu da drivern nata ya taho dan ya zata sai biyar zasu taso haka suka rabu suna dagawa juna hannu.
Hannun Maryam ya kamo ta juyo tace
"Yaya ka kaini wajen Ummi dan Allah."
"Yaushe?"
"Yanzu."
"Yanzu kuma Baby?"
Kai ta gyada ya sa hannu yana shafa fuskar ta yace
"Kiyi hakuri this weekend acan zaki yini amman yanzu mijin ki ke bukatar ki, kinga yadda kika gaji ma kuwa salon Ummi tace 'yar ta ta rame."
"Wayo dai kawai Yaya."
"Muje gida na nuna miki."
A hanya yaga masu gashin kaji ya tsaya ya siya musu suka nufi gida. Shida saura kwata suka shiga gida, tin daga compound ya dauke ta sukai cikin gida, akan gado ya ajiye ta ya fara cire mata kaya shima ya cire suka shiga sukai wanka tare da dauro alwala kananun kaya ya saka masu kyau da tsada ya fesa turare sannan ya sumbaci matar sa ya tafi masallaci. Itama shiryawa tayi ta tada sallah tana idarwa ta shige kitchen. Abu mai sauki ta fara daura musu kan ai isha'i ta gama fried supergette wacce ta hada musu lemon kwakwa ta jere a dining, dakin ta ta shiga ta kara wanka ta shirya cikin wasu riga da wando wanda wandon iyakar sa gwiwa sai rigar da ta dan sakko ta baya ta rufe, gaban kuma bata rufe ba gata shara shara ana ganin abun da ke ciki ta feshe turare ta zubo da gashin ta gadon baya, gaban mudubi ta karasa tana kallon kan ta ita kanta tasan tayi kyau juyi tayi tana sakin murmushi tare da nufar falon nasu, tana fitowa yana shigowa bakin sa dauke da sallama, yana daura ido akan sa yai mutuwar tsaye, a haka Maryam ta karasa inda yake cike da tafiyar ta mai daukar hankali tana karasawa wajen sa ta rumgume shi, shima rumgume ta yayi yana sauke wata irin ajiyar zuciya dan yau kadai da ya yini a wajen aiki ba Maryam yaji wata kewar ta ji yayi kamar ba shi ba,
"I miss you so much My Noor!"
Ya fada yana hade bakin su, ido ta lumshe ya dauke ta ya dire ta akan kujera, a jikin sa ta lafe tace
"Honey yunwa."
"Muje muci abinci."
"A'ah uhm uhmm!"
"To me kike so?"
"Ni Honey nake