Showing 210001 words to 213000 words out of 232912 words
Chapter 71 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
so."
"Ni zaki ci?"
Kai ta gyada yace
"Taso na fara ciyar dake daga baya zaki cini har ki gaji"
Hannu ta sa ta rufe fuskar ta tace
"Ni fa ba haka nake nufi ba Honey yau na gaji sosai na jima ban shiga school ba sai naji abun daban."
Ya kamo hannun ta yana fadin
"Zo muci abinci sai nai massaging din ki."
Haka ya sauko da ita yana binta da wani sihirtattacen kallo a haka sukaci suka koshi, yana jikin ta ta gama wanke wanke suka fito sukai daki, kwanciyya tayi yana mata tausa tare da mata hira mai dadi a haka ya fara sauya salon hirar tashi wanda Maryam ta bashi hadin kai har suka faranta ran junan su.
Bayan wata hudu
A ciki wata hudun nan abubuwa da yawa ya faru, wanda a lokacin Aisha ta haihu an samu namiji Yaa Alkasin ya saka masa suna Haidar, wanda bikin Rukayya da Yaa Ahmad ya rage wata biyu, sai Najwa dake turawa da kyar da tsohon cikin ta yau ko gobe.
Rayuwar Maryam da Yaa Haidar rayuwa ce da suke yin ta cikin fahimtar juna da kaunar juna, Maryam akwai sanyin hali da hakuri, wanda Yaa Haidar ma akwai kawar da kai, a cikin wata hudun nan ba wani abu na bacin rai da ya taba gilma musu dan da daya yace daya yai masa abu a take zasu bawa junan su hakuri, basa taba kaura daga junan su basa taba raba wajen baccin su, su Mami, Ummi da kowa mamakin Aliyu suke domin Aliyu ya canja sosai a gaban kowa kula yake da matar sa, tare da tarairayar ta har mamakin Aliyu suke dan ko lokacin marigaiya matar sa bai mata haka ba wani so yakewa Maryam kamar ya maida ta cikin sa, soyayya suke zubawa wacce samun irin masoyan yake da wahalar samu, gaba daya sun gama macewa akan son junan su, sun yadda sun aminta soyayyar su daga Allah ce dan yadda suke son junan su sukan su har mamaki suke, Aliyu har mamaki yake bama a bangaren nuna kulawa soyayya ko rayuwar aure a baya sai ya kwashe sati biyu bai nemi matar sa ba amman a yanzu dakyar yake iya kyale Maryam ta yini ba tare da yaji sa a jikin ta yana shan ni'imar ta, wanda Ummi da kanta ta gane yadda Yaa Haidar ke matsa mata dan ko gida suka zo yini sai yasan yadda yayi ya lallatse ta ko ya tsotse a barsa, wannan yasa kullun take kara wayar da kan Maryam, ga kuma yan uwanta da kullum nasiha da bata hanyoyin kula da kanta da mai gidan ta yake, ta zama yar gata kowa ta tatta yake. A lokacin har sunyi semester daya sauran daya su gama karatun su, kuma auren sam bai bata matsala ba dan lokaci guda suka ware Yaa Haidar na koya mata karatu sam bata da matsala ga practical da wani lokacin in yana da aikin weekend take bin sa asibiti, kowa yaga Maryam da Aliyu sai sun burge ka tare da baka sha'awa. Likitocin asibiti masu harin Aliyu kuwa suna ganin Maryam cllasic lady suke raina kan su, dan bata da makusa ko kadan ga kyau ilimi da tarbiyya da nutsuwa kowa yaga Maryam da Aliyu sai sun burge shi sosai suka dace da junan.
Maryam takara kyau tai haske ga jikin ta ba rama tai kubulbul da ita duk da ba kiba tai ba amman jikin ta ya murje kowa ya ganta sai ya so kara ganin ta haka Yaa Haidar ya kara kyau da cika kamar ba shi ba jin dadi da kula sun zauna masa arziki ya dada gaba rayuwar farin ciki mai cike da sha'awa suke gudanarwa.
Duk wannan tsawon lokacin kullum shike kai ta makaranta ya dauko ta ko da bai gama aikin ba wata rana asibiti suke komawa ta zauna a office shi kuma yana aiki duk dagowa daya da zai sai ya sumbace ta ko ya rumgume a bar sa.
*
Zaune take a dakin Haidar karami dan yau gidan Ummi suka zo suka yinar mata, Haidar ne kwance akan cinyar ta, sumar kansa take shafawa tana mai jin soyayyar yaron a cikin zuciyar ta, kamar an tsikare shi ya mike ya nufi wardrobe da kallp ta bishi, har ya dauko abu ya dawo ya zauna a gefen ta yana fadin
"Adda kinga."
Dagowa tayi tana kallon abinda yake nuna mata, picture din Yaa Haidar ne wanda ba zata manta ba tin a gida da sukaje ya dauka, wanda har yanzu yake kallon picture din, kusan kullum sai ya dauko ya kalli Abbin nasa, bai san sa ba amman yanajin son sa sosai da sosai duk da karancin shekarun sa, baya fasa yiwa mahaifin nasa addu'a, bama da Maryam ta kasance na sashi yana yiwa mamata addu'a.
"Adda kullum na duba mudubi sai naga muna kama da Abbi na, Adda har wannan abun fa."
Ya fada yana nuna kumatun sa alamar dimple.
"Adda."
Ya katse mata tunani, kallon sa tayi yace
"Adda da wannan Abbin nawa da Abbi na suna kama suma yan uwa ne?"
Murmushi ta saki tana shafa kansa, yace
"Adda ina son Abbi na dukka, Adda yaushe zani wajen Abbi na wannan?"
Picturen ta karba ta kalla sannan ta mika masa tace
"Haidar kana cigaba da yiwa Abbin ka addu'a a ko da yaushe, Abbin ka yana son ka, yana son ka tin bai san da kai ba, yana son ka tin baka zo duniya ba dan haka kaima ka so shi, soyayyar da zaka nuna masa kenan yi masa addu'a, ko da Abbin ka ba uba ne gareka ba, to Yayan mu ne, kuma yana son mu, bai son kukan mu. Kasan me?"
Kai ya girgiza, rumgume shi tayi tace
"Abbin ka ya kula dani tin ban kai ka ba."
Dagowa yai yana kallon ta, kai ta gyada masa tace
"A lokacin shi ke kaini makaranta da siya min kayan dadi kamar yadda Abbin ka ke maka."
Murmushi ya saki yace
"Adda ashe shima yana da kirki, shiyasa nake son sa Adda."
Rumgume shi tayi tace
"Yauwah my boy ka cigaba da son Abbin ka kaji, kana masa addu'a kaji kada ka taba mantawa da shi, kasan menene sakon sa a kullum gareka?"
Kai ya girgiza yana kara lafewa a jikin ta,
"Cewa yake kullum ki fadawa Ya'yan mu, ina son su, ki fada musu Abbin su na son su da kaunar su, mutumin da ke son ka tin kan kazo duniya shi kuma baya nan me za kai masa?"
"Addu'a Adda, Allah masa rahma yasa yana aljanna, Allah ya hadamu a aljanna gaba daya."
"Amin Amin Haidar."
"Adda kika ce tin kina karama yake siya miki kayan dadi da kai ki school?"
"Yes Haidar."
"Lallai shima he is kind like my Abbi ko?"
"That is why i love him Adda, i love you and My Abbi's."
"We love you too Habiby."
"Adda ki cigaba da bani labarin Abbi na kinji."
"To Haidar."
Ta fada tana jin wani abu a kasan zuciyar ta, hakika sai yanzu ta kara sanin mutuwa yankan kauna gareta, in ba da ba haka ba da tini ita da yaron ta da mijin ta suna tare, dan hawayen da ya zubo mata ta goge ta cigaba da bashi labari tana bashi yana mata tambaya shi kadai sai murmushi yake kamar yana gane komai da take fada masa.
A haka Yaa Haidar ya shigo ya same su, ya tsaya yana kallon su, cike da so da kauna, jin son su yake har cikin zuciyar sa, bama Haidar jin sa yake tamkar d'an sa yana son yaron yana tausayin sa shiyasa yai alkawarin kula dashi har karshen rayuwar sa kuma yai alkawarin ba zai taba nuna bambamcin ba ko da Allah zai bashi ya'ya.
Karasowa yayi ya zauna a gefen Maryam tare da rumgume su gaba daya sai a sannan suka san da shigowar sa, ta dago tana kallon su, ya sakar masa kiss a idanun ta yace
"Mu tafi ko?"
Kai ta gyada tana kara rumgume Haidar, dan wani iri taji a kasan zuciyar ta, ya amshi Haidar yace
"Mu tafi tare?"
Kai ya gyada ya dauke shi ya sauka a gadon, ya kalli Maryam dake zaune cike da damuwa yace
"Taso mana."
Ya fada yana mika mata hannu, kamowa tayi ta mike, Ummi suka sama a falo, ta kalle su tace
"Daman ai nasan yau sai kun dauke d'anku."
Kai Maryam tai kasa dashi tana murmushin yake, ta zauna tana fadin
"Ummi ni ba ruwa na Yaya ne fa yace mu tafi dashi."
"Sai kuje ai, Haidar tafiya zakai ka barni ko?"
Kai ya girgiza yace
"Ummi kwana biyu zanyi."
Ya fada yana nuna mata da yatsun sa guda biyu, tai murmushi tace
"To amana a kular min da yaro na."
"Insha Allah."
Suka fada sannan sukai mata sallama suka tafi, dan da kayan sa a can gidan.
*Ehemm ehemm, kamar yadda jiya ma na fada yau ma zan kara fada dan jiya naga comment sosai shiyasa nayi shafi na biyun, to yau ma zan gani in har yanzu ana son *Matar Haidar* in kuma ba a so ma zan gani. Bye see u later amman fa in naga comment, in kuma ban gani ba sai gobe in Allah ya kaimu.*
*Samira Malami, Amina Yar'addua, Aina'un Mardiyya, Zuwaira Zuzu, Ubaidah da sauransu i really appreciate, much love*
*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe Amin*
*Antty*
[12/11, 18:21] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 84
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Kan su shiga gida har Haidar yai bacci suna zuwa ta kai shi d'aki ta canja masa kaya tare da masa addu'a, bandaki ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci, tana shirin kwanciyya ya shigo yana fadin
"Me nake gani haka?"
Ya iso ya dauke ta yana fadin
"Wai me yake damun ki ne?"
Ya fada yana ajiye ta akan gado, idon ta ne ya kawo ruwa, yace
"Ba zan taba kishi da Yaa Haidar ba Maryam, amman wallahi in na ganki a damuwar ni kadai nasan me nake ji dan Allah ki fada min da me kike tina shi ni kuma in maye gurbin hakan."
Murmushi ta saki tace
"Yaya na i love u the way u re, a kullum in zan tuna da Yaa Haidar sai na tina da kai dan sanadin ka na ke raye cikin jin dadi, in Yaa Haidar ya kula dani a baya yanzu kai ke kulawa dani, in Yaa Haidar ya soni a baya yanzu kai ke so na, in na kasance da Yaa Haidar a da yanzu da kai nake tare, ka mayewa Haidar gurbin sa, dan haka ka sani kai kadai ke zuciya ta da tunani na dole na tina Yaa Haidar Yaya amman ba haka zai sa nace bana son ka ba, ina son ka, kuma in na tuna shin addu'a nake masa, please Yaya kada kai fushi ko kaji haushin sa akan haka, yau Haidar karami ya tina min da Abbin sa, kuma na kara sauke mata wani nauyi dake kaina, kai min alfarmar ko ya'ya muka haifa zamu sa musu soyayyar Yaa Haidar, dan suna masa addu'a saboda abinda yake so kenan."
"Ya'yan mu na Yaa Haidar ne Maryam, kamar yadda Haidar yake nima 'dan na, dan haka na miki wannan alfarmar kuma nima zan kasance cikin masa addu'a Allah masa rahma ya kyautata namu zuwan."
"Amin My honey."
Ta fada tana shigewa jikin sa.
Rumgume ta yayi tsam a jikin sa kamar zai mai data cikin sa yace
"In nace nafi Yaa Haidar son ki zaki yadda?"
Kai ta dago tana kallon cikin idon sa, wanda ba abinda take gani sai tsantsar son ta, ido ta lumshe tace
"Ba Yaa Haidar Yaya dole kai ne me sona a yanzu fiye da kowa, ni na isa na karyata Yaya na bayan baka taba batan rai ba kullum kula kake bani kamar 'yar sa, abinda Innan Abbi na ta fada kenan nake ganin ta fada ne kawai cewar ina dacen masoya a lokacin ban san da gaske take ba sai a yanzu nake gaskatawa, hakika nagode Allah da ya jarrabcen ya kuma bani ikon cinye jarabawar har yai min canji da mafi alheri, Allah ya jikan Yaa Haidar, ya barni da kai har a aljanna Yaa Haidar, ina son ka ina kaunar ka kuma na yadda da duk soyayyar ka."
Idon ta cikin nasa take maganar nan wanda yaji son ta da kaunar ta na kara ninkuwa a cikin zuciyar sa, goshin sa ya hade da nata inda hancin su ke gugar juna, ya kara yin kasa da fuskar sa bakin su ya hade da na juna, wani irin kiss yake bata mai ma'anoni da manufa da yawa, a haka ya cigaba da romancing nata tare da faranta ran juna su kamar ba ita ba ta zage suna shan soyayyar su.
*
Washe gari da safe, sam sun manta da Haidar baccin su suka hau yi, wanda Haidar ya farka wajen takwas, da kan sa yai brush ya fito falo, ya kunna kayan kallo ya kai mbc 3 ya zauna yana kallon cartoon, da yaji yunwa ya shiga kitchen ya nufi store ya dauko fresh yoo da biskit ya dawo ya zauna yaci ya koshi daga haka ya cigaba da kallon sa, wanda bai san lokacin da bacci ya dauke shi ba, sai karfe goma suka farka, wanka sukai suka shirya sai da ta zata bude kofa ta tuno da Haidar karami da sauri ta fita ana fadin
"Honey mun manta da Haidar."
Ya fito da sauri yana fadin
"Kuma ya tashi?"
Suka fita a falo suka same shi yana bacci gefen sa robar fresh yoo da ledar biskit din da yaci, karasawa Yaa Haidar yayi ya dago Haidar yana rumgumewa Maryam ta nufi kitchen dan hada musu breakfast. Sai da ta gama suka zo ta je ta karai masa brush suka karya, a jikin su ya yini daga ya fada jikin wannan sai na wannan, da yamma Yaa Haidar ya dauke su suka je park, wanda daga can suka shige wani reaturant acan sukai dinner daga nan store sukaje sukai shopping sannan suka koma gida, haka the next day ma da yamma suka fita zaga gari sai dare suka dawo.
Washe gari Monday suka shirya suka tafi aiki, bayan sun ajiye Haidar a makaranta, sai yamma Yaa haidar ya dauko Haidar sannan suka wuce suka dauki Maryam daga school, satin sa daya yace wajen Ummi zai koma wannan yasa suka mai dashi.
*
Yau sai shida zasu fito daga lecture wannan yasa tin kafin su shiga karfe hudu ta kira shi, lokacin fitowar sa kenan daga treater ya ji kiran nata dauka yayi yana fadin
"My Baby."
"Uhmm i miss you Honey."
Wani sihirtacen murmushi ya saki yace
"I miss you more ko nazo na dauke ki muje gida mu rage gajiyar dake tare da mu."
"Da kuwa naji dadi."
"Karatun fa."
"Uhmmm Allah yaya na fara gajiya da ba dan burin ka bane da tini na ajiye shi na zauna na rumgume miji na ina samun lada, amman Honey kalla fa kaga yau tin safe har shida ban kara saka ka a ido na ba ban jini a jikin ka a uhmm uhmm ni wallahi i miss you Honey."
Ta karashe maganar da sakin kukan shagwaba, da kyar ya iya bude office din sa ya shiga ya fada samman kujerar dake office din tare da sakin wata irin ajiyar zuciya ido ya lumshe hannunsa d'aya cikin sumar kansa, yana jin yadda tsigar jikin sa ke tashi na kukan da Maryam take masa wanda ba hawaye sai tsabar tsokana da son tada masa da hankali, A hankali cikin laushin murya ya kirata
"My Noor!"
"Uhmm Honey!"
Tai maganar cikin zallar shagwaba, kina so nazo makarantar yanzu ko? Kin tadan hankali na ba abinda nake so sai kasancewa dake gashi na bada appointment da wani Babban mutum zai zo karfe biyar kina so na taho ne?"
Ashagwabe tace
"No honey amman ka sani i miss you so much."
"Na sani Baby nima haka baki ji jiki na ba duk ba dadi na rashin ki, gaskiya in ba a canja muku wannan lecture ba zan na zuwa ina dauke matata sai na dawo da ita four din."
"Uhmm"
Ta sauke masa wani nunfashi duk da ba sa tare sai da ya sagar masa da jiki yace
"Baby am sorry kinji sauran watanni mu huta ko?"
A shagabe tace
"Eh Honey i love you i miss you."
"Miss you more me kika ci?"
"Bana jin yunwa."
"Hmmm ban yadda ba kije kici abinci yanzun nan kan ku fito zan zo daukar ki kan six kinji?"
"Yes honey bye."
"Bye."
*
Karfe biyar da rabi ya gama da asibiti, gida ya nufa cikin hanzari so yake kan six din ya karasa wajen Maryam.
Karfe biyar da arba'in ya iso k'ofar gidansu ya fito a gaggauce ya shiga gidan yai bangaren Mami a tattsaye suka gaisa sannan ya fito yai bangaren Ummi.
Lokacin daya shiga falon ba kowa, yana sallama kai tsaye ya nufi stair amman motsin Ummi da ya jiyo a kitchen yasa ya juya ya nufi kitchen din, a gaban sink ya gano ta tana wanke wanke kitchen din ya dumame da kamshi.
"Ummi nah."
Ya fada yana karasawa tare da amsa abin da take dauraye wa ya karasa wanke wa, tace
"Dr ya kake ya gida? Ina daughter?"
Murmushi ya saki yace
“Lafiya lou Ummi, Baby fa Ummi tin safe dana fita daga gida ban k'ara komawa ba yanzu nan ne ma zanje na dauko ta yau six zasu fito, Ummi nasan ta gaji ba abinda zata iya in mun koma shiyasa nazo na amsar mana abincin Ummi."
“Allah sarki My Daugther, Allah muku albarka, ai kune kunki mai aiki da kan ku koma ta rage mata wani aikin, yanzu ace kan ta fita sai tayi aiki, sannan ta dawo ace sai tayi aiki? Gaskiya dai Aliyu dole a samar mata mai aiki."
Ta fada tana nufar wajen kwanukan ta dauko flask ta fara zuba masa abincin da tayi, vegetables rice tayi sai miyar da taji kaji sai hadin salad da zobo da ya sha kankana ta zuba a basket tana fadin
"Gashi nan maza kaje dan shida saura kada tai ta jiran ka."
Amsa yayi yace
"Thank you so much Ummi, we really love you."
"Maza jeka Allah muku albarka."
Ya juya har ya kai kofa ya juyo yace
"Ummi My Son fa?"
"Nasan suna hanya shima."
"Agaishe shi zamu zo mu dauke shi yai mana weekend."
"Ba inda zashi kuna barin sa da yunwa bakwa tashi da wuri in kaga yazo to sai na