Showing 111001 words to 114000 words out of 232912 words

Chapter 38 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1256

Tea din!"
Idon ta ne ya ciko da kwalla. Yace
"Try it!"

Cup din ta dauka ta kai bakin ta dumim tea din yasa ta kafa kai sai da tasha rabi sannan ta ajiye, kirji ta dafe yace
"No kar kiyi kinji!"
Kai ta gyada amman yadda take jin tashin zuciyar bata san lokacin da ta mike da sauri tayi bandaki ba. Da sauri yabi bayan ta.

Ummi na sauka ta samu Farouk zaune a falo. Kallon sa tayi tace
"Ah Farouk kai kadai zaune anan!"
Kai ya shafa yace
"Nazo wajen Hamma ne!"

Sama ta kalla tace
"Yana sama ai! Kaje ka same shi!" "Toh fita zakiyi?"

"Eh zani aiki ne!"
"Adawo lafiya Allah tsare."

"Amin!"
Ta juya ta fita shi kuma ya haye sama ya nufi dakin Ummi ya murda. Kakarin aman ta ya jiyo da sauri ya juya ya fita yana yamutsa fuska. Anan falon sama ya zauna yana pressing phone nasa.

Ganin ya kwashe wajen minti goma bai fito ba yasa ya nufi dakin. Ganin su yayi sun fito a toilet din Maryam na gaba Aliyu na bayan ta. Kan gado ta kwanta taja bargo ta rufa ya karaso cikin kulawa da tausayi yace
"Sannu!"
Kai ta gyada ya dago yana kallon Farouk dake tsaye fuska a yamutse dan Farouk ba dai kyamkyami ba.

"Kaje daki na ka daukon wata leda akan kujera!"
Da sauri ya juya bai jima ba ya dawo ya mika masa leda ya juya ya fita. Ruwa ya dauka a ciki ya hada ya saka mata nan take bacci ya dauke ta. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya kwashe kwanukan wajen ya fita dakin

Farouk ya gani zaune ya kalle shi ya nufi stair da sauri Farouk ya karaso yana fadin
"Kawo big bro!"
Ya amsa ya sauka Aliyu yabi bayansa. Kitchen ya kai ya dawo ya sami Aliyu a kasa yace
"Hamma wai wacece wacan ne?"

Dagowa yai ya kalle shi sai yai sauri yai kasa da kansa yace
"Uhmm ina kwana Yaa Haidar!"
"Ka tashi lafiya?"

"Alhamdulillah!"
"Mukullin motar yana kan dressing mirrow!"
Yana fadar haka ya fara danne danne a waya.

"Nagode Allah kara bude!"
"Amin!"
Ya juya ya nufi dakin sa. Wayar sa ce tai kara ya dauka yace
"Ummi menene?"

"Anjima mai aiki zata zo shine nace bari na fada maka."
"Allah kawo ta lafiya."

"Ya me jikin?"
"Na saka mata ruwa bacci take yi!"
Ya fada ya mike ya nufi sama dai dai fitowar Farouk ya kalle shi ya fita kawai yana tunanin to wacece wannan yarinyar.

Bacci ya same ta take yi sauka yayi ya koma dakin sa ya fara aiki a system din sa. Har karfe sha biyu yajiyo ana knocking ya sauka ya ga mai aikin ce. Suka gaisa sannan ya bata hanya. Kitchen ta shiga tai wanke wanke ta gyarawa Ummi kayan miyan da ta saka ta dan basa mata girki iyakar su wanke wanke da sauran su. Aliyu na bude mata ya juya ya koma dakin lokacin ruwan ya kare ya zare mata ya sauka ya zauna a falo.

Yana zaune yajiyo sallamar Inna kai ya dafe ya amsa. Ta shigo ta zauna tana fadin
"Ina mahaifiyar taka?"

"Ta fita aiki!"
Mikewa tayi tai sama tace
"Ba wajen ka nazo ba ai da kake sha min kamshi!"

Ya bita da kallo sannan ya dauke kai. Maryam ta sama kwance amman idon ta biyu ta kalle ta tace
"Sannu Uwa ta ya jikin?"
Mikewa tayi tai mata alama da hannu ina kwana? Inna tace
"Lafiya ya jikin?"

Tai mata alama da da sauki. Tace
"To Allah kara sauki!"
Ta amsa da amin a zuciya. Sannan tace
"Kina jin dadin nan din ne?"

Kai ta gyada mata tace
"Ko dai zaki zo daki na?"
Kai ta gyada! Tace
"To taso muje kinji!"

Ta mike Inna ta fita Maryam tabi bayan ta. A kasa suka samu Aliyu bata kula shi ba ta yi gaba Maryam ta kalle shi sannan tabi bayan inna. Kai ya jingina da kujera yana mai lumshe idon sa. Suna shiga tace
"Kinga dan dakin nawa ko? Zauna akan kujerar kinji!"

Ta zauna tana bin dakin da kallo kamar dakin amarya ga kyau ga tsafta. Inna tace
"Me zan kawo miki?"
Kai ta girgiza. Inna tace
"Ki saki jikin nice mahaifiyar wanda ya kawo ki gidan nan su hudu na haifa Baban shine babban wannan na dakin da muka baro wai shi Dr sunan sa Aliyu baban nasa shine babba sunan sa Suleiman sai wanda kike wajen matar sa, Usman sai Takwarar ki mai sunan mahaifiya ta wacce ta mutu tin suna yara, sai autar su Nusaiba dake aure acan kasashen waje. Su uku suka rage min amman alhamdulillah ina jin dadi kamar me ya'ya goma dan suna kulawa dani.

Babar Aliyu uwa da uba daya suke da wacce kike wajen ta Aisha ita kuma sunan ta Hauwa ya'yan ta hudu Aliyu ne babba sai mata guda uku ta aurar da biyu Asiya da Hannah daya tana can makarantar kwana me suna Najwa, sai abokiyar zaman ta Barira wacce ta haifi ya'ya biyu Umaru da Bilkisu.
Sai Aisha wacce da ta haihu yaran suke mutuwa ta haifi ya'ya biyar amman duk babu mai rai.
Wannan yasa take rike da Aliyu duk da dai tin kan ta fara haihuwa yake wajen ta dan tana son yara gashi Allah bai bata ba.

Sam Barira bata da dadin zama ta saka Aisha a gaba yadda ta tsani Aisha ko Hauwa kishiyar ta bata tsana ba na rasa dalili ni kuma Allah ya dauran son Aisha dan yarinya ce mai tarbiyya da ladabi ga kyauta ita ta koyawa Aliyu shiyasa hannun sa yake a bude dan duk safiyyar Allah, in zai fita sai ya ban kudi yadda yake min tamkar ni na haife shi bar shi dai da miskilancin sa. Sai dan banzan kwadayi a cikin sa. shi kuwa Farouk sai kyale kyale kamar me haka kullum yake kamar mace ba shi da aiki sai surutu inya zauna ya cikan kunne to kinji kadan daga yan gidan a sannu zan na fada miki irin rayuwar da muke ciki wata ma da idon ki zaki gani."

Murmushi Maryam tayi Inna tace
"Oh na manta ban fada miki siriki na Abubakar ba mijin Nusaiba wacce nace suna waje yaron kirki kenan wallahi uwa ya dauken yana sona ya'yan su uku da Ammar, Widad sai Muhsin."

Kiran sallah aka tada Inna tace
"To kinji sallah tashi muje kiyi alwala kizo muyi sallah nayi dambu zaki ci ai ko?"
Tin da ta samu ciki yau ne aka fadi abu taji tana son ci sai dai tasan in taci me zai biyo baya.

Bandakin Inna ta kai ta wanda yake a wanke a goge tas dashi. Alwala sukai anan falo sukai sallah bayan sun idar Inna ta zauna tace
"Ina wannan Aliyun da kika gani to ba fa aure ne dashi ba yayi aure shekara biyar kenan da mutuwar matar amman yaki ya sake auren ni tsoro na daya ma kar muje aljanna ce ta kuma aure shi."
Aliyu ne ya shigo wanda tin daga bakin kofa yake jin muryar Inna ya shigo da sallama ya samu kujera ya zauna.

Ta kali Maryam tayo kasa da kai cikin muryar rada tace
"Kinganshi ko?"
Kai ta gyada Aliyu ya dauke kai. Inna ta mike tace
"Bari na kawo mana abinci!"

Ta shiga kitchen ta hado musu abinci kowa a plate din sa. Ajiyewa Maryam tayi tace
"Allah yasa yai miki dadi!"
Ta zauna ta fara cin nata tace
"Ai dai ba nama bane bare kace na maka rowa."

Maryam ta dauki spoon ta dibi dambun Aliyu ta kalla da yake kallon ta. Maida spoon din tayi ta tura masa abincin kai ya girgiza sai kuma ya mike ya dauki plate din ya kalle ta yace
"Tashi muje kici a can kisha magani."

Bai jira jin ta bakin Inna ba ya fice. Inna tace
"Oh kada ta zauna a waje na kenan lallai Aliyu!"
Maryam ta mike ta kalle ta, tanaiwa mata alamar zata dawo ta fita. A hankali ta fara tafiya zuwa sashen su.

Farouk da ya dawo zai je sashen Inna ne ya kusan yin karo da ita dan waya yake dannawa bai kallan gaban sa, da sauri taja baya, ya dago da sauri yana ganin Maryam yai baya da sauri yana hade fuska yace
"Menene haka bakya kallon gaban ki ne?"

Hannu ta hade tana bashi hakuri, wani kallo ya watsa mata ya bar wajen da sauri, itama da sauri ta nufi sashen Ummi tana waiwaye. Aliyu ta sama a falo ya nuna mata kan kujera ta karasa ta zauna ya mika mata maganin da ya ballo sannan ya bata ruwa. Amsa tayi ta fara sha tana sha tana hawaye dan bata son shan magani. Bayan ta gama ya kalle ta yace
"Me kike so ki ci?"

Plate din da ya shigo dashi na dambun da Inna tayi ta kalla, yace
"Zaki ci wannan ne?"
Kai ta gyada ya kalli dambun yace
"Kar ya saki amai fa!"
kai ta girgiza alamar ba zai sa ta ba

Daukowa yayi ya dauki spoon yai cokali daya, yayi dadi yaji gyada da zogale dan haka ya mike mata, amsa tayi sai kuma ta mika masa tai masa alama da yaci. Kai ya girgiza yace
"Ci abinki!"
Diba tayi taci cokali uku taci ta ajiye dan ji tayi ya tsaya a wuyan ta. Ruwa ta sha ta koma ta kwanta a gefe.

Ya kalle ta yace
"Har kin koshi?"
Kai ta gyada kawai ta lumshe idanun ta. System din sa ya janyo ya cigaba da aikin da yake yana yi yana satar kallon Maryam dake kwance har bacci ya dauke ta.

A ransa yace
"Tana can ta cika mata kunne da hira ko wa yace mata hira take so yanzu hutu take bukata."
Ya dan saki tsaki yana cigaba da aikin sa. Yana zaune mai aikin su Baba Habi ta fito dan a bangaren su Mami take ita da sauran masu aiki ta karaso falon tace
"Dakta na gama ni zan tafi sai Hajiyar ta dawo."

"To Baba sannu sai anjima!"
Ta fita ya cigaba da abinda yake yana zaune akai sallah la'asar, Maryam ya tasa ya shiga yai alwala ya fita masallaci. Alwala tayi tai sallah ta dauki Alkur'ani tana karantawa. Hudu da kwata ya dawo kitchen ya shiga ya bude firij ya dauko Fresh Yoo ya dawo falo ya same ta tana karatu a cup din tangaran ya zuba ya fara sha yana aiki yana kallon ta.

Bayan ya gama ya mike ya kunna TV ya koma ya cigaba da aiki, karfe shida saura Ummi tayi sallama a kofar dakin nata. Aliyu ne ya amsa Maryam kuwa sai bin kofar tayi da kallo. Ummi ta shigo ta karasa wajen Maryam dake ta kallon ta tace
"Sannu ya jikin?"
Da sauki tai mata nuni sannan ta kalli Aliyu tace
"Doctor ya gidan da me jiki?"

"Alhamdulillah!"
"Allah kara sauki!"

Ta mike tace
"Bari na hau na sauko!"
Ta mike tayi sama. Bata jima ba ta sauko ta canja kaya hannun ta rike da leda ta karaso ta dafa Maryam tace
"Sannu!"

Kai ta gyada ta kalle Aliyu tace
"Dr sannu da jinya Allah ya saka da aheri!"
"Haba Ummi sai kace wani abu nayi ai is my job!"

"Allah maka albarka!"
"Amin."

"Me zamu dafa ne?"
"Ummi just do sometime simple dan naga kin gaji!"
Maryam ta kalla tace
"Daughter ke me kike son ci?"

Kai ta girgiza ta kalli Aliyu tace
"Me taci ne yau?"
"I can say nothing since she just eat three spoon of dis thing!"

Ya nunawa Ummi plate din da ya rufe na dambu. Ummi ta bude tace
"Wa ya bata?"
"Kema kin sani. Inna ce."

"Maryam to bakya so?"
Kai ta gyada ta kalli Aliyu tace
"Kai fa?"
Baki ya tabe ya girgiza kai.

Ummi tace
"To ni bari naci da a zubar sai na girka ko supagette ce!"
Ta zauna ta ci sannan ta shiga kitchen ta wanke yalon da ta siyo sannan ta fito ta ajiyewa Aliyu da Maryam ta koma kitchen dan yin aiki. Daya Aiyu ya dauka ya mike yabi bayan ta.

Tana aiki suna hira akan aikin ta yawanci yace
"Ummi yanzu ya za ayi da yarinyar nan?"
"Name fa?"

"In zaki aiki da safe wajen wa za a barta!"
"Ba matsala ko da Baba Habi na barta kan dai mu dawo."

"Ummi tana bukatar kulawa fa."
"To Aliyu ya za ai?"

"Shekara ta kusa karewa gashi ban dauki hutu ba i think, i am going to take it now dan na kula da ita sosai dan akwai magani da allurar da na daura ta akai na matsalar rashin maganar ta ne me kika ce?"
"Hutun ai ba zai fi 1 month ba Son!"

"Yes is just one month Ummi! But by then nasan cikin ya kara girma since yanzu yana four month ina sa ran in ya kara kwari zai rage bata wahalar nan me kika ce?"
"Bansan me zance ba Aliyu, my son u are such a kind person Allahu ya biya ka ya baka lada yai maka albarka Amin!"

"Amin ya Hayyu ya Qayyum thank you so much Ummi!"
"U are always welcome my son!"

"Ramadan remain three week fa!"
"Allah nuna mana zaki Umrah ne?"

"Tayaya zan tafi na bar Maryam.".
"Sai ku tafi tare!"

"Ba wahala?"
"Mu bari muga yanayin jikin ko tinda goman karshe zamu tafi."

"Shikenan! Abbah naji yace in anyi 15 zai tafi shima yai min magana nace Maryam."
"Insha Allahu by then jikin ya kara sauki."

"Allah ya yadda!"
"Amin!"
A haka take girkin yana taya ta aiki har suka gama fried supagette da papper chicken suka jere a dining. Maryam kuwa taji dadin yalon taci da yawa. Tana zaune su Ummi suka gama. Aliyu ya shiga yai alwala ya tafi masallaci Ummi da Maryam sukai sallah anan falo.



*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.*


💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 45

By
*MARYAM S INDABAWA*



*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)



Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Karfe takwas da kwata Aliyu ya shigo tare da Abbah a falo suka zauna Abbah ya kalli Maryam yace
"Ya jikin?"
Tai masa alama da sauki. Sannan ya kalli Aliyu yace
" ya jikin nata kuwa?"

"Abbah da sauki sosai!"
"Allah kara sauki ta ci abinci kuwa?"

"Ai kasan sai a hankali zatana ci a sannu zata daina duk aman nan da rashin cin abincin insha Allahu."
"Allah ya yadda!"

Ya mike yai sama. Ummi tabi bayan sa, sun jima sannan suka sauko Abbah sanye da jallabiya daga gani wanka yayi dining suka shige. Ummi tace
"Ku taso muci abinci!"
Aliyu ya mike yana kallon Maryam dake girgiza kai. Yace
"Bazaki ci ba!"

Kai ta gyada ya nufi Ummi ta fara zuba masa ya dakatar da ita wai ya ishe shi. Ta kalli dan abincin tace
"Haidar what wrong with you!"
"Nothing Ummi!"

Abbah ya dago ya kalle su yace
"Me yake faruwa?"
"Abbah baya son cin abinci fa sam!"

Kai yai kasa dashi yace
"Ciki na ne ya cunkushe two days kuma ban jima da shan youghurt ba."
"Alright kadai na kiyayewa bana son rashin cin abinci da girman ka."

"Insha Allahu Abbah zan kiyaye!"
Suna Dining suka jiyowa Inna, Ummi ta mike tana fadin
"Barka da zuwa Inna!"

Aliyu da ya gama ya mike ya shige dakin sa. Inna ta bishi da kallo tace
"Yaron nan ya nuna min iko akan yarinyar nan yanzu dan Allah abinda yai min dazu ya kyauta."
Abbah ya mike yace
"Me Aliyun naki yayi?"

"A'ah naku dai. Wallahi yaron nan muna tare da uwata yazo ya dauke ta dan na bata abinci ni fa tsurfar sa na damuna ace mutu ba zai ci abincin gargajiya ba sai na zamani rayuwa ta tafi a haka kuwa. Yana yaro dai kato dashi amman yanzu rashin cin abinci da tsurfa duk tasa ya kare."
"Kiyi hakuri Inna."

"Wai me yasa baku da aiki sai nayi hakuri karfin ku Aliyun yafi da zai abu baza ana masa fada ba."
"Kiyi hakuri Inna za ai masa."
Ummi ta fada. Inna tace
"To Allah yasa."

Ta nufi Maryam da ta jingina da kujera tana fadin
"Sannu Uwata ya jikin?"
Dagowa tayi ta sakar mata murmushi tai alamar da sauki.

Inna ta mika mata cup din kunun da tayo mata tace
"Maza sha abin ki kan wancan bokan turan ya fito ya hanaki sha bana son ki kwan da yunwa sam!"
Amsa tayi ta kafa kai kadan ta sha ta ajiye cup din dan bata so tasha yadda zai saka ta amai.

Inna tace
"Yai dadi ko?"
Kai ta gyada. Inna tace
"Ai nasan zai miki dadi."

Ta mike tace
"Bari naje na kwanta sai da safe ko?"
"Allah bamu alheri Ummi da Abba suka fada."

Abbah ya bita suka fita. Suna fita Aliyu ya fito yana bata fuska. Ummi tace
"Zo nan!"
Aliyu ya karasa tace
"Bana so daga yau ka kara hanata cin abun Inna naga ba wani cin abincin take ba bare ace zai mata illa da ace bata ci ba ai gwara taci ko yaya ne ko? Kana gani anan baci take ba na Innan take dan tabawa kadan fa."

"To shikenan Ummi ba zan sake ba."
"Allah maka albarka."

"Amin ya hayyu ya qayyum tasha maganin ta taje ta kwanta ko?"
Da kan sa ya bata sannan ya nufi dakin sa.


*
Washe gari tare suka je asibiti dan Ummi ta tafi aiki dan haka tana kwance yana mata karin ruwa ya gama abinda zai yi karfe biyu bayan ya dawo daga masallaci suka koma gida lokacin Ummi ta dawo dan ranar da wuri ta dawo. A falo suka zauna gaba dayan su.

Karfe 5:15pm suna zaune Mami ta shigo dakin da sallama. Suka amsa ta karaso tana kallon Maryam. Mikewa Ummi tayi tana fadin
"Sannu da zuwa!"

Samun waje tayi ta zauna sannan ta kalli Aliyu dake daddana waya. gaisawa sukai da Ummi sannan Aliyu ya dago yai mata barka da gida. Ta amsa Maryam ta gaisheta da hannu ta amsa tana fadin
"Ya jikin?"
"Jiki da sauki!"
Tai nuni da hannun ta.

Ummi ta kalli Maryam tace
"Wannan sunan ta Mami ita Yaya tace kuma mahaifiyar Aliyu mata ga Yayan miji na kin gane?"
Kai ta gyada tana murmushi. Mami tace
"Ya jikin nata dai?"

"To da sauki zamuce amman fa ba abinda take ci, ko taci zata amayar ne."
"Ikon Allah irin cikin Maryam kenan. Irin wannan cikin wahala ne dashi wallahi Allah ya raba lafiya dai amman kinyiwa Inna magana a samar mata na hausa kuwa?"

" 'Dan naki zai yadda ne?"
Mikewa yayi ya kara waya a kunne ya fice. Da kallo suka bishi sannan Ummi tace
"Kisan sa sam bai yadda da traditional things din nan. Kina gani common dan abu Inna ke kawo mata amman sai yayi ta kwakwafi ya ga abun is nutritive in na fada ma sai ya fara cewa is not first class kaza da kaza, kinsan likitocin nan sam basu yadda da gargajiya ba su dai komai nasu ne mai kyau."

"Ai fa nasan za ai haka kin manta Maryam dauke ta yayi suka bar kasar amman kuma da Allah yayi ba rabon yaron da ita suyi rayuwa gaba ba gashi mun rasa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login