Showing 78001 words to 81000 words out of 232912 words
Chapter 27 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
girgiza kawai ta juya ta fita. Karasowa yayi gefen gadon yace
"Maryam menene fada min?"
Hawaye take sai girgiza kai take. Ammi na fita ta kalle su tace
"Ku tashi mu tafi gida!"
Mikewa sukai Yaya Fadima tace
"An sallame ta ne?"
Ammi bata, bata amsa ba kawai ta fice sauran suka bi bayan ta ita kuwa dakin da Maryam take ta koma. Nan ta samu Alkasim yana tambayar Maryam amman sai kuka take. Fita yayi ya koma dakin doctor yace
"Me result din ya nuna?"
"Is positive!"
Ido ya zaro yace
"Impossible!"
Sannan ya fita a dakin da sauri. Ya nufi dakin da Maryam take
"Tashi muje wani asibitin a kara test ban yadda da wannan ba."
"Oh haka suka ce da cikin dai?"
Yaya Fadima ta fada. Kai ya gyada. Kallon Maryam sukai da jikin ta ke ta rawa dan wani zazzabi da ke son kamata. Kan ta sukai suna mata sannu ganin kamar tana firgita yasa ya kira likita allura yai mata bacci ya dauke ta.
Yaya Fadima ce ta kalli Yaa Alkasim tace
"Kai me kake tunani akan wannan lamarin?"
"Bazan taba yadda ba, nasan Maryam ba yar iska bace wama za ace yai mata cikin?"
Ya tambaya sai kuma yace
"Haidar za a ce ni shaidane Maryam da Haidar ba mazina ta bane wallahi ba zasu taba aikata zina ba dan nasan halin su duk su biyu suna da imani da tsoron Allah, Allah ba zai jarabce su da wannan mummunan aikin ba domin suna kiyaye hukuncin Allah nasan ba dai dai bane ba wani ciki da Maryam take dashi shiyasa nace zamu je wani asibitin mu kara dubawa."
Ajiyar zuciya Yaya Fadima ta sauke tace
"Wannan haka ne Yaa Alkasim amman dole mu bari ba yanzu ba kaga halin da take ciki mu bari muga ya jikin nata in yaso sai muje wani asibitin! Amman ya kake ganin su Ammi suka dauki alamarin?"
Kai ya girgiza yace
"Ban sani ba!".
"Cewa tayi duk mu tafi gida fa."
"To abar wa a wajen ita Maryam din?"
"Abinda yake bani tsoro kenan kar su Ammi su kasa fahimtar 'yar su, kar su zarge ta da wani abu."
"Anya kuwa?"
"To ban dai sani ba."
Sukai shiru suna kallon Maryam dake baccin wahala dan da ka kalle ta zaka san ba baccin dadi take ba.
A kofar gida duk sukai parking suka fito kowa cikin tashi hankali da baci rai suka shiga gida wanda fitowar Ummah kenan ta gansu a wannan halin ba karamin dadi taji ba. Falon Ammi duk suka tafi, Yaa Muhammad da Ibrahim sai Yaya Zainab da Ummulkursum zama tayi suma duk suka zauna.
Ummah parking motar ta tayi ta fito ta nufi cikin gidan bangaren Ammi ta nufa wanda lokacin Yaa Muhammad yace
"Ammi me ke faruwa ne?"
Shiru Ammi tayi can ta dago ta kalle su tace
"Mummunan abu na shirin ya faru damu koma nace ya faru damu... Ace acikin gidan nan za a samu wanda zai yi ciki ba aure."
Tayi shiru dan abun ba karamin tsoro ya bata ba. Yaa Ibrahim yace
"Da gaske cikin ne da Maryam?"
Dummmm haka Ummah taji ta zaro ido da sauri tana fadin
"Ciki ciki! Kuma Maryam?"
"Shine likita ya tabbatar!"
Maganar Ammi ta dawo da ita da tunani da zancen zucin da take da sauri ta juya ta nufi mota hankali a tashe take fadin
"Ciki ciki! Maryam ke da ciki? Garin Yaya wannan jarababben yaron kan ya mutu sai da ya sadu da ita kenan, daga daura aure yaje wajen ta ko me?"
Shiru tayi tana tuna abinda taji Ammi ta fada wai
"Mummunan abu na shirin ya faru damu koma nace ya faru damu... Ace acikin gidan nan za a samu wanda zai yi ciki ba aure"
"To suna so suce cikin ba na Haidar bane ko me ko suna so suce kan ai aure suka tara."
Kai ta girgiza tana fadin
"Nasan wane Aliyu ba zai taba kusantar zina ba kamar yadda nasan Maryam to ya akai abin ya faru. Dole na dauki mataki tin kan Hajiya Binta taji batun nan dan nasan a duniya ba abinda zata so kamar taga jinin Aliyu ko da kuwa shege ne wanda na tabbata da kyar in cikin nan shege ne dole na batar dake Maryam dole na batar dake da dan cikin ki, Binta ba zata taba ganin jinin ta ba ko na dan ta dole na batar da ke kamar yadda na batar da Abubakar daman da tamu dake da tamu da ta Hajiya Amina zan samu na jefi tsuntsu biyu da dutse daya za na batar muku da yarinya na saka muku tsanar ta sannan na batar da jini Hajiya Binta."
Wata dariya tayi tana fadin
"Komai zai zo yadda nake so kuma yadda zan tsara."
Unguwa zata amman sai ta canja hanya ta tafi gidan bokan ta.
*
"Ammi amman kina ganin da gaske cikin ne?"
Yaya Ummulkursum ta fada.
"Nima dai abun ya bani mamaki anya kuwa?"
Yaya Zainab ta fada.
"Likita zai karya ne. zai yi mata sharri ne?"
Ammi ta fada. Kai suka hau girgizawa. Yaa Ibrahim yace
"Ba zai ba amman yakamata mu canja asibiti a kara zuwa wani a tabbatar ko?"
"Haka ne Yaya!"
Yaya Zainab da Ummulkursum suka fada.
"Kai na ya daure na rasa wane tunani zanyi!
"Ammi please ki nutsu ni a gaskiya bana zargin Maryam da aikata zina sai dai in wani tsautsayin ne ko wani abun!"
Yaa Ummulkursum ta fada.
"In wani tsautsayi ne ya hana ta fada mana!"
"Ammi kinsan ta da kunya. Kuma abinda Yaya Ummulkursun ta fada haka ne amman yanzu in cikin ne na wa za a ce?"
Yaya Zainab ta fada.
"Kada ku daurawa bawan Allah dake kabarin sa kwance cikin rahmar Allah. Nasan Aliyu yaro ne mai imani da ilimi da kunya ba zai taba aikata haka ba, ba zai aikata zina ba."
"Ammi ita kuma Maryam din fa?"
Yaa Abdullah ya fada wanda ya jima yana tsaye yana jin tattaunawar tasu. Shiru tayi kawai can ta mike tace
"Bari na gani ko Abbin ku yana ciki!"
Ta mike ta fita suka zauna suna tattaunawa. Matan duk tausayin Maryam ya dada kamasu shi me yake shirin faruwa dasu ne wannan wane irin jarabawace Allah ya basu ikon cinye ta amman suna tsaka mai wuya. Ammi da ta shiga taga Abbi baya nan zama tayi tana tunanin mafita dan kan ta ya kulle gaba daya Maryam na da ciki kai karya ne itama ba zata yadda ba ace tana da ciki. Haka tai ta tunani har aka fara kiran sallah magariba da sauri ta mike ta dauro alwala tazo tayi sallah. Bayan ta idar ne kuma tai addu'a wanda ta dan samu nutsuwa har ta hau tunanin a wane hali Maryam take a lokacin. Mikewa tayi ta shiga bangaren ta, ta samu su Zainab da Ummulkrsum tace
"Ku kira min Abdullah ya kaini asibiti ku kuma kuzo ku tafi gida kunji."
"To Ammi!"
Suna cikin kiran sa ya shigo tace
"Yauwah muje ka kaini asibiti!"
Suka tafi.
*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin*
Maryam Suleiman
"Antty*
ο»Ώο»Ώο»Ώππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 29
By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
A asibiti Fadima da Yaa Alkasim ne zaune sunyi shiru suna tunanin kowa da abinda yake tunani. shigowar Ammi ne ya sa suka mike da sauri ta kalle su, ta kalli Maryam tace
"Ya jikin nata?"
"Da sauki!"
"Ki tashi Abdullah ya kai ki gida!"
Ta fada tana kallon Zainab.
"Ammi baya gari kuma na nemi alfarmar ya barni na kwana tare da Maryam."
"Shikenan kije gida ni zan kwana da ita."
"A'ah Ammi ni zan kwana kije ki huta dan Allah!"
Zama tayi ta zuba ma Maryam ido tace
"Tin yaushe take baccin?"
"Bayan fitar ku jikin ya tashi shine akai mata allura."
"Shiru Ammi tayi. Yaa Abdullah ya karasa yana kallon kanwar tasa da ta rame sosai tausayi ta bashi dan haka sai ya juya ya fita kawai dan zuciyar sa ba karamin karyewa tayi ba. Sai goma suka tafi suka bar Fadima a wajen ta.
Ammi na komawa gida ta nufi bangaren Abbi wanda dawowar sa kenan. Zama tayi tace
" Kaci abinci ne?"
Dagowa yai ya aika mata da wani kallo wanda ya bata mamaki.
Kasa shiru tayi tace
"Na jima ina jiran ka dan ina so muyi maganar akan Ummi "
Ummi take kiran Maryam wani lokacin saboda sunan mahaifiyar sa ne.
"Ai yar kice duk abinda kika yanke ya dace!"
"Bangane ba Abbi!"
"Kome tayi da sanin ki!"
"Wai kaima ka yadda da tana da cikin?"
"Saboda me bazan yadda, naje asibiti yafi biyar ana min test ana fada min positive. Ke zan fara tambaya cikin waye a jikin ta, kada kice min na Haidar ne!"
"Innalillahi wainna illahir rajiun Yanzu ni kake zargi akan cikin jikin Ummi, zan sani na boye maka shin me ka dauken da Ummi ne? Naga kafi kowa sani na da Ummi kasan halin mu dan me kuma zaka daura mana laifi baka taba kawowa ko fyade akai mata ko wani abu ba....."
"Kinga ko kina son ki kare ta, in fyade ne wata uku dayi bata fada ba a haka tasan tana da ciki aka daura mata aure da yaron nan, Allah yaso baya raye da wane hali zai shiga kinsan dai yadda yake son ta."
"Dan Allah ka daina fadar haka wa ka sani wanda ya taba zuwa zance gun Ummi. Haidar ne kadai mane min ta inma tuhuma za ai shi za a tuhuma."
"Na fada miki kada ku daurawa yaro nan, yana can kwance cikin kabarinsa cikin salama, kada kisa a tashe shi ana tambayar sa dan Allah!"
"Amman Alhaji......."
"Dan Allah Amina ki kyale ni, tashi kije yanzu bana son magana ki kyale ni da abinda nake ji. Wai yau ni a cikin gida na 'ya ta take dauke da cikin da bamu san uban sa ba. Allah nagode maka Allah ka yafen in wani laifi nayi ka jarabcen da wannan masifar!"
Ammi kallon sa ta tsaya yi yana gama fadin addu'a yai ciki. Hawaye ne ya zubo mata lallai suna cikin tashi hankali da gaske dai da cikin nan. Mikewa tayi ta koma bangaren ta, ta zauna kawai ta rasa abin yi har wajen sha biyu idon ta biyu daga baya ta tashi ta dauro alwala tazo ta tada sallah.
Kwana tayi akan sallaya tana addu'a akan lamarin yau ko da cikin shege ne a jiki Maryam dole ta tausaya mata dan yarinyar tana jin jiki amman dan me Abbi ya yadda da Aliyu ya kasa yadda da 'yar cikin sa. Ita bata zargin Maryam da son zuciya amman to ta ina ta samu ciki dan me bata fada musu ba shin a ruwa ta sha ko me dole dai sai an tara ake samun ciki to ita a ina ta tara da kuma wa har ta samu ciki.........
*
Da safe da ciwon kai Ammi ta tashi na tsananin damuwa ko abinci su Baba Ramma ne sukayi. Yaa Alkasim ya amsa ya tafi asibiti. Akan sallaya ya samu Maryam dan sai wajen takwas ta tashi tin jiya da akai mata allura sallolin ta, ta rama ta zauna tana addu'a ga Allah da kuma Yaa Haidar wanda a ko da yaushe bata taba mantawa dashi a cikin addu'ar ta. Yaya Fadima ce ta gaishe da Yaa Alkasim sannan Maryam ta dago ta daga hannu ta gaishe shi. Ya amsa yana fadin
"Ya jikin?"
Da hannu ta amsa masa. Sannan yace
"Allah ya kara sauki!"
"Amin!"
Yaya Fadima ta fada. Ya ajiye abincin yace
"Ki hada mata ko tea ne ta sha!"
Kai Maryam ta girgiza mikewa yayi ya dawo kusa da ita yace
"Ki daure ki sha kinji kanwata!"
Da hannu tai masa alamu da cewa in tasha amai zatai. Kai ya girgiza yace
"Ba zakiyi ba insha Allah, ki daure kisha."
Ya kalli Fadima yace
"Hada mata!"
Ta hada mata ta zuba mata dankali da aka soya da kwai, amsa yayi ya zauna a kusa da ita ya dibi tea din a teaspoon ya bata, amsa tayi ta hadiye da kyar tana runtse idon. Yaa Alkasim yace
"Ko kefa *Matar Haidar* "
Da sauri ta dago ta kalle shi sai hawaye. Kai ya hau girgiza mata yace
"Kiyi hakuri kada kiyi kuka kinji!"
Kai ta kife a jikin sa tana mai zubar da hawaye dago ta yayi yace
"A duniya abun da Haidar yafi tsana shine zubar da hawayen ki, haba yanzu abinda baya so kike yi, shin kina ganin in bakya duniya zai abinda yasan bakya so. In har kiina son Yaa Haidar da son ya kasance cikin farin ciki akan ki kina kiyaye abinda yake so da wanda baya so. Kinji!"
Dagowa tayi yasa handkerchief ya fara goge mata hawayen sannan ya kara bata tea din da kyar ta amsa ta hadiye tana dafe kirjin ta, ya dan shafa bayan ta a hankali yace
"Sorry kinji!"
Yaya Fadima tace
"Dazu mukai waya da Abban Iham yace anjima zai dawo in kun gama sai ka kaini gida dan na kintsa ko?"
Kai ya gyada ya kuma debowa ya bata ta amsa idon ta na cikowa da kwalla dan har ga Allah bata so damun ta yake a kirji ga cikin ta da taci abu yake mata ciwo.
Dankalin ya dauko yai gefen bakin ta da sauri ta mike ta shiga bandaki a guje dan karnin kwan da ya doke ta duk da ya sha hadi an saka wadataciyar albasa da tafarnuwa da black papper ga curry sam ba karni amman ita da yake da dalili sai gashi ya tada mata da zuciya. Bayan ta gama ta fito tana haki yaya Fadima ta gyara bandakin. Nurse ta shigo tai mata allura sannan ta bata magani shima da kyar ta sha sannan Yaa Alkasim ya bukaci su basu sallama taje ta fadawa doctor yazo ya kara duba Maryam sannan ya sallame su.
So sukai su fara kai Fadima gida daga baya sai su dawo gida amman Maryam tace ya fara kai ta taje ta kwanta dan jiri take gani. Dan haka a bakin gate ya ajiye ta, ta fito tana dafa bango fitowa yayi zai kamata ya shiga da ita ta girgiza masa kai tai masa alamar zata iya tafiya da kanta.
"To shiga na gani!"
A hankali ta nufi kofar ta shiga, yana ganin shigar ta ya juya ya koma mota suka tafi. Abbi na shirin fitowa yaga Maryam ta shigo ta nufi sashen Ammi. Karasa fitowa yayi tana shiga ta kwanta akan three sitter tana mai da numfashi, Ammi ta taso da sauri tana fadin
"Sannu ya jikin?"
Hannun Ammi ta kamo ta rumgume a jikin ta tana wani irin kuka mai taba zuciya. Ammi tace
"To menene na kukan?"
"Kukan munafurci ne kuma ba a gida na ba!"
Abbi ya fada yana shigowa ya jefa musu wani kallo da sauri Ammi ta mike tace
"Haba Abbi bakaga a halin da take ba...."
"Ki min shiru Amina ke kike son daurewa yarinyar nan gindi, wallahi ba za a rainar min cikin shege a gida na ba....."
Dum dum dum haka kirjin Maryam ya buga yanzu Abbi har yana yadda cikin shegene me yasa ba zai tsaya yai bincike ba, tasan Abbi akwai saurin zuciya amman ya kamata ya tsaya yai bincike kan ya yanke hukunci ko?
"Me kake nufi?"
Maganar Ammi ta dawo da ita daga tunanin da take.
"Sai ta bar min gida ta tafi can wajen wanda yai mata cikin ta haife ya kula da ita tinda tana da wanda ya fimu zata bashi kan ta ba tare da sanin mu ba."
"Abbi abi komai a sannu ni gani nake ko cikin nan na wani ne zai kasance in ba na Aliy....."
"Na fada miki kada ki soma bari ki bata damar daura masa sharri tinda baya duniya bare yace ba haka bane."
"Abbi...."
"Amina wallahi ba wanda zai canja min hukuncin da na riga na yanke, in har bata son na tsine mata to ta bar min gida, kuma ban yadda taje wajen iyaye na ko yan uwan ta ba. Taje wajen wanda yai mata in ta haihu su dawo tare hukunci ya hau kan ta in ba haka ba kar ta sake ta dawon gida taje ta karasa abinda ta fara."
Suman zaune Maryam tayi jin kalaman Abbin ta. Ammi kuwa cikin gigita tace
"Me kake nufi?"
"Abinda kika ji na fada. Dan haka ta tashi ta fice min a gida."
"Ba inda zata in kuwa har Ummi zata bar gidan sai dai mu tafi tare!"
"Kofa a bude take amman ban yadda ta zauna min a gida ba."
Ya juya zai fita sai ya juyo ya kalli Maryam da sauri ya dauke kai daga kallon ta yace
"Kada na dawo na sameki a gidan nan. Kije ki kawon uban cikin jikin ki in ba haka ba kada ki kara kallon gidan nan a matsayin gidan ku."
Ya juya ya fita fuuuu. Ammi zama tayi tana kuka. Maryam ta dauko paper ta rubuta
"Ammi ki daina kuka, ke kike hanani kuka mu dauki tamu kalar jarabawar nasan Abbi yana cikin bacin rai ne amman Ammi ki sani ba zan aikata abinda addini ya haramta ba. Ammi ni zan tafi kafin Abbi ya dawo!"
Ta bata takardar ta shiga daki ta dauki check book dan bata san inda ATM din ta yake ba ta dauki jaka ta fito a bakin kofa ta samu Ammi ta durkusa alamar neman yafiya Ammi ta kamo ta suka shiga daki tace
"Ba zan barki tafi wani wajen ba Ummi dole duk inda zaki na kasance tare dake, zan hakura da auren mahaifin ki na kula dake da abinda ke cikin ki, hannun ka baya taba rubewa ka yanke, bansan me Allah ya ke nufin mu dashi ba, zan kasance dake a ko da yaushe."
Paper ta dauko ta fara rubutu, tace
"Kada kice haka Ammi, akai na zaki rabu da zuri'ar ki nasan kowa yasan me nake tare dashi tsana ta zai yi zanje zan rayu da ciki na da abinda zan haifa tinda nasan ko na fadi na wane ba yadda zakuyi ba. Ammi ki sani zan kula da kai na, ki yafe min Ammi ki nemar min yafiya a gun Abbi!"
"Bafa inda zakije!"
"Amma kinji abinda ya fada ko? Ban taba sabawa wani a cikin ku ba yanzu ma bai kamata na saba muku ba bayan ni ce mai laifi gwara nabi komai a hankali wata rana sai labari wata rana komai zai wuce, fatana nima yanzu na mutu kawai nabi *Miji nah* bazan iya rayuwa ba Yaa Haidar ba, Ammi ki yafe min!"
Ta rubuta ta mike Ammi ta kamata tana gama karantawa ta mike ta rumgume ta tace
"Naji zaki tafi amman kije gidan Yaya Fadima zan miki visa ki tafi wajen Ummu ki!"
"Ammi, Abbi yace kada naje gidan kowa nasa."
"Na sani amman