Showing 69001 words to 72000 words out of 232912 words

Chapter 24 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1257

min da yarona ki fada masa Abbi nasa yana son sa, yana kular min dake kada ya bari kiyi kukan komai. Ki kasance jaruma a duk inda kika tsinci kanki. Ki rike Allah shi kadai zai dafa miki ki dinga min addu'a ki sa yaran ki suna min addu'a. Ki sa yaran ki suna min addu'a ki fada musu suna da wani Abbi mai son su tin kan suzo kullum burin sa ya gansu. Ki yafe min *Matar Haidar* kada ki manta dani duk runtsi duk wuya. Allah ya shiga lamarin ki ya rabaki da duniya lafiya. Allah ya rabaki da Baby na lafiya. Allah miki albarka yai miki tukwici da gidan Aljanna. Ina son ki, ina kaunar ki, zanyi kewar ki. Allah miki albarka!"
Ya fara maganar yana lumshe ido maganar sa kuma ta fara sanyi.

Hawaye kawai Maryam take dan kalaman sa ba karamin dukkan ta suke ba ta kasa gane inda ya dosa ma gaba daya.
"Bazaka tafi ka barni ba, bazaka tafi ka barni a wannan rayuwar ba. Ni matar kace kai kadai, kada ka manta kai ka fada *Matar Haidar* taka ce kai kadai dan Allah kada ka tafi ka barni ai ciwo ba mutuwa bane zaka rayu Yaya zaka rayu zan kasance mata ta gari mai son farin cikin ka da kula da kai. Kai ka dai ne farin ciki na. Yaran mu zasu tashi tare damu zasu san mu gaba daya su so mu ka daina cewa ba zaka san su ba, ka bari dan Allah."
Ta kare maganar tana kuka ta dago sa ta rumgume a kirjin sa. Ji tayi ya sauke wata ajiyar zuciya ya sakar mata nauyin sa wanda a hakan yasa ta leka fuskar tasa gaban ta ne ya fadi ganin yadda yake mata murmushi amman idon sa a rufe.

"Yaa Haidar!"
Ta kira sunan sa. Shiru taji tace
"Sannu ka samu bacci kenan sannu!"
Ta kara tallafe shi. Sai dai me gaban ta ne yake ta yin luguden faduwa.

Ammi da Mamah ne suka shigo dakin, kokarin janye shi ta fara amman ta kasa dan yai mata nauyi, Mamah tace
"Bacci ya samu?"
Kanta a kasa dan kunya tace
"Eh!"

Ammi ta karaso ta kalle shi sosai sai ta juya ta fita da sauri. Abbi ta kira ya karaso tace
"Abbi kaje ka duba Aliyu kamar fa ya mutu!"
"Me?"

Ya fada yana cewa
"Innalillahi wainna illahir rajiun!"
Ya juya ta kara kiran sa ya juyo tace
"Kaga dare yayi kayiwa su Mamah da Maryam magana su zo mu tafi kan su gane me yake faruwa!"

Kai ya gyada kawai. Ya nufi dakin. Mamah ya kalla yace
"Sha biyu saura tinda ya samu bacci ya kamata ku tafi ko?"
"To Alhaji!"

Ya isa ya janyewa Maryam Aliyu daga jikin ta, sannan yace
"Ki kwantar da hankalin ki, kinga ya samu bacci da ya tashi zai ji sauki."
Kai ta gyada tana zubar da hawaye. Mamah ta fita itama tabi bayan ta har ta kai bakin kofa ta dawo ta tsaya a gaban gadon tana kallon sa, ji take kamar ta kwana a gun sa dama Abbi yace ta kwana, dan ko ta tafi ba nutsuwa zata samu ba ita ta sani. Abbi yace
"Kije Mama nah kinji."

"To Abbi kai masa sannu in ya tashi,.."
"Toh."

Ta juya ta fita. Yaa Alkasim ta gani a bakin kofa tace
"Yaya zan tafi in ya tashi dan Allah ka kira ni. "
"Toh!"

Ammi ta kama hannun ta suka fice da sauran matan aka bar Abbah da Abbi da Yaa Alkasim sai Yaa Muhmmamd. Abbi kuwa yana ganin Maryam ta fita ya matsa jikin gadon yasa hannun sa a hancin Aliyu yaji ba numfashi hannun sa ya dago ya taba jijiyar nan ma bata motsawa bayan kunnen sa yasa yatsan sa nan ma babu motsi kai ya girgiza yace
"Allah ya jikan ka, Annabi ya amshi bakuncin ka."

_*Comment din ku na jiya ya bani dariya da yawa gaskiya, abu daya zance muku shine wannan fa labarin baya ne, kada ku damu ku cigaba da bibiya ta a sannu kowa zai farin ciki kamar yadda nake yawan fada to yanzun ma haka ne, fata na dai ni sakon da nake son isar wa ya isa inda nake son yaje.*_

_Masu kuka da fadin Maryam ta basu tausayi, masu jin haushin Haidar sai dai nace ku cigaba da bibiyar alkalami na a sannu zaku gane komai, har yanzu dai bamu sani ba Haidar da gaske ya mutun ne ko me?_

~Muje zuwa wasa farin girki~

*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan, Allah yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*


Maryam Suleiman
*Antty*
ο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 24

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*



Ya ja masa abu ya rufe fuskar sa. Yaa Alkasim ne ya shigo yana ganin haka yace
"Abbi me ya faru?"
Kai Abbi ya girgiza, Yace
"Sai dai muyi hakuri!"

Dai dai shigowar Abbah da Yaa Muhammad kenan. Abbah yace
"Ya rasu ko?"
Kai Abbi ya gyada masa kawai yai shiru. Abbah yace
"Allah ya jikan ka Aliyu Allah yasa can tafi nan Allah ya yafe maka. Ni bakai min komai ba inma kayi a rashin sani ne kuma na yafe maka. Allah ya jikan ka Aliyu...."

Ya kasa karasawa saboda muryar sa dake rawa. Abbi ya karaso ya dafa shi yace
"Kayi Hakuri Allah masa rahma."
"Amin!"

Yaa Alkasin kuwa gaban gadon ya karasa cikin shock yake kallon Aliyu dake rufe bude shi yayi ya zuba masa ido yana fadin
"Anya kuwa Abbi, kalli fa!"

Ya nuna sa yace "Yana numfashi Abbi bai mutu ba, ba yanzu zai mutum ba Abbi kazo ka duba kaga."
Abbi ya girgiza kai ya dawo ya kara duba Aliyu ya dago yace
"Sai hakuri fa Alkasim!"

Dagowa Alkasim yayi yace
"Abbi kalli fa yana numfashi."
Tausayi ya bawa Abbah, Abbi da Yaa Muhammad dan ba numfashin da yake yi. Abbi yace
"Muhammad kira likitocin suzo su kara duba shin."

Ya juya tare suka dawo da wasu nurse da Doctors su Abbi suka basu waje duk suka fita, aka barsu suna kokarin su dawo da nunfashin sa. Amman ina Allah ya amshi abinsa, babu yadda suka iya babu yadda zasuyi saboda wanda ya hallice sa ya dauke wanda ya fisu son shi ya dauke, wanda kowa na can ne, kowa ita yake jira can ne gidan gaskiya ba nan ba Allah ya bamu ikon cikawa da kyau da imani. Allah jikan musulmai yasa sun huta ya kyautata namu zuwan, Amin.
Bayan minti kusan ashirin suka fito gaba dayan su. Da sauri Alkasim ya karaso yace
"Bai mutu ba ko?"

Kai ya girgiza sannan ya dafa shi yace
"Am sorry to say...."
Baya Alkasim yayi da sauri Doctor ya taro shi ya shiga dakin da Aliyu yake. Ruwa ya shafa masa ya farfado yana ganin gadon Aliyu ya mike ya nufi wajen yana fadin
"Dan Allah kuce min karya ne bai mutu ba. Ku kalli fa yana numfashi wallahi yana numfashi kalli cikin sa yana dagawa da komawa."

Kalla sukai sukaga sam ba abinda ke motsi a jikin sa dan haka suka kama Alkasim suka fita dashi suka samu Abbi da Abbah sukai masa bayani. Alkasim kuwa yaki yadda Aliyu ya mutu sai cewa yake su kara dubashi. A haka suka cike komai sannan suka dauki gawar Aliyu aka tafi gida da ita.


*
*
*
Tin da suka fita daga asibitin take kuka ta rasa na menene tasan dai tana tsoron kar abinda Aliyu ya fada ya tabbata kuma tana tsoron kada ya tashi cikin sa yai ta ciwo. Gaba daya ta gama rudewa da fita a hankalin ta domin kuwa bata gane komai da kowa sai zuciyarta dake ta dukan tara-tara kamar zata ballo kirjinta ta fito. A haka suka karasa gida Ammi ta kamata ta sukai ciki. A falo suka samu Inna, Yaya Zainab, Yaya Rabi, Yaya Ummulkurusm, Yaya Hauwa da wasu kannen su Ammi da Abbi. Suna shiga suka hau tambayar ya jikin nasa. Ammi ce tai karfin halin cewa da sauki sannan ta wuce da ita ta kai ta dakinta anan ta samu su Aisha da Rukayya da Zarah da Yaya Fadima duk idon su biyu suna jiran dawowar su.

Jikin Yaya Fadima ta fada tana sakin wani kuka mai ban tausayi da sauri Ammi ta juya ta fita Aisha da Rukkayya da Zarah duk suka karaso suka rufe Maryam suna lallashin ta. Kuka take kamar ranta zai fita dan har numfashin ta yana daukewa yana dawowa.


Mamah ma na komawa aka hau tambayar ya jikin sa. Kanwar ta Hajara ita ta basu amsa Mamah ta shiga daki ta zauna. Yaya Hauwa ce ta shigo ta zauna tace
"Yaya dan Allah kada kisa damuwa ki masa addu'a!"
"To Hauwa."
Ta fada ta zuba tagumi kawai.


Karfe sha biyu da rabi su Abbi suka karaso gida bangaren Aliyu aka wuce da gawar Aliyu. Abbi da Abbah ne sukai masa wanka. Abbi ya aika Yaa Muhammad ya debo kayan da za a bukata a dakin sa. Ta kofar baya ya shiga ya dauko duk abinda za'a bukata suka dawo akai masa wanka aka shirya shi cikin shigar sa. Suka ajiye shi anan falon sa. Aliyu ya kara tsayi da haske da ka kalli face din sa ta kara kyau sai murmushi dake dauke akan fuskar sai ka zata zai yi motsi.

Alkasim kuwa kuka yake yana fadin
"Abbi wallahi bai mutu ba dan Allah kada ku ce ya mutu ku bari ku gani zai tashi dan Allah zai tashi."
Abbi ya kama shi yace
"Alkasim mutuwa gaskiya ce fa kuma duk mai rai mamaci ne, shi da Allah ya kira haka Allah yayi muma muna tafe a ko da yaushe muna jiran zuwan ta. Kai shiru kai masa addu'a zuwa safiyya za a kai shi gidan sa na gaskiya in ya tashi kan lokacin shikenan. Kai da Muhammad ku zauna ni zanje na sanar da gida yanzu zan dawo."

Abbah ya kalla yace
"Kaje ka sanar da Hajiya Binta, halin da ake ciki ko?"
"Toh!"
Tare suka fita shi da Abba lokacin daya har da rabi. Abbah ya nufi sashen sa, Abbi ya tafi gida.

Yana shiga ya zauna wayar sa ya dauka ya fara neman layin Mamah. Tana zaune akan sallaya taji karar wayar ta dauka yayi tana ganin Abbah ta kai kunne tana fadin
"Ya jikin nasa?"
"Kizo bangare na, na dawo yanzu."

Ya kashe wayar. Jiki na rawa ta mike ta nufi dakin Abbah. Zaune ta same shi ta karasa ta zauna tace
"Ya jikin nasa?"

Shiru yayi yana kallon kasa.
"Alhaji!"
Ya dago ya kalle ta cikin tausayi. Tace
"Nace ya jikin sa?"

"Zauna kiji!"
Ya kama hannun ta ya zaunar. Zama tayi ya kalle ta yace
"A ko da yaushe yadda da kaddara mai kyau da mara kyau yana daga cikin shika shikan muslunci kuma Allah kan jarabci bawan sa dan ya gwada imanin sa."

Hawaye ne ya fara zubo mata. Yace
"Bance kiyi kuka ba, amman ina so ki amshi hukuncin Allah da yai mana shi ya bamu Aliyu kuma in yaso shi zai dauke abinsa. Daman amana ce Allah ya bamu to duk lokacin da ya amshi abin sa kar muce dan me. Kina gani dai yanzu ba mu san ina dan uwan sa ya shiga ba wanda kullum muna cikin tashin hankali da damuwa na rashin yana wane hali yana raye ko baya raye amman wannan munga makomar sa, Allah da ya bamu ya fimu so ya amshi abinda dan haka sai muyi masa godiya. Mu bishi da addu'a Allah ya jikan sa, Allah ya kyautata namu zuwan Allah ya jikan sa yasa Aljanna makomar sa, Allah ya yafe masa."

Mamah ya kalla ya dauki hannun sa ya fara goge mata hawayen dake zubo mata, yace
"Kada kiyi masa kuka kinji addu'a zaki masa."

"Allah ya jikan ka Aliyu, Allah yasa can tafi nan. Halin ka na gari ya bika. Baka taba batan ba Aliyu Allah ya yafe maka. Allah ya gafarta maka Allah....."
Muryarta ta fara rawa Abbah ya rumgume ta yana lallashin ta da bata baki akan kada tai masa kuka.

Daga nan suka mike sukaje tai masa addu'a ta koma daki ta shiga ta sanar da kannen ta tace kada a tashi masu bacci da asuba sa ji. Haka ta zauna tana tai wa Aliyu addu'a zuciyar ta kuwa sai zafi take mata kamar zata fashe amman ta daure bata bari kuka ya zubo a idon ta ba.


*
Abbi na shiga bangaren sa ya shiga, Ammi ya aika aka kira takaraso da sauri tace
"Alhaji ya ake ciki?"
Kai ya girgiza mata kawai yace
"Sai dai hakuri."

"Innalillahi wainna illahir rajiun!"
Ammi ta fada tana zama akan kujera.
"Allah ya jikan ka Aliyu, Allah yai maka rahma, Allah yasa can tafi nan, halin ka na gari ya bika!"

"Amin!"
Abbi ya amsa. Sannan yace
"Kada ku sanar da Mama nah halin da ake ciki yanzu."

"Toh"
Ta mike ta karasa bangaren ta ta sanar da yan uwan ta sannan ta kira Fadima ta fada mata tace kada su fadawa Maryam. Ta amsa ta koma.

Akan sallaya ta samu Maryam zaune rike da carbi tana ja. Kallon ta tayi cike da tausayi sannan ta kalli su Aisha tace
"Ku kwanta ku dan huta."

Maryam ta juyo ta kalli Aisha tace
"Kira min Yaa Alkasim kiji ya jikin Yaa Haidar din!"
"Toh!"

Ta dauki waya ta fara neman layin nasa amman har ta gama ringing bai dauka ba. Sau uku tana kira baya dauka ta kalli Maryam tace
"Kila suna bacci ne."

Hawaye ne ya zubo mata ta mike ta fita compound ta tsaya taga motocin gidan duk suna nan bangaren Abbi ta shiga taga ba kowa fita tayi ta nufi bangaren Yaa Alkasim nan ma ba kowa a ciki. Bangaren Yaa Muhammad ta shiga ta samu Anty Rabi zaune tana ganinta ta mike tace
"Lafiya Maryam?"

"Anty ina Yaa Muhammad?"
"Basu dawo daga asibiti ba!"

"Da motar wa suka je naga duk motocin suna gida."
"Ina jin da motar Yaa Haidar ne."

Mikewa kawai tayi ta fita. Dakin Ammi ta shiga ba Ammi dan haka ta juyo ta koma daki ta hade kai da gwiwa kawai tana kuka. Aisha ce ta taso ta dafata ta fashe da kuka itama dan fitar ta Yaya Fadima take fada mata Yaa Aliyu ya rasu.

Dagowa Maryam tayi tace
"Kukan me kike Aisha?"
"Dole nai kuka mana Maryam tayaya kina kuka zan kasa kuka ba zan iya ba, kina karya min zuciya in kina kuka dan Allah ki daina kukan nan."

"Ya zanyi to? Ya zanyi na rasa yaya zanyi kukan kawai nake ji Yaa Haidar nake son gani ko jin muryar sa amman tayaya danasani ban baro asibitin nan ba, danasani acan nai zamana, na kula da miji na."
Ta kare maganar tana sakin kuka. Rumgume ta Aisha tayi tana fadin
"Zaman ki ba abinda zai kara ko zai hana. Kiyi tawakalli ke kike samu a mahanga in mun kauce please ki daina kuka kiyiwa Yaa Haidar addu'a kawai."

"Ina masa amman kinsan me jiki na yai sanyi."
Ta kamo hannun Aisha, ta daura a kirjin ta tace
"Kinji ko? Kinji yadda take buga min ko? Ina son Yaa Haidar ba zan so abu ya same shi ba na kasa nutsuwa da halin da na baro shi yana shan wahala ina ma ciwon zai dawo jiki na. Ke shaidace ko ya abu ya samu dayan mu dayan mu yana ji a jikin sa. Yaa Haidar wani sirri ne a rayuwa ta, Yaa Haidar rayuwa ta ne. Yaa Allah ka bawa bawan nan naka lafiya, Yaa Allah kada ka dauken wannan bawan naka nasan kafini son sa amman shine jigo na garkuwa ta. Allah ka cika mana burin mu, mu tsufa tare, mu haifi yara da jikoki tare sannan mu mutu tare ga kabari na ga nashi sannan Allah ka hadamu a aljanna. Amin Ya hayyu ya qayyum!"

Ta fada tana shafawa. Wani sabon kuka Aisha ta saki dan sanin addu'ar ta ba mai amsuwa bace wacce take dan shi ya riga ya mutu shin ya zata dauki wannan abun in taji cewar Yaa Haidar ya mutu. Gefe kawai taja tana sakin kuka dan abin ita kanta ya bata tsoro.

Mutanen da jiya ke tare ya rumgume ta yana godiya da Allah ta zama matar da kowa ya shaida ashe ba rabon zama ashe farin cikin kenan. Duk soyayyar da sukewa juna shikenan ta kare ta mutu lallai duniya abar tsoro ce. Sai tsoron Allah ya dada kamata ta rufe ido kawai tana mai jin tausayin aminiyar tata. Haka suka kwana a zaune Maryam na kuka Aisha na kuka an rasa me rarrashin wani ma.

Suna zaune aka fara kiran sallah asuba, nafila Aisha ta tashi tayi dan Maryam ta kasa mikewa dan yadda kafafun ta sukai wani sanyi suna zaune sukaji an kira sallah asuba amman sam ta kasa tashi gashi tana son ta kara tada sallah. Sai da Yaya Fadima ta gama sannan ta kalli Maryam tace
"Bakya sallah ne?"

Hawaye ne ya zubo mata tace
"Na kasa tashi kafafu na kamar ba ajikina suke ba ki taimakan."
Mikewa Yaya Fadima tayi ta Kamata har bandaki ta raka ta, shigar ta kenan aka idar da sallah sannan aka sanar da jana'idar Aliyu da za ayi nan da karfe takwas na safe. Tana bandaki sam bata ji ba ta fito tana dafa bango dan har wani jiri take gani. Da sauri Aisha ta mike ta kamata ta tayar da sallah ta jima tana kan sallaya tana addu'a bayan ta gama tai azkar.

Agogo ta dago ta kalla taga karfe shida da rabi. Aisha ta kalla dake rike da carbi tace
"Ki kara kira min Yaa Alkasin naji ya jikin Yaa Haidar!"
Wayarta ta zaro ta fara neman layin Yaa Alkasim amman me a kashe take wayar. ajiyar zuciya ta sauke tace
"Kinji wayar tasa wai a kashe."

"Dan Allah kira min Yaya Fadima!"
Ta fada tana gyara zaman ta. Mikewa Aisha tayi ta nufi dakin Ammi. Anan ta samu Rukayya da Zarah suna ta kuka dan jin mutuwar tasu kenan da sauri suka fita dan tabbatar da cewa wane Yaa Haidar din, fada masu cewa shine yasa suka zauna suna ta kuka sun kasa tafiya wajen Maryam ma. A haka Aisha ta shiga ta same su Yaya Fadima na basu baki.

"Yaya Fadima kizo inji Maryam!"
Mikewa tayi tace
"Ince dai bata ji sanarwa nan ba?"

"Bataji ba so take a kira mata ma Yaa Alkasim taji ya jikin Yaa Haidar?"
Ta karasa maganar tana share hawayen idon ta.

"Muje!" Suka fita tare. Suna shiga suka jiyo sautin kukan ta, hannun ta rike da kan ta tana kukan.



*Allah ka jikan musulmai ka kyautata namu zuwan kasa muyi kyakyawan karshe.*


*Amin.*

πŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 25

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*





Dafata Yaya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login