Showing 162001 words to 165000 words out of 232912 words

Chapter 55 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1247

zo gida yi mata lalle, Inna ce ta shiga dakin da Maryam take rike da flask din pepper soup din da tayi mata da kan ta, tace
"Ni duk kin rame Maryam ko abinci ne bakya ci maza sha ki samu ki kwanta ki huta."

Basma tace
"Mai lalle fa tazo."
Inna ta kalli Basma tace
"Abincin ne ba zata ci ba?"

"A'ah amman...."
"Dan Allah rufen baki, ki barta taci tukkuna, tun safe take garari a titi wai gyaran gashi yanzu kuma daga ta fito wanka na zuba mata abinci sai kizo kice ai mata lalle."

Tsoka biyu taci ta ture ta mike zata fita, Inna tace
"Oh ba zaki ci ba?"
"Inna na koshi baki na dukka babu teste."

"To me zan miki yanzu."
"Barshi kawai Inna bari naje ai min lalle."

Ta fita. Aka fara lallen sai kusan Magrib aka wanke lallenta da yayi kyau ba kadan ba.



*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani. Amin.*



*Antty*[11/30, 12:53] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 66

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Washe gari Kamu da Yini, bayan azahar mai make up da aka yi hiring ta zo tayi ma Maryam very light make up da ya fito da ainahin kyanta na 'yar fillo, ta saka wani lace mai tsadan gaske da Abba yayi mata an mata dauri da head din kayan, ko tsinke ba a taba ba a lefenta ba, gaba daya kayan da zata yi fitan biki Abba ne yayi mata su, tayi kyau har ta gaji barin ita da dama bata make up, kowa sai kallonta yake cike da sha'awa, Aunties din Muhammad da Step mum dinsa Momyn Jawahir duk sun zo, da friends dinsu duk sun zo suma, da Ummi da Mami da Momy lace suka yi, ko kai ka gansu sai sun burge ka, Mama ma ta shigo cikin jama'ah ana ta gaisawa, sosai hakan ya basu Mami mamaki sai dai basu ce komai ba. A haka aka cigaba da shagalin biki, Ummi na lura da Maryam throughout the program bata da walwala kana gani kasan tana da damuwa. Bayan anyi kamu angwaye suka zo sosai Muhammad yai kyau sai sheki yake da tashin kamshi, abokan sa sosai sukai masa kara, shi kansa ya gane Maryam bata cikin haiyacin ta a haka aka tashi taron yana kara lallashin ta.

*
Washe gari haka akai dinner mai kyau da tsari wacce ta hada manyan mutane yan boko.

10pm har an tashi dan Ummi tace bata son ai abun dare nan, suna dawowa Ummi ta ja Maryam dakin Aliyu wanda rabon Maryam dashi wajen sati daya, wanda ko wajen shagalin bikin ta bata ganshi ba.

Ummi ce ta zauna ta kamo hannun Maryam ta zaunar tace
"Maryam ba nace ki kwantar da hankalin ki ba, or do you have any problem da baki son fada min ne?"
Maryam ta girgiza mata kai cikin sanyin murya tace "Ba komai Ummi...."

Sai kuma ta sunkuyar da kanta hawaye ya fara taruwa idonta, Ummi tayi tunanin kila duk fargaban da ko wace amarya ke yi da zulumin barin gida ne ke damun yar tata, ko kuma tana tsoron rayuwar da zata shiga a cikin wadan da bata sani bane, da haka sai ta jawota kusa da ita ta shiga kwantar mata da hankali cikin taushin murya, Maryam dai sai gyada mata kai take hawaye na sakko mata, Ummi ta rumgumeta tace
"Bana son wannan kukan Maryam, today is ur happy day, ki saki ranki please"

A hankali Maryam tace "Na daina"
Ummi tace "Good ki koma daki ki kwanta ki huta kinji."
Kai ta gyada sai kuma Ummi tace
"Zauna ina zuwa dan nasan ba kici komai ba."

Shiru tayi, Ummi ta fita. Aliyu ne ya shigo dakin cike da damuwa ya fada saman kujera yana mai lumshe idon sa sheshekar kukan da ya jiyo yasa ya mike da sauri yana kallon ta. Sanye take cikin kayan dinner ta wanda yake wani dakakken army green ne an daura mata head shima army green ba karamin kyau yayi mata ba da yake fara ce sai ya kara fito mata kyan ta, ga make up din da akai mata kamar a dauke ta a gudu, ko a wajen dinner haka Muhammad ya dinga yaba yadda tai kyau, yan uwan sa ma sosai suke fadin Muhammad yayi dacen mata.

Kamar tasan kallon ta yake ta dago wanda tana dagowa suka hada ido, da sauri ta mike ta karaso inda yake zaune a kasa kan carpet ta zauna tace
"Yaya me yake damun ka? Kaga yadda ka koma kuwa?"

Murmushin karfin hali yayi ya jinginar da kansa da kujera tare da lumshe idanun sa, tace
"Yaya."

Ta kasan idon sa ya kalle ta yace "Na'am."
"Yaya me yake damun ka?"

Kai ya hau girgizawa, cikin tausayawa hawayen dake idon ta suka zubo tace
"Kagan ka kuwa Yaya ka rame sosai kalli fa."

Murmushi yayi kawai tace
"Please Yaya ka fada min me yake damun ka i promise to help you throughout insha Allah."
Ido ya lumshe yace
"It's too late"

kallonsa kawai Maryan take, kafin tace komai yace "Yanzu me kike bukata wanda ba a siya miki ba?"
Rufe fuskarta tayi da sauri da hannayen ta da suka sha lalle sukai kyau dasu, kamo hannun ta yai yana kallon hannun ta can ya dago yana kallon ta yace
"Kin zabi aure akan karatun ki ko?"

Ido ta dan zaro tace "Burin Yaya na zama cikakkiyar likita yaga na gama karatu na dogara da kaina, to ina mai son sanar maka burin ka zai cika zan kasance maka yadda kake so Yaya."

Kai ya hau girgizawa kawai tare da lumshe idon sa, tace
"Yaya please kai ma ka daure ka fitar da mata wacce zata kula da kai, kaga da kana da aure da yanzu matar zata kula dakai, ji yadda ka rame."

Ido ya bude yace
"Bani da mai so na, mai sona Maryam ce kadai, kuma yanzu bata raye, a baya na zata bayan ta ba zan sake son wata 'ya mace ba amman sai gashi kwanan nan son wata ya shiga rai na, wacce son ta daga Allah yake shi ya halicce shi a zuciya ta, ban taba son wata mace kamar ta ba, ita ce macen da nake ma son da ni kaina ban san irinsa ba"

Da mamaki Maryam ke kallon sa tace
"Wacece wannan Yaya ka fada mata."

Yanayin sa ne ya canja launin idon sa ya canja zuwa ja, a hankali yace
"Da farko ban zaci son ta nake ba dan ba irin wannan kalar son nai mata ba, tausayin ta nake da burin naga na inganta rayuwar ta ta yadda zatafi karfin komai da gori a rayuwar ta, ina tsananin tausayin ta wanda ni kaina ban taba tunanin tausayin da nake mata zai rikide ya koma so na aure ba, amma...."

Maryam dake ta kallonsa ta zaro ido tace
"Yaya tasan kana sonta kuwa?"
Ya girgiza kai a hankali yace "Taki ganewa har yanzu"

Maryam tai murmushi hade da tagumi tace
"Meyasa baka fada mata ba?"
"Ina tsoro kar taki amsar soyayya ta ne bansan wane hali zan shiga ba."

"Akan me zata ki amsa soyayyar ka Yaya, bayan you are very handsome... After that ma, Yaya menene aibun ka na dabi'u ko wacce mace zata so ta same ka, ka bar wani tsoro ka tunkare ta kawai ni na fada maka zata amshe ka fiye da tunanin ka. Kana da kyau, and you are a gentle man so babu macen da zata iya wofantar da bukatar, you should stop being afraid zata amshe ka, kila ma tana ganin ka taji tana sonka

Bai san lokacin da wani murmushi ya subce masa ba yace
"Me ya saki kuka?"
"Yaya bari mu gama naka mana ka fada min a ina take zan sanar mata da burin zuciyar ka."

"Na fada miki it's too late domin an bada ita auren ta ma za ayi."
"Ayyah Yaya to ya zamuyi Yaya nauyin bakin ka ya jayo amman kasan me i will always put you in my prayers Allah ya kawo maka mace ta gari mai son ka."

Murmushi kawai yayi yace
"Uhmm fada min me yasa ki kuka?"
"Ban sani ba tinda aka fara bikin nan am restless and Yaya meyasa u didn't attend my wedding?"

"Shagalin mata ne but tomorrow i will be there insha Allah."
Ya fada yana dage mata gira murnushi tayi yace
"To sai me kema kin rame amarya da rama me kika sa a ranki?"

"Am thinking of leaving you all Yaya, zanje inda ban sansu ba zanyi wata rayuwa Yaya ban sani ba ko zasu amshen da so da kulawa."
Tana fada hawaye ya fara zubo mata, magana ta cigaba da yi cikin kuka tana fadin
"Na kasa nutsuwa akan alamarin nan ina tsoro da fargaba Yaya."

Hannun ta ya kamo yana murzawa a hankali, shiru tayi ya saki hannun ya dago kanta ya fara goge mata hawayen yana fadin
"Ki daina kuka i am there with u always so kar ki saka damuwa kinji?"

Ido ta lumshe hawayen dake ciki ya gangaro ya saka handkerchief ya goge mata yace
"Yanzu me kika ci?"
Kai ta girgiza yace
"Bari na kira Ummi a samar miki abinci."

Ummi dake bakin kofa tana jin duk hirar Aliyu da Maryam ta bar wajen ta koma kitchen kiran Aliyu ne ya shigo ta daga tace
"Son lafiya?"

"Ummi kinbar 'yar ki da yunwa."
"Gani nan ina kitchen ai."

Ta kashe wayar ta dauki tray din ta fito ta nufi dakin Aliyu, ajiyewa tayi ta zauna tana fadin
"Ana sallama ne?"
"Eh gata nan sai kuka take sai kace akan ta aka fara aure."

Tai murnushi ta mike tace
"Bari naje Abban ku ya dawo."
Ta mike ta fita, da kan sa ya zuba mata abinci ya mika mata ta dauka zata ci ta kalle sa tace
"Kaima baka ci komai ba Yaya."

"Ke dai kici."
Fuska ta shagawabe kamar zatai kuka tace
"Please come and join me."

Ta saka masa spoon tare suka ci abincin a plate daya suna cikin ci Ummi ta shigo har suka gama sannan Maryam ta dauke kwanukan ta dawo tai masa sai da safe ta tafi.

Aliyu kuwa wanka yayi yazo ya kwanta dan yai bacci amman sam bacci yaki yazo sai tunanin da yake wanda ya haifar masa da zazzabi da ciwon kai, duk da halin da yake ciki haka ya mike yayo alwala akan sallaya ya kwana har asuba bai bacci ba sai da ya dawo daga masallaci yasha maganin bacci da kyar bacci ya dauke shi.


A bangaren Maryam ma haka bayan tai wanka ta kwana a kusa da Basma kasa baccin tai sai juyi da take wanda ganin zata bata lokaci ne a tunani ta mike ta tada sallah kwana tayi tana sallah da addu'a akan auren ta da rayuwar ta ta baya Allah ya dawo mata da komai wanda ta sha kuka kan asuba idon nan ya kumbura, fuskar ta tai jawur ga wani ciwon kai tana sallah asuba bacci ya dauke ta a wajen da tai sallah.



Karfe goma ta farka da wata matsananciyar faduwar gaba, mai gyara ce tazo dan haka nan aka hau mata wanda ya dauke su awa biyu sha biyu aka gama ta shiga tai wanka da ruwan turare ta fito ta turare mata jikin ta da kamshi mai dadi da sanyi, zama tayi mai make up tazo zatai mata kememe ta hana tace bata so, wani ubansun less fari tas aka dauko mata ta saka riga da zani ne sai farin mayafi wanda duk stones din su fari tai daurin ta normal amman sai tai kyau sai kyal-kyali take da ka kalle ta zaka san bata cikin nutsuwar ta, gefen gado ta koma ta zauna Jawahir ce ta shigo tana buda hadi da fadin
"Amarya ta ango."

Maryam ta dago ta kalle ta cikin wani yanayi mai wuyar fasallatawa, Jawahir ta karaso cike da damuwa tace
"Lafiya Sister me yake faruwa ne tin jiya naga yanayin ki ya canja dan Allah ki kwantar da hankalin ki yaya yana son ki muma muna son ki to damuwar menene su Ummi kuna tare na tabbata Yaya zai miki abinda kike so dan Allah ki saki ranki Yaya ta uwar Ya'yan Yaa Khalifa, Yayar Jawahir."

Najwa da Basma ne suka shigo suna fadin
"An gama shiryawa ne?"
Najwa tace
"Ah ya ba ai make up din ba?"

Basma tace
"Tace bata so."
"Amman saboda me Maryam?"

Kai kawai ta dauke dan ko magana ma bata so, Najwa ta mike tace
"Uhmm kinci abinci to?"
"Bata ci komai ba."
Basma ta fada.

Najwa tace
"Jeki ki debo mata ni bana son amarya da rashin cin abinci dan nima lokaci na ban zauna ba cin abinci ba."
Jawahir tace
"Miskilancin Amarya ya tashi yau ango zai sha fama."

Najwa tace
"Da ta shiga hannu zata sake."
Sukai dariya. Wayar Najwa ce tai kara ta kai kunnen ta tana fadin
"Hello Aisha."

Tai shiru tana sauraran ta can tace
"To shikenan zan turo miki ai nazata yau ma ba zaki iya fitowa ba."
Tai shiru sai tace
"To sai kinzo."

Ta kashe wayar tana kallon Maryam da take danna wayar ta wanda bata san me take dannawa ba dan bata jin dadi duk jikin ta wani iri yake mata ga damuwa da take ciki, ga faduwar gaba, Najwa tace
"Ina makwabciyya ta da nake baki labarin sun dawo daga Canada last month ita ce zata zo kinsa bata samu tazo kowanne event ba saboda tsohon ciki gareta bata jin dadi amman tace yau zata zo."

Wacce akewa maganar ma bata san anayi ba sai da Jawahir ta tabo ta, ta dago da sauri, Najwa tai dariya tana fadin
"Wai wannan har bakin ya mutu yau za a shiga hannun mazaje ai ke ki godewa Allah ma da saurayi ne, hmmm wallahi in da mai mata ne ko,? Ko irin su Yaa Aliyu da aka jima da rasa mata sai ya kusan kashe ki."

Dagowa Maryam tai idon ta cike da kwalla, Najwa tai saurin matsowa tana fadin
"Me ya faru Sister dan Allah ki kwantar da hankalin ki."
Ido ta lumshe kawai. Basma ce ta shigo hannun ta rike da tray ta ajiye a gaban Maryam tace
"Ummi tace ki shanye peper soup din nan tas."

Ture kayan tayi tana kokarin kwanciyya akan gado Najwa ta taro ta tana fadin
"Kisha ko tea ne da peper soup din, wallahi zaki wahala in kika ce ba zakici komai ba."

Ummi ce ta shigo tana fadin
"Ina Maryam din maza kici abincin nan kinji ko?"
Maryam ta kalle ta cike da damuwa Ummi tace
"Dauki kisha naza ina kallon ki."

Tea'n da Ummi ta hada mata mai kauri ta dauka ta sha jin dumin sa yasa ta shanye tas Ummi ta sata agaba ta sha peper soup sai da ta gama sannan ta fita, komawa tai ta kwanta, karfe daya tayo alwala ta tada sallah.


*
Bangaren Aliyu ma sai wajen sha biyu ya farka dan rabon sa da bacci yau kusan kwana uku in ya kwanta ko awa bayayi yana bacci sai tunani da kwana akan sallaya, jiki a mace ya mike ya shiga ya jima a bandaki ya fito ya zauna a gefen gado yana goge jikin sa mai ya shafa sannan ya mike ya taje gashin kansa. Wata sabuwar farar shadda ya saka wacce take kyalli ta warwali, yar ciki da babbar riga ce agogon azurfa ya saka ya murza bakar hula ya saka bakin takalmi hadi da feshe jikin sa da turare agogo ya kalla yaga daya saura, da sauri ya mike dan yana son ya samu hudubar juma'a,

Counter ya dauka tare da wayar sa da mukullin motar sa, fita yayi a dakin yana mai dannan counter din bakin sa na motsi alamar tasbihi yake yi, a haka ya fito falo wanda yai dai dai da fitowar Ummi daga bene har ya kai kofa tace
"Dr!"

Tsayawa yayi ya juyo yana amsawa, ta karaso tana fadin
"Na shiga yau wajen uku kana bacci kaci abinci?"
Agogo ya kalla yace
"Ummi in an sauko zanci bari naje kar na rasa sallah."

"Wanne masallacin zaka kasan dai yau za ai daurin auren Maryam."
"Ummi ai acan muke sallah."

"To adawo lafiya Allah kiyaye hanya."
"Amin."
Ya juya ya fita.


A bakin gate din masalacin suka hadu dasu Abbi bayan yai parking motar sa, ya karaso yana kallon su duk kansu basa cikin walwalar su, ya durkusa ya gaishe su, Abba yace
"Allah maka albarka."

Kai ya amsa yana fadin
"Amin Abba."
"Kayi hakuri da duk abinda yazo maka a rayuwa wani abun alheri ne a rayuwa, sai daga baya za a gani, mu iyayen ka ne duk abinda zanuyi maka rashin so ba zai saka muyi maka ba sai dai son da muke maka Allah maka albarka."

Kasa gane maganganun su Abbi yayi, Abbi yace
"Mu shiga daga ciki."







*Allah ya jikan musulmai ya kyautata nanu zuwan yasa mu gama da duniya lafiya. Allah yai mana rahma. Amin.*





*Antty*
[12/1, 18:00] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 67

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*




Suka shiga a gefen Abbi Aliyu yai sallah. Ana idar da sallah liman ya nemi shaidun madaura auren da za ayi, Abba da Abbi da Yayan su Ummi suka karasa wajen Liman, nan aka bada health status din amarya da ango Abba ne ya zaro kudi a aljihun sa ya ajiye a take aka daura aure.

Aliyu dake zaune a inda yake bai taba zaton sunan da yaji an kira na angon ba ana daura auren, haka ya dinga kallon Abba da Abbi ko kiftawa babu, Farouk ma cike da mamaki yake kallon su Abbi. Aliyu kuwa ko motsi ya kasa, can ya lumshe ido ya bude zuciyarsa na bugawa.

Abba ne ya karaso wajen ya sakar ma Aliyu murmushi yace
"Ina fatan ba zaka bani kunya ba. Allah ya taya ka riko."
Kasa gane inda zancen Abba, Aliyu yayi.....


*
Maryam ce kwance akan gado bayan ta idar da sallah counter ce a hannun ta tana dannawa tare da motsa bakin ta, idon ta a lumshe yake, Jawahir da Najwa na falo suna zazzaune, Basma ce kadai zaune a gefen gadon, kamar ance ta bude idon ta ya sauka akan agogon dakin su wanda ya nuna biyu da yan mintuna, bugawar zuciyar ta ce ta dadu tai saurin mai da idon ta, ta rufe tabbas tasan by this time an riga da an daura auren shikenan ta zama matar Muhammad Auwal, wani yanayi ta fada wanda ta kasa gane wane iri ne, mamakin ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login