Showing 225001 words to 228000 words out of 232912 words

Chapter 76 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1236

ita aka cigaba da gudanar da yini ranar tana cikin yan uwan ta suna ta hira abinsu.

Karfe shida aka tashi wanda Yaa Haidar yana unguwar anan yai sallah, yana karasowa Tasleem ta ganshi da sauri ta karasa ta bude mota ta shige, suna waya da Maryam yana cewa ya karaso ta shiga dagowa yai ya kalle ta yace
"Menene haka?"
"Dan na shigo motar ka Yaya."

Kai ya dauke tace
"Ina yini?"
"Lafiya lou."

"Yaya a gidan ka zan kwana fa."
Dagowa yai zai magana ya hango Maryam ta karaso kan yai magana ta kama kofar ta bude turus tayi ganin Tasleem ta hade fuska kicin kicin tana jiran ta sauko amman sai taga ta kara juyawa tana fadin
"Yaya mu tafi tinda ta fito."

Kallon su ta tsaya yi, Aliyu zai magana Tasleem tace
"Ki shiga mu tafi mana."
Ta fada tana mata fari da ido, kofar motar ta rufe ta juya Aisha ta gani zata shiga mota da sauri ta bude baya ta shiga, Yaa Alkasim ya juyo yace
"Ke lafiya?"

"Ku ajiye ni a gidan Ummi."
"Ina Yaa Haidar din?"

"Bai zo ba."
Aisha ta shigo ya tada motar ya bar wajen, Yaa Haidar da ya cika da mamaki ganin ta rufe kofa ya bude side din sa da sauri ya fito amman ina bai ga Maryam ba, ciki ya koma yana duba ta amman sam ba ita ba alamar ta, dawowa yayi ya shiga mota ya dauki wayar sa yana kiran layin ta amman tana ganin kiran taki ta dauka, Tasleem ya kalla ya aika mata da wani kallo yace
"Sauka."

"Yaya nace a gidan ka fa zan kwana."
"Nace ki sauka ko?"
Da yadda yai maganar sai da ya bata tsro bata san lokacin da ta sauka a motar ba, ya tada motar ya bar wajen, gidan Ummi ya nufa ransa a matukar bace dan me zata tafi kuma yana kiran ta taki dauka, Yaa Alkasim na sauke ta ta nufi sashen Inna dan tasan Inna ce kadai taza goya mata baya, tana shiga ta shige bedroom din ta tai kwanciyyar ta, Inna da ta fito daga toilet tace
"Ah anan zaki kwana ne!"

Kai ta gyada tace
"Eh Inna ki ara min zani ma na cire kayan nan."
"Tashi ki dauka."

Ta nufi kofa,
"Inna."
Maryam ta kira ta. Juyowa tayi tace
"Menene?"

"Inna yunwa nke ji."
"To bari na samo miki wani abu "
Ta juya ta fita. Wanka ta shiga tayi ta fito ta saka kayan Inna ta tada sallah tana kan sallaya Inna ta shigo da kwano ta ajiye mata har da ruwa da lemo.

Maryam na murmushin yake tace
"Amman nagode hajiya ta."
Ta juya zata fita tace
"Inna dan Allah ko da yaya zai zo kice ya barni na kwana ni kwanciyya ma zanyi."

"Shikenan kici ki kwanciyyar ki sai da safe."
Ta fice. Yana shigowa yai parking mota sashen Ummi ya nufa kai tsaye ya tafi sama tana dakin ta dan shigowar ta kenan ya shigo ta kalle shi tace
"Ah baku tafi ba."

Ki ya gyada yaxe
"Ina take."
"Wa?"

"Maryam mana Ummi wai kawai ta taho ta barni acan"
"Maryam din je ka duba dakin a su Nawa suke kila su ta biyo."
Ya juya ya shiga, ba ta nan amman duk da haka sai da ya tambaya ko tare suka taho duk suka ce a'ah fita yayi kawai ya tafi yin alwala yai sallah dan yasan bangaren Inna ta tafi kenan tinda ya tambayi masu gadi sunce ta shigo.

Sai da ya idar sannan ya nufi sashen Inna inda Maryam har taci abinci tai sallah ta kwanta. Inna ya sama a falo tana gyangyandi, a hankali ya tsallake ta ya nufi bedroom din ta, Maryam na kwance tana juye juye dan duk ta kasa baccin ya shigo dakin, kamshin turaren sa ta fara juyo wa da sauri ta juyo sukai ido hudu dashi yana tsaye a jikin kofa ya harde hannu a kirjin sa, juya masa baya kawai tayi tana kara lullu'ba.

Karasawa yayi kan gadon ya ciccibo ta da sauri ta fara kokarin sauka amman yadda ya rumgume ta a kirjin sa ta kasa dan haka kuka kawai ta saka masa, kofa ya nufa da ita, ya bude suka fita falon Inna sai baccin ta take, tace
"Ni anan zan kwana ka ajiye ni."

Ko kula ta bai ba zatai magana ya hade bakin su wanda sai da suka fita daga falon ya saki bakin nata, har cikin mota ya saka ta wacce yai parking a kofar part din Inna ya zagaya ya tada motar suka fice a gidan tin da suka fita take kuka, yana jin ta zuciyar sa kamar ta tarwatse haka yake ji dan bakin ciki ga kukan da take masa yana taba zuciyar sa, ganin ta raba masa hankali gida biyu yasa yai parking a gefen titi batai aune ba taji yai kasa da kujerar ta ya kwantar tare da rufa mata baya ya hade bakin su yana bata wani hot and romantic kiss wanda yasa kukan nata ya tsaya cak sai da ya dauki kusan minti goma yana kashe mata jiki da salon sa sannan ya sake ta. Lakwas tayi akan kujerar idon ta a lumshe, ya dago yana kallon ta yana sakin wani murmushi da shi kadai yasan manufar sa. Motar ya tayar suka karasa gida, yana zuwa yai parking har ya fito idon ta a rufe, ya zagayo ya bude barin da take ya ciccibe ta tana jin sa amman tai masa shiru, kofa ya bude suka shiga ciki direct bedroom ya ajiye ta akan gado, bai wata wata ba ya fara cire mata rigar jikin ta, sai da ya cire ya kunce zanin jikin ta ya zare ya rage daga ita sai underwear da vest, juya masa baya tayi hawaye na zubowa a idon ta, kayan jikin sa ya cire ya hau gadon ya janyo ta jikin sa, danshin hawayen ta yaji da sauri ya juyo da ita yana fadin
"Wai me yake faruwa ne?"

Ture shi ta farayi tace
"Bama kasan me yake faruwa ba."
Ta dire kafar ta a kasa da sauri ya janyo ta ta dawo saman gadon, wata rumguma yai mata wacce ta dole ta hakuri da son tashin da take,
"To ki fada min menene?"

Banza tai masa yace
"Rashin fada min shi zai kawo rashin fahimta a tsakanin mu, yadda muka faro da sanin sirrin juna da fahimtar juna bai kamata ki canja haka ba."
Kuka ta fashe dashi ya hau lallashin ta yana fadin
"Naji kiyi hakuri to, akan Tasleem ne?"

Kai ta gyada yace
"To ke menene na damun kanki, uhmm."
"Me ya kawo ta motar ka? Har take cewa na shiga mu tafi."

Rumgume ta ya karayi yace
"Ina zuwa ne fa ta shiga, ke kuma kika zo kuma kika tafi kika barni dan wa nazo wajen?"
"Amman dan me ka barta ta zauna a motar bayan kasan zan fito, ni ka fada min in kana son ta ne."

Kai ya hau girgizawa yana fadin
"Lala lalah ni mijin Maryam ne kadai, kuma Maryam ce kadai *Matar Haidar* dan haka ba wata mace da nake so in ba Maryam ba."
Kanta ta kwantar a kirjin sa tace
"Ni in haka ne ba ruwan ka da ita."

"An gama ranki ya dade."
Ya fada yana kissing bakin ta, ido ta lumshe ta dago yace
"Amman ke sai kiji haushi ki taho, ke da mijin ki, kin bata dama kenan fa."

"Bana son nayi abinda ba zai mana dadi bane."
"Da kika tafi dakin Inna me kike nufi?"

"In yi kwana na man, ai nasan da ka shigo idon ta biyu ko bakin kofar dakin ba zata barka ka karaso ba."
"Lallai ma 'yar nan kina son kina hukuntani da yin nesa dani bayan kinsan abinda yafi komai wahal dani kenan."

"To ya zanyi ai ba kai ka dai kake wahalar ba."
Ta fada tana dan lasar wuyan sa, ido ya lumshe ya zura hannun sa cikin vest din ta yana shafa saman cikin ta zuwa marar ta wanda take jin abun, take ya yafara hautsina mata tunanin ta nan da nan ta birkice masa suka hau sarrafa junan su son ransu.


*Wallahi da farkon fara rubuta MATAR HAIDAR ban taba zaton zai samu masoya masu karanta shi ba, ashe dai haka ake karanta MATAR HAIDAR, hakika a ko wanne littafi ina haduwa da masoya wanda ko bayan littafin zumuncin mu ke kara daurewa, akwai da yawa daga cikin makaranta littafi na da suka zamar min tamkar yan uwa, mun yadda da juna, hakika ina godiya ga masoya makaranta MATAR HAIDAR, wanda na sani da wanda ban sani ba dukkan ku ina godiya Allahu ya bar kauna. Amin*


*Allah ya jikan musulmai yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.*



*Antty*
[12/14, 19:48] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 88

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Washe gari daurin aure tare suka tafi ya ajiye ta a gida ya nufi wajen daurin auren, a gida ta samu su Najwa da Yaa Hanna dan duk kwana sukai, bata dade da zuwa ba Aisha da Rukayya suka karaso, Basma da taga Maryam ta rumgume ta, Maryam ta ture ta tace
"Ni ba ruwa na dake daki 'kaki zuwa ki kwanan mana"

"Kai Anty ance gidan ku ai bai zama."
Basma ta fada, Najwa, Maryam ta kalla ta harara tace
"Nagode shiyasa ai Rukayya ma taki tazo Allah ya saka min tinda abinda kuke min kenan."

"Ba wani nan Rukayya ai ke shaida ce da muka ce zamuje ba hana mu yayi ba."
Najwa ta fada tana mai da tambayar ga Rukkaya

"Abu kusan shekara dan iskanci."
Maryam ta fada, Aisha ta dafa ta tace
"Ke rabu dasu kada su zo din."

Kamar zatai kuka tace
"Amman ai ba dadi ko?"
Dariya Aisha tayi, dan Maryam in abun yazo akwai shagwaba ji akan dan wannan abun zatai kuka, Anty Hanna da ke jin su tace
"To ba sai suyi tayi ba, ai ni abinda nake so kenan, Yaya yana kular min dake."

Kallon Anty Hannah suke ta dan harare su tace
"Taso kinji kanwata in baki wani sirrin da zaki kara rikita Yaya."
Ta kamo hannunta suka mike, Najwa da Aisha suka ce
"Haba Anty muma muna so."

"Ba wanda zan fadawa tinda tsiya kuke mata."
Sukai sama abinsu acan ma lallashin ta tayi, tare da nuna mata yadda zata cigaba da kula da mijin ta, haka Yaa Asiya da Bilkisu suka shigo suka same ta suka zauna suna tattaunawa da hirar su. Can sai gasu Najwa nan da Aisha gaba dayan su.

Sai yamma da za ai Walima Tasleem ta zo gidan cikin wani material wanda akai masa wani banzan dinki, a kasa ta zauna wajen da aka saka kujeru tana kallon kowa d'ai d'ai, Maryam kuwa na sama Najwa ta tsare ta wai dole ai mata kwalliya inda ake mata amman duk ta gaji, sai da aka gama gaba dayan su sunyi anko cikin wata atamfa da sukai anko sosai sukai kyau kamar a debe su gudu, Najwa, Anty Hanna, Asiya, Bilkisu, Aisha, Rukky, da ita, kasa suka sauko suka bar Maryam wajen Haidar dake mata rigima ta dauko masa lemo, suka nufi store ta dauko masa ta bashi ya amsa yana fadin
"Thank you Adda nah."
Yai mata kiss a kumatu yai sama wajen Ummi.

Ta mike tana murmushi tare da fara neman layin Aliyu dan basuyi waya ba tin dazu, yana cikin mutane yaga kiran dan sunje reception ya fito yace
"Ya dai Baby?"

"Ina ka shiga ina ta missing naka."
"In zo mu tafi gida?"

"Kai Yaya sai dare."
"Yanzu zamu karaso gidan ai."

"Ohk sai kunzo."
"Bye muahh."
Ta kashe wayar ta fita, tana fita ta karasa wajen su Najwa da suke zazzaune, Tasleem na gefen Najwa Maryam ta zauna a gefe Aisha, Aisha tace
"Uhmm an gama soyayyar?"

"Ina ai bazamu taba daina soyayya ba ni da Honey."
Hannu Najwa ta tafa tace
"Rashin kunya su Anty Hanna suka koya miki kenan ko?"

Baki ta murguda tace
"A gun mijin nawa ne ya zama rashin kunya."
Sukai dariya suna hira abinsu.

Jawahir ce ta kira ta bayan ta dauka tace
"Uhmm ni daman nasan yau ba zan ganki ba please dear kinsan bani da wata 'kawa bayan ke dan Allah kizo kinji."

"To yanzu ya zanyi Yaya bai dawo ba."
"Zan kira Baby sai ya fada masa please Dear."

"Ok kira shi nima zan kira shi yanzu sai mu taho dasu Najwa."
"Yauwah dear."
Ta kashe wayar, ta fara neman Yaa Aliyu, yana dauka ta sakar masa shagwaba yace
"Ya dai Baby."

"Yaya gidan su Jawahir zamu tafi."
"Me zakuyi acan?"

Cikin kissa da iya magana tana yi tana shagwabe murya tace
"Kasan fa yadda muke sam bata da wata 'kawa bayan ni."
Duk da basa tare amman sai da yaji tsigar jikin sa ta tashi da yadda tai maganar dan haka yace
"To ya za ayi?"

"Najwa zata kaimu."
Ido ya lumshe yace
"Baby ki kula da kanki."

"Insha Allahu, thank you my love, bye."
Ta kashe wayar tana fadin
"Ku tashi muje gidan su Jawahir."

Aisha, Najwa, Rukky, Bamsa da Maryam suka tafi, acan ma yinin ake sosai suna tare da amarya har akai magariba ta shirya motocin daukar amarya suka zo aka tafi da amare.


Maryam ce zaune a kusa da Jawahir da ta rike hannun ta abokan ango na addu'a Yaa Farouk sai murmushi yake bakin sa yaki rufuwa. A haka suka gama ya mike zai rakasu su Aisha ma suka mike dan duk mazajen su sunzo, Yaa Haidar ne bai karaso ba bayan sun fita Jawahir tace
"Wallahi tsoro nake ji Sis."

Dariya Maryam ta saki tace
"Haba Jarumar mata, menene na tsoro uhmm."
Ta fada tana kanne mata ido, hararar ta tayi tace
"Abar wasa na zamar miki ko?"

"No sorry nasan Yaya he is gentle dear."
"Uhmm!"
Ta fada tana kamo hannun ta ta saka a kan kirjin ta, yadda zuciyar take bugawa, wannan yasa Maryam ta fara lallashin ta, suna cikin haka Yaa Haidar ya kira cewa yana kofar gida.

Da dabara da wayo ta tafi ta bar Jawahir inda suka hadu da Yaa Farouk a waje, sukai sallama suka tafi.


*
Washe gari da safe a makare suka tashi, saboda gajiyar biki, wajen karfe sha daya, ta fito falon sanye da wani wando wanda iya kar sa cinya da riga karama gashin ta ya baje a gadon bayan ta, ji tayi ya rumgumo ta yana fadin
"Ki tsaya ni man."

Juyowa tayi ta rumgume shi tace
"Honey yunwa nake ji."
Ta fada tana diddire kafar ta daukar ta yayi yace
"Muje na samar miki abinci ni da na kwakwule ki."

Ya ajiye ta akan kujera, ta dago tana sakin murmushi, kamar ance ta kalli bakin kofa, ta kalla, ido ta dan zaro ganin ta tsaye a bakin kofar.

Wani murmushi ta saki, tana kara shigewa jikin Yaa Haidar idon ta akan kofa tana kallon Tasleem dake tsaye ta zuba musu ido, Yaa Haidar da bai gajiya da kasancewa da ita ya kara rumgume ta yace
"Ke da kika ce yunwa kike ji."

"Uhmm amman ba abinci zan ci ba."
Hannu ya zura cikin rigar ta yana shafa cikin ta da ya d'an taso yace
"To me zaki ci."

Hannu ta saka tana zagaye bakin sa dashi tace
"In na sha wannan ma ai zan koshi."
Tana fada tare da fara kissing bakin nasa, Yaa Haidar da abinda yake so kenan ya biye mata suna kissing junan su, kamar wanda basu taba ba haka suke jin wani dadi da basu taba jin irin sa ba, gaba daya ta manta da wata Tsaleem Yaa Haidar da bai san da zuwan ta ba kuwa yana ta bidirin sa, Tasleem kuwa ganin abu yana son yafi karfin ta yasa ta fice a gidan da sauri hawaye na zubo wa a idon ta, bata taba zaton Yaa Haidar haka yake son Maryam da kula da ita ba dan tana ganin shi bai da lokacin mace amman sai gashi akan idon ta yadda yake kula da ita, tabbas akwai wani abu a kasa da ta kasa sani. Ko da yake jiya tana jin hirar su Anty Hannah da suke fadin canjawar Yaya da yadda suke shan soyayyar su basa kunyar kowa, hawaye taji ya fara zubo mata na karaya tabbas tana son Yaya amman taga alama dole ta hakura dashi tinda a baya da bai da kowa ma bai kula ta ba ina yanzu da yake da wacce matar mai kama da aljannu yar iska wacce take ta'ba miji a gaban ta. Ita kadai ta dinga zagin Maryam har ta koma gidan Sitti ranta a matukar bace, danasanin zuwa Nigeria take gaba daya.

Sai da suka kara samun nutsuwa sukai wanka sannan ya shiga kitchen cornflask ya hada mata ya kawo mata ta fara sha sannan ya shiga yai worming farfesun kayan cikin da tayi jiya ya debo kayan tea, anan jikin sa ya hada mata tea bayan ta sha taci kayan cikin yana kallon ta yana jin son ta na dada shigar sa, sai kuma mamakin cin da take yanzu wanda a da karamin cup take sha na tea amman yau Maryam ce ta sha cornflask tasha tea taci kayan ciki, murmushi yake ta dago tace
"Ya dai Yaya?"

Dariya yayi yace
"Baby na yanzu abinci kike ci"
Baki ta dan turo tace
"Ai Babyn ka ne."

Hannu ya daura akan cikin ta yace
"Allah maka albarka."
Ta saki murmushi tace
"To kaci mana."

"Kin koshi?"
Kai ta gyada sannan ya fara ci. Bayan sun gama tare suka gyara gidan duka kara wanka sukaci kwaliyya abinsu suna zauna suna kallo tana jikin sa sai da zai tafi massalaci sallah ta tuna da wata Tasleem ita kadai a daki ta dinga dariya tana fadin
"Ko ina ta tafi."

Bayan ya dawo daga masallaci yace
"Baby zani gida gobe su Momy zasu tafi zanje muyi sallama."
Bai rufe baki ba ta dauki mayafi tana fadin
"Zan rakaka Honey."

Kallon ta ya tsaya yi, yasan yana cewa a'ah to daru zata hau yi masa dan haka ya kamo hannun ta kawai suka fita, gidan Ummi suka fara zuwa, suka gaisa suka tafi bangaren Inna dake zaune tana ganin su ta washe baki tace
"Ah Maryam kune bakya gajiya duk zaryar nan da aka sha kika kara biyo sa kuka fito ai kya zauna a gida ko dan ki huta ko?"

"To ai ita tace sai ta fito ni ba ruwa na."
Yaa Haidar ya fada, Maryam ta kalla, Maryam ta girgiza mata kai, Inna tace
"Ba wani nan, kai kuwa da baka son tai nesa dakai, wai ya akai shekaran jiya na neme ki na rasa."

Baki Maryam ta turo tace
"Ba zuwa yai ya dauke ni ba, har da rufen baki dan kada na tashe ki ki taimakan."
"Yanzu Aliyu haka ka koma da jaraba ace yarinya ba zakana daga mata kafa ba."

Mikewa yayi ya nufi kofa yana fadin
"Amman Inna ai dai naga matata ce ko?"
Salati Inna ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login