Showing 105001 words to 108000 words out of 232912 words

Chapter 36 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1242

ki zanyi ko muyi zaman mu anan."

"Oh yadda kuka min da ko? To in kana son haka sai dai ka auri ta gida ita ce zata iya rayuwar da kake so kullum kuna nan, gidan ku a rufe amman in ka auro ta waje kuwa bazata iya jura ba zataga an takura ta."
"Ummi na kenan kina so dai kice nayi auren gida ko? Ummi u know who is Maryam please from all my slibing wacece take da hali da dabi'u irin na Maryam? Ta riga ta sangartani da komai nata i can't  live with any girl expect her, she is my only love Ummi!"

Ya mike a hankali. Ummi ta kamo hannun sa ta nuna masa inda ya tashi komawa yai ya zauna ta hada masa baƙin tea da zuma dan bai shan suga zuma mai kyau yake samo musu sukai using. Bread din da ta gasa da kan ta yaji inibi ya gasu ta bude masa da dankali da kwai a wani bowl sai pepper soup din kayan ciki.

Tea din kadai ya sha ya dan kalli Ummi yana shafa ciki yace
"Ummi na koshi fa!"
Fuska ta bata yai saurin saka hannu ya dauki slice na bread guda daya ya gusura wanda dadin sa da laushi yasa ya lumshe idon sa. Shi ya cinye sannan ya karya wuya yace
"Dan Allah Ummi ki tausayawa yaron ki wallahi na koshi!"

"Allah in nai tafiya ka kara damu na akan na dawo bakan cin abinci sai na kara sati akai."
Kunne ya kama da hannu yace
"Affuwan Ummi! Muje naga Yarinyar can anjima zan turo a daukon ita."

Ya nufi stair tabi bayan sa a bakin dakin ya tsaya Ummi ta karasa cikin dakin da sallama sai da ta shiga sannan ta bashi izinin shiga ya shiga da sallama. Tana kwance kudundune cikin bargo dan yau da zazzabi ta tashi kuma.
"Ya jikin nata?"

"Bacci take amman da zazzabi ta tashi?"
"Me taci?"

"Ba komai tin jiya da taci abincin Inna!"
"Bayan ta dawo dashi."

"No ta tashi cikin dare ta kara ci!"
"Ya zauna kuma?"

"Eh ya zauna."
Agogon hannun sa ya kalla yace
"Zan aiko anjima a tafi da ita!"
Ya juya ya nufi kofa Ummi na binsa a baya sai da ya fita ta fito ya tsaya tai gaba yabi bayan ta.

A falo suka tsaya ya durkusa yace
"Ummi zan tafi pray for me!"
"Allah kai ka lafiya ya dawo dakai lafiya, Allah ya tsare min kai a duk inda kake ya baka halak din ka ya kare ka daga cin haram ya sa maka albarka a neman ka. Allah maka albarka!"

Hannun ta ya kamo yaiwa Kiss sannan ya amsa da
"Amin Ummi na jazakallahu bil khair!"
"Same to you son!"
Ya dauki jakar system din da dake kan dining ya nufi kofa yana daga mata hannu.

Yana fita ya hadu da wani matashin saurayi wanda yake fari dogo dashi. sanye yake da dogon wando pencil,  crazy sai riga t-shirt kyakyawa ne shima dan gayu sai tashin kamshi yake. Daga gani sashen Inna ya nufa, karasowa yayi yana murmushi yace
"Barka da safiyya Akee!"
"Ka tashi lafiya?"

Ya fada ya juya! Amsar jakar system din sa yayi suka nufi sashin Inna sannan yace
"Alhamdulillah!"
"Banganka da asuba ba?"
Aliyu ya jefa masa tambayar.

Kansa yai kasa dashi yace
"Na dan makara ne Hamma amman ai na samu last raka'at!"
Ya fada yana shafa sumar kan sa mai cike da gashi irin gyaran yan samari yan suwaga din nan. Kai kawai Aliyu ya gyada.

Compound din Inna a share tsaf dashi tin daga daki har wajen kamshi yake yi. Ido ya lumshe ko ba komai yana son tsaftar Inna duk da ta tsufa bata wasa da tsafta ta tsani kazanta. A hankali suka karasa kofar falon cikin muryar sa mai sanyi yayi sallama. Inna dake zaune gaban ta tea da bread da wainar kwai da fura da nono dukka ta dago ta amsa tana fadin
"To fa!"

A hankali ya shiga dakin ya nemi kujera daya a ciki ya zauna. Kanin sa Farouk dake bayan sa ya shigo ya samu kusa dashi ya zauna.

Kallon sa Inna tayi tana Murmushi tace
"Miskili kafi mahaukaci ban haushi."

"Ina kwana?"
"Lafiya lou wallahi ni na gaji da ganin ka kana zuwa gaishe ni da safe ina laifin da rana ko yamma wato lokacin kayi aure kazo daga gidan ka. Haba wa Malam ai sai yafi armashi."

Shiru Aliyu yayi ya zuba mata ido. Inna ta  rausayar da kai tace
"Eh mana ka kuwa san ni'imomi da falalar da ni'imomin dake cikin aure, ko auren da bakaji dadin sa bane da kaki ka kara wani ai aure shine cikar mutunci da kimar kowa a duniya amman kalle ka babban mutum mai kima amman ba aure wallahi wani ana fada masa baka da aure zai ji kimar ka ta ragu a wajen sa.

Farouk ne ya miƙe tare da fadin
"Ke in anzo gaisheki sai ƙaƙale-ƙaƙalen zance tsiya kika iya. In baki nemi fada ba kya nemi rigima ni na tafi dan inada aikin yi."
Hararar shi tayi tare da cewa
"Tafi daga nan!"

Sai kuma ta juyo ta kalli Aliyu tace
"Dan Allah wa ya saka dashi ne wai? Ni me ma ya kawo ka waje na? Kar kace gaishe ni kazo yi dan baka gaishe ni ba sai rashin kunya da kazo kai min. Ina ruwa na ma da kai ne dan Allah."

Harara ta yayi kana ya juya ya fita. Inna ta rike haba tace
"Kayiwa Uwar ka!"
Aliyu kuwa kai ya jingina da kujera sai kuma ya dago ya kalle ta yace
"Maganinki ya kare koda saura?."

Da sauri tace
"Kai ni kyale ni da shan magungunan nan lafiya ta lou fa. Bana bukata."
Mikewa yayi yace
"Kin huta kudi na ya huta ni na tafi sai na dawo!"

Ya zura hannu a aljihu ya zaro 2k ya ajiye mata. Tace
"Allah yayi albarka Allah kiyaye yaron kirki!""Amin!"

Ya amsa ya juya ya fita. Farouk ya sama makale da waya a kunne yana ganin sa yace
"Am sorry my love ga Yaya bari na raka sa i will call you later!"
Ya karashe maganar da murmushi a fuskarshi, shi kuwa Aliyu kauda idon shi yayi yaci gaba da tafiyar sa. Sannan suka jero suka nufi sashin Mami.

Suna shiga yayi gefen dama, inda wani tamfatsetsen part mai tarin girma yake, a hankali suka karasa cikin part ɗin, wani babban falo suka fara ratsawa kana suka wuce zuwa cikin wani corridor sai gasu a wani fitinenne falo mai wadatar tsabta da ƙamshi. Abbah suka sama zaune akan kujera hannun sa rike da carbi ga Alkur'ani a gaban sa banda sautin da yake tashi na karatu a hankali.

Zama sukai sannan sukai kasa da kansu gaba daya. Aya ya kai sannan ya dago yana tasbihi a bakin sa ya kalli yaran nasa ya saki murmushin jin dadi hadi da fadin
"Allah muku albarka!"
"Amin!"

Sannan Aliyu ya kara yin kasa da kansa yace
"Barka da asuba Abbi!"
"Barka kade da fatan an tashi lafiya?"

"Alhamdulilah!"
Sannan Farouk ya gaishe shi ya amsa yana musu nasihar sa ta kullum akan suji tsoron Allah a duk inda suke su rike gaskiya da amana sannan ya sallame su suka fita.

A babban falo suka samu Mamah tana zaune tana ganin Aliyu da Farouk ta harari Farouk tace
"Me kake har yanzu baka tafi ba?"
Kai yai kasa dashi. Aliyu ya kalle shi ya mika masa car key yace
"Keep the bag inside thank you! Take care bye!"

Ya fada yana durkusawa yace
"Ina kwana Mamah!"
Ba tare da ta kalle shi ba tace
"Lafiya lou!"
Ta mike ya fice Farouk ma fita yayi amman bai tafi ba ya tsaya a wajen motar sa.



*Alla jikan musulmai ya kyautata namu zuwa Amin.*

*Antty*


💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 42

By
*MARYAM S INDABAWA*
Hakuri da Juriyya Online ✍
HAJOW

*Bismillahir Rahmanir Rahmin*

Stair ya nufa yana tasbihi har ya karasa kofar dakin Mami. Knocking yayi ta bashi izinin shiga sannan ya shiga. Tana zaune a gefen gadon ta ya karasa ya zauna akan center carpet din dakin sannan ya zame hular kansa. Hannun ta ta daura akan sa tai masa addu'a sannan ta dago tana kallon sa.
"Ina kwana Mami?"

"Lafiya lou! Ya kake ya aiki?"
"Alhamdulillah!"

"Ya Ummin naka da me jiki?"
"Da sauki!"

"Masha Allah!"
Kai yai kasa dashi sannan yace
"Mami ni zan tafi!"

"To Allah tsare yai albarka ya kare a kula a kiyaye aiki da neman halak duk inda haram take ka guje ta dan abinda zata kara maka,  sharri ne tare da ita halak kuwa duk kan kantar ta zaka same ta da albarka a cikin ta. Allah tsare!"
"Amin Mami nagode! Sai na dawo!"
Sannan ya mike Mami ma ta mike tare suka fito suka samu Mamah a falo ya nufi kofa ita kuma Mami tayi sashen Abbi.

Daga nan parking lot ɗinsu mai ɗan karen girma da kyau, duk zagaye suke da fulawowi masu kyau. Ya nufa,  Wasu tsala-tsalan motocine da a ƙalla sun kai su takwas sai sheƙi sukeyi. Wajen wacce zai shiga ya nufa blue black ce sai sheki take ya nufi ta ya sa hannu zai bude Farouk dake cike ya bude kallon sa ya tsaya.

Ya fito yana murmushi yace
"Na jira ka fito mu tafi ne!"
Ya bashi hanya ya shiga ya rufe masa kofa. Glass yai kasa dashi wanda yake tint yace
"Me kake so?"

Kai ya shafa yace
"Ba komai Hamma!"
"Kai dai!"

"Please Hamma motar ka dayar nan nake so tinda naga ka daina hawan ta!"
"Wacce a ciki?"

"Red colour din!"
"Ok key din yana clinic in naje zan dauko maka yayi maka?"
"Yes Hamma na godiya nake Allah saka da alheri ya kara budi!"

"Amin! Ka kiyaye kaji abinda Abbi dai ya fada Allah tsare!"
"Amin Hamma Allah tsare hanya!"

Ya daga kai yana fadin
"Amin!"
Sannan ya tada motar Farouk sai da yaga ya fita sannan ya nufi motar sa ya shiga yabi bayan sa.

Cikin nutsuwa yake driving yana yi yana tsabihi da addu'ar tsari a haka har ya karasa babban asibitin da yake aiki. A cikin rumfar adana motor da aka rubuta Dr Aliyu Suleiman a samanta anan yai parking sai da ya dauki minti sama da goma sanna ya bude murfin motar, a hankali ya zuro ƙafafunshi ya fito. Wani massenger sa ne ya karaso da sauri car key din ya bashi ya bude ya dauko system din sa da wayoyin sa. Cikin nutsuwa ya fara taku yana ratsowa cikin farfajiyar Hospital ɗin.

A nutse yake tafiya massenger sa na take masa baya har suka shiga cikin asibitin gaba ɗaya Nurses ɗin dake ƙoƙarin fitowa sunyi maza suka koma baya, tare da rusunawa suka haɗa baki wurin cewa.
"Barka da hantsi Dr A.S"
Kai kawai ya gyaɗa musu yaci gaba da tafiya, tafiya mai tsayi yayi ya shiga  cikin wani ɗan corridor dake gefen daman sa  wanda shi zai sadashi da office din sa.

Yana zuwa bakin office din ya tsaya da sauri messenger dake biye dashi rike da jakar system din sa ya karaso ya bude masa. Da Sallama hadi da bismillah ya saka kafar sa ta dama cikin office din. Ajiyan zuciya yaja a hankali saboda ɗan karen ƙamshin da ya ziyarci hancinta, Office din ya hadu iya haduwa kai ba ka ce a cikin asibiti kake ba dan tsaruwa da kyau da tsabtar sa.

Yana shiga Office dinshi, ya nufi kan katon table din dake gaban sa wanda ya ke katon gaske zama yayi messenger ya ajiye masa bag da wayoyin sa. Budewa yayi ya dauko ta ya kunna ya fara aikin daya kawoshi. Bayan minti na ya dago ya kalli agogon hannun sa har goma da rabi, messenger dake tsaye yace
"Hassan Abubakar shine first call him!"
Ya juya ya fita ba a jima ba patient din ya shigo cikin mutunci da girmamawa suka gaisa sannan ya duba shi ya sallame shi.

Haka ya duba mutane biyar da sukai booking ganin sa wanda lokacin ya kai masa karfe daya wanda daya yake tashi dan yaje yai sallah kan ya dawo ya cigaba da aiki. Alwala ya shiga yayi ya fito ya nufi masallaci daya da kwata sukai sallah sai daya da rabi ya fito.

Wayar sa ya zaro a aljihu ya kai kunnen sa yace
"Ok kaje gida yanzu ka dauko min wata patient ban son bata lokaci fa."
Ya dauke wayar ya koma office.

Zama yayi yana aiki a system. Karfe biyu da kwata akai knocking dagowa yayi ya kalli kofar sannan ya bada izinin shiga wasu nurses ne guda biyu suka shigo rike da Maryam. Kan gadon dake dakin suka kwantar da ita sannan suka juya suka fita.

Wayar sa ce tai kara ya dauka yace
"Thank you!"
Sannan ya kashe. Gadon ya zubawa ido na wasu dakiku sannan ya karasa a hankali yana zuwa gaban sa yaji wata muguwar faduwa gaba har sai da ya dafe kirjin sa. Ido ya lumshe a hankali ya dago ya kalle ta duk da ba abinda yake gani a tare da ita dan hijab ne har kasa a jikin ta fuskar ta kuma ta rufe da hannun ta.
"Ya sunan ta?"
Ya fada a zuciyar sa, tare da lumshe ido, a hankali ya juya wajen jakar laptop din sa ya bude zip ya dauko folder ta dake ciki. Idon sa ya kai kan sunan ta wanda ya karasa bugun zuciyar sa daduwa.

"Maryam Muhammad Jabeer!"
Ajiyewa yayi a hankali ya karasa yace
"Maryam!"
Ya fada kamar me tsoron yin magana, a hankali ta bude fuskar ta tana kallon sa.

Kan sa na kasa ta fara kokarin mikewa. Juyawa yayi yace
"Zaki iya tashi ki taso!"
Kai ta gyada ya nufi kujerar sa, ita kuma ta mike ta fara tafiya taku daya, biyu, uku, hudu taji jiri na dibar ta neman wajen da zata dafa tayi ta rasa baya tayi zata fadi wanda shi kuma lokacin ya juyo kenan ganin ta a wannan halin yasa cikin zafin nama ya karaso ya taro ta ta fada jikin sa, ninkawa bugun zuciyar sa tayi, wannan yasa yai saurin runtse idon sa da karfi. Maryam kuwa ta riga da ta saddakar kawai waduwa zatai taji ta a jikin mutum kara rike shi tayi kam tana mai da ajiyar zuciya. Ido ya bude a hankali akan fuskar ta. Wacce take fara tas ga ciwo ga rama wanda ba abinda kake gani sai dogon siririn hancin ta da idanun ta da suka zurma a ido rufen ma. Sai lips dinta sirara pink kala.

Ido yai saurin daukewa daga kallon ta sannan a hankali ya karasa gaban table din nasa ya zaunar da ita ya juya ya koma wajen zaman sa. A hankali ta daura kan ta akan table din ta lumshe idon ta.

Shiru yayi yana kallon system din sa bayan kusan minti goma a hankali yai gyaran murya dagowa tayi tana kallon sa da idanun ta da suka rame take jin ciwo har cikin idanun ta dan ita ciwo take ji a ko ina na jikin ta hatta farce yana mata ciwo.

A hankali ya ɗan ɗago ƙwayan idanunshi ya kalleta. Kanta a sunkuye fuskar ta gwanin tausayi dan daga fuska zaka gane tana cikin wani irin yanayi na ciwo, wahala,  da neman taimako

A hankali ya kalli Folder ta dan tsoron ambaton sunan ma yake, idanunshi ya lumshe saboda wani irin bugu da yakeji zuciyarshi yana son Maryam amman meyasa ko me sunan yaji hankalin sa yake kasa kwanciya ji yake ina ma ace ita ce. Sunan na masa kwarjini da wuyar fada.

Kamar me koyon magana yace
"Maryam ko?"
Kai ta gyada kan ta a kasa. Shiru ya karayi can ya mika mata wani memo yace
"Magana zamuyi zaki iya?"

Sai a sannan ta dago ta kalle shi taga yana turo mata memo da pen, kai ta gyada ta amsa. Yace
"Ki fada min gaskiya wacece ke?"
Kallon sa ta tsaya yi. Ya gyada mata kai.

Pen ta dauka shi kuma ya maida ido kan system ya fara danne danne, bayan sakkani ta mika masa. Amsa yayi ya duba
"Bansan ni wacece ba wallahi ban san komai nawa ba bansan kowa nawa ba!"

Ya karanta ya dago ya kalle ta sannan ya mika mata yace
"Kika ce sunan ki Maryam!"
"Eh Sunana Maryam Muhammad Jabeer!"
Ta rubuta masa, kai ya gyada yace
"Tayaya kika san sunan ki?"

"I didn't know!"
Ta bashi amsa a rubuce ya kalle ta yace
"Wa zaki iya tunawa a rayuwar ki!"

Hawaye ne ciki idon ta ta fara rubutu tace
" *Mijin Maryam* miji na kawai zan iya tunawa Yaa Haidar!"
"Where is he?"

"I just didn't know i only know Yaa Haidar as my husband and i loss him from their i can't recall any thing except My Ammi."
Kura mata ido yayi can ya dauke kansa yace
"Ummi na macece mai tausayi da son taimako i hope zaki zauna da ita tsakani da Allah kuma ba zaki cutar da ita ba!"

Kai ta gyada tai masa bayani da hannu kan cewa bazata cutar da ita ba. Ta gode kuma. Kai ya jingina da kujera yace
"Yanzu me yake damun ki?"

"Komai ciwo yake min bana jin dadin komai na rayuwa!"
Ta fada idon ta na cikowa da kwalla. Tausayin ta ne ya kama Aliyu yace
"How old are you?"

"Seventeen year old!"
Tai masa nuni da hannu.
Tausayin ta ya kara ji dan yarinya ce sosai ace tana cikin irin wannan rayuwar ga ciki ba miji and babu iyaye ko wani nata yanzu in da ba Ummi ce ta dauko ta bafa wane hali zata shiga.

Waya ya dauka yai magana da daya daga cikin nurses din sannan ya ajiye wayar ya cigaba da aiki a system din sa. Ba a jina ba akai knocking ya bada izinin shiga nurse ce ta shigo tace
"Gani Dr A.S"

Paper ya zara yai rubutu yace
"Gasu nan wadan nan test din nake so ai mata ina son result din yanzu, wanda ba zai samu yau ba ayi kokari a samar min su gobe."
Amsa tayi ta kalli Maryam dake kwance jikin table din nasa.

Kallon ta yayi yace
"Ko ba zaki iya bane a kawo kujera?"
Kai ta girgiza ta mike a hankali tana cije baki,  nurse din ta kama hannun ta suka fara tafiya a hankali. Da ido ya bisu har suka rufe kofar dakin. Ajiyar zuciya ya sauke yana jingina kan sa da jikin kujera.

Awar su biyu da fita suka dawo da Maryam direct kan gadon dakin ta wuce da ita dan ba karamin galabai ta tayi ba ga zazzabi ga yunwa ga ciwo. Kwanciya tayi, Aliyu yana kallon su sanna Nurse din ta karaso ta mika masa result din amsa yayi ya duba agogon hannun sa 3:52pm lokacin sallah la'asar yayi dan gashi can ana tada harama mikewa yayi ya fita a office din masallaci yaje bayan an idar da sallah ya dawo.

Wayar sa dake aljihun sa ta hau kara zarowa yayi ya tsaya kallon kiran har ya katse sannan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login