Showing 177001 words to 180000 words out of 232912 words
Chapter 60 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
ta kai kunne tace
"Uhmmm."
"Anya kuwa *Matar Haidar* ce?"
"Uhmm uhmm me ka gani?"
"Ban taba ganin *Matar Haidar* ta kashewa Haidar waya ba."
"Yaya...."
"Na'am nayi laifi Matata amman kiyi hakuri nima ba yadda zan yi gobe zan zo zan fada miki dalili amman ki min alkawari sama min mafita."
"Nayi."
"Yauwah my Love, fada min Ya My love take?"
"Ba lafiya."
Da sauri yace
"Meyake damun ta?"
"Kewar ruhin ta take."
"Haba Baby na ko da ace ruhin mu na nesa da juna na tabbata ina tare da ke a zuciyar ki."
"Ni dai Yaya wallahi i miss you."
"I miss you more dear am sorry ba zan sake ba."
"Promise?"
"Yes i promise."
"To gobe da yaushe zaka zo"
"After mosque."
"Allah kaimu."
"Wacce kwalliyya zanyi miki?"
"Kaima ka san ai kowacce shiga kai kyau kake Yaya."
"I love you Baby."
"I love you more Yaya."
"To aje a maida waya a kwanta kinji?"
"To Yaya sai da safe."
"Allah tashe mu lafiya."
"Amin."
Ta kashe wayar ta lumshe ido tana jin wani so da kaunar sa na kara shigar ta, hakika bata san halin da zata shiga ba in ta rasa Haidar mikewa tayi ta maida wayar ta sannan ta dawo ta kwanta ita kadai.
Rukayya da Aisha ne suka shigo dakin suka same ta kwance suka karasa suna fadin
"Ya dai?"
"Kewar Yaya nake."
"Kai Maryam kefa ko?"
"Ni fa me? Ku kunsan soyayya kuwa, Yaya ya gama zama jini da hanta ta, wallahi baki ji yadda nake ji ba na rashin sa, ji na nake incomplete kamar bani da lafiya kamar bani ba."
Filo ta rungume tana fadin
"Myyyy."
Aisha ta mike tace
"Allah shirya ki."
Juya musu baya tai tare da lumshe ido tana tuna wani daga cikin moment din da sukai spending da Haidar a haka bacci ya dauke ta cike da mafarkansa.
Washe gari kamar yadda ya fada bayan an sako daga masallaci ya wuce makarantar su, bakin gate din ya karaso, tint glass din ya sauke, fuskar sa ta bayyana gate man din da sauri ya washe baki yana fadin
"Barka da zuwa Dr."
Hannu Haidar ya mika masa yana fadin
"Ya aikin?"
"Alhamdulilah kwana biyu?"
"Wallahi aiki ya mana yawa."
"Allah sarki jiya Baba Khamis yake maganar ka yake cewa kwana biyu Allah yasa lafiya."
Dan murmushi yayi ya zura hannu ya damko kudi ya mika masa yana fadin
"Alhamdulilah."
Amsa yayi yana godiya nan da nan ya bude masa gate din ya shige parking yaje yayi sannan ya fito, sanye yake da sky blue din shadda sai kyalli take ya saka bakin takalmi sau ciki, da bakin agogo, hannun sa rike da hular sa, sakawa yai akan sumar sa mai yawa ga taushi sai sheki take, sosai yayi kyau, ciki ya shiga ya nufi office din Principal kai tsaye, yana tafiya suna gaisawa da ma'aikatan wajen, a haka har ya karasa office din principal din yana shiga ya ganshi zai fito amman ya koma yana fadin
"Aliyu kwana biyu."
Kai ya sunkuyar yace
"Wallahi Abba aiki ne ya janye ni."
"To ya aikin yasu Alhaji Suleiman din?"
"Suna lafiya."
Sakatare din sa ya kalla yace
"A kira masa Maryam in ya gama ka rufe min office din."
"Ok Sir."
Ya juya ya tafi Haidar ya masa godiya yana zaune suka shigo su uku, Maryam ta tsaya jikin kofa tana kallon sa, cike da so da kauna, su Rukayya suka karasa gaisawa sukai da Rukayya da Aisha sannan ya mike yana kallon Maryam dake kallon sa, ya karasa gaban ta ya durkusa yace
"Doke ni dan Allah."
Su Aisha suna dariya suka fice, sai da suka fice ya dago yana kallon ta sai kallon sa take, mikewa yayi ya kamo hannun ta suka zauna akan three sitter, dan murmushi ya saki ganin sai dauke kai take, yace
"Tinda ba zaki gaishe ni ba ni bari na gaishe ki ina yini?"
Dan murmushi ta saki tace
"A'ah."
Yace "To me?"
Kafada ta make sai kuma ta mika hannu ta shafa fuskar sa tace
"Yaya baka da lafiya ne?"
Hannun ta ya kamo yace
"Kema baki da lafiya ne? Duk kin rame."
"Ban kai ka ramewa ba Yaya."
Ido ya lumshe, yace
"I miss you Baby."
Hannun ta ta janye tace
"Nima haka."
Ya dago yana kallon ta cike da so da kauna, ji yai wani son ta yana kara shigar sa, tai masa kyau duk da sanye take cikin farin hijab amman gashin gaban goshin ta duk ya kwanta, na girar ta ma ya kara yin baki kamar tayi jagira, ga na idon ta da ya kara yin gazar gazar, sai lips din ta da suka kara pink dasu kamar ta shafa man lebe da sauri ya dauke idon sa daga kallon ta a hankali ya fara magana
"Kan na ce komai ina mai baki hakuri da rashin zuwa na na kwana biyu nima ba a son raina bane, domin na fiki shiga halin damuwa saboda na riga na saba da kasancewa dake hakika na sha wahala na rashin ki *Matar Haidar* "
"Ba komai Yaya, amman wannan wane irin aiki ne ya rike min miji na ba ruwa na dashi."
Tai magana cike da shagwaba.```
*Allah mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*
*Antty*
[12/3, 11:39] Maryam S Indabawaπ₯°: ο»Ώο»Ώππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 72
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
βπ»βπ»βπ»
πππππππ
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
``` "Maryam....."
Ya kira sunan ta a hankali da sauri ta dago tana kallon sa, dan kan Haidar ya kira sunan ta ana dadewa in kuwa ya kira ta tabbata babban abu ne, dan haka ta mika masa hankalin ta gaba daya tace
"Na'am Yaya."
"Maryam ina da matsala ina da damuwa."
"Amman Yaya baka fada min ba."
"Bana son hankalin ki ya tashi bama in kika kasa magancen."
"Allah ba zai kawo abinda zan kasa magance maka ba."
"Ko menene?"
Kai ta gyada, ya dago yana kallon ta sai ya dauke ido sa yace
"Maryam ina bukatar ki."
Murmushi ta saki tace
"Nasan da haka Yaya."
"Wannan bukatar daban da waccan, a kwanakin baya ina fama da wani ciwon ciki wanda da kai na na gano dalilin sa, aure nake so, mace nake so, da farko na dauki ciwon da wasa amman a yanzu ciwon na neman ya kwantar dani, in yaci jiki na zan iya rasa rayuwa ta a ko da yaushe, solution daya ne Maryam shine nayi aure na tara da iyali na, nayiwa Ummi maganar a matso da auren mu tace wata nawa ne ya rage, a yadda nake ji na Maryam ba zan iya kai wannan lokacin ba ina bukatar mace a tare dani, na sani ko wanne namiji yana da bukatar mace amman ni nawa na yanzu abun yai yawa bansan ya akai haka ba.
A duk lokacin da nazo na ganki na koma hankali na na bala'in tashi nakan rasa nutsuwa ta na kan shiga wani mawuyacin hali wannan yasa na yanke shawarar rage zuwa sai dai shima bata haifar min da d'a mai ido ba dan koyaya naji sautin muryar ki ni kadai nasan halin da nake shiga ga kewa da son ganin ki, Maryam yaya zanyi na rasa madafa."
Ya fada idon sa na canja launi, saukowa tayi daga kan kujera ta kama hannayen sa hawaye na zubowa a idon ta na tausayin Aliyu, ya kalle ta, yana share mata hawayen sannan yace
"Matsalar mu kusan daya ce domin kema wannan ciwon marar naki ba zai taba barin ki ba in ba aure kikai ba."
Kai ta hau girgizawa tace
"Yaya kana kuma azumin?"
Hannun ta ya kama yace
"Ina yi, amman yanzu da kyar yake kaiwa."
"Yaya to ya ya zamuyi?"
"Yaya ko Ammi zanwa magana?"
"A'ah!"
"To yaya zamuyi? Ka samo mana mafita."
Shiru yayi tace
"Kaji Yaya."
"Shikenan zan samo insha Allahu,"
Ya mike yana fadin "Bari na tashi."
"Ina? daga zuwan ka."
"Babyyy."
Ya kira sunan ta da wani sauti da yasa sai da tsigar jikin ta ta tashi, ido ta lumshe tana fadin
"Uhmm uhmm Yaya..."
Tai maganar kamar zatai kuka.
"Ki barni na tafi kar nai abinda ba kyau."
Tai murmushi tace
"Ina kaunar ka Yaya na."
"Nima ina kaunar ki Baby na."
Ya nuna mata hanya yace
"Muje!"
Ba musu tabi bayansa ya dauki ledar da ya kawo musu abu ya fita, a bakin office din ya tsaya tace
"To Yaya sai gobe ko jibi?"
Wani kallo ya aika mata yace
"Sai kin ganni dai."
"Please Yaya kada ka dade kamar yanzu."
"To Baby na, wannan shagwabar kara zautani take."
Ta dago tana masa wani kallo ya matso daf da ita yace
"Kina son ki haukatani ko?"
Juyawa tai tana girgiza kai hadi da murmushi yace
'Ungo sai munyi waya."
Ya mika mata ta rissina ta amsa tace
"Thank you Yaya."
"Ba godiya hakkinane."
Tai murmushi tace
"Ka gaishe min da su Ammi da Mami."
"Zasuji."
Ya juya yana juyowa yana daga mata hannu, itama hannu take daga masa tare da sakar masa murmushi, juyowa yai yana kallon ta a hankali ta motsa bakin ta, ta furta
"I Love you Yaya!"
A hankali ta furta wanda dan yana ganin ta yasa ta gane me ta fada, ido ya lumshe yana furta mata
"I love u more."
Sannan ya juya ya fice a gate din itama tayi cikin hostel din su, daki direct ta shiga ta kwanta a saman gado tana mai lumshe idon ta, wani son Yaya Haidar taji na azalzalar zuciyar ta, hannu ta daura akan zuciyar ta, tabbas bata da wanda take so, Yaa Haidar shi ya sabar mata da komai, shi ya koya mata wannan son ta, ta yadda ta aminta Yaa Haidar ba zai taba cutar da ita ba domin kuwa ta sani kowa da yasan alakar su tin tana karama duk inda zashi tare suke zuwa har yanzu da yake aiki, wanda a wajen aikin sa duk wanda yasan waye Haidar to tabbas yasan Maryam domin daga dakin Haidar, motar sa, office din sa duk hutunan Maryam ne a makale, kuma duk abinda yake akwai lokacin Maryam, wanda kome yake zai katse shi dan baya shiga lokacin ta bama in yana gida, iyayen su kowa har mamakin wannan irin soyayyar suke, kowa fatan alheri yake musu a rayuwar su.
Bayan kwana biyu da magariba ta samu kiran sa, dauka tayi cike da zumudi tace
"Yaya nah."
"Na'am Matata."
"Yaya ya aikin?"
"Alhamdulillah."
"Yau da kasala da faduwar gaba na tashi duk bana jin dadi Yaya me yake damun ka?"
Ido ya lumshe yana mai dan cije lips din sa yace
"Baby ciwon cikin nan ne yau ya tasar min, nayi niyya nazo na ganki amman ban samu dama ba."
"Ayyah sorry My, kaje asibiti? Ya cikin? Ya kake ji? Sannu Yaya kasha magani?"
Jigina yayi da gado yana lumshe ido yace
"Baby na fada miki matsala ta, maganin ma sam ya daina min aiki."
"Innalillahi yanzu Yaya ya zamuyi?"
Ta fada hawaye na zubo mata, tare da shesheka.
Cikin dauriyya yace
"Dan Allah ki bar kukan nan ina nan ina samo mana mafita insha Allahu cikin week din nan zan samo mana mafita kinji?"
Sheshekar kuka ta fara yace
"Wallahi zafin yadda kike zubar da hawayen ki yafi zafin ciwon da nake ji."
"Na daina Yaya."
"To my Baby yanzu ya karatun?"
"Uhmm Alhamdulillah."
"Exam sauran kwana nawa?"
"Few week Yaya."
"Baby ta kusa ta tabbata a *Matar Haidar* kenan, bai kai three month bafa."
Kai ta gyada yace
"Allah nuna mana wannan lokacin."
"Amin Yaya yanzu ya kake ji?"
"Da sauki my love yanzu ma zan fita na je na gaishe dasu Abbi yau tin asuba bamu hadu ba."
"Agaishe min dasu ina Yaa Alkasim?"
"Bai jima da fita ba."
"Ok!"
Daga nan suka dan taba hira sukai sallama. Ammi ta fara kira Ammi na ganin kiran ta katse wayar ta kirata, dauka tayi ta kai kunnen ta ta gaishe da Ammi, Ammi ta amsa tace
"Meyake damun ki Ummi?"
"Ammi, Yaya ne bashi da lafiya."
Ta fada tana sheshekar kuka.
Ammi tace
"Kuma shine kike kuka?"
Sheshekar kukan tta cigaba dayi, Ammi tace
"Yi shiru to ki fada min kema baki da lafiyar ne?"
"Tin safe nake jin faduwar gaba Ammi, ga zazzabi dake son rufeni, uhmm Ammi dan Allah kukai Yaya asibiti a dubashi a fada masa me yake damun sa, kuma Ammi yace....."
Sai tayi shiru, Ammi tace
"Me yace?"
"Uhmm uhmm ba komai amman Ammi please ku kaishi asibiti."
"To za a kaishi ki daina kuka, kar kisa damuwa kinji zan kirasa yanzu sai muji me yake damun nasa."
"Yauwah Ammi ina Abbi?"
"Yanzu ya shigo ya shiga watsa ruwa."
"Ammi ki gaishe shi yaushe zaki zo?"
"Zan shigo insha Allahu."
"To sai da safe."
Sukai sallama, Ammi tabi wayar da kallo tana jinjina soyayyar Maryam da Haidar, tana cikin tunani taji sallamar Aliyu cikin sanyin murya yai sallamar daga ji kasan baya jin dadi.
Ta amsa ya shigo sanye yake da wandon jean sai farar riga mai gajeran hannu sai kamshi yake duk ya rame ya zauna a kasa kansa a kasa yace
"Ina yini Ammi?"
"Lafiya lou Haidar ya kake ya gidan ashe baka da lafiya me yake damun ka?"
Kai ya dan sosa yace
"Ciwon ciki ne Ammi amman ai yayi sauki."
"To kaje asibiti yanzu Ummi ta kira tana kuka wai mukai ka asibiti."
Murmushi yayi, Abbi ya shigo yana fadin
"Waye ba lafiya?"
Ya shigo ya zauna Ammi ta ce
"Haidar ne."
Ya kalli Haidar da kansa ke kasa duk ya fada yace
"Me yake damun ka Haidar?"
"Abbi ciwon cikin nan ne dai amman da sauki."
"An maka sceening kuwa ya kamata kaje ai maka."
"Insha Allahu Abbi, ina yini?"
"Lafiya lou ya jikin?"
"Naji sauki."
"Allah kara sauki."
Abbi ya janyo katon tray din da Ammi ta ajiye zai zuba Ammi ta sauka ta zuba masa, ya kalli Haidar yace
"Taho muci Haidar."
Kai ya girgiza Abbi yace
"Bashi ragowar papper soup din yaje yaci."
Ammi ta bashi flask din zai gardama Abbi yace
"Tashi maza kaje kaci, zan maka tofi in nagama ko Alkasim ne na bawa ya kawo maka Allah kara sauki."
"Amin Abbi nagode."
Ya mike ya fita, da Alkasim sukaci karo tare suka tafi gidan su ya zauna a falo yasha pepper soup din har goma sannan sukai sallama.
*
Waya ce a kunnensa yace
"Ahmad yanzu me kake ganin zamuyi?"
"No best solution shine kuje kuyi auren sirri a daura muku aure in yaso ka samu ka biya bukatar ka kaga ai bakai sa'bo ba."
"Baka ganin mun sa'bawa iyayen mu."
"Aliyu wannan ita ce last chance ko zakaje ka fadawa su Abba kana fama da sha'awa suyi maka aure, tinda baku sa'bawa Allah ba ai mai sauki ne, su kuma iyayen naku kwa fada musu daga baya, bayan bikin ma ba daukar lokaci za ai ba tana makaranta kaje ka dauko ta friday a daura auren kuyi weekend tare waya sani babu uhmmm."
"Zan je wajen ta gobe zamu tattauna duk yadda ake ciki shikenan."
"To amman fa sai ka kashe ta da kalamai tinda tana son ka ma na tabbata zata aminta."
Da wannan shawarar sukai sallama.
*
Washe gari ya nufi makarantar su, lokacin da tazo ta ganshi kuka ya saka masa, cikin tashin hankali ya mike ya dawo gaban ta ya durkusa yace
"To kukan menene Baby?"
"Yaya kaga yadda ka rame kuwa? Kana shan magani?"
Ya dan saki murmushi yace
"Ina sha mana. Yanzu dai daina kukan nan muyi wata magana."
Dagowa tayi tana kallon sa idon ta duk hawaye yace
"Solution na samo mana."
Hawayen ta hau gogewa ya zauna yana kallon ta yace
"Mun tattauna da Ahmad kuma matsaya daya muka samu in ba ita ba ni ban ga wata mafita ba."
Batai magana ba kallon sa kawai take tana jiran taji mafitar yace
"Aure zamuyi Maryam amman auren sirri."
Da sauri ta kalle shi cike da alamar tambaya, kai ya gyada mata yace
"Yes, shine kadai solution tanan ne kadai zan same ki a halak dina kuma mu samarwa kanmu mafita, ba haramci zamuyi ba da auren mu."
"Yaya ba wata mafitar sai wannan."
"Babu ko kina son mu mallaki kanmu ta haramtaciyar hanya ne?"
Kai ta hau girgizawa yace
"To ko zakije ki fadawa su Abba cewa ga abinda yake damuna?"
Nan ma kai ta girgiza yace
"Ko kin samo mana mafita?"
"A'ah Yaya."
"To fada min menene abun mafitata, ni a gani na tinda ba mu sa'bawa mahallici na ba ai ba wata matsala kuna kwana nawa ya rage mana."
Ajiyar zuciya ta sauke ta karaso tana fadin
"Yaya in akai auren zaka warke?"
"Insha Allahu."
Hawaye ne ya zubo mata tace
"Na amince."
Kallon ta ya tsaya yi, tai kasa da kanta hawaye na zubo mata
"Tinda ba haram bane dan na taimake ka ne Yaya na yadda zan baka komai nawa in har bai zama haramci ba zan baka farin ciki na da rayuwa ta, na yadda dakai kai mai so nane da kauna ta ba zaka tabai min abinda zai cutar dani ba, na yadda Yaya na zama *Matar Haidar.* "
"Allah miki albarka!"
"Amin."
Ya mike yace
"Tafiya zanyi zanzo ranar Friday sai mu tafi ko?"
"Allah ya kaimu."
Sukai sallama.
*
Ranar juma'ar da ba zata manta ba ita ce ranar da Yaa Haidar yazo mata da kudurin sa wanda ya bada card cewar likita zata je ta gani kamar yadda take zuwa lokaci zuwa lokaci ana dubata, ba bata lokaci saboda sun san Haidar aka bashi ita, suna shiga mota ya kalle ta yace
"Zamuje wajen wani malami Ahmad yana can zai zama waliyi ki, ni kuma Malamin zai zama waliyi na ina fatan ba matsala."
Kai kawai ta gyada, a haka suka karasa gidan malamin Haidar ya kashe motar ya fito ya zagaya ya bude mata, ta fito jiki a sanyaye suka karasa rumfar, wanda Malamin ne da Ahmad a zaune, a gefen Haidar ta zauna suka gaishe dashi, ya amsa yana fadin
"Itace yarinyar?"
Kai Aliyu kawai ya gyada, Malamin ya kalli Maryam yace
"Ya sunan ki?"
"Maryam."
Ta fada murya a sanyaye, yace
"Aliyu ya min bayanin komai akan lalurar sa wanda yace ya sanar dake haka ne?"
Kai ta gyada, yace
"Da gaske kina son sa zaki aure shi?"
Kai ta gyada yace
"Kin yadda a daura muku aure yanzu?"
Kai nan ma ta gyada, duk abin nan da ake akwai mai musu vedio, har ya gamai mata tambayoyi sannan ya kira aminan sa, a take aka daura auren Maryam Muhammad Jabeer da Aliyu Suleiman Abubakar akan sadaki dubu dari ga dan kunne da sarkar da abin hannu na gwal, bayan an gama aka basu certificate din su sannan sukai sallama da Malam Aliyu ya amshi wayar da akai musu vedion komai.```
*Allah mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*
*Antty*
[12/4, 17:33] Maryam S Indabawaπ₯°: ο»Ώππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 73
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
βπ»βπ»βπ»
πππππππ
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
_Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)
Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani da maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko da nono suyi bulΒ² nono ko yakai silifas yamushewa kikai amfani dashi zakiga canji
Maganinmu bashi da side effect mun hadashi da tsirrai da saiwoyi kalaΒ² domin Y'an uwa mata
Muna kano muna tura