Showing 87001 words to 90000 words out of 232912 words
Chapter 30 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
Wani less ta saka blue black ta yafa farin mayafi sannan tai sallah anan kan sallaya. Bayan ta idar tazo ta tashi Maryam da har lokacin zazzabi bai bar jikin ta ba. Ita ta kamata ta kai ta bandaki ta hada mata ruwan tai alwala a zaune tai sallah dan jiri take gani. Tin jiya da dare aka sallame su amman saboda ba wanda yazo daga gida kuma itama tana gama cin abinci bacci ya dauke ta yasa suka kara kwana. Dakin likita taje ta sanar masa patient din nan fa bata da lafiya. Tare suka dawo ya same ta cikin tsananin zazzabi.
Kallon Matar yai yace
"Tasha maganin ta na jiya?"
"Bata sha ba dan abinci ma tana yin one spoon ta amayar shine take ta bacci sai yanzu ta tashi."
"Bari na aiko nurse ta dibi jinin ta naga ko akwai abinda ke damun ta."
"Ok!"
Ya fita bai jima da fita ba nurse ta shigo ta dibi jinin ta sannan ta fita. Tana zaune wayar ta, ta hau kara dauka tayi tare da murmushi tace
"Son ka tashi lafiya?"
Ta can gefen yace
"Alhamdulillah sai dai missing Ummi na zai kashe ni."
"Subhanallah! Am sorry my Son insha Allahu yau zamu karaso. Jiya mun samu dan accident ne!"
Da sauri yace
"Garin yaya shiyasa bana son tafiya mai tsayi a mota ya kuke ba wani problem ko?"
"Haba Son Calm down ba wata matsala wata yarinya ce ta shiga gaban titi bama mu buge ta ba ta suma so shine muka kai ta asibiti yarinyar dai bata da lafiya ne ma tin jiya aka sallame ta amman ba wanda nata yazo shiyasa."
"Ummi to ya take ya jikin nata?"
"Da sauki yanzu za ai mata test duk abinda ake ciki insha Allahu zuwa anjima zamu taho nasan yanzu Abba ma zai karaso."
"Ok Ummi ki kula min da kanki sosai da sosai."
"I will insha Allahu! Ina Yar uwa ta?"
"Tana nan ban fita ba yanzu na tashi da missing Ummi na."
"Ok bari na kira ta mu gaisa. Nima nayi missing naka fa My Son two week din nan kamar two month haka nake jin su."
"Love you Ummi!"
"Love you too My Son bye!"
Ta kashe wayar tana kiran number Yayar tata. Sun gaisa take fada mata matsalar da suka samu.
"Kina da matsala wallahi Aisha ki taho kawai ba dai kin ce ta kira yan uwan ta ba sa zo su cigaba da kulawa da ita ke menene naki na tsayawa kina fama da ita uhmm!"
"Yaya ai taimako ne ni nasan taimakon da zan nema nan gaba."
"Ai kinyi na Allah. Allah kuma ya gani zai baki lada."
"To shikenan sai anjima"
"Aha!"
Sukai sallama. Abba ne ya kira ta akan ya karaso tace ya shigo dakin ya shiga ta gaishe shi ya kalli Maryam dake bacci yace
"Yarinyar nan amman tana wahala da yawa bata da lafiya dai ko?"
"Haka nake tunani shiyasa nasaka Doctor yai mata test a gano me dame ke damun ta."
"Allah bata lafiya."
"Amin!"
Ya kara kallon Maryam yace
"Yan uwan ta basu zo ba."
"Ina tunanin wani abu akan ta, bari dai ta farka muji."
"To!"
Knocking akai suka bada izinin shigowa, daya daga cikin securityn su ne ya shigo ya gaishe da Ummi sannan ya ajiye mata basket din ya shigo dashi. Suna zaune doctor yasa aka zo aka dauki Maryam a wani gado.
*Allah ya jikan musulmai, ya kyautata namu zuwan. Amin*
*Antty*
[11/14, 12:39] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 33
By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
******
Kano
A lokacin da Abbi ya dawo daga masallaci ya shiga bangaren Ammi a dai-dai lokacin Ammi ta farka daga baccin da take tun jiya cikin hanzari Abbi ya karaso yana mata sannu tare da taimaka mata ta zauna, bin dakin Ammi tafarayi da kallo a hankali abunda yafaru yafara dawo mata sabo fil a kwakwalwanta nan take hawaye suka fara zubowa akan kuncinta kallon mijin nata tayi cikin rawar murya tace
"Shin da gaske ne abunda kunnuwana suka jiyemun ko kuma mummunan mafarki nayi..!"
Abbi baice da ita komai ba, dan halin da yake ciki, mahaifin sa Malam ya aiko yaje a yau yau din nan wanda ya tabbata akwai matsala bai sam a yaya Malam zai dauki abun ba. Kallon ta Abbi yayi ya mike ya nufi cikin toilet itako ta bishi da kallo zuciyarta na bugawa saboda tsabar tsoro da fargaba bai dade ba ya fito yace
"Ki tashi ki kimtsa kiyi sallah lokaci na tafiya..!"
A hankali tafara saukowa daga kan gadon ta nufo inda yake ta dafa bayansa cikin sanyin murya tace "Alhaji Ina tambayarka kamun shiru ina Maryam take, da gaske ba a ganta ba?"
Runtse idanu Abbi yayi cikin tsantsar bakin ciki da bacin rai ji yake kaman ya hadiye zuciya ya huta da kyar ya iya saita kansa ya juyo ya kwakulo murmushin dole ya daura akan fuskarsa saboda Dr yace a guji abunda zai bata mata rai ko ya tsorata ta nan kusa, dafata yayi cikin tsigar rarrashi yace
"Kije kiyi sallah lokaci na wucewa zan miki bayanin komai zuwa anjima..!"
Ya karisa yana mai kama hannunta ya nufi bakin toilet da ita, haka ta rika binshi duk da tana cikin fargaba da tsoro amma kuma haka nan taja bakinta tayi shiru tabi umarninsa, yana ganin ta shige ya juya ya fita falo bai jima ba ya koma daki akan sallaya ya tarar da ita tana lazimi don haka sai ya koma sashen sa ya shiga bathroom shima ya watsa ruwa har ya fito ya fara shafa mai bayan ya gama ya kimtsa a cikin fararen kaya a dai-dai lokacin ne ya koma sashen Ammi ya same ta akan sallaya har lokacin tana ganin sa ta mike tana ninke sallaya hade da gaishesa fuskarsa dauke da murmushi ya juyo yana amsawa hade da tambayarta ya karfin jikin nata yanzun tace dashi Alhamdulillah da sauki sosai kafun ya sake cewa wani abu wayanshi dake kan gado tayi ringing.
Sai da gabanshi yafadi ganin numbern dake yawo akan screen na wayar cikin sanyin jiki Abbi ya daga wayar
"Malam yace a yau yake bukatar ganinka.."
Iyakacin abunda aka fada kenan wayar ta yanke wani yawu mai daci ya hadiye, zuciyarsa cike da fargaba da kuma tsoro dakyar ya saita kansa ya kama hanyar fita yana mai cewa
"Idan kin gama shiri ina jiranki a falo kuma kiyi sauri munkusa makara.....!"
Baki a sake ta bishi da kallo kirjinta na cigaba da bugawa tunani take ina Maryam take? Sannan me Abbi yake nufi da kin gaya mata komai? To wai ma ina zasuje can kuma ganin babu inda tunani zai kaita yasa ta bude wardrobe a kasalance ta dauko kayanta ta saka babu wani kwalliya ta dauki mayafinta kawai ta rufa ta fito a falo kuwa ta tarar dashi.
Baice da ita komai ba ya nufi hanyar barin dakin ta bishi a baya suka nufi parking space inda Alkasim da Abdulah suke tsaye suke jiran fitowansu, da daddaya suka rika gaishe ta da tambayar ta ya jiki itama jiki a sanyaye ta rika amsawa tana mai karewa gidan kallo kamar ranar ta fara ganin sa, haka nan suka shiga suka tada motar maigadi na musu Addu'an dawowa lafiya.
Alkasim ne ke Jan motar a yayin da Abdullah ke zaune a gefensa su Abbi kuma suna zaune a baya, duk yadda Ammi taso tambayan Abbi abunda ke faruwa hakan ya faskara saboda bai bata fuskan hakan ba haka suka cigaba da tafiya shiru babu mai magana.
Dan su Yaa Muhammad da su Yaa Ummulkhairi sun rigasu barin garin tin safe saboda Ammi bata tashi ba shiyasa su Alkasim basu tafi ba, duk da Alkasim bai so ya tuka Abbi ba dan ba yadda zai yi amman yana jin ciwon abinda Abbi yayiwa Maryam yanzu ko tana wane hali duk damuwar sa ya take ya jikin ta.
******
ADAMAWA
4:20pm
Tassss.... Kakeji Malam ya dauke Abbi da wani gigitaccen marin da ya tsorata dukkan wadanda ke cikin dakin saboda hakan bai taba faruwa ba a tarihin gidan, Malam mutum ne shi da bai yadda da dukan ya'yansa ba duk wani laifi da zakai masa sai dai ya kiraka yayi maka wa'azi ko matansa ne baya barin su dakar masa ya'ya sai dai idan a bayan idonsa amma sai gashi yau Malam harda mari, cikin tsananin bacin rai Malam yake bin Abbi da kallo idanun nan nasa sunyi jazur kaman garwashin wuta babu wanda bai tsorata da ganin yadda Malam ya koma ba saboda basu taba ganin hakan ba daga gareshi duk tsawon zamansu dashi cikin wani irin yanayi Malam yafara magana
"Hakika Muhammad ban taba tunanin cewa baka da hankali ba sai yau, bantaba tunanin zaka aikata irin wannan danyen hukuncin batare da ka sanar dani ba"
Cikin zubar hawaye Abbi ya kalli mahaifin nasa yana kokarin yin magana amma Malam ya dakatar dashi ta hanyar daga masa hannu, wani yawu mai daci ya hadiya kirjinsa na cigaba da bugawa, Malam maida idanunsa yayi ya kalli Ammi yace
"Sannan ke kuma kika kasa kira ki sanar dani abinda ya faru tinda shi yafi karfin ya fada min ko? ya koreta daga gidan batare da kunyi yunkurin fada min ba ko? To ina zata in ba nan ba?"
"Yace kada tazo wajen iyayen sa da yan uwan sa...."
Wani kallo da ya watsa mata ne yasata hadiye maganartata ba shiri tana mai sauke idanunta kasa saboda bazata iya juran ganin nasa idanun ba, safa da marwa Malam yake yi a tsakiyan falon tsit kakeji kaman babu wata halitta dake motsi a cikin perlourn duk da cewa a cike yake saboda family house ne Abbi ne da Yayan sa Usman kadai suka bar garin da gidan, gaba dayansu a tsorace suke da yanayin mahaifin nasu don basu taba ganin bacin ransa haka ba juyowa yayi ya kara maida idanunsa kan Abbi sannan cikin kunan rai ya cigaba da cewa,
"Dan kai ka hada mu da ita shine kake so ka nuna iko akan ta kace kar tazo wajen yan uwan ka, to ka sani zan iya rabuwa da kai amman ban rabu da ita ba, akwai wata karin hausa da aka ce abin kwan yafi kwan dadi...."
Ya dago ya kara kallon Abbi yace
"Hakika yau ina cikin wani irin bakin ciki da bacin rai wanda bantaba tsintar kaina a cikinsa ba tunda nazo duniya, wai shin anya ma kanada tunani kuwa, kana tunanin wannan hukuncin daka dauka akan Maryam kayi daidai kenan? Daka koreta gidan ubanwa kake so taje? Shin kayi tunanin hannun wa zata fada? Kayi tunanin wani irin hali zata shiga? Kana tunanin Maryam zata aikata wannan gagarumin laifin? Kafun ka tuhumeta yanada kyau kai kafara tuhumar kanka saboda Allah subhanahu wata'ala yace " idan kabi Matar wani kaima za'abi naka, idan kabi kanwar wani kaima za'abi naka, haka nan idan kabi yar' wani kaima za'abi naka" shin kayi tunanin hakan kafin ka koreta daga gidan ka..?"
Malam ya karasa maganan yana mai bin dukkan mutanen dake falon da kallo zuciyarsa na suya kaman zata ballo kirjinsa ta fito, wuri ya nema ya zauna yana mai sauke ajiyar zuciya ya dauki tsawon lokaci kansa a kasa baice komai ba, a cikinsu babu wanda yayi koda tari ne saboda a tsorace suke, Abbi ne cikin sanyin murya ya fara magana
"Ya Allah kaine shaida akan komai tunda nake a rayuwata ban taba aikata zina ba."
"Shiyasa nake tabbacin cewa Maryam bazata taba aikata abun ashsha ba na tabbata kaddarace kawai ta fado mata saboda ban gina zuri'ata da gurbataccen jini ba kaman yadda nima nawa mahaifin bai ginani akan hakan ba, Allah ka wadatani da arziki dai-dai gwargwado ka kuma wadatani da ya'ya' ka horemun ilimin addini ka darajani a idon duniya tun ina matashina, a cikin ya'yana babu wanda ya taba dauko wata hanya da ta kwaucewa fadin ka ya Allah, tunda nake a rayuwata baka taba kaddaramun wani abu na batanci ba a cikin zuri'ata sai wannan abu da yafaru yanzun wanda ni inada tabbacin cewa wannan wata kaddarace wanda ka saukar mana a cikin zuri'armu baki daya amma maimakon mu rungumi wannan kaddara hannu bibbiyu mu kuma yi kokarin cinye wannan jarabawa daka daura mana sai gashi muna kokarin butulce maka muna kokarin mantawa da irin ni'imar da muke ciki na tsawon shekaru muka...........!"
Malam kasa karasawa yayi saboda muryarsa da yafara sarkewa da alama kuka ne yake son kubce masa don haka sai yayi shiru kawai yana maida kansa kasa idanunsa kuma suna fidda ruwa, dukkansu kura masa idanu sukayi kowa jikinsa yayi sanyi jin furucin Malam hakika maganganun sa ya shige su sosai sai a yanzun ya tabbatar da ganganci da kuma kuskuren da ya tabka a rayuwarshi wani hawaye mai dumi ne ya zubo masa akan kuncinsa a hankali ya rarrafa ya nufi inda mahaifin nasa yake ya kamo kafarsa cikin muryan kuka yace
"Dan Allah Malam kayi hakuri hakika ni Muhammad na zama mai butulci ga ubangijina bacin rai ne ya kaini ga aikata hakan amma dan Allah kayi hakuri karkayi fushi dani...!"
Sai da ya dauki tsawon lokaci batare da yace komai ba kafun daga bisani ya mike ya basu baya cikin kakkausar murya yace
"Na baku kwana biyu rak daga kai har yan'uwan naka kuje ku nemo inda Maryam take ku dawo da ita cikin gidan nan...!"
Yana kaiwa nan ya fice daga falon ya nufi waje, suma da daddaya suka rika barin perlourn har suka watse ya rage daga Abbi sai su Yaa Muhammad da su Inna, a hankali Abbi ya matso kusa da Inna amma kafun yayi yunkurin yin magana ta mike tabar masa perlourn, zuba mata idanu yayi har ta bacewa ganinsa, Hajja ce ta dafa kafadarsa jiki a sanyaye ya juyo yana kallonta, cikin muryan rarrashi tace
"Muhammad ka kwantar da hankalinka insha Allahu za'aga Maryam ka cigaba da yi mata addu'a kai mahaifinta ne fushin ka akanta mummunan hadarine a gare ta don haka addu'a shine maganin komai!"
Kamo hannunta yayi cikin sanyin murya yace
"Haka ne Hajja amma dan Allah ki tayani bawa Malam da Inna hakuri saboda bazan iya jure fushinsu akaina ba..! Maryam kuma na daina fushi da ita Hajja na yafe mata, Allah ya bayyana mana ita."
Shafa kanshi tayi tana Murmushi cikin son kwantar mishi da hankali tace
"Karkadamu insha Allahu zanyi iyakan kokarina akan hakan yanzun dai ka tashi kufara shirin tafiya saboda kufara bada cigiyar ta kasan da karfi karfi akan bugi karfe..!"
Jinjina kai yayi yana mai mikewa a yayin da take mishi Addu'an Allah yabada sa'a, fita yayi ya nufi dakin mahaifiyarsa don bayajin zai iya tafiya batare da neman addu'a ta ba sai dai kuma ya shiga dakin ya kare maganarsa ko uffan batace dashi ba haka ya karashi zamansa ya fito, sai dai kuma wani abun mamaki a lokacin da suka shiryawa tafiya sai suka nemi Ammi suka rasa abun yayi bala'in dagawa kowa hankali cikin rawar jiki Abbi ya kira layin ta amma kuma yaki shiga kowa fa hankalinsa ya fara tashi magana har yakai kunnen Malam dake zaune a masallaci don haka cikin hanzari ya shigo cikin gidan don jin gaskiyar zancen.
Inna ce take sanar sa Malam cewar Ammi da Alkasim sun tagi neman Maryam in sun dace to in basu dace ba tace can wajen Ummun ta zata tafi ba zata iya zama ba tare da tasan a halin da Maryam take ciki ba.
Malam na jin haka ua juya kawai yayi ya wuce batare da yace komai ba, Abbi ji yayi gaba daya duniyar tai masa zafi shin da wanne zaiji da fushin iyayensa akansa ko kuma da rashin matarsa uwar yayansa?
A haka yayiwa yan'uwansa sallama cikin sanyin jiki suka wuce shida su Fadima da Yaa Muhammad. Sai Yayan sa Kawu Usman, Kawu Abubakar, Kawu Aliyu da Kawu Umar saboda su shiga cikin gari su bada cigiyarta a gidajen redio ko Allah zaisa a dace dan Malam gaba daya yake fushi dasu
Su Abbi kuma sunje duk inda ya kamata su samu information akan Maryam amma shiru basu samu ba don haka suka wuce gidan TV da radio da kuma police station suka bada cigiyarta amma kuma duk da haka basu hakura ba sai da suka rika yawo a cikin garin Kano amma ko alamanta basu gani ba har washe gari, sai bayan kwana uku su Kawu Abubakar suka wuce Adamawa a yayinda shi kuma Abbi ya cigaba da aikin neman Maryam yana mai addu'a a cikin zuciyarsa akan Allah yasa a dace ga Ammi da dole sai yaje biko.
Bayan su Kawu Usman sun dawo suka fadawa Malam ba wani abu da aka samu akan Maryam har lokacin, zama yayi a daki yai duba, a halin da yaga Maryam tabbas tana cikin wahala amman kuma yana ganin wani hasken alheri na tunkaro ta wanda yasa ya samu nutsuwa sannan a duban da yayi ya gane har da asiri a barin ta gida wanda ya rasa wanda ya aikata mata wannan abin, yarinya karama a jefa ta duniya, wannan yasa ya kara tashi sosai da addu'a ba gashi ba har ga almajiran sa wanda ake kwana mata sauka da addu'oi.
*Allah ya jikan iyayen, yasa muti kyakyawan karshe. Amin*
*Antty*
[11/14, 12:40] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 34
By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Satin su Yaa Alkasim daya a Kano suna aikin cigiyar Maryam amman ba wani labari, wanda Ammi ta sa ya samar musu visa suka tafi, lokacin da Ammi taje gida yan uwan ta sunyi murna da zuwan ta duk da daga kallo daya suka gane tana cikin damuwa bayan an bata waje tai wanka taci abinci ta shirya ne, da yamma ta nufi dakin Mahaifiyar ta, Ummu na zaune ta shiga Ammi ta zauna, Ummu tace
"Ina Maryama na zata tare zakuzo ai, tinda ba lafiya ce da ita ba."
Damuwar dake kan fuskar Ammi ce ta kara daduwa tace
"Mahaifin ta ya korata duniya Ummu, bamu san inda Maryam ta shiga ba, na taho akan ba zan koma ba har sai ya nemo min diya ta."
"Me yake faruwa ne?"
Zama Ammi ta gyara tace
"Bayan doguwar jinya da Maryam tayi, mun dawo gida jikin yaki dadi gaba daya wannan yasa muka koma asibiti ana zuwa aka gane tana da ciki har na wata uku da kwanaki."
Shiru duk sukai can Ammi ta sauke ajiyar zuciya tace
"Ummu, wai ace Abbi ni yake zargi da daurewa Maryam gindin yin ciki ki fada min tayaya zan bar Maryam ta zubar da mutuncin