Showing 21001 words to 24000 words out of 232912 words
Chapter 8 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
ta rugo a guje tana fadin
"Sister."
Maryam ta dago itama ganin Nawa ta karaso a guje tana jan kafa suka rumgune juna suna dariya mutane da yawa sai da suka tsaya kallon su, Aliyu kuwa tsaki yayi yace
"Ji yadda kuka tarawa nutane jama'a."
Su basu sani ba sai sakin juna da sukai suna murnushi sai suka kara rumgune juna Sitti kuwa ba abinda take sai murmushi jakar Najwa ta dauka ta karasa wajen su tace
"Ni bakya murnar ganina ko Maryam."
Sakin Najwa, Maryam tayi ta rumgume Sitti tace
"Sannu da zuwa Sitti."
"Na sameku lafiya."
"Alhamdulillah."
"To mu karasa mota." Najwa ta kama hannun Maryam sukai gaba, suna tafe maryam na jan kafa Najwa tace
"Ciwo kika ji sis?"
Labari Maryam ta bata tace
"Yaya yana nan da halin sa kenan."
Baki Maryam ta tabe suka karasa jikin mota su Yaa Aliyu suka karaso ya bude musu mota, duk suka shige baya ya dago yana kallon su yace
"Ni drivern ku ne?"
Maryam ta shige jikin Sitti, tace
"Sis ki koma gaba."
"Ni a kusa dake zan zauna."
"To mushiga tare."
Wani kallo ya galla musu yace
"Motar haya ce da zaku shiga ku biyu gaba, dallah sauko ki shiga."
Najwa ta sauko jiki na rawa ta bude front seat ta shiga Maryam ta kara shigewa jikin Sitti tana mamakin fadan Aliyu duk da tasan bai da fuska amman bai yin fada, dagowa tai ta kalli Sitti tace
"Sitti ki bashi hakuri."
"Ni nayi laifin ku da kukai laifin sai ku bashi hakuri."
Shiru Maryam tayi a haka suka karasa gidan sitti wanda aka gyara dan sabon fenti ma akayi masa saboda dawowar ta aka canja furnitures, suna shiga Ummi da Mami na compound wajen motar sukayo suka bude sashen da Sitti take Ummi ta kamo hannun ta, Mami ta amshi handbag din ta suka farai mata sannu da zuwa.
Yaya Asiya, Yaya Hannah da ya'yan su ne suka fito duk suka rufe Sitti suna mata sannu da zuwa. Cikin katon falon ta aka shiga Sitti ta zauna akan kujera aka fara gaishe ta da mata ya hanya. Maryam da Najwa kuwa suna dakin Sitti sai hira suke cike da farin ciki ganin juna.
A falo kuwa an cika Sitti da kayan abinci kala kala dan kowa sai da yayi mata girki na gani na fada, Sitti ta kasance cikin farin ciki ganin yadda suma suke farin cikin ganin ta da son faranta mata shekarar ta kusan hudu bata kasar in sun hadu dasu Mami sai dai ko a saudiya dan haka murnar da ya'ya da jikokin suke ciki ba a fada kowa kulawa yake bata da nuna kulawar sa a gareta, da kyar suka barta ta shiga dan ta watsa ruwa tai sallah la'asar, a daki tasamu su Maryam dan su ko abincin ma ba suci ba.
Sitti tace
"To anyi sallah dai."
Suka mike sukai alwala sitti ta shiga tai wanka ta fita ta saka kaya tai sallah sannan duk suka fita, Maryam da Najwa dining sukaje sai da suka zabi abinda zasuci sannan suka zuba a plate suka fara ci. Aliyu ne ya shigo Sitti ta kalle shi tace
"Habiby bakaci abinci bafa."
Dining ya kalla yace
"Eh yanzu zanci."
"Ya kamata dai."
Ya nufi dining ya zauna, Maryam ta kalle shi tace
"Me zan zuba maka Yaya?"
Abinci su ya kalla ya nuna mata kular Ummi dan yasan Ummi ce tayi, zuba masa tayi ta ajiye masa ruwa da lemo suna cin suna hira, dagowa yai ya wulla musu wani kallo shiru sukai suka karasa sukai daki.
Kan gado suka kwanta Maryam tace
"Bari na kira Jawahir."
Nan ta kira ta saka musu a speaker sai hira suke dan tin ba yau ba Maryam ta hada Najwa da Jawahir suna chat sosai.
Sai after isha'i mazajen su Yaya Hannah da Asiya suka zo gaishe da Sitti kowa da kayan dadi a hannu ya ajiye mata
Sannan sukai sallama suka dauki matan su, basu jima da tafiya ba Abbi ya shigo a kasa ya zauna ya gaishe da Sitti yai mata ya hanya yar hira suka taba sannan Najwa ta fito ta gaishe shi yai mata murnar kamalla karatun ta, yai mata sallama shi ya dauki Mami suka tafi.
Aka bar Ummi da Haidar dan Aliyu bai dawo daga masallaci ba, sai wajen tara ya shigo yace
"Ummi mu tafi ko?"
Sitti tace
"Bazaka ka zauna mu kwana hira ba."
Yai dariyar da bai fiya yin ta ba, wacce ta kara fito da ainahin kyan sa, ya shafa sumar kansa yace
"Yau ki huta zan zo mu sha hira kan na tafi."
"To shikenan."
Ya kalli Ummi ganin ta dauki Haidar yace
"Maryam fa?"
"Ai tace anan zata kwana."
"Ummi Amma...."
"Au a wajen nawa ma ba zata kwana ba."
Sitti ta fada kai ya shafa yace
"Sitti to ki kula da ita."
Tai murmushi tace
"Da Ina cewa zan dauke ta, ta dawo wajena ita da Najwa duk da Najwa ta kusa ta tafi kaga ita ai sai mu karasa."
"Tab Sitti sangartata ai zakiyi gwara tana gida Ummi na sa mata ido."
"Kai sangarta ka nayi."
"Allah Sitti ai na sani."
Ummi tai waje yace
"Sitti gobe zan zo na dauke ta.
"Ba zaka barta tai ko sati ba."
"Itama ba zama zatai ba Zaki gani."
Ya karasa ya rumgume ta yace
"Sai da safe."
Ta mike ta rakasu har mota sannan ta koma ta rufe kofar Baban falo tayi cikin dakin da su Najwa suke, dariyar su ta fara jiyowa ta karasa tace
"Oh ku bakwa jin bacci ko?"
"Bacci tin yanzu Sitti kije ki kwanta ki huta sai da safe."
"Shikenan ga wacan gashin naman kuje kuci kusa dayan a firij."
"To Sitti Ina su Ummi?"
"Sun tafi."
Ido ta zaro tace
"Anan zan kwana?"
"Menene da nan din?"
"Ni gida zan tafi."
"To sun tafi sai ki bari gobe Kya tafi."
Najwa tace
"Kai Sis ni na zata zan samu 'yar uwa anan."
Kafada ta make tace
"Na bar Ummi ita kadai."
Sitti ta juya tace
"Uhmm ni sai da safe."
Najwa tace
"Bari na dauko mana Nlnaman."
Wayar ta, Maryam ta dauka ta fara kiran Ummi, suna hanya Ummi taga kiran ta dauka tace
"Daughter lafiya?"
"Ummi shine kuka tafi?"
"Au kin fasa kwanan?"
"Ummi ni ba zan iya bacci anan ba."
"Haba Daughter menene da nan din kiyi zaman ki gobe kya dawo kinji?"
Kai ta gyada tace
"Ina Haidar?"
"Gashi yai bacci."
"Yaa Aliyu fa?"
"Gashi yana tuki."
"Oh kuna tare?"
"Eh!"
"Sai da safe."
Ta kashe wayar, Aliyu yace
"Wacece?"
"Kaima ka sani wai ita bata son kwanan kuma."
"Hmmm."
Yai murmushi yai horn a bakin gate din gidan nasu.
Kwana sukai suna hira tsakanin Maryam da Najwa, anan Najwa take fada mata zancen saurayin ta Abdul cewar ya rigata dawowa Kuma yace tana dawowa zai turo ayi maganar auren su, Maryam tai murmushi tace
"Kace nan kusa zamusha biki."
Kai ta gyada tace
"Ki fara shiri."
Sukai dariya, Najwa tace
"Nasan gobe zai zo to ya me zamu tsara masa?"
"Ki bar min komai kawai "
Suka tafa sai wajen uku suka kwanta kuma karfe biyar saura suka mike, sallah sukai sannan suka gyara gidan tsaf suka saka turaruka masu dadin kamshi sannan suka shiga kitchen hada breakfast sai da suka gama, suka shiga wajen Sitti dake zaune akan darduma tana jan carbi, har kasa Maryam ta durkusa ta gaishe ta sitti ta amsa tace
"Ya gidan?"
Murmushi Sitti tayi tace
"Lafiya lou Sitti akwai abinda kike bukata ne?"
"A'ah duk abinda kukai ya isa."
"To bari na hada miki ruwa."
Maryam ta shiga ta hada nata ruwan wanka, Sitti ta shiga tayi wanka ta fito ta shirya tana fitowa falo suka fito suka jere mata kayan abinci Sitti ta kalli Maryam tace
"Sannu Maryam da aiki."
Ta faraci su kuma suka wuce sukai wanka suka shirya sannan suka fito tare suka karya sannan Maryam ta koma kitchen ta cigaba da hada kayan abincin rana da anda za ayiwa Abdul.
Karfe biyu suka gama komai Najwa taje ta kwanta wai bacci za tayi, Sitti da Maryam kuma suna falo suna hira cike da so da shakuwa, jefi jefi makwabta da yan uwa na zuwa yiwa Sitti sannu da zuwa, har akai la'asar Maryam ta shiga ta tashi Najwa sukai sallah sannan ta shiga shiryawa biyar saura yana compound din gidan Najwa da Maryam ne suka fito shigo dashi.
Yana tsaye jikin mota hannun sa daya cikin aljihun rigar sa dayan kuma yana danna waya yaci shadda har da hula idon sa sanye da glass yai kyau sai tashin kamshi yake, tinda ya hango su ya zubawa Najwa ido har suka karaso Maryam tace
"Haba ai ko dan ni ka kauda ido."
Nuna ta yai da wayar hannun sa yace
"Maryam ko?"
Kai Najwa ta gyada tana murmushi yace
"Na sani ita zatai min haka."
"To ai kai naga gaba daya baka da alkunya da ka bari in na bar wajen sai kai ta kallon ta."
"A matsayin ki name?"
"Sirikar ka mana."
"Yess u re my in-law but sis Inlaw kuma karama ma ko?"
Najwa ta kalla tace
"Ban girme ki ba?"
Dariya tayi tace
"Hhhh lallai 'yar nan ni din."
"Kai nice 'yar ki?"
Sukai murmushi tace
"Month daya muke fa."
"Ah haba?"
Abdul ya fada yana kallon su, Maryam tace
"Kuma nice babba fa ni 1 ita 15."
"Yes kece Babba amman ke ba yaya ta bace? Kin gane saboda nima jikan Sitti ne dan haka ni yayan ki ne ke kuma yayar Najwa yayi?"
Najwa ta kalla tai wa gwalo, Najwa ta kalli Abdul tace
"Kai Honey kagani ko tana min gwalo."
"Rabu da ita ai ba zan bata tsaraba."
"Kai a'ah rabamu zatai."
Sukai dariya Maryam tace
"To kazo mu shiga mun barka tsaye ko?"
Suka nufi babban falo inda Sitti ke zaune suka zauna ya gaishe ta yai mata ya hanya suka taba hira sannan suka tafi dakin baki inda aka kai masa hadaddun girkuna da lemuka.
Maryam da Najwa na zaune bayan ya gama cin abinci suna ta hira abinsu, bude gate sukaji Maryam dake kusa da window ta bude labule ido ta zaro ta maida labulen ta ajiye, Najwa tace
"Waye?"
"Yaa Aliyu."
Baki Najwa ta tabe tace
"Sarkin fada."
Ciki ya shiga ya samu Sitti ita kadai rike da Alkur'ani ya shiga ya zauna yana fadin
"Uhmm nagaji."
Ta kalle sa tace
"Ya aikin?"
"Alhamdulillah."
Ta mike ta zubo masa abinci ta ajiye ya amsa yace
"Ya naji gidan shiru ina su Najwan?"
"Abdul ne yazo suna wajen sa."
"Waye Abdul?"
"Wanda yake neman auren ta."
"Kuma shine sukaje da ita Maryam din?"
"To menene dan taje su gaisa yau dai su hadu."
"Uhmmm"
Ya dauki spoon din abinci ya kai baki taunawa yai ya hadiye ya dago ya kalli Sitti yace
"Ummi ce ta kawo miki abinci?"
"Me kaji?"
"Dandanon girkin Ummi."
Murnushi Sitti tayi tace
"Maryam ce tayi."
"Maryam ita tai girkin?"
"Eh bata muku girkin ne?"
"No Sitti kamar na Ummi fa."
"To ita da Maman ta dan ta iya girki irin nata shine wani abu, yarinyar nan tana da tsafta da safe kan kace me ta gyara gidan nan ta saka masa kamshi ga breakfast lallai na yadda rainon Aisha ce dan Aisha ma akwai tsafta bata son kazanta sam ga iya girki to kaga itama kamar Aisha take."
Abincin sa ya cigaba da ci yana gyada kai dan yai masa dadi gaskiya sosai, dan haka ya cinye tas sannan yasha ruwa ya jingina da kujera yace
"Gida nake so na tafi na gano Haidar tin safe rabo na dashi."
"To ka tafi mana."
"Maryam nazo dauka."
"Cewa tai zata tafi yau."
"Gobe zata makaranta Sitti."
"Kai da Aisha nasan ba zaku bar min Maryam ba, Hauwa kuwa haka ta bar min Najwa gashi yanzu ma muna tare kila aure ne zai rabamu kawai."
"Itama fa ba iya zaman nan din zatai ba."
Kiran sallah akai ya mike yace
"Sitti bari naje nai sallah ki fada mata ina idarwa zan zo mu tafi."
Ya fita yai alwala ya tafi masallaci. Abdul ma sallama yaiwa sitti ya tafi gaba daya.
Sallah sukai suna falo suna hira Sifti tace
"Yayan ki yazo wai zaku tafi."
"Yauwah."
"Au so kike ki tafi?"
Najwa ta fada, murmushi Maryam tayi tace
"A'ah gobe da makaranta fa."
"Ba sai a kawo miki kayanki ba."
"A'ah nayi missing Ummi na."
"Kwana dayan."
"To ina na taba zuwa na bar Ummi a cikin shekarun nan uku zuwa hudu."
Sai bayan sallah isha'i ya shigo ya zauna Sitti ta shafa addu'a tace
"Ka dawo?"
"Eh tana ina ta fito mu tafi."
"Tana ciki."
Ya mike ya nufi corridor dakin ya kwalla mata kira da sauri ta mike tana amsawa ta fito tace
"Gani Yaya."
"Kizo mu tafi."
"Toh."
Ta koma tacewa Najwa dake waya
"Sai gobe."
Ta fice a dakin Najwa ta biyo ta, taiwa Sitti sallama Sitti tace
"To sai yaushe?"
"Zanzo da weekend."
"To Allah kaimu sai da safe."
Har bakin mota Najwa ta rakata suka tafi suna dagawa juna hannu.
Tin da ta koma gida kuma sai ta mai da hankalin ta akan karatu suna waya da Najwa dan Najwa ma taje gidan ta gaida su Inna sannan ta koma wajen Sitti.
A dawowar su Inna har an saka auren Najwa da Abdul wata bakwai, aka tsayar dan haka dagin har sun fara shirye satin su uku da dawowa tinda Yaa Aliyu ya dauko ta bata koma ba, shiyasa tin jiya Friday ta fadawa Ummi zataje.
Saukowa tayi daga bene sanye da maroon kalar doguwar riga, sai brown kalar mayafi da ta yafa sai kamshi turare take wajen Ummi takarasa tace
"Ummi na sauko."
Dagowa Ummi tayi tace
"Ah har kin shirya?"
Zama tayi a gefen kujera tace
"Eh Ummi."
*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*
*Antty*
[10/23, 14:11] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 7
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Dis page is for you Sis *AISHA BASHIR* thanks for ur support i reallu do appreciate 😘😘😘
Mikewa Ummi tayi ta shiga kitchen ta dauko wata babbar leda ta mi'ka mata ledar tace
"Ki kai wa Sitti."
Ta amsa sukai sallama ta fita ta shiga mota Baba Anas ya tada motar suka tafi, suna zuwa Sitti ta amshe ta da murnar dan tana son Maryam sosai Maryam ta rumgume Sitti cike da jin dadin ganinta ita ma, Maryam tace
"Nayi kewar ki Sitti."
"Ba wani nan, amman kika guje ni."
"Kai Sittj nasan Najwa ce zata hada mu, Sitti makaranta shiyasa."
"To anan hanaki zuwa za ayi?"
"A'ah Amman na bar Ummi ita kadai."
"Uhmm ke da Aliyu ban San wa yafi son Ummin nan ba."
Murmushi Maryam kawai tai
Sitti tace
"Yasu Aisha da Hauwan da Barira?"
"Duk suna lafiya."
"Ina Innan taku?"
"Tana lafiya lou sunce a gaishe shi."
Mikewa tayi tai hanyar dakin Najwa tace
"Tana Ina ne?"
Ta shiga dakin kwance ta ganta akan gado tana waya juyowa tayi tana ganin Maryam ta kashe wayar ta rumgume ta, sai kuma ta sake ta, tace
"Bama ruwa na dake."
"To ba gashi na zo ba."
"Sai yanzu wajen uku saura har na kira Abdul nace yazo fa."
"Ah shikenan nayi hira ta da Stti na"
Hararar ta tayi tace
"Bari na kira nace ya fasa zuwa kawai."
"Ah ah bari kawai."
Ta dauki waya ta fara kiran layin Abdul bai dauka ba har ta kira sau biyu, Maryam ta mike tana ajiye mayafi tace
"Me zan samu a gidan ne?"
Ta fita tace
"Sitti wane kayan dadin zan samu."
Ta fito ta zauna a gefen Sitti, tare da dauka kan ta a kafadar Sitti. Sitti tace
"Ina Haidar?"
"Yana tahfiz."
Ta fada ta mike ta Shiga kitchen bata Jima ba ta fito da bowl a hannun ta da lemo ta zauna a kusa da Sitti ta Fara ci, tana cikin ci sukaji sallama daga bakin kofa. Amsawa sukai Abdul ya shigo tare da abokinsa, Sitti tace
"Sannun ku da zuwa, ashe mai gidanane."
Murmushi Abdul yayi yana kallon Maryam da ta ki kallonsa Sitti tace
"Bismillah ku zauna."
Zama sukai Maryam ta dago tana ganin Abdul ta zaro Ido tace
"Ashe ango ne."
Yai murmushi ya durkusa yace
"Ina yini Sitti?"
Suka gaisa, Sitti ta kalli wanda suke tare tace
"Muhammad ko? Kwana biyu tinda ka baro can ban kara ganin ka ba."
Yai murmushi yana kallon inda Maryam take ita kuwa duk da tana jin Ido akan ta bata dago ba, murmushi yayi yace
"Wallahi Sitti na dawo naji dadin gida Nigeria shiyasa nai zamana."
Da sauri Maryam ta dago kai jin muryar kamar ta san me ita tana ganin sa ta sauke Ido duk ta kasa sakewa, Sitti tace
"Ai yafi wallahi ya gidan da iyayen naka? Ya aiki? Ko kayi aure ne?"
"Alhamdulillah suna lafiya A'ah Sitti tukkuna dai."
"To Allah ya kawo mace ta gari mai sonka."
"Amin Sitti nagode."
Abdul yace
"Maryama ya gida da school? Ai na miki magana a online shekaran jiya naga baki ban amsa ba."
"Uhmm ni wayar fa wani lokacin mantawa nake da ita."
"To saurayin ki fa?"
Ido ta zaro tace
"Saurayi kuma a'ah tukkuna dai."
Yai murmushi yace
"A'ah nifa ban yadda ba da kike cewa baki dashi."
"Aliyu ne zai barta kula wani namiji."
Sitti ta fada, tace
"Kana ganin Najwa ma yaushe ta fara soyayyar ai sai da ta bar gida in dan ta shine ba zata fara ba cewa yake ma wai tai kankanta da aure."
Dariya dukka sukai, Muhammad kuwa kallon Maryam kawai yake wanda idon sa da take ji akan ta ya hanata sakewa Sitti tace
"Maryam kawo musu ruwa mana."
Da sauri ta mike ta shiga kitchen jingina tayi da bango tana mai da numfashi kamar wacce tai gudu, Ido ta lumshe tace
"Meyasa nake haduwa dashi ne?"
Ta jima kan ta fito dauko tray mai dauke da lemo da ruwa da cups ta ajiye ta koma kusa da Sitti ta zauna kamar zata shige jikin ta, Abdul yace
"Ya naga yau baki sakewa ne ko bakya jin dadi ne?"
Kai ta girgiza sai kuma ta mike da sauri tace
"Bari na kira Najwa."
Tayi dakin da Najwa take, rike ta ganta da waya ta zauna tace
"Me kike ne?"
"Sai neman number Abdul nake taki shiga."
Murmushi tayi tace
"Wanne Abdul dake falo wajen Sitti."
"Ah haba dai tin dazu fa nake kiran sa amman bai dauka ba."
"To yanzu dai ki tashi kije."
Najwa ta mike taje gaban mudubin ta shafa hoda da dan man lebe ta shafa turare mai kamshi ta dauki mayafi tace
"Yaya?"
"Kinyi kyau Amarya."
"Tin yanzu da saura."
"Kamar yau ne."
"To Allah nuna mana."
"Amin."
Ta kamo hannun ta tace
"Tashi muje."
"No kije."
Kallon ta ta tsaya tace
"Kamar ya?"
Ta bata fuska mikewa tayi tace
"Muje."
Suka fita sai hira suke da Abdul da Sitti, Muhammad dai sai murmushi yake yana danna wayarsa, su Maryam suka zauna suka gaisa da Najwa da Abdul da Muhammad nan aka cigaba da hira gaba daya a parlon Maryam dai na jikin Sitti a kai a kai Muhammad ke kallon ta, har kusan Asr, sannan suka fita sukai sallah da suka dawo a falon ba'ki suka zauna Najwa tayi tayi da Maryam suje amman taki zuwa dole ta tafi ita kadai.
Har magariba sai da suka dawo daga sallah Muhammad yace
"Wacece yarinyar nan Abdul?"
Abdul yai murmushi yace
"Ko dai kana ciki ne Muhammad?"
Shafa kansa Muhammad yayi, tare da murmushi Abdul yace
"Haka ne?"
Murmushi Muhammad ya sake sannan yace
"Na santa ne shi sa nake tambayarka"
Da mamaki Abdul yace
"Haba, amma ban ga ta nuna alamar ta san ka ba"
Murmushi Muhammad yayi yana shafa sajensa yace
"Ni na nuna alamar na santa