Showing 33001 words to 36000 words out of 232912 words

Chapter 12 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1275

yai murmushi yace
"Ke kam kin cika cikakkiyar bafulatana kina da kunya da yawa, any way zan iya tafiya?"

Kai ta gyada yace
"To ki gaida min da Ummi and please kina shan magani da hutawa, kiji?"
Murmushi tayi ya mike itama ta mike suka fita daga dakin, ya kalle ta yace
"Ki koma ciki."

"Bari dai na karasa dakai waje, kafata duk tai tsami."
Ya kalle ta yace
"Ai da kinyi magana na matsa miki kafaffun."

Ido ta zaro tana girgiza kai yace
"Ko Jawahir zan aiko tai miki?"
"A'ah nagode."

A bakin kofa ta tsaya shima ya juyo yana kallon ta, tace
"Naji dadi sosai da ziyara nagode."
"Kar ki damu ai hakki nane."

Tai murnushi yace
"Ki koma kije ki huta Allah kara sauki."
"Amin nagode."

Yace
"Ki koma mana."
Tace
"Kai dai kaje."

Juyawa yai ya nufi motar sa, sai da ya isa jikin motar sannan ya juyo kai ta langwabe ya daga mata hannu yana mata bye bye, ta sakar masa murmushi dai dai danno kan motar Aliyu, dauke kai tayi da sauri, ta maida kallon ta kan Muhammad da ya kafeta da manyan idanuwansa, murya can kasa yace
"I love you."

Fuska ta rufe da hannu, dawowa yai wajen ta yace
"I have always loved you from day 1, ranar da na fara ganin kin nan, ranar dai da ba a yadda dani ba,"

kasa kallonsa tayi dan in ta tuna itama abun kunya yake bata ga gaban ta dake faduwa ganin Aliyu ya karaso gate, ganin hankalin ta baya wajen yasa yace
"Bari naje sai munyi waya."
"To nagode."

Ta fada tana juyawa dan shiga gate amman yadda gabanta ke faduwa yasa har jikinta ya fara rawa, a parking space ta hange sa kai ta dauke tana satan kallon sa ta gefen ido, shima ita ya bi ta da ido fuskarsa dauke da wani yanayi da ta kasa fahimta, ganin ya baro wajen da yake yasa ta fara sauri tana waiwaye bata ankara ba tai tuntube ta fadi, kafar ta rike tana yarfe hannu dan akan gwiwar ta, ta dira da sauri ya karaso yana fadin
"Kina tafiya kin wai waye ba dole ki fadi ba."

Hawaye ne ya hau zubo mata, ta fara yarfa hannu tana fadin
"Wayoo kafata."
"Sannu me take miki?"

Ya kalli gwiwar ta da ta gurje ya janye hannun ta, jini ya gani a jikin siket din, cikin tashin hankali yace
"Subhanallah sannu tashi mu karasa ciki sai nai miki dressing."

Mikewa ta fara kokarin yi ya taimaka mata, tana taka kafar ta durkushe tana hawaye ya dago ta yace
"Sannu taka a hankali."
Tana kara takawa ta saki kara, ya kalle ta yace
"Ba zaki iya tafiya ba?"

Hannu ta hau yarfewa hawaye na zubo mata tace
"Yaya zafi wayoo kafata......"
Bata rufe baki ba sai ji tayi ya dauke ta gaba daya da sauri ta kamkame sa dan ji tayi kamar zata fadi a haka ya fara tafiya da ita, a falo suka samu Ummi tana ganin su ta mike tana fadin
"Subhanallah me kuma ya faru?"

"Faduwa tayi."
Ya fada yana ajiye ta akan kujera, Ummi tace
"Faduwa kuma a garin yaya?"

"Rashin kallon gaba sai kace yarinya."
Ya mike ya shiga daki, Ummi ta kalle ta tace
"Garin Yaya?"

"Ban lura ba nai tuntube shine na fadi."
"To sannu."

Aliyu ne ya fito daga dakin sa rike da first aid box Maryam na gani ta tsorata tini idon ta ya fara kaduwa, ya ajiye ya dage siket din farar kafar ta ta bayyana, ido ya runtse da sauri yana kau da kai, ya bude ya dauko spirit da cotton wool, ya bude ya dangwala ya goge wajen cikin sauri yai mata dressing din ya mike yana fadin
"Kila bugewa ki kai. Ungo wannan ki shafa zata sake."

Ya mika mata wani kwalba, yana bata ya bar wajen, da kallo suka bisa, sai kuma ta dauki kwalbar ta bude ta lakuta ta shafa a kafar, tana gamawa ta mike tana dingishi, Ummi tace
"Zaki iya?"

Kai ta gyada mata tayi sama, tana shiga ta fada saman gado ta kwanta tana murmushi, juyi tayi tace
"Nima na iya wayyo ai."


*
Saukowa take daga bene tana danna waya, dagowar da zatai taga Aliyu na kallon ta, kai ta dauke ta cigaba da saukowa tana yamutsa fuska tana gama sauka ta fara dingisa kafa, da kallo ya dinga bin ta har ta karaso yace
"Har yanzu kafar bai saki ba?"
Kai ta gyada yace
"Ko targade kikayi ne?"

Kai ta girgiza tace
"A'ah."
Kallon ta yayi tai saurin yin kasa da ido yace
"Tayaya kika san ba targade bane."

"Ai naji ya rage zafin ba kamar dazu ba."
"Ok ki cigaba da tafiya bakya kallon gabanki, gobe daga benen ma zaki fado."
Yana fada ya fice ta murguda baki tace
"In kai zaka turo ni ba."
Ta cigaba da tafiyar ta normal ba dingishin.


Monday suka koma makaranta amman bataje ba, saboda bata gama warwarewa ba har lokacin ba karfi a jikin ta sosai gashi bata samun bacci sosai da dare sai da safe ta fiya yi shima in Aliyu ya takura mata tasha magani sannan ne take yi. Jawahir duk ta damu bama da take zuwa makaranta ba kawar tata.

Maryam tana kwace a falo kan three sitter, kallo take taji ana knocking mikewa tayi ta nufi kofar ta bude, Jawahir ta gani tsaye bakin kofar ta saki murmushi tace
"Sister."

"Na'am jiki yai sauki kenan?"
Kai ta gyada tana fadin
"Bismillah."
Suka shiga Maryam ta karasa firij ta dauko mata lemo da ruwa ta ajiye tace
"Bari na zubo miki abinci nasan daga school kike..."

"A'ah kinsan naci wani abu a school."
"Wannan ba abinci bane."

Ta shige kitchen ta fito ta ajiye mata abincin tace
"Sauko kici."
"Ni na zama acici daga zuwa sai ci ko dubaki ban ba."

"Ni ba bakuwa bace, dan Allah sauko kici."
"To ya jikin?"

"Naji sauki fa. Yaya ne ma ya hanani zuwa wai sai na kara warwarewa."
Tai murmushi tace
"Yaya dai Yaya kullum Yaya ko dai."

Duka ta kai mata tace
"Bana so."
"To sorry naga jiki yai kyau sai dai kin kara ramewa daman ke aba gaki ga kamar ki."

Hararar ta Maryam tayi tace
"Dame kwado yafi gaya?"
"Da mai da yaji da magi kinga kuwa ai yafi sa."

"Ni dai kici abinci."
"Zanci ai ina Ummi?"

"Ta tafi aiki bata dawo ba."
"Ayyah yau sai ke kadai kenan."

"Uhmm ai gobe ko ya hanani da ya fita zan taho."
"A'ah ki zauna sai monday kawai kan nan kin kara murmurewa ba wani abu ake ba yanzu kinsan farkon komawa duk course outline suke bayarwa kuma baki da matsala."

"Ah haba ai shikenan."
Ta fara cin abincin suna hira har ta gama, tace
"Alhamdulillah."
"Ke da driver ne a kai masa ruwa ko?"
"A'ah Yaa Muhammad ne ya kawo ni."

Ido Maryam ta zaro tace
"Kuma kika barshi a waje."
"Tab Yaa Khalifa ai da tini ya tafi yaje bayan layin ku yace in ya gama zai kirani."

"Ok yasu Momy?"
"Momy bata dawo ba ni kadai na dawo saboda school nima da bari nai sai weekend din muka dawo tare kawai."

"Gaskiya since ba wani abu ake ba."
"Wallahi."

Wayar Jawahir ce tai kara tana dubawa tace
"Yaa Khalifa ya dawo kenan."
Ta dauka ta kai kunnen ta tace
"Gani nan."

Maryam tace
"Oh sai tafiya kenan."
"Uhmm ai in na kara minti daya zai iya tafiya ya barni."

Ta mike Maryam ma ta mike tana fadin
"Nagode sosai da ziyara."
"Kar ki damu mun zama daya."

Suka fita tare, wata mota ce mai kyau da tsada ta gani bata zata shine a ciki ba sai da taga ya sauke glass din, yana kallon ta kamar zai hadiye ta, kai ta dauke suka karasa still kallon ta yake babu ko kiftawa babu, har suka iso sannan ya dauke idon sa, Maryam ta sunkuyar da kanta tace
"Ina yini?"

Cikin cool voice dinsa yace
"Lafiya lau"
Ta kalli Maryam tace
"Da kyar ya gane gidan fa ni kuma nace ba zan nuna masa ba tunda ya taba kawo ki, before cewa ma fa yayi ya manta ki, sai da nai masa kwatance."

"Jawahir talkative wa ya tambaye ki to?"
Ta bude ta shiga, tace
"Yaya bakai mata ya jikin ba?"

"Ohk."
Ya fada yana kallon Maryam da tai kasa da kai yace
"Ya jikin?"

"Alhamdulillah."
"Allah kara sauki, bansan nan zata kawo ni ba da na kawo miki kayan dubiya."

Murmushi Maryam tayi tace
"Nagode."
Jawahir tace
"Sis sai munyi waya ki gaida Ummi in ta dawo da Haidar."

"Zasuji nagode."
Ta dago ta saci kallon Muhammad tace
"Ku gaida gida."

Kai ya gyada mata yana kashe mata ido daya, da sauri ta juya, ya bi ta da kallo yana murmushi, Jawahir ta dan kalle shi taga Maryam yake kalla, tai murmushi tace
"Yaya wannan kallon fa?"

Kai ya dauke yana murnushi kawai, tace
"Ko dai ko dai?"
Hararar ta yayi yace
"Bana son surutu."

"To an ba da ita dai."
"What?"
Ya tambaya da sauri ta kyalkyake da dariya tana fadin
"Na kama ka."

"Da akai me? Ina nufin me ruwa da kike ce an bada ita."
Dariya tayi tace
"Ah ah fa."
Kai ya dauke ya fara driving din sa bai kuma kula ta, ita kuwa sai dariya take kasa kasa.


Bayan ta koma mamaki Maryam ta dinga yi meyasa Muhammad ke boye ma Jawahir bai san ta ba da yana son ta, tabe baki tayi ta cire hijab kwanta akan kujera tana lumshe idon ta da sauri ta bude ido tana duba agogo shida saura Yaa Aliyu bai dawo ba bayan yau laraba biyar ma wani lokacin yana gida, to ko wani aikin ya tsayar dashi, Haidar fa? Ko da yake tasan dole yana wajen sa tinda tare suke dawowa in yana da wani abu ma zai sa drivern sa ya kawo shi gida.


Tsakanin Maryam da Muhammad kuwa soyayya suke duk da Maryam bata fiya sakewa ba, in tana wani abu sai taji ta incomplete ko ta kasa masa wani abun shi kuwa bai jin komai kulawa yake bata duk da tana hana shi zuwa amman shi a takure yake da gayya yake kai Jawahir makaranta dan su hadu, akwai lokacin da yace saboda me take kin barin shi yazo sai tace
"Yaya ne baya so."

Yace
"Yaya baya so?"
"Uhmm."
"Jika ki zai ya shanye?"
"Uhmm...."

"Shikenan!"
Kawai yace abin na basa mamaki ya rasa wa zai tambaya shin Yayan nan Yayan gaske ne ko kuwa a yadda take cewa Yaya shi ya dauka uwar su daya uban su daya amman ya fara tunanin wani abu in har haka ne da matsin bai kai haka ba, shi na miji ne dan haka yana gamin anya Yayan nan ba son ta yake ba. Zama yai yayi tunani ya samarwa kan sa mafita.


Muhammad ya nunawa Maryam yana son ya aiko gida sai ta nuna tsoro take ji, cikin muryar sa mai sanyi yace
"Maryam bakya so nane?"
Kai ta girgiza yace
"Maryam ni mutum ne wanda in ina son abu da zuciya daya nake son sa, ba zan iya cigaba da rayuwa a haka ba ina son nima na samu na yi aure bakiga Najwa ba sauran wata hudu auren su, so nake da an gama nasu a hau shirye shiryen namu ni da zaki yadda ma da an hada kawai."

Murmushi tay tace
"Kai a'ah karatun nawa fa?"
Murmushi shima yayi yace
"Wani lokacin in kikai abu kamar bakya so na."

"Kada kace haka dan Allah."
"To gashi nan."

"Ni ba haka bane kasan irin karatun mu bama yanzu da zamu shiga asibiti in da aure abun zai min wahala."
"To shikenan naji amman ni dai zan nemi su Abba su san dani please ki yadda."

"Shikenan."
"Kin yadda?"

Tace
"Eh."
"Nagode my wife."

"Tin yanzu?"
"To kwana nawa ne?"
Murmushi kawai tayi. Har ta manta da abin ma bayan kwana biyu Abba ya aika aka kira ta, ta same shi a dakin sa.

Abba yace
"Maryam kinsan wani Muhammad?"
Dagowa tai da sauri ya sakar mata murmushi yace
"Kinsan shi kenan?"

Kasa tayi da kanta, yace
"To je ki."
Ta mike ta fita da sauri, Ummi ta shigo tace
"Gani."

Yace
"Zauna mana."
Zama tayi yace
"Wani yaro Muhammad dan gidan Minister of petrol ne yazo waje na yanzu."

"To Allah yasa lafiya."
"Lafiya lou, Maryam ya gani yakeso yace yana son a bashi dama su dai dai ta kansu in hakan yayi sai a sanya rana da harkar bikin su."

"Masha Allah amman Alhaji kan a basa dama a fara bincikar halin sa, kan su hadu dan kar muje kuma yana da wani halin a bar yarinya ta fara soyayya da shi kuma a zo daga baya agane hali."
"Nima nai tunanin zanje muyi magana da Yaya zan saka Aliyu da Farouk su bincika mana."

"Yauwah Allah yasa albarka."
"Amin."
Ya mike yace
"Bari naje wajen Yaya dan naga motar sa kafin ya fita."

Yaje ya samu Abbi, Abbi yai na'am suna zaune a falon ma ya kira Aliyu da Farouk da yake weekend ne duk suna gida, zama sukai Abba yai musu bayanin komai, Farouk ji yai zuciyar sa kamar ta fito Aliyu kuwa ba zaka gane a halin da yake ciki ba sam bayan Abba ya gama bayani yace
"Muna so ku bincika mana ya yaron yake."

"Insha Allahu Abba."
Aliyu ya fada, Farouk ma yace
"Allah bamun iko."
"Amin."

Suka tafi, duk sunje sunyi bincike Muhammad bai da wani mummunan hali ko kadan yaro ne mai tarbiyya da hankali, kuma ba wanda ya boyewa Abba dan shima Abba ya bawa wasu da yawa dan haka Abba ya kira shi ya ya bashi damar zuwa zance, murna wajen Muhammad kamar me?

Aliyu na ta shirin tafiyar sa wanda ya rage kwanaki a cikin lokacin duk ya burkice Ummi ta rasa gane kansa, in tai magana sai yace yana kewar tane.

Ranar da Muhammad yace zai zo da kyar ta sanarwa Ummi, Ummi na kasa a zaune ta sauko ta zauna a kusa da ita, Ummi ta kalle ta tace
"Lafiya Daughter?"

Kasa tayi da kai ta kasa magana, Ummi tace
"Fada min mana me kike so?"
"Ummi daman wannan ne yai min waya wai zai zo yau."

Tana fada tai kasa da kai, Ummi ta kalle ta tana susunne kai tai murmushi tace
"Ni kuma ake jin kunya Daughter?"

Jikin Ummi ta shige tace
"To Allah ya kawo shi." Da gudu Maryam tai sama, taso tai kwalliya amman ganin kada Ummi tace dan zai zo zata shiyasa ta hakura kawai, wata orange kalar doguwar riga ta saka wacce duk jikin ta stone ne ta mata kyau ta shafa turare tana gaban mudubi ya kira wayar ta, dauka tayi yace
"Na karaso."
"To ka shigo."

"Ok."
Ta mike ta fita falo, dakin Ummi ta shiga ta tsaya a bakin kofa Ummi tace
"Ni dai na zama sirikar ki ko?"

Kai ta girgiza tana rufe fuskar ta da hannayen ta, Ummi tace
"Ya karaso kenan?"
Kai ta gyada, Murmushi Ummi tayi tace
"To jeki ku zauna a barrander ko?"

"To Ummi."
Ta fada tana juyawa, a babban compound ta same shi jikin motar sa, tinda ta fito ya zuba mata ido har ta karaso, tace
"Sannu da zuwa."

"My wife."
Ta danyi murmushi, tace
"Muje to."

"Ok."
Tai gaba yabi bayan ta, a barander suka zauna inda wajen yake da table da kujeru guda hudu ya zauna ta zauna a can gefe tace
"Ina yini?"

Kallon ta yake yace
"Wannan kunyar fa haka Maryam?"
Kai ta girgiza yace
"To ki dago yau magana zamuyi dan mun fara kokarin sai ta rayuwar mu kinji."

Kai ta gyada, mai aikin su ce tazo ta kawo masa lemo da ruwa yai godiya ta koma, Maryam ta zuba masa lemon ya dauka ya kurba ya ajiye yace
"Nagode."
Tai kasa da kai. Gyaran murya yai cikin muryar sa mai dadi da sanyi yace
"Na miki bayani akai na tin kwanaki, kinga gidan mu, da yan uwa na da aboki na komai kike so ki bincika ki tambayi Abdul zai fada miki ba zai miki karya ba."

Kai ta gyada yace
"Akwai abinda kike so kuma kike son ki sani?"
Kai ta girgiza yace
"Shikenan kofa a bude take ko ba yau ba in kina bukatar jin abu daga gare ni sai dai ni ina da bukatar sanin wani abu akan ki, wannan Yayan naki Maman ku daya?"

Ji tayi gaban ta ya fadi abu da ta jima da mantawa ya dawo mata kwakwalwar ta ta shiga kai koma, yadda ta fada duniyar tunani, yace
"My wife."

Da sauri ta dago wanda idon ta tini yai ja, ga hawaye da ya taru a ciki, shima take ya shiga damuwa yanayin ta ya sauya idon ta har ya kada yai jawur kallon ta yayi yace
"Subhanallah meya faru?"
Kai ta girgiza ta mike.......



*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*




*Antty*
[10/30, 13:46] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 11

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW



*Bismillahir rahmanir rahim*


*
Ji tayi gaban ta ya fadi abu da ta jima da mantawa ya dawo mata kwakwalwar ta ta shiga kai koma, yadda ta fada duniyar tunani, yace
"My wife."

Da sauri ta dago wanda idon ta tini yai ja, ga hawaye da ya taru a ciki, shima take ya shiga damuwa yanayin ta ya sauya idon ta har ya kada yai jawur kallon ta yayi yA yace
"Subhanallah meya faru?"
Kai ta girgiza ta mike tana fadin
"Kayi hakuri."

Sai tayi cikin gida da sauri, dakin ta ta shiga ta fada saman gado rayuwar ta take son ta tuno so take ko ta halin yaya ta tuno wani abu amman ina ta manta tasan dai ta kasance a wannan gidan wanda yake shine gatan ta a duniya kawai su suka rufa mata asiri suka zame mata iyaye da family, shin su waye iyayen ta? Ina suke? A baya ne take shiga wannan halin na son lallai sai ta tino su waye iyayen ta wanda in tai wannan tunanin yake saukar mata matsanancin ciwon kai saboda damuwa in ba sa'a ba sai ta kwanta ciwo ma.

Bata san lokacin da bacci ya dauke taba, Ummi ta leko dakin ta ganta kwance ta rufe kofar kawai ta barta da dare Aliyu ya aika Haidar ya kira Maryam, lokacin har ta saka kayan bacci, kana ganin ta zaka gane tana cikin damuwa, hijab ta dauka har kasa ta daura sannan ta fita, ba kowa a falo dan lokacin tara ta gota, dakin ta nufa ta kwankwasa aka amsa ta bude a hankali, zaune ta same shi akan kujera da remote a hannu.
"Gani."

Ta fada tana duban shi sai taga ya daure fuska, itama fuska daure dan daman bata cikin walwala tun dazu da aka famo mata inda yake mata ciwo. A ranta tace
"Miskilanci na shi ya tashi kenan."

Bai kalle ta yace
"zauna"
Ta zauna, ya dago ya dube ta yace
"Waye Muhammad?"

"Nima ban san shi ba."
Wani murmushi yayi yace
"Bana son karya, ke kuma yanzu kina son ki koya ko?"

Kai ta girgiza yace
"Nasan kin sanshi tinda ke kika bashi dama zuwa wajen Abba, buri na akan ki, ki tsaya kiyi karatu, kamar yadda kike fita da point mai kyau ya zama har karshen karatun ki haka amman ke kin nuna kin girma aure kike so ko? Ki sani in nace a'ah ba wanda zai ce eh dan haka ba zan bar yaron yana zuwa wajen ki bane dan ya hanaki karatu, ko da tafiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login