Showing 99001 words to 102000 words out of 232912 words
Chapter 34 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
three sitter dake gefe ta kwantar da ita Abba kuwa har yayi kan stair.
Ummi tabi bayan sa daki ta same shi har ya shiga bandaki babbar rigar da ya cire ta ninke sannan ta wuce dakin ta. Alwala tayi ta fito ta tada sallah. Tana idarwa ta mike ta fita. Abba ta sama zaune akan sallaya. Bandaki ta shiga ta hada masa ruwan wanka sannan ta fito tace
"Yallabai na hada maka ruwan wanka fa."
"Nagode Allah yayi albarka!"
"Amin!"
Ta juya ta fita. Kasa ta sauka ta karasa kusa da Maryam da har bacci ya dauke ta. Dafata tayi ta bude idon ta a hankali.
Hannun ta ta kama tace
"Taso muje kiyi wanka kiyi alwala ki sallah sai ki kwanta ko?"
Mikewa tayi jiki a sanyaye tabi Ummi sama. Dakin dake kusa da nata ta kai ta ta shiga ta hada mata ruwan wankan. Wardrobe ta bude ta dauko mata sabon pant da doguwar riga. Ajiye mata tayi akan gado da hijab. Maryam na fitowa ta zura kayan ta hau kan sallaya ta tada sallah. Tana idarwa tai addu'a tare da azkar kwanciyya take son yi amman kuma bata son in ta kwanta tayi bacci dan yamma tayi sosai.
Kai ta jingina a jikin gado tana jan carbin da ta gani a gefen gado. Ummi ce tai sallama itama tayi wanka ta saka doguwar riga marar nauyi an mata dinkin bubu ta daura dankwalin kayan sai kamshi take yi. Hannun ta rike da juice da cup ta shigo. Ajiye wa tayi tace
"Sannu ya jikin!"
Murmushi Maryam tayi tai mata magana da hannu alamar Alhamdulillah.
"Allah kara sauki!"
Kai ta gyada. Ummi ta bude juice din ta tsiyaya mata a cup amsa tayi ta shanye shi tas sannan ta rike cup din ta fara kokarin kwanciyya a kasa.
Ummi tai saurin kamata tana fadin
"Ki daina kwanciyya a kasa tashi ki hau gado amman kada ki bacci kinga yamma tayi ko?"
Kai ta gyada ta koma kan gadon ta kwanta kawai.
Ummi tace
"Zan fita me kike son na dafa miki?"
Kai ta jujjuya alamar ba komai. Ummi ta shafa kan ta tace
"Sannu!"
Ido ta lumshe mata ta juya ta fita.
Tare suka sauka ita da Abba. Bangaren dake gefen ta wanda bai kai nasu ba flat ne shi bai da bene nan suka nufa.
Tin daga compund din da zai dauki akala mota sama da uku wanda yake dauke da shuke shuke yake a share tas. Har kofar falon suka karasa sukayi sallama. Inna dake goge goge ta dago tana amsa sallamar tasu. Shiga sukai suka zauna akan kujera, ta karaso ta zauna hannun ta rike da handkerchief da take goge goge wanda na rasa me take gogewa domin komai na dakin yana nan tsaf sai daukar ido yake.
Daki ne mai kyau falo madaidaici an zuba masa kujeru masu kyau da tsada milk colour an saka milk kalar labule wanda kasan dakin ma duk milk tile ne sai kyalli yake da sheki kamar ba a rayuwa a dakin kuma kamar ba dakin tsohuwa ba. Dakin sai kamshi turaren wuta yake da sanyin AC da ta kunna.
"Ina yini Inna?"
Suka hada baki wajen gaishe ta, baki ta tabe ta ce
"Lafiya lou ashe kun ga dama kun dawo mutanen da suka ce kwana goma sha hudu zasuyi yau kwanan ku nawa?"
Ta fada tana tsare su da ido. Ummi tai kasa da kai Abba yace
"Inna matsala aka samu, kuma kinsan halin tafiya ita ke da kai ba kai kake da ita ba."
Baki ta tabe Ummi tace
"Kiyi hakuri Inna mun sameku lafiya ya gidan?"
"Gida yana nan kalou sai dai fa tin da kuka tafi waccen ta daina kawon abincin ta sam ke dai yayar kice nasan ba yadda zaki ba. Daman ganin ido ne yasa take kawon dan taga kina kawon ita kar ace bata kawon ko? Ita kuwa dayar yo ko ta kawon ai baci zan ba girkin ta sam ba dadi, ke ni wallahi kyamkyamin ta ma nake."
Ummi tai murmushi tace
"To Inna ai na dawo sai na cigaba da kawo miki."
"To ai shikenan a haka kuma wancan gantalallen yaron nata yake zuwa min nan kwadayi da gayya nake abu mai dadi na cinye ko sammasa bana yi."
"Waye a ciki Aliyu ko Umar?"
Abba ya tambaya yana murmushi.
"Waye banda Aliyu uban yan kwadayi!"
"Inna amman shima ai yana kawo miki kayan kwadayin!"
"A shekara sau dayan. Kasan Allah Shehu a shekara sau daya yake kawon!"
"To ai muna kawo miki ba shikenan ba."
"Amman dai Shehu yadda nake dawainiyya da yaran nan tin haihuwa ya dace ace haka suka dauken kamata yayi komai suka samo su kawon ko dan Allah."
"Haka ne Inna!"
"Uhmm to kana ji sai mu shekara biyu kwandala bata hadamu ba kayan ci kuwa bai fi a shekara sau daya ba fa!"
"To Inna sai hakuri yaran zamanin haka suke ai!"
Ummi ta fada.
"Daman ku kuke kara daure musu gindi, Allah yaso na haifi Shehu da Suleiman da Nusaiba ga kuma Abubakar shi ya dauken uwa duk da bani ce uwar sa ba to me abun Aliyu da Umaru zai karen a duniya bayan yara nab basu dauken komai ba."
"Ayi hakuri Inna."
"In ban hakura ba ya kike so nayi Aisha?"
Abba yai gyaran murya yace
"Inna bakiji dalilin dadewar mu ba fa!"
"Zai wuce ka ce min aikin ka ne baka gama ba Shehu!"
"Ba haka bane Inna mun gama aiki a iya ranar da na dauka sai dai mun taho shine muka samu dan hatsari a hanya."
"Na shiga aljanna ban fito ba ni Hauwa'u ina fatan dai ba abinda ya same ka ko?"
"Babu Inna wata yarinya muka so mu buge amman Allah ya takaita wahalar wanda tsoratar da tayi yasa ta suma!"
"Kaji raguwa daga an kusa a bege ka sai suma amman wannan kwai raguwa da zan ganta da na ga mai mata kuwa."
Murmushi Ummi da Abba sukai sannan Abba yace
"Shine muka kai ta asibiti to kinga mune silar sumar bai kamata mu tafi mu barta ba, dan haka muka zauna har wajen awa takwas bata farfado ba."
"Kai duniya abun mamaki baya karewa yanzu daga an kusa bige ka sai suma har kayi awa takwas sai kace ba mutum ba anya mutum ce kuwa Shehu. Aisha dan Allah mutun ace ba a bige ka ba ka hau suma haka ake yi?"
"Wallahi Inna muma mun tsorata sai da likitoci suka kwantar mana da hankali shiyasa muka dada kwana dan sai dare ta tashi wanda muka so mu dankata a hannun iyayen ta sai kuma yarinyar ashe bata da lafiya."
"Ahaf kaji zance ai daman da walakin ace daga an kusa bige ka sai suma."
"Wallahi Inna yarinyar dai ashe bata ma magana daga cin abinci sai amai baki ganta ba yarinya karama duk ta rame ta dashe haka muka kwana zazzabi mai zafi a jikin ta wanda washe gari Aisha ta sanar dani nace ayi wa likitoci magana shine sukai bincike sosai akan ta."
"Inna in kinga yarinyar abin tausayi wai ashe tayi rashin lafiya shine ta rasa maganar ta, sai jini ta da yai mugun hawa."
Ido Inna ta zaro tace
"Duk ita kadai yarinya karama."
"Inna ba ma wannan ba ciwon zuciya ya kamata ga karamin ciki dake wahalar da ita."
Tagumi Inna ta zuba tace
"Duk ina iyayen ta?"
*Allah ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe Amin.*
*Antty*
[11/17, 14:03] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 39
By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Abuja
Kallon Abba Ummi tayi sannan ta sauke ajiyar zuciya tace
'Inna ina zaton yarinyar tayi losing memory dan bata iya tuna komai na rayuwar ta sai mutum biyu Ammin ta da Yaa Haidar da ta fada min. Wanda Yaa Haidar din shine mijin ta!"
"Allahu Akbar. Allah yasa ba irin halin Aliyu nan gidan ne dashi ba. Yanzu ya jikin yarinyar?"
"Inna likitoci sunyi mana bayani yarinyar tana bukatar kulawa sosai. Dan tana cikin hatsari wannan abun shi yafi damu na, na rasa ya zanyi ya zan ajiye ta. Dan garari kawai take a cikin garin Bauchi bata san garin da kowa dake cikin garin ba bata tina kowa da komai a rayuwar ta ta baya."
"Ikon Allah wannan wacce irin jarabawa ce ace ka rasa komai naka da mijin ka ga ciki ga bakasan inda kake ba."
Abba yace
"Shine Aisha ta nemi alfarma akan tana son ta karasa kula da yarinyar har lokacin da Allah zai sa ta tuno yan uwan ta."
"Hakan yana da kyau!"
"To shine yau Aliyu yayi mana booking flight muka taso har yarinyar."
Ido Inna ta zaro tace
"Kuka taho da ita ina?"
Kallon kallo akai da Abba da Ummi. Abba yace
"Nan gidan!"
"Yanzu Shehu baka ganin ba matsala ka dauko yarinyar da baka sani ba ka kawo cikin iyalin ka. Haka fa kukayi mana shekarun baya. Shin kuka sani ko aljanna ce ma. Ni da farko na ji tausayin ta kuma na yadda da labarin amman kuna cewa kun kawo ta kuma sai naji tsoro nake ganin anya da gaske ne kada fa ta cutar da mu."
"Inna ta kenan da mukai haka a shekarun baya yanzu wa yafi ki jin dadin sa. Naga ya dauke ki kamar yadda kike a wajen mu. Kuma Inna ina ce ke kan ki baki taba kawo laifin sa ba tinda muke sai a yanzu kuma haba Inna. Nasan Inna ta ba abunda take tsoro a duniyar nan daga mutun har aljanna. Allah kadai take tsoro. Kuma nasan Inna ta akwai tausayi imani da taimako nasan zata taimakawa ko wanene dan Allah shi zai biya ta in ma ya cutar da ita dan kansa. Nasan Inna zata taya mu rikon yarinyar nan tsakani da Allah ko Inna ta?"
Abba ya karasa yana lankwasar da kan sa da neman taimakon Inna.
"Daman ai ni bana tsoron kowa, kuma ina son taimako yanzu me zance sai dai nace Allah ya bamu ikon rike ta da amana, Allah yasa ta tina da gida ya sauke ta lafiya."
Baki Abba da Ummi suka hada suna murmushi suka ce
"Amin Inna."
"Ya jikin nata?"
"Da sauki sai dai ba abinda take iya ci."
"Allah sarki haka za ai jinya ba cin abinci bari maza na tashi na samar mata abu da zata dan ji dadin bakin ta."
"To Inna me za a kawo?"
"Ba abunda za a kawo dan jiya Aliyu yayi min cefane kayan da nake bukata."
"To Inna godiya muke."
Ta mike ta nufi kitchen tana fadin
"Bari na shiga kan a kira magariba."
"To Inna muma mun tafi sai anjima!"
Suka mike suka fita. Ummi tace
"Ni nasan daman Inna sai tace wani abu!"
"Amman kuma ai kinsan tana da saurin sauka ko?"
"Haka ne kasan ta ai wata rana ta nuna tana son abu wata ranan akasin kowa mai laifi ne in tai niyya."
"Haka ne amman ku da yaran ku zaku taimaka mana mu rabu lafiya."
"Kai ma kasan muna iya kokarin mu."
"Haka ne."
Abba ya nufi gate din da zai sada shi da masallacin gidan Ummi kuma bangaren dake kusa da nasu iri daya ta shiga. Da sallama ta shiga sashen amman ba a amsa ba ciki kawai ta shiga. Hajiya Barira na zaune tana kallo. Ummi tai murmushi ta kalle ta tace
"Sannu da gida Hajiya!"
"Yauwah!"
Ta amsa ba tare da ta kalli inda take ba. Kai ta dauke tayi sama itama bata bi ta kanta ba. Tana zaune a daki hannun ta rike da waya ta jiyo muryar Ummi na sallama. Da sauri ta dago tana fadin
"Ummin Aliyu ashe yau din dai kuna tafe!"
"Wallahi Yaya, Aliyu ya saka mu a gaba sai fa cewa yayi kawai yai mana booking flight."
"Au da kenan ba yau zaku dawo ba."
"Gaskiya dai da wuya dawowar mu yau din nan, saboda jikin yarinyar amman Aliyu yace mu dawo zai kula da ita komai da komai."
Fuska ta sauya tace
"Har yanzu jikin dai to ina yan uwan ta?"
"Yaya bata san inda suke ba sam bata magana fa ba wanda ta sani nata fa."
"Me kike nufi?" Bayani Ummi tai mata. Tagumi ta saki tace
"Tarihi na son maimaita kan sa dai kenan ko?"
"Wancan da banbanci da wannan, wannan fa har da ciki."
"Hmm duk da haka ke kuma kece uwar yan tsuntuwa ko?"
"Yaya to menene Allah dai ya bayyana alhalin su gaba daya."
"Amin to ya jikin nata?"
"Da sauki!"
"Dan Allah dai ki kula tinda bamu san wacece ba kar muje me cutar wa ce."
Murmushi Ummi tayi tace
"Insha Allahu haka ba zai faru ba Allah zai dubi zuciyoyin mu, yanzu."
Kai ta gyada kawai. Ummi tace
"Yakamata muje kigan ta ko?"
"To muje!"
Suka mike suka fita ba kowa a bangaren nasu dan haka suka fita kawai. Bangaren Ummi suka nufa nan ma ba kowa sama suka nufa suka shiga dakin da Maryam take duk yadda taso kar tai bacci bata san lokacin da baccin ya dauke ta ba.
Kallon ta suka tsaya yi. Ummi tace
"To kingan ta Yaya!"
"Na ganta gaskiya yarinya ce sosai, Allah sarki!"
Ta karasa tana leka fuskar ta sosai. Sannan ta dago tace
"Allah bata lafiya daga gani duk inda ta fito cikin jin dadi ne. Kalli fatar ta smooth duk da bata da lafiya."
"Haka ne!"
Ta mike ta nufi kofa tana fadin
"Bari naje yau Inna tace na mata farfesun tarwada."
"Hajiya Inna kenan!"
Ummi ta fada tana bin bayan ta. Fita sukai tace
"Ai da bakya nan kullum sai tayi fada wai kinje kunki ku dawo in ke ba zaki dawo ba ki bar dan ta ya dawo."
Murmushi Ummi tayi lokacin da suka karaso bakin kofa tace
"Ai nasan za ai haka. Allah dai ya rabamu da Inna lafiya."
"Amin sai anjima!"
Ta fita ita kuma ta shiga kitchen abincin dare ta daura musu wanda bata jima da daurawa ba aka kira sallah sama ta hau ta shiga dakin da Maryam take ta dauro alwala sannan ta fito ta tada Maryam dake bacci. Bandaki ta shiga tai alwala ta fito ta tada sallah anan dakin.
Ummi na idarwa ta koma kitchen ta karasa abincin daren ta. Ana isha'i ta gama ta jere komai a dining sannan ta gyara wajen da ta bata sama ta hau tai wanka ta canja kaya sannan ta fito ta shiga dakin Maryam kwance ta same ta akan sallaya. Karasawa tayi ta leka fuskar ta. Ido ta bude a hankali ta fara kokarin mikewa.
"Yi kwanciyar ki!"
Komawa tayi ta kwanta. Ummi tace
"Me kike so na samar miki kinga ba kyau zama haka da yunwa ba ko?"
Kai ta girgiza. Ajiyar zuciya Ummi ta sauke tace
"Ko dan kisha magani kya samu wani abu ki danci fadamin me kike sha'awa."
Bata fuska tayi kamar zatai kuka ta girgiza kai.
Ummi tace
"To shikenan bari naje naga ko Abbah ya dawo na bashi abinci ko? Ko zaki sauko kasan?"
Kai ta girgiza ta lumshe idon ta kawai dan ita kadai tasan me take ji. Mikewa Ummi tayi ta fita. Abbah ta sama a falo yana kallon TV.
Zama tayi tana fadin
"Ashe ka dawo sannu da zuwa!"
"Yauwah ai nasan kina can wajen 'yar ki!"
"Haka ne. Nagama abinci muje kaci ko?"
Mikewa yayi ya nufi dining Ummi na binsa a baya. Bayan ya zauna ya kalli Ummi da ta fara serving nasa tuwon farar shinkafa da miyar agushi da taji jan nama sai kamshi take.
"Ina Maryam din ita?"
"Kasan ba zata iya ci ba!"
"To me take so?"
"Tace bata son komai tin dazu nake tambaya in akwai abinda take so nai mata amman tace babu!"
"To amman haka zamu zauna ba ci ba sha?"
"Nima dai abin dake damuna kenan amman bari Aliyu ya dawo naji ya za'a ko?"
"Allah kawo shi lafiya."
Ya fara cin abincin ya kalli Ummi dake zaune yace
"Ke bazaki ci ba?"
"Sai anjima!"
"Alright!"
Ya gama ta kwashe wanda yaci ta kai kitchen ta wanke sannan ta fito.
Tana fitowa Inna na shigowa bakin ta dauke da sallama. Amsawa Ummi tayi ta amshi basket din hannun ta tana fadin
"Sannu Inna!"
"Yauwah ina mai jikin?"
"Tana sama!"
Suka karasa falon. Abbah ya mike yana fadin
"Sannu da zuwa Inna!"
"Yauwah Shehu tin dazu da kuka fita ina kitchen sallah kadai ke fito dani sai yanzu na gama na tsaftace wajen na taho kawo mata Allah yasa dai bata ci wani abun ba."
"Sannu Inna ba abinda taci tana kwance!"
Ya kalli Ummi yace
"Aisha kira ta!"
Ummi tai sama Inna tace
"Barta bari nazo da kai na."
Tabi bayan Ummi Abbah shima ya mara mata baya. Tana kwance akan sallaya suka shiga. Ummi ta karasa ta dafa ta. Ido ta bude a hankali ta fara kokarin mikewa Ummi ta taimaka mata ta zauna ta jingina da gado tana dafe kan ta dake mata ciwo ga jiri kamar zai fadi.
"Sannu!"
Duk sukai mata ta jinjina kai kawai. Inna tace
"Sannu Uwa tah ya jikin?"
Ido Maryam ta bude ta gyada mata kai. Inna tace
"Sannu Allah sauwake!"
"Amin!"
Suka amsa da Amin. Inna ta amshi basket din ta dauko flask ta ajiye ta dauki serving spoon ta bude flask din kamshi ya cika dakin. Ido Maryam ta lumshe. Fita Abbah yayi Inna ta dauki plate ta saka serving spoon ta zuba mata ta dauki spoon ta saka sannan ta dauki cup ta zuba mata kunun da tai mata ta ajiye.
Maryam ta kalla sannan ta kalli Ummi tace
"Taimaka mata taci!"
Dauka Ummi tayi. Maryam ta hau girgiza kai tana nuna mata amai zatai in taci.
Inna Ummi ta kalla. Sanna tace
"Inna wai in taci amai zatai"
"Waya fada mata. Ta gwada ci dai!"
Maryam ta kalle ta fuska kamar zatai kuka. Inna tace
"Duk wahalar da nai a banza kenan. Ai kuwa sai kinci kinji ko!"
Ummi ta sauke ajiyar zuciya tace
"Daure kici kinji ko kadan ne!"
Ta diba tayi wajen bakin ta dashi a hankali ta bude bakin ta Ummi ta zuba mata ido ta lumshe ta hadiye da kyar. Tsami tsamin faten yasa taji dadin bakin ta dan haka sai ta dinga amsa Ummi na bata sai da sha rabi sannan ta kau da kai. Kunun Ummi ta bata amsa tayi shima tsamin yasa ta dan kurba sannan ta kau da kai.
Kai ta jingina a jikin gado tana sauke ajiyar zuciya. Inna ta washe baki tana fadin
"Yauwah kuke fa Uwa ta. Sannu Allah yasa ya zaun...."
Bata karasa maganar ba Maryam ta mike a guje tayi bandaki. Amai ta dinga yi kamar zata amayar da kayan cikin ta. Ummi tabi bayan ta, ta dafe bayan ta tana mata sannu.
*Allah ya jikan musulmai yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*
*Antty*
[11/17, 14:04] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 40
By
*MARYAM S INDABAWA*
Hakuri da Juriyya Online ✍
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Wata Motoci kirar Rolls Royce, Motace mai tsananin sheƙi da azabar kyau motar sabuwace dal, sai she'ki da ɗaukar ido takeyi komai na motar farine 'kal sai glass d'inta daya kasance tint mai duhu. Wani kyakyawan matashine mai cikar haiba da kamala da kima, uwa uba kwarjininsa mai cika idon mutane, farine