Showing 93001 words to 96000 words out of 232912 words

Chapter 32 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1246

kowa kamar yadda Hajiya Mama ke min gori cewa daya nake da wanda bai haifa ba bani da baya bani da wanda zan kalla naji dadi amman Alhamdulillah Allah ya tsairar da Maryam da d'an cikin ta Allah ya kiyaye min su."

Haka ta dinga maganganu tare suka gama kukan su da Ammi suka jajanta sannan Mami ta mike ta tafi gida. Tana shiga ta hadu da Umma, gaban Mami ta sha tana fadin
"Ah mutanen Saudiyya an dawo ashe sai kika dawo kika ji mummunan labari batan sirikar ki ko? To ki daina murna da cikin jikin ta a sannu zai bare kuma ita da gida har abada."

Mami bata taba tankawa Umma in tana wannan abun amman a ranar sai ta dago tace
"Rana dubu ta barawo rana daya ta mai kaya, ki sani in kina taba wasu kina zama lafiya wata rana zaki tabo wanda ba zaki kwan ba, kuma ta Allah ba taki ba, in Allah yayi yaro zai zo duniya ko ana muzu ana shawo sai yazo dan haka ki daina tutiya kuma Alhamdulillah ko ayau za a bada shaida da tarihi cewa na haifa daya ya mutu, daya kuma ya 'bata kuma kila nan da wata rana Allah ya bayyana wanda ya bata ban taba ji a raina Abubukar ya tafi kenan ba ina ji yana can cikin rayuwa mai inganci kuma zai dawo min gidan nan da jikoki masu yawa da albarka."

Tana fada ta juya, duk da jikin Umma yai sanyi amma batajin zata ki tankawa Mami dan haka ta hau tafa hannu tana fadin
"Ayi mu gani."




*Allah ka jikan mu, kasa muyi kyakyawan karshe. Amin*



*Antty*


💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 36

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*



Mami ta shige dakin ta, ta fada saman kujera tana fashewa da kuka, wanda tana cikin kukan ta fara tuna komai na rayuwar su, Alhaji Suleiman saurayin ta ne tin tana makarantar sakandare, wanda anan suka hadu lokacin yaje musu bautar kasa, wanda tin lokacin yake son ta yaso suyi aure da sun gama makaranta sai dai mahaifin Mami dan boko ne baya aurar da yaran sa har sai yaga ya sama musu gurbi a makarantar gaba da sakandare wannan yasa da Abba yaje akan yana son a bashi damar ya turo amman Baba yace sam a'ah, wanda shi kuma Abba a gida an matsa masa dan a lokacin ya gama bautar kasa ya fara aiki kuma suna da rufin asiri, rashin bashi damar aure shi yasa ya fara neman Masauda Hajiya Umma kenan wanda sukai aure ba tare da sunyi wata soyayya mai tsayi ba sai da sukai aure Abba ya gane wasu halaiyar Umman da basu da kyau sam, bata da kunya sannan bata da ladabi, a haka Abba yake hakuri da ita shekara daya, biyu, uku, hudu Umma bata taba ko da batan wata ba, gashi Allah ya daurawa Abba son ya'ya wannan sam bai dame shi ba yana addu'a Allah ya kawo mai albarka. A shekara ta biyar ne suka hadu da Mami wanda a lokacin har ta gama degree din ta wannan shi ya dawo musu da soyayyar sa wanda a lokacin ya tura iyayen sa cikin hukuncin ubangiji akai komai na auren su, wanda lokacin da za a kawo Amarya nan jikin gidan su Ammi aka kawo Mami, wanda tare suka tare da Umma dan sabon gida ne sai sa Mami zata tare itama Umma ta tare bayan Abbah yai mata komai na gidan.

Mami macece mai hakuri, da ladabi da biyayya, tin da tayi sati yan uwan ta suka zo suka rakata makwabta wannan yasa tin lokacin suke zumunci da Ammi, Umma kuwa ba inda ta shiga a unguwar haka suka cigaba da zama sam Mami bata shiga harkar Umma dan sashen kowa daban amman in dai Umma zataga Mami to sai ta shiga harkar ta Mami kuwa bata kula ta dan in ta ganta zata gaishe da ita amma Umma bata amsawa, ana cikin haka Mami ta samu ciki, zo kuga murna wajen Abbah da yan uwan sa nan soyayyar kowa ya dawo kan Mami dan daman tafi kyautata musu akan Umma, kowa murna yake tin da cikin Umma take mata asiri akan cikin ya bare amman da yake Allah yayi da rabon cikin a haka har cikin ya girma ya isa haihuwa Ammi ita ta kai Mami asibiti ta haifi dan ta kato kyakyawa namiji, wanda ba wata matsala a ranar aka sallamo su, nan yan uwa aka cika gidan kowa yana zuwa ganin Baby, ranar suna yaro yaci sunan mahaifin Abba aka saka masa Abubakar suke kiran sa da Sadik, tin daga Sadik Mami bata kara samun ciki ba har lokacin wanda Ammi a lokacin ta haifi Ummulkhairi, ta haifi Zainab, duk da itama ba kwaninka take ba wasu ta zarar shekara uku wasu ma hudu, banda Yaya Ibrahim da yake babban dan da kadan Yaa Muhammad ya dan girmi Abubakar da shekara biyu, bayan shekara wajen takwas Mami ta kara samun wani cikin wanda tana laulayi Ammi itama ta samu ciki, Mami ta haifi da namiji aka saka masa sunan mahaifin ta Aliyu suka kiran sa da Haidar, wanda bayan wata uku Ammi ta haifi namiji itama aka saka masa Alkasim tin daga nan Mami bata kara haihuwa ba, Ammi kuwa bayan Alkasim ta haifi Fadima shekara uku tsakani ta haifi Abdullah wanda bata kara samun ciki ba sai da Abdullah ya shekara shida wanda har ta fitar da rai, a lokacin kuma Alkasim da Aliyu suna da shekara goma goma, a wannan cikin sosai Ammi tasha laulayi da bata tabayin irin sa ba, Haidar kuwa dan gidan Ammi ne ko da yake ba shi kadai ba har Abubakar saboda yaran gidan da amintakar Mami da Ammi yasa yaran ma kan su a hade yake.

Tin Haidar na yaro yake da tausayi ko yaya yaga mutum bai da lafiya ko yana jinya zai ta damuwa yana kula dashi to haka ce ta faru tsakanin sa da Ammi domin tana laulayi shi ke kula da ita da mata sannu komai ya samo kuma yace Ammi, wanda wannan ya kara sa musu shakuwa da Ammi, lokacin da ta bar laulayi kuma ya dinga addu'a Allah yasa Ammi ta haifi mace, a haka cikin Ammi ya isa haihuwa, Mami ita ta kai ta asibiti, ta haifi yar ta mace kyakyawa dan duk ya'yan Ammi duk kyaun su saboda sun hada mahaifn su bafulatani mahaifiyar su kuma jisin larabawa yasa suke kyawawa dasu dan haka Maryam tafi dukka kyau, lokacin da suka dawo Haidar ya dauke ta ya kalli Ammi yace
"Ammi ina son ta zaki bar min ita?"

Ammi tai murmushi tace
"Na bar maka ita Haidar."
To fa wannan statement din Ammi shi yasa Haidar kara son Baby, ranar suna aka sakawa yarinya Maryam sunan mahaifiyar Abbi, dan sauran ya'yan nasa duk suna ya'yan Manzon Allah ya saka musu sai a yanzu da ya sakawa Maryam sunan mahaifyar sa.

Kowa son Maryam yake dan ita ce auta gashi Ammi ta jima bata haihu ba sai kan ta, dan haka Maryam ta tashi cikin gata da soyayyar ahalin ta bama Haidar bai yadda sam Maryam tayi kuka, dan ko rigima take duk abinda take so zai samar mata, itama kuma da taga Haidar ta bar rigima in kuwa tana kuka yana lallashin ta kamar shima yai kukan haka yake ji, sosai suka shaku komai shi yake mata, da aka yaye ta kuwa ko kukan nono batai ba dan tare suke yini suna gida wajen Mami yai ta bata kayan ciye ciye wata rana ma shi ke mata wanka ya shirya ta sai dai suje wajen Ammi su gaishe ta.

Kowa yasan yadda Haidar ke so da kulawa da Maryam, da aka saka ta a makarantar su, ita sha biyu ake tashin su, ana tashin su yake daukar ta tare suke komawa aji tin malaman su na hanawa har suka daina dan a lokacin yana SS 1. In homework ne ba me koyawa Maryam sai Aliyu dan in zakai mata ma zata ce baka iya ba ita dai Aliyu, a isilamiyya ma rabi tana ajin su tana ajin su Aliyu ko an korata zata dawo. Komai Haidar ya samo Maryam duk kudin sa Maryam, in yaga kayan wasa ko kayan ado duk ita.

Shekarar sa sha biyar yai graduation hade da sauka inda yai jamb duk ya samu lokacin Yaya Abubakar yana can kasar waje yana karatu shi da Yaa Muhammad da Yaa Ibrahim, so akai a tura Haidar amman sam yaki saboda Maryam, haka kullum yake rakata makaranta lokacin tana nursery 2.

Haka rayuwar su take tafiya kullum duk abinda zai yi sai ya saka Maryam da bukatar ta a gaba, wanda kullum shi yake kai ta makaranta da yamma ya dauko ta weekend kuma ta tafi tahfiz. Tin tana yarinya take da hazaka.


Kwance yake a dakin Alkasim cikin bargo yana baccin sa, Maryam ce ta fito daga bangaren Ammi sanye da uniform din ta sabbabi dasu, wando ne blue black sai riga mai dogon hannu wacce take har cinyar ta sai hijab dan karami bayan ta rataye da jaka kafar ta sanye da cover shoe baki da farar safa, sai kamshi ta, Ammi ce ta leko tana fadin
"Kar kije ki tashe shi fa Ummi."

Juyowa Maryam tayi tana mata murmushin ta mai kyau wanda dimple din ta ya lotsa tana fadin
"Ammi ganin sa fa kawai zanyi."
Tsayawa Ammi tai tana kallon ta, ta juya ta nufi sashen su Yaa Abdullah, dakin Yaa Alkasim ta shige kan gadon ta fada tana fadin
"Yaa Haidar ka tashi zan tafi school ka tashi kaga kwalliya na yau zan tafi primary 1."

Bai ko motsa ba ta bude bargon ta ja hancin sa da sauri ya bude ido, yana daurawa akan ta ya saki wani murmushi ya mike yana kallon ta, yace
"Baby na kinyi kyau iyyee Baby na ta zama babba."

Mikewa tayi tana juyawa tace
"Yes Yaa Haidar zan tafi school nace bari nazo na gaishe ka."
"To ai baki gaishe nin ba."
Durkusawa tayi tace
"Ina kwana Yaya?"
Ya dago ta yana fadin
"Kin tashi lafiya?"

Kai ta gyada ya mike suka fita yana fadin
"Muje na rakaki makarantar naga sabon ajin da princess din na zata shiga."
Keyn mota ya amsa ya tayar suka nufi makarantar ajin ta na da suka je dan amsar promotion letter bayan ya amsa ya bude yaga an mata double promition, da ya tambaya malamar tace zata iya a abar ta a ajin.

Wannan yasa Maryam ta fara daga primary 2 kuma cikin hukuncin Allah ita take daukar ta d'aya dan Maryam da ka koya mata abu sau daya ya zauna akan ta, ga kula daga Yaa Haidar dan zai tsaya tai homework har lesson yake mata dan haka bata da matsala sam.

Abbi na son Maryam dan tin tana karama take da hangen nesa ga ladabi da biyayya. Shakuwa sosai sukai da Aliyu dan ko d'aya bai da lafiya to tabbas daya ma zai kwanta ciwo dan tare suke jinyar su, ita Maryam akwai raki da kuka da rashin son shan magani haka Aliyu zai ta lallashin ta. In kuwa shine ba lafiya shima tai ta kula in yana shan magani tana kuka tana masa sannu tana fadin da zafi ko?

Lokacin dasu Abubakar suka dawo dasu Yaa Muhammad Abba mahaifin Abubakar ya danka masa daya daga cikin company sa wanda wannan yasa Umma kamar ta mutu, nan ta kara tashi da bin malamai, wani uwan asiri da tayi wanda Sadik yana kwance cikin dare kawai ya mike ji yai gidan gaba daya ya masa zafi da sauri ya debi kayan sa ya fara hadawa a cikin akwati da takardun sa, haka ya gama ya fito daga cikin gidan yana kallon harabar gidan yana son gidan amman wani abu yaji gidan yai masa zafi da sauri ya fice wanda zuciyar sa ta fara tura sa ce masa kawai take ya bar wajen. A haka ya dinga tafiya yana nausawa bai san inda yake tafiya ba.

Washe gari an sha neman Sadik amman ba a same shi ba sosai hankalin iyayen ya tashi da aka je neman taimako aka duba musu cewar yaron yana raye sai dai yayi nesa da gida, a haka aka cigaba da masa addu'oi da neman kariya a gareshi. Umma kuwa ko a jikin ta inda ta fara aika mugun nufin ta ga rayuwar Aliyu. Domin tayi alkawarin tinda bata haihu ba, ba wamda zai gaji dukiyar Alhaji kuma Mami ma ba zata taba ganin jinin ta ba.


Anan BUK Haidar ya fara medicine din sa, wanda ko yana makaranta aka tashi su Maryam shi zai dauko ta, shekarar da zata shiga JSS 1 shekarar ya gama karatun sa, wanda lokacin Abbi ya kai ta MANS College, lokacin da aka gamai mata komai zo kuga kuka zata tafi ta bar Yaa Haidar, shi ya dinga bata kwarin gwiwa da lallashin ta kuma yai mata alkawarin duk sati zai na zuwa yana ganin ta.

Ranar da za a kai ta makaranta da safe ta fito cikin uniform din ta daga kallo daya zaka gane tana cikn damuwa bata samu tai bacci sosai ba, tsaye yake jiki motar sa sanye da bakar shirt da shudin wando jeans hannayensa duka zube cikin aljihun. Ya kara zama cikakken namiji, wanda yake fari kyakyawa dan iyayen sa gaba da baya fulani ne, gashin kan nan nasa yai baki sidik sainkyalli yake, idanun sa manya wanda suke a lunshe dai dogon hancin sa da madaidaicin pink dun lips dinsa. A hankali ta ambaci sunansa "Yaya Aliyu?"
Ya lumshe idanunsa da suka kumbura suntum saboda rashin isasshen bacci da shima bai samu ba, ta karasa ta fada jikin sa tana fashewa da kuka dago ta yayi yana goge mata hawayen dake zubowa yace
"Baby na kina so nima nai kukan ne?"

Kai ta girgiza tana mai kallon kyakyawar fuskar sa yace
"To in bakya nai miki kuka kiyi shiru."
Hannu tasa ta goge hawayen da yake akan fuskar ta yace
"Yauwa koke fa Matar Haidar."

Ta saki murmushi, a motar sa ya kai ta makaranta suka je akai mata komai da komai da wanda har an bata aji da komai.

Bayan su Abbi sun mata sallama sun tafi har Yaa Aliyu ya juya zai tafi sai kuma ya juyo, idanuwanshi sun sauya launi daga farare sol zuwa na damuwa, "MARYAM!"

Ya kira sunan ta da wata murya tamkar ba tashi ba.
A hankali ta juyo ta ce, "Na’am Yaya Aliyu!"
Ya ce, "Zo"

Tare da ya fito ta da hannun daman shi. Ta karasa ta je gare shi suka tsaya suna kallon juna kamin ta sadda kanta kasa a dalilin nauyin da kwayar idanunshi yai mata.

"Don Allah Maryama ki tsaya ki yi karatu sosai kin ji? Nasan bazaki bani kunya ba....."
Ta dago ta dube shi idanunta fal da hawaye, ta ce, "Insha Allah Yaya Aliyu zan dage fiye da a gida."

A haka yai ta lallashin ta har tai shiru, daga nan sukai sallama ya juya ya fara tafiya yana juyowa yana daga mata hannu itama tana daga masa har sai da ya daina hango ta dan sun tafi.

Ai kuwa haka ya maida makarantar kamar gida, dan duk sati yana hanyar makarantar duk security sun san shi, haka principal din da yake abokin Abbi ne ma yasan Aliyu da sauran malaman makarantar. Bata da matsala dan in yazo tai tai masa shagwaba shine kawo mata kaza da kaza dan haka sai bata damuwa tinda duk sati yana tafe. Sai da ya tafi service din shine ta sha wahala wanda kullum kuka in ya kira ta a waya tai tai masa kuka da shagwaba shima baya wata bai zo ya ganta ba in kuwa sukai hutu shima daukar hutu yake ya dawo gida yai ta biyewa shirmen ta.


*Allah ya jikan musulmai yasa muyi kyakyawan karshe. Allah ya yafe mana. Amin*



*Antty*
💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 37

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*





A haka Maryam ta tashi da soyayyar Aliyu, wanda yana gama service ya samu aikin dan haka bai wata wata ba ya siyi filaye ya dankara gini, lokacin da ta shiga SS1 ne Haidar ya fara nunawa Maryam zallar soyayyar da yake mata, wanda a gaban kowa yake kiran ta da *MATAR HAIDAR* babu wanda a lokacin bai san soyayya Maryam da Aliyu ba, makaranta kuwa a sati sai yaje sau biyu sau uku, dan haka ita ji take tamkar ma a gida take, Haidar ya gama koya mata yadda zata so shi da yadda zatai rayuwa dashi, soyayya suke mai tsafta wanda kowa yake sha'awar su.

Tana SS2 tazo hutun second term yana cikin mota yana jiran ta ta fito zasuje shopping, wanda ta fito sanye da doguwar riga, da hijab din ta zuwa gwiwa tai kyau ta karaso tana yamutsa fuska fitowa yai yana fadin
"Menene yake damun *Matar Haidar* ?"

Kofa motar ta kama ya bude mata ta shiga ta zauna ya juyo yana kallon ta yace
" *Matar Haidar* "
Dagowa tai tana cije baki yace
"Fada min me yake damun ki?"

Hannun sa ta kamo tace
"Yaya tin jiya gefen ciki na yake min ciwo sai naji yana soka min."
"Dai dai ina?"

Hannun sa ta kamo ta daura a kan marar ta, tana lumshe ido, murmushi ya dan saki yace
"Baki ga komai ba kuma?"
Baki ta dan turo tace
"Me kenan?"

Wajen kunne ta yai da baki sa yace
"Blood."
"Which kind of blood?"

"Haila."
Ya fada a hankali. Ido ta zaro tace
"Yaya nifa ban fara ba har yanzu kuma ma ni wallahi bana so na fara yanzu."

"Why?"
"Ni kawai bana so nafi jin dadi yanzu ba ruwana da wani kazanta."

Murmushi yayi yace
"Dole kuma kiyi ba, yarinya ki fara shirya masa daga yanzu zuwa ko da yaushe dan kin girma."
Dagowa tayi ta aika masa da wani kallo, ido ya lumshe yace
"Zaki zautani da wannan idanun naki."

Kai ta dauke sai kuma ta dan cije bakin ta tace
"Wallahi Yaya yana damuna ka bani magani."
"Muje daga nan ma biya clinic ko?"

Ya tayar da motar suka bar wajen yana fadin
"In kuma abin yazo yanzu ya zaki ji?"
"Yaya Allah bana so ni nafi so after i graduate naga fa yadda wasu ke wahala a school yana bani tsoro ni da ace ba zan nayi ba."

Tai maganar cike da damuwa, yace
"Ki rufa mana asiri mana, in bakya yi akwai probability ba zaki haihu ba fa."
"Kai kuma kana son kids ko?"

"Yes now."
"Shiyasa nake tsoron kar na haifa maka yara ka maida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login