Showing 171001 words to 174000 words out of 232912 words

Chapter 58 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1254

da gaske anga Maryam.

Ammi ce ta amshi wayar tana fadin
"Hello Alkasim me kace?"
Cikin murna da farin ciki yace
"Tabbas Ammi yau naga Maryam"

"Alhamdulillah Alla kulli halin, Akasim tana ina? Ya take? Ina cikin? Bani ita."
"Ammi ki kwantar da hankalin ki yanzu muka rabu amman zuwa da safe zan kai mata sai kuyi magana"

"Ba zan iyaba Alkasim hadani da 'ya dan Allah."
Abbi ne ya amshi wayar ya fita ya maida ta normal yace
"Alkasim fada min me yake faruwa?"

"Abbi, Maryam tana asibiti bata cikin hankalin ta saboda ganin Aisha da tai ta suma to bata farka ba amman tabbas naga Maryam yanzu ma muna asibitin."
"To shikenan zan sa ai mana booking flight insha Allahu gobe da safe zamu iso ka kula da yar uwar ka."

"Insha Allahu."
Ya kashe wayar ya koma wajen dakin Maryam inda ya samu su Abba da Abbi sun zo suka gaisa Ummi tai musu bayani, suka kalle shi sukaga tabbas suna kama da Maryam.

Karfe goma Abba yace kowa yazo a tafi gida a bar Maryam, Aliyu yaso ya zauna amman Ummi ta kada shi, haka Aisha ma dan haka duk suka tafi cike da fargaba.


*
Washe gari kan goma asibiti ya cika da yan uwa dan su Anty Asiya, Hanna, Bilkisu, Aunty Nusaiba, Najwa da Basma ga Farouk duk sun zo, duk sammakon su Yaa Alkasim da Aisha sai suka tadda su sunyi mamakin wannan alamarin da karamcin wadan an mutanen sosai. Amman har lokacin bata tashi ba Aliyu hankalin sa ya tashi ya kira likitoci suka kara dubata da kansa ma ya duba komai lafiya dan baccin ma lafiya zai kara mata dan in ta samu wadatacan bacci zai sa damuwar ta ta ragu sosai da sosai. Karfe sha biyu jirgin su Ammi ya sauka da tawagar Yayen Maryam su Yaa Muhammad, Yaa Abdullah, Yaya Fadima Har da Mami mahaifiyar Haidar.

Wanda daga nan asibiti suka taho kai tsaye, wanda wajen da suke ya cika ba masaka tsinke dan har daki guda aka basu dan sun cika kofar dakin da Maryam take. Bayan sun shiga sun zauna Ummi tace
"Sannun ku da zuwa."
Suka gaisa cikin mutunta juna. Ummi ta nuna Ammi tace
"Kece mahaifiyar Maryam ko?"

Kai ta gyada, Ummi tai murmushi tace
"Ga kama nan."
Ta nuna Fadima tace
"Wannan yayar ta ce kenan?"
Kai ta gyada.

Ummi tace
"Yanzu Aliyun zai zo sun shiga dakin da su Abba ne shiyasa..."
Bata rufe baki ba Abba da Abbi suka shigo dakin bayan su Yaa Aliyu sai Yaa Abubajar dake biye dasu a baya, wanda yana shigowa Mami ta mike tana kallon Abubakar shima kallon ta yake cike da kaduwa tace
"Sadik...."

Ya matso yana nunata bakin sa yai nauyin furta komai, sai kuma a hankali ya sulale ya fadi kasa a sume ruwa aka yayyafa masa ya farfado yana waige waige tare fadin
"Ina Mami na dan Allah ku kira min ita."

Nami ta dafa sa tace
"Sadik gani nan nice."
Da sauri ya shige jikin ta ya rumgume ta tsam, Ummi, Mami da Abba da Abbi mamaki suke to wacece wannan kenan Maryam tana da alaka da Abubakar tinda ga gashi a yan uwan Maryam ne Abubakar yaga wannan matar yake kiran ta Mami wanda basa dai kama amman ta jini zaka gano akwai alaka.

Abbin Aliyu ne yace
"To Alhamdulillah, wadan nan ne iyayen Maryam din?"
Suka gaisa sosai sannan Abba da Abbi da Abbin Yaa Aliyu suka mike suka nufi dakin da Maryam take aka bar matan suna dan tattaunawa amman gaba daya hankalin Ammi naga taje ta ga yar ta. Dasu Abbi suka shiga sukaga Maryam ba karamin samun nutsuwa yayi ba ya sauke wata ajiyar zuciya wacce bai taba sauke mai dadin ta ba iri ta yau dan sai da ta bayyana yace
"Alhamdulillah."

Ya karasa yai mata tofi suka fito, sannan su Ammi da Ummi duk suka shiga Ammi da taga Maryam kuka ta saka ta rumgume ta tana taba ta sai ta kara rumgume ta tana ganin tamkar mafarki ne Yaa Fadima ma sai kuka, Mami kuwa mutuwar Haidar ce ta dawo mata sabuwa dan ganin Maryam sai ya tuno mata da abubuwa masu yawan gaske. A haka suka bar dakin dan ba a son hayaniya haka su Ammi dasu Ummi suka zauna a daki suna tattauana batu akan batan Maryam da Abubakar.

Wanda Mami mahaifiyar Haidar ita ce mahaifiyar Abubakar, a take aka kira Dadyn sa aka fada masa nan shima ya kamo hanya. Da yamma dasu Inna suka zo ganin jikin Maryam suka taho da Haidar, wanda su Ammi na ganin Haidar sukaga tsasan kamar sa da Aliyu. Rumgume shi sukai suna kuka yaron kuwa sai share musu hawaye yake yana cewa
"Ummi me akai musu suke kuka?"

Sai kuma yace
"Ummi ina Adda ta banganta ba jiya Ummi ki kaini wajen Adda ta."
Aliyu ya gani ya tafi wajen sa a guje yace
"Abbi ina Adda ta."
Daukar sa yayi yace
"Addan ka bata da lafiya Haidar muje kai mata addu'a kada kai kuka nasan Haidar dina jarumi ne ko?"

Kai ya gyada suka shiga, Haidar har da tofa mata ayyatul kursiyyu falaki da nas da amannarasulu ya tofa mata yace
"Allah ka bawa Adda ta lafiya."
Haidar ya rumgume Haidar a jikin sa yace
"Almin my son."

Haka asibiti ya zama kamar gidan biki dan safiyya nayi yake cika wanda har dare sai wajen goma zuwa sha daya kowa yake tafiya Ummi ita ke kula da Maryam, su Ammi an basu boys quarter acan suke zaune duk da su Abbi sun so su kama hotel ko gidan Alkasim, Fadima ce ta tafi can gidan Yaa Alkasim da safe kuma su dawo asibiti.

Kwana ta uku a wannan halin a na hudun ta farka wanda kan kace me likutoci sun hau kanta, suna gwaje cikin hukuncin Allah ta samu nutsuwa domin kuwa jinin ta ya sauka, sai da tai wanka Ummi ta bata abu mai ruwa ruwa ta sha sannan yan uwa suka fara shigowa suna mata sannu, su Yaya Asiya, Yaya Hanna, Yaya Bilkisu, Najwa, Basma, da Yaa Farouk duk suka duba ta bayan su sai Mami da Yaya Nusaiba da Inna da Sitti bayan sun fita ne Ammi da Abbi da Alkasim da Yaa Muhammad da Yaa Abdullah, da Yaya Fadima suka shigo da sallama dagowa Maryam tayi da sauri tana ganin Ammin ta, ta dire kafar ta daga kan gadon da take ta sauko ta karasa a guje ta fada jikin ta tana sakin wani kuka mai taba zuciya.

Ammi ta rumgume ta tana mai kukan itama Abbi ne ya lallashe su suka zauna ta kwanta a jikin Ammi tana mai jin tamkar a mafarki take ganin Ammi gata ga Ammi ga Abbi ga yan uwan ta. Sallama ta juyo wanda tana dagowa taga Mami ce da Dady da Yaa Abubakar wanda yake dauke da Haidar sai a yanzu ta kara ganin kamar da suke sosai, take mutuwar Haidar ta dawo mata ta mike a jikin Mami tana kokarin sauka a gadon Mami ta karaso tace
"Yi zaman ki Maryam yi zaman ki."

Sai ta rumgume ta suka hau kuka kamar ransu zai fita duk dakin kuma sai kuka banda mazan amman idon Alkasim har ya kada dan sosai ya ke jin kewar Haidar da jin mutuwar sa. Dagowa tai ta nuna Yaa Abubakar tace
"Mami waye wannan? Tin gani na dashi a shiga shakku akan sa duk da ba sanin sa nayi ba."

"Shine yayan Aliyu."
Kallon sa take tana kara ganin kamar sa da Aliyu da kuma Haidar. Dan Haidar ba abinda ya baro Baban sa. Hawaye kasa tsayawa yai a idon Maryam Haidar ya sauko yazo yana goge mata har da rumgume ta kamar yadda take lallashin sa yana fadin
"Adda Ammi ki daina kuka nima kina so nayi, in bakya so nayi ki daina inji Adda ina sonki Adda."

Ba wanda Haidar da Maryam basu bawa tausayi ba. Haka dai rayuwar asibitin ta ranar ta zama ta farin ciki sai da idon Maryam yai ta zubar da hawaye da ta daga kai taga yan uwan ta sai hawaye anyi lallashin anyi amman taki ta daina.

A jikin Ammi take tin zuwan su, har yanzu da yake yamma likis, kofar dakin aka turo aka shigo da sallama. Ammi ta amsa Maryam ta dan kalle shi ta kasan idon ta da yai jajir dan a hakan ma hawaye take. Har kasa ya durkusa ya gaishe da Ammi, Ummi dake bandaki ta fito tana fadin
"Yau ina ka shiga ne Dr?"

"Ummi munyiwa wasu aiki ne, ban samu kaina ba sai yanzu ya jikin nata?"
Ya tambaya yana karasawa wajen gadon, a hankali Maryam ta dago suka hada ido, ya kali Ummi yace
"Ummi me kuma akai mata take kuka?"

"To Haidar ai gaka nan gata sai ka tambaye ta ko?"
Ta juya ta fita, Ammi ma mikewa tai ta fita ya karasa wajen ta ya zauna a gefen gadon ya kamo hannun ta, wanda sukaji wani irin abu da ba zasu taba jin irin s ba, dan murza hannun yayi yace
"Me yake damun ki yanzu?"

Kai ta girgiza hawaye na taruwa a idon ta, yace
"Kin tabbata?"
Kai ta gyada yace
"Kinga yadda abu ya koma ko?"

Shiru tayi ya dago kanta suna kallon junan su yace
"Kiyi hakuri ki daina tada hankalin ki, a yanzu kin fi kowa gata, ke da aka guda saboda rashin asali yau ga asalin ki, yau ga zuri'ar mu, mu daku duk mun zama daya kin samu dadin zuri'a dan har abada kin zama zuri'ar mu, dan haka ki bar damuwa ga su Ammi, da Ummi nan gasu Asiya da Fadima nan gasu Haidar so me zai saki kuka uhmmm?"

Hawayen da ya gangaro kan fuskar ta yasa yatsan sa yana goge mata yace
"Ki bar kukan nan, bana son naga hawayen ki na zuba sam, in har aure dani ne bakya so ba zan miki dole ba, nai miki alkawarin zan sauwake miki sai ki auri Muhammad tinda ga asalin hakan yayi miki?"







*Allah ya jikan mu yai mana rahma yasa muyi kyakyawan karahe. Amin.*




*Antty*
[12/2, 11:07] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 70

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Kuka ta fashe dashi ta fada jikin sa wanda suka kara jin wannan abun da ya tsarga musu har tafin kafar su, kuka take sosai wanda yake jin sa har cikin kasan zuciyar sa, hannun sa ya daura a bayan ta yana lallashin ta tare da fadin
"To ya isa kinga bakya jin dadi kuma ba ason damuwa a tare dake ko akan wani can zaki mana asarar kanki, kin fi son sa akan ahalin ki?"

Kai ta hau girgizawa yace
"To ki daina kukan kinji."
Kai ta gyada ya hau lallashin ta har ta daina ya dago ta yana taba jikin ta da ya dau zafi yace
"Me yake miki ciwo yanzu?"

Kanta ta nuna masa ya daura hannu akan zuwa wuyanta wanda tsigar jikin ta ta wani irin mike yace
"Zazzabi ma nake ji a jikin? Kin sha maganin ko allura zan miki?"

Fuska ta shagwabe ta koma ta kwanta ya rakwafa yace
"Oh allurar kike son kenan ko?"
Da sauri ta dago wanda hakan yasa fuskar su ta hadu da juna hannayen sa yasa ya tallafonta yana dage mata gira a hankali yace
"Ayi allurar?"

Kafada ta make sai kuma ta fashe da kuka yace
"A'ah da wasa nake ba za ai miki allura shikenan."
Kai ta gyada dai dai jin an kwankwaso, suka bada izinin shigowa Aisha ta shigo hannun ta rike da basket tace
"Sannu Patient."

Ta kalli Aliyu tace
"Sannu Dr ya me jikin?"
"Da sauki."

Basket ta ajiye tana ganin Maryam na matsawa daga kusa da Aliyu, kai ta dauke tace
"Abinci na kawo mata Dr gashi nan ka bata taci."
Wani kallo Maryam ta zabga mata tace
"Ni na koshi."

"Kasan Allah tin tea bata kara shan komai ba, yanzu naje nai mata pepper soup din ko zataji dan dadin bakin ta."
"To sannu mungode."

Ta juya tana wa Maryam gwalo ya dauki bowl ya zuba mata ya dauki spoon ya ajiye akan stool ya karasa ya daga ta ya jingina ta da filo ya fara bata da kansa sosai taci sannan ya barta da dabara ya bata magani ta sha lokacin likita yazo ya kara dubata, bayan ya gama Aliyu yace
"Ya jikin nata?"

"Da sauki sosai sai dai naji zazzabi yanzu."
"Abinda na gani kenan."

"Zan bata maganin insha Allahu zai sauka."
"Please in ba damuwa a bamu sallama mu karasa a gida kaga yadda muke cika asibitin nan."

"Eh ba wata matsala sai ka cigaba da duba ta a gida din amman dan Allah a kula da bata mata rai, sannan ki rage tunani kinji?"
Ya fada yana kallon Maryam.

Kai ta gyada yace
"Allah kara sauki."
Ta amsa da amin ya juya ya fita. Daga nan suka hada kayan su suka tafi gida.


*
Washe gari gaba dayan su ne zaune a falon Abbi, banda Mama da ko asibiti bataje duba Maryam ba da taji anga ahalin sai ma karyawata tayi dan bata so ba, ta so rayuwar ta ta lalace gaba daya.


Abbin Maryam ne yace
"Ba abinda zamu ce muku sai godiya da yadda kuke rike mana Maryam da Abubakar Allah ya biya ku da gidan aljanna hakika ku mutanen kirki ne samun irin ku sai an tona ba abinda zamuyi muku sai addu'a Allah ya saka muku da mafificin alheri ya biya ku da gidan Aljanna."

"Ah haba ai yiwa kai ne, dan yanzu daga Maryam har Abubakar ai duk namu ne duk mun zama zuri'a daya."
Abbin Haidar ne yai wannan maganar.

Mami dake zaune jikokin ta a jikin ta ta rasa ina zata sa kan ta dan murna yau ita da ake cewa ba zata taba ganin jinin ta ba sai gata ga danta ga jikoki har guda shida na Abubakar biyar na Haidar d'aya, kai alhamdulillah, hakika a baya Allah ya jarabce ta amman amsa kaddarar ta yau Allah ya bata wannan tukwincin ba abinda zata ce sai Alhamdulillah, Haidar kuma Allah masa rahma.

Dady ne yace
"To yau zamu juya kamar yadda muka sanar muku, sai dai muna neman alfarmar a ara mana Maryam da Abubakar da mai dakin da jikokin dan mu kai su gida, yan uwa su gansu in yaso sai su dawo gaba daya, kuma muna fatan zaku zo inda muke dan zumunci yanzu muka fara dan hakika kun mana abinda ba zamu taba mantawa ba."

Abba ya saki murmushin farin ciki yace
"Ah haba ba komai Allah ya kiyaye gaba ya tsare na baya ba komai kuje dasu Insha Allahu zamu muma mu zo muga gidan gaba daya."

Haka aka cigaba da hira, da muyasar number waya da address, Maryam na daki a kwance idon ta lumshe amman ba bacci take ba, kan ta ke mata wani irin ciwo, Yaya Fafima da Aunty Asiya da Najwa da Hannah da Aisha sai hira suke, Aisha ce ta kalli Maryam ta mike ta karasa tace
"Besty wai jikin ne?"

Mikewa tayi ta jingina tare da sakin murmushin karfin hali kawai. Ummi ce ta shigo tace
"To Daughter ya jikin?"

"Da sauki Ummi."
Wajen durowa ta karasa ta bude ta dauki akwati ta hau zuba mata kayan da zata bukata tana fadin
"Yau sai Kanon dabo Daughter."

Gaban ta ne ya fadi, dan tabbas ta tino komai na rayuwar ta ya tsayar mata da tunani kan Haidar da gaske ta rasa Haidar da gaskiya ba zata kara ganin Yaa Haidar ba, bata da damuwa a yanzu sai ta rashin Yaa Haidar wannan kadai ke sata kuka da damuwa sosai.

Kallon Ummi take har ta gama hada mata kayan sannan ta fita dasu ba a jima ba ta shigo tana fadin
"To ku taso."

Maryam ta mike ta fada jikin Ummi tace
"Ummi yaushe zaki zo?"
"Insha Allhu kwanan nan kusa dan ni zan zo na dauko amaryar Aliyu."

Sam ta manta da wani Aliyu ma sai yanzu ta tuna da auren su da Aliyu da haka sai ta share kawai haka suka fita ita da Ummi a falo taga su Ammi ta karasa ta gaishe su sannan suka mike zasu fita, har ta kai bakin kofa ta juyo tana kallon kofar dakin Yaa Aliyu ko yana ina, juyowa tayi ta nufi dakin nasa, tana bude kofa suka kusan cin karo da Aliyu da sauri tai baya wanda ta kusan hantsilawa da sauri ya taro ta ta fada saman kirjin sa, kamshin turaren sa mai dadi ya doki hancin ta, dagowa tayi tana kallon kasa. Aliyu yace
"Ya akai?"

Da sauri ta janye jikin ta tare da juyawa tana girgiza kai, wucewa tai ta nufi kofa ya kalle ta ya saki murmushi suka bar wajen.

Bangaren Inna su Ammi suka nufa wannan yasa itama ta bisu can, duk suna zauna suna tattaunawa da Inna, Maryam ta shiga da sallama duk suka kalle ta, Inna ta mika mata hannu tace
"Zo Uwata zanyi kewar ki duk da ba jimawa zaki ba."

Maryam ta karasa Inna ta rumgume ta tana fadin
"Kunganta nan ko, tana daya daga cikin jikoki na da na fiso, wallahi yadda nake jin ta ko su Asiya bana jin su, naji dadi da su Shehu suka aura ta ga Aliyu, dan na yaba tabbas da Maryam wanda in wani ya same ta munyi asara, matsala daya ita ce sai tayi hakuri da mijin nata dan miskili ne dan taimako tabbas ya mata dan zan iya cewa yafi su Aisha ma kula da ita to shi matsalar sa kenan da sun tambayen daman da zance su aurawa Umaru to amman ba yadda zanyi tinda sun aurawa Alin Allah yasa albarka ya basu zaman lafiya, kuma ina fatan su kawo min ya'yan su."

"Insha Allahu Inna muna kara godiya da yadda kuka amshi Maryam a matsayin taku ba tare da kyama ba duk da tazo da ciki a tare da ita, har kuka aura mata d'anku a haka kuka rike ta da yaron ta, tabbas ba abinda zamu iya saka muku dashi."
Ammi tai magana hawaye na kawo idon ta.

Ummi tace
"Haba Ammin Maryam ai yiwa kai ne."
"Haka ne Allah kuma ya jikan ku ya bamu ikon kyautata muku."

"Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum!"
Suka fada, Mami tace
"To mu zamu wuce sai kunzo din."
Duk suka mike suka fita, Maryam da Inna suka fito Inna rike da hannun ta har wajen mota suka rakasu, Farouk ya ja mota daya Aliyu dayar duk suka shiga suka nufi airport. A airport Maryam na jikin Mamah dan wasu abubuwan sai a yanzu take kara recalling nasu jikin ta yai sanyi, Haidar na wajen Ammi, har aka kira su, sukaiwa su Ummi da Yaa Haidar da Farouk Sallama,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login