Showing 9001 words to 12000 words out of 232912 words
Chapter 4 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
dauka har gidan zan aiko a dauken abu na shikenan ni bazan abun arziki ba ke da son kyale kyale "
"Hajiya Mami."
Anty Asiya ta fada sannan a karasa tace
"Bari naje nasan Abbin Abid sai ya tsaya a main falo."
Ta fita tare suka shigo ya gaishe da Mami sannan ya mike ya fita. Maryam ta dauki ledar Anty Asiya sukai sallama da Mami sannan suka fita.
"Zo muje nayiwa Mama Sallama."
Waje Maryam ta nufa tace
"A'ah je ki fito."
Ta kalle ta, ta dauke kai. Mota ta saka kayan suka tsaya ita da mijin Anty Asiya suna ta hira bata jima ba ta fito suka nufi sashen Ummi dan ya gaishe ta Anty Asiya kuma tai mata sallama. A falo suka same ta suka gaisa yana tambaya ina su Aliyu tace
"Tinda suka tafi sallah kila suna masallaci."
"Tare suke da Abokina kenan."
"Suna tare."
Yace
"To zamu tafi Ummi sai da safe."
"Ku gaida gida ku gaida su Abid."
"Zasuji."
Suka mike suka tafi Anty Asiya ta shiga taiwa Inna sallama. Inna tace
"Yanzu mai gidan naki yazo ya cika ni da alheri kai Allah masa albarka ya kara budi dai."
"Amin Hajiya Inna ina zuba ido fa."
"Zamuzo ai tinda abokiyar fitar tai hutu."
Tai mata sai da safe suka tafi. Har mota ta rakata Abbin Abid ya debi kudi da yawa ya mika mata taki amsa sai da kyar tai godiya sannan suka fita ita kuma ta juya tai bangaren su.
Ummi ta direwa kudin, Ummi tace
"Na menene?"
"Yaya Nazir ne ya bani."
"To madallah angode sai kije ki ajiye."
Zamewa tayi ta kwanta akan cinyar Ummi tace
"Ki ajiyen Ummi."
Ta dauki remote ta canja channel. Suna cikin kallo su Yaa Aliyu suka shigo zama su sukai shida Haidar. Maryam ta gyara kwanciyya tace
"Ummi yaushe Abba zai dawo."
"Kila sai weekend."
Baki ta tura tace
"Yau fa Talata da saura gaskiya."
"Ai kamar yau ne."
"Allah dawo dashi lafiya."
"Amin."
Ummi ta fada ta kalli Aliyu tace
"Abinci fa?"
Dining ya kalla yace
"Yau na gaji ne wallahi."
"Maryam ta zubo muku to."
Shiru yayi wannan yasa Ummi tace
"Zubo musu kinji Daugther."
Ta mike ta zubo musu sannan ta nufi sama tace
"Bari naje na kira Jawahir."
Da kallo ya bita ya dawo da kallo kan abinci suka fara ci shi da Haidar tas suka cinye suka sha lemo da ruwa.
Tana shiga daki ta fada saman gado tare da fadin
"Wash Allah na"
Wayarta, ta janyo ta fara dubawa missed call din Jawahir ta gani har guda biyar kira ta farayi amman sai da ta kusan tsinkewa aka dauka, cikin muryar bacci tace
"Ina kika shiga ina ta kira tin dazu?"
"Wallahi ina kasa badai har kinyi bacci ba?"
"Wallahi ke baki kwanta ba."
"Bana jin bacci ai kece kasa."
"Naji ai bacci duniya ne. Ni sai da safe mayi waya"
"To Allah tashe mu lafiya."
"Amin."
Ta kashe wayar ta mike itama ta shiga ta watsa ruwa tazo ta saka kayan bacci tare da yin sallah.
*
Tsaye take a bakin kofar dakin Inna, sanye da doguwar riga ta material black wanda akai zanen gida gida da fari da maroon, maroon kalar mayafi ta yafa sai cover shoe maroon da hancbag din ta rike a hannun ta, sai dayan hannun da take rike da waya, sai kamshi take, duk da batai kwalliya amman tayi kyau fuskar ta tai fresh alamun tana cikin jin dadi, Inna ce ta fito yafe da mayafi tana rufe kofar dakin nata, sai da ta gama ta karaso tace
"Na tsayar dake ko? Kayan wutar na kashe Kar naje na jawo gobara tinda bama gidan, Ina kuma Haidar din?"
"Yayi can gate."
"To muje."
Ta fada tana daukar ledar dake gefe amsa Maryam tayi Inna tai gaba Maryam na biye da ita a baya. Suna fita compound suka wuce parking space dake can gefen gate.
Haidar suka gani cikin motar Aliyu, Inna tace
"To Ina driver kira sa yazo mu tafi."
Bakin gate ta nufa ta leka ta kira shi, ta karaso tace
"Taho mu tafi Haidar."
"Ina zaku?"
"Gidan Anty Hanna."
"Kuzo na sauke ku."
To kawai tace ta nufi wajen Inna, Inna tace
"Hanasa zuwa yai ko?"
"A'ah wai muje ya Kai mu."
Driver ta kalla tace
"Malam Anas bari muje Aliyu ya dire mu kai zaman ka sai mun dawo."
"To Hajiya Allah kiyaye ya tsare a gaishe su."
Suka nufi wajen motar duk suka shiga baya, motar ya tayar suka dauki hanya gidan Anty Hanna
Wata unguwa suka shiga mai kyau da tsari wanda gidajen manya ne duk layukan ma kwalta ne a kai. Horn yai a wani katon hadadden gida, Mai gadi ya leko yana ganin Aliyu ya hau bude gate sai da ya bude Aliyu ya tura hancin motar cikin gidan ya nufi can gefe yai parking. Yaran gidan jin mota suka fito a guje su hudu ne, suna ganin Inna suka tafi suka rungume ta suna fadin
"Oyoyo Inna."
Ta kama hannun Yar karamar tace
"Takwara ta."
Ta dauke ta. Sauran sukai wajen Maryam suna fadin
"Oyoyo Anty."
Da dai dai ta rumgume su, sannan suka karasa wajen Haidar Baban ne yace
"Lah Uncle."
Yai wajen sa a guje ya karasa yace
"Ina yini Uncle?"
"Lafiya lou Arfat ya school?"
"Alhamdulillah."
Ya shafa kan sa sauran sukazo suka gaishe shi. Ya kalli Maryam yace
"Ni na tafi."
"Bazaka shigo ba"
Kai ya girgiza ya shiga mota. Anty Hanna ce ta fito cikin shigar ta mai kyau tace
"Oyoyo Inna ta."
Ta rumgume Inna, ganin motar Aliyu na reverse yasa ta saki Inna da sauri ta karasa tace
"Yaa Aliyu ba dai tafiya ba."
Ya tsaya, yana sauke glass din motar, ta karasa tace
"Haba ai ka shigo ka sha ko ruwa ne ko?"
"Sauri nake nagode."
"Dan Allah Yaya ka shigo kai fa ba zuwa kake ba kuma yau kazo ai ka shigo mu dan gaisa dan Allah."
"Ok!"
Ya gyara parking lokacin su Inna har sun shige, ya fito sukai cikin gidan tana fadin
"Amman naji dadi wallahi."
Suka shiga main falon wanda yake katon gaske da set din kujeru sun fi set uku, ta Kara dosar wata Kofa yace
"Ki barni nan Hanna."
"Please Yaya."
Yabi bayan ta. Wani hadaden falo suka Kara shiga wanda anan su Inna suka yada zango ta shiga ta nuna masa kujera tana fadin
"Sannu da zuwa."
Tayi kitchen da sauri sai ga masu aikin ta nan dauke da tray tray daya flask ne akai dayan Kuma wasu bowl ne masu murfin glass sai dayan kuma lemuka ne da ruwa da cups da plate and spoon. Anan kasa suka zube kayan suka gaida su Inna sannan suka koma ciki.
Hannah ta fito tana murmushi tare da fadin
"Sannun ku da zuwa."
Ta karasa ta fara zuba masa lemo a cup ta mika masa tace
"Ina yini Yaya?"
"Lafiya lou ya gida da yaran."
Ya fada yana kurbar lemon.
"Alhamdulillah."
Ya kalli Islam mai sunan Inna yace
"Zo nan Yar tsohuwa."
Ta karasa ya dauke ta yarinya ce yar shekara biyu Wanda Haidar ya girme ta da shekara daya. Yace
"Ke bakya magana?"
Hannah tace
"Sai ta sake daku tukkuna."
Ta karasa wajen Inna tace
"Sannu Yar tsohuwa ya hanya?"
Suka gaisa sannan Maryam ta gaishe ta tana tambayar yasu Ummi da Mami. Rabin cup yasha ya ajiye ya mike yace
"Bari na tafi."
Ta karaso tace
"Ah haba Yaya bakacin komai bafa."
"Ke wannan uban kayan da kika dire kadai ya sa mutum taji tsoron cin abinci sai kace wanda mutum hamsin zasuci. Ni na koshi."
"Dan Allah Yaya ka zauna ko cake ne kaci."
Kai ya girgiza ya zura hannu a aljihu ya zaro yan dubu dai dai sababbi fil ya kira Arfat yace
"Ungo."
Ya bashi guda biyar biyar sannan ya bawa Sharifat sai Annuwar da Islam har da Haidar duk suka hada baki su kace
"Mungode Uncle Allah Kara budi."
"Amin."
Ya fita dauke da Islam Haidar na rike da hannun sa, Hannah tabi bayan sa har wajen mota suka karasa ya shiga ya debo kudi masu yawa ya mika mata tace
"Har dani Babban Yaya nagode Allah kara budi. Allah jikan Anty Maryam."
"Amin."
Ya mika mata Islam ya kamo Haidar yace
"Sai Kun dawo kaji my son."
Hannu ya daga masa yace
"A dawo lafiya Abbi."
Ya rufe kofa yai reserve ya nufi gate ya fita hana fita motar mai gidan na karasowa dan haka ya tsaya a bakin gate da sauri Sagir ya fito ya karaso wajen Aliyu yace
"Yau Babban Yaya ne a gidan kenan."
Ya bashi hannu suka gaisa sannan sukai sallama ya koma mota ya wuce shi Kuma ya shiga gida. Yana parking ya nufi cikin gidan a falo ya samu su Inna nan ya zauna suka gaisa aka cigaba da hira da shi dan Sagir ba ruwan sa shi ko da su Mami yaje hira yake musu bare kuma Inna kaka da Maryam kanwa. Su Haidar kuwa suna can ana ta wasu abinsu.
A gidan suka yini sai da sukai magariba suka ci abinci sannan suka fara haramar tafiya har gate duk suka fito dan rakasu. Hannah ta bawa Maryam babbar leda tace
"Ke da Haidar."
Ta bawa Inna wata leda tace
"Nagode sosai Inna Allah kara lafiya da nisan kwana."
"Amin."
Sagir kuwa a envelope ya bawa kowa kudi da kyar suka amsa suka shiga mota drivern gidan ya tafi kai su gida. Suna zuwa gida suka tadda Aliyu ya dawo daga masallaci zai shiga gida.
Tare suka karasa ya dauki Haidar sukai part din Mami, Maryam kuma ta raka Inna sannan ta fito ta koma bangaren su. Ummi ta Sama a falon sama ta Karasa tace
"Yau kuma Ummi kina sama?"
"Gidan duk da Dadi bakwa ban."
"Ya gida?."
"Alhamdulillah."
Ya dire Mata ledar tace
"Anty Hannah ta bani sai Yaa Sagir ya ban wannan."
Ta mika mata, bude ledar tayi turaruka ne sai wasu fashion na dankunne da sarka da agogo da abin hannun sai kaya na Haidar Yaa Sagir kuma 20k ya bata. Ummi tace
"Allah ya saka da alheri, dauki ki kai daki."
"Ummi ki dauki turaren mana."
"A'ah kiyi amfani da abun ki."
Murmushi Maryam tayi ta nufi dakin ta ajiye a kan mudubi ta wuce bandaki ta watsa ruwa ta fito tayi sallah sannan ta fita falo, daga ita sai kayan bacci. Kusa da Ummi ta zauna tace
"Anty Hanna na gaishe ku."
"Muna amsawa. Saura gidan Bilkisu "
Fuska Maryam ta taba. Ummi tace
"Itama fa 'yar uwar kice kuma ba zataji dadi ba in taji kinje gidan su Asiya da Hannah bakije gidan ta ba."
"To Ummi ai kinsan Mama bata so Ina zuwa gidan ta."
"Amman me Abbi yace miki."
Fuska ta tabata, ki daure kije kinji?"
"To Ummi."
"Gidan su Jawahir fa?"
"Ummi nifa ban son zuwa gidan su, gidan su gidan 'yan gwamnati a hanani shiga ma."
"A'ah Maryam ba mai hanaki ki daure kije mata dai ita bini bini tana nan ba ga ita ba, baga mahaifiyar ta ba ga alheri amman ke kinki kije haba Maryam."
"Zan samu naje insha Allahu kan mu koma."
"Allah ya yadda."
"Amin "
Sallamar Aliyu sukaji da sauri Maryam ta mike tai dakin Ummi, Ummi tai murmushi tana amsa sallamar ya karaso ya zauna yace
"Ummi yau kuma ban kika shigo?"
"Eh gidan ba dadi nayi kewar Haidar."
Yai murmushi Haidar ya karasa yqce
"Ummi ki kira min Abba."
"Oh Abba zan kira maka?"
Ya gyada kai ta dauki waya ta kirasa bayan sun gaisa tace
"Wai Haidar ne yace a Kira masa kai."
Abba yai murmushi yace a bashi nan Ummi ta bashi ya dinga ma Abba surutu yace
"Abba yaushe zaka dawo?"
Kwanciyya Maryam tayi a dakin daga haka bacci ya dauke ta. Sai wajen goma Aliyu ya tafi. Daki ta shiga taga Maryam na bacci dan haka ta canjawa Haidar kaya sannan suka wuce dayan dakin suka kwanta.
**
Washe gari Yaa Farouk ya kaita gidan Anty Bilkisu duk yadda Bilkisu ke son Maryam ta sake da ita kamar yadda take sakewa da sauran 'yan uwan nasu, amman bata sakewa sai dai su dan taba hira suna hirar ne tace
"Maryam ki cire yadda Mama ke miki dan Allah ki dauken kamar yadda kika dauki sauran 'yan uwan namu, Ina gani fa ko Najwa da bata kasar kin fi sakewa da ita akai na, Mama tana da matsala amman mahaifiyar mu ce muna hakuri muke da ita ban san me yake damun ta ba sam."
Hannun ta Maryam ta kamo tace
"Haba Anty Bilkisu ni daya na dauke ki da Anty Asiya da Anty Hanna, ki daina damuwa kuma Mama ai uwa tace nima."
"Nagode. Amman meyasa bakya son zuwa da Haidar?"
"Sun fita da Yaa Aliyu ne."
"Shima Yaa Aliyu bai zuwa sai dai mukan yawan yin waya."
"Hmm in dai Yaa Aliyu ne can ma ba zuwa yake ba, ke sai ya kira ma bai kira su ba haka Najwa ke mita kullum tace ita tana wata duniya bai kira sai dai taji suna waya da sitti. "
"Allah sarki ya karatun kuwa?"
"Alhamdulillah sauran kwana biyu ma mu koma."
"Allah taimaka to."
"Amin."
Haka suka dinga Hira har akai la'asar ta kira Yaa Farouk yazo ya dauke ta amman bashi ya zo ba sai bayan magariba. Sukai sallama ta fito ta shiga mota suka dauki hanyar gida
Suna tafe yace
"Yaushe zaki gidan su Jawahir ne?"
"Uhmm Yaya ni ban son irin wadan nan gidajen."
"Saboda me?"
"Gidan 'yan siyasa bana son Ina shige musu"
"Jawahir din?"
Kai ta gyada yace
"Amman ba amana, ita kullum tana gidan ku."
"Nima wata rana zani amman ba yanzu ba."
"To Allah kaimu."
"Amin."
"Me kike so mu siya kan mu koma gida?"
"Ni ba komai."
"Ko furar."
Shiru tai tana murmushi, yace
"Da nama."
Dan hararar sa tayi tace
"Tinda ga kwadayayya ko?"
"A'ah nifa bance ba."
Ya isa wajen da ake ajiye mota yace
"Zaki shiga?"
Kallon wajen tayi ta girgiza kai tace
"A'ah je ka dawo."
"Ok Ina zuwa."
Ya fita, harabar wajen take kalla bai Jima ba ya dawo ya bude mota ya shiga ya tayar suka bar wajen.
Suna shiga gida yai parking ta fita, ya biyo bayan ta, da leda a hannun sa, suna tafiya tana gaba yana bin ta a baya wayar sa ce tai kara yana dubawa yaga Mama ce Ido ya lumshe ya daga kai yana kallon taga inuwar ta ya hango ya kai wayar kunne tace
"Kazo nan."
Wayar ya kashe yace
"Maryam!"
Juyowa tayi, ya mika mata ledar yace
"Gashi sai da safe."
Amsa tayi tana murmushi tace
"Nagode Yaya "
Shima murmushin ya sakar mata ya juya ya nufi sashen su, ba kowa a falo dan haka ya nufi bedroom din da sallama ya shiga amman Mama bata amsa ba, ya zauna yace
"Gani Mama."
Wani kallo ta jefa masa sannan tace
"Menene ma a tsakanin ka da ita?"
"Wa?"
"Waccan yarinyar."
Kai ya sosa yana murmushi yace
"Mama....."
Hannu ta daga masa tace
"Yi min shiru. Nasan me zakace min, to kada ka soma dan wallahi na haramta aure tsakanin ka da wannan shegiyar yarinya ban aminta ba."
"Saboda me Mama?"
"Saboda bana so...."
Ta mike tare da juya masa baya yace
"Mama."
"Fita ka ban waje Farouk."
Ya mike ya zagayo gaban ta yace
"Kiyi hakuri."
Sannan ya fita a dakin. Abbi ya gani a bakin kofa ya juya yabu bayan Abbi har zai wuce Abbi yace
"Zo nan Farouk."
Suka zauna a nan falo yace
"Meyake faruwa?"
"Abbi akan Maryam ne wai dan ta ganmu tare shine take zaton soyayya muke."
"Kai soyayya kuka?"
Kai ya girgiza dan yasan in har Abbi yasan yana son ta to an gama shi kuma baya son tashin hankali. Abbi yace
"Maryam 'yar uwar kace dan haka ka cigaba da kyautata mata, kada ka soma nuna musu bambamci tsakanin ta dasu Aisya."
Kai Farouk ya gyada, Abbai yace
"Tashi kaje."
Ya mike yace
"Sai da safe.
Dakin sa ya shiga ya fada saman gado yana tunanin me Mama take yi ne.
Maryam na shiga ta ajiye ledar hannun ta da wacce 'Farouk ya siya mata da wacce Anty Bilkisu ta bata, Ummi tace
"Daughter 'yar gata 'yan uwan ta."
Murmushi tayi tace
"Alhamdulillah Ummi, ni kai na shaidace suna sona nima ina son su, ina kewar 'yar uwa Najwa."
"Ai fa kila so take sai ta gama sannan ta dawo gaba daya."
"To sitti fa?"
"Wannan Yayan ku zaki tambaya."
"Uhmmm."
Ta mike ta dauko plate, zuba naman tayi ta dauki robar fura daya ta fara sha tana Santi, naman ma kadan taci sai furar da ta sha sosai Ummi taci itama sannan ta wuce sama tai wanka tare da alwala tai sallah ta kwanta.
A haka suka fara shirye shiryen komawa makaranta. Ranar lahadi tana zaune bayan ta tsefe kan ta, saloon take so taje a wanke mata dan tasan in ta koma makaranta ba lokaci ne da ita ba.
Saukowa tai daga bene sanye da doguwar riga abaya baka sai mayafin ta, da ta yafa tace
"Ummi zan tafi."
Ummi dake zaune ta dago tace
"To amman za ai miki kitson ko?"
Fuska ta bata tace
"Ummi wallahi zafi kitson."
"Sai kizo kina damuna da in miki calba ko?"
"Ummi itama da zafi fa kike min."
"Oh da zafi nake miki ko to ban sakewa."
Jikin Ummi ta kwanra tace
"A'ah Ummi kiyi hakuri wasa nake."
"Shikenan sai kin dawo, na miki transfer kudin."
Sumbatar Ummi tayi a kumatu tace
"Nagode Ummi Allah Kara budi."
Tai mata murmushi ta fita, tana fita ta nufi wajen motar su, Baba Anas ya karaso yana fadin
"Kin fito?"
Kai ta gyada tace
"Kayi hakuri na barka kana ta jira ko?"
"Ah ba komai Hajiya."
" 'yar ka dai Baba."
Yace
"To 'ya ta."
Ta budi baya ta shiga, wata mota ce ya faka a gefen su, Baba Anas ya shiga dai dai fitowar ta, da sauri Maryam ta dakatar da Baba Anas dake niyyar tada motar tace....
*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*
*Antty*
[10/23, 14:06] Maryam S Indabawaπ₯°: ο»Ώο»Ώο»Ώππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 4
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
βπ»βπ»βπ»
πππππππ
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ta budi baya ta shiga, wata mota ce ya faka a gefen su, Baba Anas ya shiga dai dai fitowar ta, da sauri Maryam ta dakatar da Baba Anas dake niyyar tada motar tana fadin
"Baba Anas tsaya kaga Jawahir."
Ya dakatar da driving din yace
"Ban lura da ita ba."
"Ba komai."
Ta fada tana bude motar, Jawahir da har ta Isa bakin kofa tajiyo Maryam na kiran ta da sauri ta juyo, ganin Maryam ta dan hade rai tace
"Nifa ba wajen ki na zo ba."
"Ah haba Sister ta."
Kai ta dauke sukai ciki tace
"To me nayi ne wai."
Ummi dake ciki tace
"Baki tafi ba Daughter?"
Ganin Jawahir yasa tace
"Ah Jawahir ce sannu da zuwa."
Kan Jawahir a kasa ta karasa ciki tace
"Wallahi Ummi."
Ta karasa ta zauna a kasa tana gaishe da Ummi, Ummi ta amsa tace
"Koma sama ki zauna."
Ta mike ta koma Maryam ta kawo mata lemo da ruwa ta dan harare tace
"Nifa wajen Ummi nazo ba wajen ki ba."
Ummi tace
"Ai kuwa dai."
"Haba Ummi ki sa baki ai nayi niyyar zuwa fa ni ranar me ma ya faru?"
"Uhmm ke kika sani "
Ummi tace
"Ina Momyn taki!"
"Tana gida tace a gaishe ki."
Zama Maryam tayi tace
"Allah yayi ba zamuyi sabani ba."
"To Ina ruwa na ko munyi sabanin ma ai ba wajen ki na zo ba. Ina Haidar?"
"Yana wajen Yaa Aliyu."
Maryam ta bata amsa sannan ta kalli Jawahir tace
"Gobe sai school ko?"
Share ta tayi, Ummi