Showing 222001 words to 225000 words out of 232912 words
Chapter 75 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
idon ta, tana ganin Yaa Haidar ta saki murmushi tana fadin
"Yaya."
Zama yayi yana kama hannun ta yace
"Ya jikin Baby?"
Baki ta tabe kamar zatai kuka tace
"Yaya kai na shi yake damuna."
Hannu ya daura akan nata yana fadin
"Sannu kinji Allah sauwake."
Kai ta tace
"Ya hanya ina Ummin?"
"Suna waje ita da Ammi? Me kike so?"
Kai ta girgiza tace
"Ba komai Yaya baki na duk ba dadi."
"Sannu kinji?"
Kai ta gyada ya zura hannun sa cikin rigar ta ya daura a kasan marar ta yana shafa wajen a hankali a hankali, ido ta lumshe tana jin kewar mijin nata, daya hannun ya daura akan ta yana shafa kan nata, a haka Ummi da Ammi suka shigo har da Mami da zuwan ta kenan wannan yasa Aliyu ya tashi da sauri ya gaishe da Mami tare da fita ya barsu a wajen ta, jikin Ummi ta lafe tana zuba mata shagwaba, Ummi na ta biye mata, sosai Mami da Ammi abun ya burge su suka kara yabawa Ummi na yadda take son Maryam.
A haka sukai kwana biyu wanda Ummi ce ke kwana a wajen Maryam sam ta hana Ammi da Yaya Fadima sai dai su zo, Yaa Aliyu ma sai kula yake da matar sa, dan dakin aka bar musu in ba wani ne yazo dubata ba suna makale da juna, ranar da sukai kwana biyu aka sallamo su suka kom gida, washe gari suka daga da Haidar Karami saboda makaranta, haka ta cigaba da jinya wanda sai da tai sati hudu a Kano sannan ta koma gida wanda shima ba gama warwarewa tayi ba, anan gidan Ummi suka cigaba da rainon cikin ta wanda a haka da kyar take zuwa makaranta, wani abun ma sai ta dawo Yaa Haidar yake kowa mata, satin ta uku da dawowa suka fara jarabawa wanda a lokacin aka kai kudin auren Yaa Farouk da Jawahir.
Da kyar a haka yau lafiya gobe babu suka gama jatabawa wanda a lokacin bikin Jawahir saura sati uku, wanda yai dai dai da cikar cikin Maryam wata uku, ba laulayin nan sam sai kwadayi kuma, ganin ta murmure yasa Yaa Haidar ya dauke matar sa suka koma gidan su da mai aikin Ummi dan Yaa Haidar yace sai ita in ba ita ba baya son wata mai aiki.
Satin su biyu da komawa gida aka fara bikin Jawahir inda suka sha shagali har Rukkayya sai da tazo itama da cikin ta wata biyu, Maryam na mata tsiya tace
"Daman nace tare zamu sauke."
A lokacin bikin su Momy da Basma suka zo har da su Tasleem, wacce itama an sa mata ranar auren ta amman son Aliyu na nan cikin zuciyar ta, a dinner suka hadu lokacin zuwan su kenan dan da kamar ba zasu zo ba sai da Yaa Haidar ya gama sha'anin sa sukai wanka ta saka wani blue less sai zare silver da stone dinkin doguwar riga ne sosai yai mata kyau, ta saka silver takalmi mai tsini da jaka da farin mayafi sosai tayi kyau duk da ba make up ba amman tayi kyau kamar ka sace ta ka gudu.
Tana gaban mirrow tana gyara daurin ta Yaa Haidar ya karaso sanye da sky blue din shadda sai zuba kamshi yake ya saka yar ciki da babbar riga, hannu ya mika mata ta saka masa agogon azurfa da ya mika mata, ta dago ta mudubi taga yana kallon ta, dan jin gina tayi dashi tana fadin
"Honey kallon fa?"
"Ta yadda zan fita dake da wannan kwalliyar bayan maza zasuje su ta kallan min matata."
"Oh oh oh! Wai Yaya kai ka dai ne mai mata da za ai ta kallo na."
"Kyan naki ne yafi na kowa."
Ido ta zaro tace
"Tab ai kuwa Yaya akwai wadan da suka fini kyau."
"A idon na ba wacce ta kai ki kyau, ba wacce ta kamo kafar ki ko tsarar ki, ke mata ma duk maza nage ganin su, ke kadai nake gani a matsayin mace, so ki bar zancen wasu, wallahi ke me kyau ce, nagodewa Allah da ya bani ke Alhamdulillah, yanzu ya za ayi?"
"Na me fa?"
"A fasa zuwa dinner nan."
Jikin sa ta fada tana kukan shagwaba tace
"Abinda kai min a bikin Najwa zaka mai maita min ko Yaya?"
Rumgume ta yayi yana murmushi kasa kasa dan sai yanzu ya tino da lokacin da ya hanata sakat, kafa ta hau bubbugawa da sauri ya rike ta yana fadin
"Haba Baby, our baby fa, kila yana bacci zaki tashe shi kina bubbuga kafa ni fa da wasa nake."
"Da gaske?"
Kai ya gyada ya janyo ta ya rumgume ta, jin irin rumgunar da yai mata yasa tasan yana son ya cika ta da salon sa ne dan kawai zuwa dinner ta shiririce da sauri ta janye jikin ta ta nufi kofa tana fadin
"Ni dai wallahi dare yanayi Honey."
Bayan ta yabi yana fadin
"Zan kamaki ne."
Suka fita shi ya bude mata mota ta shiga sannan ya rufe ya zagaya. Suna karasawa inda ake dinner yaki bude kofar motar ta juyo tace
"Honey menene kuma?"
"Allah kamar mu juya."
Idon ta ne ya fara kawo ruwa, da sauribya fara lallashin ta yana fadin
"Ki rufan asiri kar Ummi taga hawaya tace na saka mata 'ya kuka."
Tai murmushi ta rumgume shi, tace
"Kuma kai din ne ba."
Zai magana yaji ana knocking, ta gefen Maryam ne ya dago yaga Tasleem ce, da yake tint ce wannan yasa bata ganin su, zooming glass din yai kasa yadda iya kan sa take gani kawai dan Maryam na kwance a jikin sa.
"My love!"
Ta fada, wani dum Maryam taji a kirjin ta ga wani abu ya tsaya mata a kirjin ta, kallon Tasleem yake yace
"Yaushe kuka zo?"
"Jiya."
Ta fara kokarin bude mota taji a rufe, murya ta shagwabe tace
"Oh My love ka bude min mana."
Da sauri Maryam ta dago, ta dannan tare da tura kofa, turus Tasleem tayi tana kallon Maryam dan sam bata gane ta ga, taji ance yayi aure amman hakan bai sa ta cire damarar ta ba duk da Abban ta ya bada ita ga dan abokin sa, amman ganin Maryam ba karamin girgiza ta yayi ba, yarinyar kyakyawa ga iya kwalliya duk da batai wani heavy makeup ba amman tayi kyau, ba kamar ita da tai heavy makeup ba. Kan ta farga taji an rufe kofa da sauri ya fita yana kiran ta, kamar ba zata tsaya ba sai kuma ta tsaya, ya karasa inda take ya sha gaban ta ya mika mata handbag din ta yana fadin
"Menene to?"
Wani kallo ta watsa masa tace
"Sai ka koma wajen ur love."
Dan murmushi ya saki yana fadin
"Kishi ya motsa."
A cikin ransa. A fili kuwa cewa
"Ah ah fa Baby kar na koma kuma kizo kina jin haushi."
Dagowa tai ta sakar masa wani kallo, na kenan sai ka koma din?" Hannun ta ya kama yace
" *Matar Haidar* ita kadai."
Duk da taji dadin kalmar amman tana tsoro kar fa ace ya auri wannan fitsararriyar yarinyar ai kuwa da ta kade, dan kalmar da Tasleem ta fada kawai ta tsaya mata a wuya sam taji ta ji ta wuce mata.
Idon ta ne ya kawo kwalla da sauri ya janye ta suka koma gefen motar sa inda Tasleem ta kame tana kallon su, ita kanta tasan sun dace da juna, gani ya rumgume ta yana lallashin ta da wasu tsadaddun kalamai wanda bata san me yake fada mata ba yasa taji zuciyar ta ta baci da sauri ta bar wajen ranta a bace amman tai alkawarin sai ta batawa Maryam rai kafin su rabu.
*To fah Tsaleem ya da haka?*
*To wa ya sani ko Tasleem ta shiga gidan Haidar a ta biyu, tinda ta nace, kuma naga takwara akwai kishi kamar My Sis Nusy* π
*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu gama da duniya lafiya."
*Antty*
[12/13, 12:33] Maryam S Indabawaπ₯°: ο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώο»Ώππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 87
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
βπ»βπ»βπ»
πππππππ
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*ο»Ώ
Daga baya mota suka koma sai da ya gama shanye jan baki ta sannan ya kyale ta, ta dago tana masa hararar wasa mai cike da so da kauna, daurin ta ta fara gyarawa ta kalli kan ta a mirrow, duka ta kai masa a kirji tana fadin
"Shine ka shanyen jan baki ko?"
"To ya za ayi Ranki ya dade?"
"Kaje ka siyo min yanzu."
An gama ya fara kokarin tada motar da sauri ta zare mukullin tace
"Yadda zakaji dadin mai dani gida ko?"
Yai dariya yace
"Sai na kawo karshen rigimar ko?"
"Yaya."
Ta kira sunan sa, ya kalle ta dan yadda ta kira sa kadai zaka san abun da zata fada mai mahimmanci ne,
"Matar Yaya."
Ta saki murmushi tace
"Ni dai in mun shiga kada kayi dariya kaji."
Dariya yayi yace
"To saboda me?"
Baki ta turo tace
"Ni bana so."
"To toh an gama ranki ya dade uwar gida kuma amarya a gidan Aliyu Haidar."
Ta bude jaka ta dauki mudubi ta shafa man lebe, kallon ta yake har ta gama ta gyara daurin ta sannan tace
"Ya nayi?"
Tai maganar tana dage masa gira, murmushi ya saki yace
"Yes kamar mu koma gida."
Hannu ta sa zata bude kofa yai saurin saka lock yace
"Ranki ya dade ki tsaya ki daina abu da sauri fa yanzu kin san akwai little a cikin ki."
Ya fada yana shafa cikin nata cikin wani salo, hannun sa ta buge tana mai shagwabe fuska kamar zatai kuka tace
"Allah Honey ka bari."
"Na bari."
Ya fita yana dariya ya zagayo ya bude mata kofa ya mika mata hannun sa ta kamo ta fito ya rufe a haka suka karasa hall din da yake cike da mutane hannun ta cikin nasa, kowa ya sha kwalliya ya kece raini bama da yake sun hada biki da masu siyasa.
Suna shiga Yaa Muhammad ya hango su sai da gaban sa ya fadi dan tin ranar dinner su bai kara ganin Maryam ba sai yau, sai yaga ta kara kyau tai haske da sauri ya dauke ido yana istigifari dan yadda shaidan yasa zai fara yabon matar wani, hannun Maryam cikin na Yaa Haudar suka fara shiga nan su Yaa Hannah, Yaa Asiya da Yaa Bilkisu da Najwa da Basma wanda suka sha kwalliya cikin hadadden less suka karaso suka rufe su suna liki tin kan su karasa tsakiyar hall din nan aka hau musu kirari, Tasleem bakin ciki kamar ta hadiyi zuciya.
A haka sukaje suka gaishe da su Ummi da Mami, da Momy, da Mama sannan suka karasa wajen da aka ware musu ita dashi wanda an anjiye musu lemo da ruwa, tana zama ya kalle ta yana sakar mata murnushi, ta dan harare shi tace
"Murmushin me kake?"
"Shikenan ni kuma ba zan wa matata murmushi taji dadi ba."
"Hmm Yaya wannan daban kayi shi."
Wani murmushin ya kara ta mike tace
"Kaga ni bari naje wajen amarya da ango."
"Yanzu fa kin zama Anty ki zauna zasu zo su kwashi gaisuwa."
Ya fada yana dawo da ita ta zauna, ai kuwa ana kiran amarya da ango su fito wajen su Yaa Haidar suka fara zuwa mai vedio da camera suka hau biyo su har suka karaso aka hau musu picture nan su Najwa suka karaso duk akai dasu daga nan suka shiga fili suna musu liki sosai sukai musu liki, su Najwa, m Yaya Hannah ana ta rawa, Yaa Haidar ya janyo hannun Maryam dan yaga yadda Najwa ke jijjiga ta wai sai tai rawa shi kuwa bai son ana jijjiga ta dan baya son a wahalar masa da Babyn sa.
Suna zama ta bude ruwa ta tsiyaya a cup ta mika masa amman yai bai sha ba ya kai mata baki dan kurba tayi, sannan ya sha sauran ta, akan idon Tasleem da ta kasa dauke ido akan su, su kuwa basu san da ita bama. Maryam dake kallon wajen da su Najwa suke rawa sai murnushi take, kamar an ce ta dago ta hango Yaa Muhammad na tinkaro su, da sauri ta dauke kai tana danna wayar dake hannun ta, tana jin kamshin sa ya farai musu sallama amman bata dago ba har ya karaso bakin sa dauke da sallama cikin muryar nan tashi mai sanyi, Yaa Haidar ya amsa yana dagowa dan yaso ya gane muryar, ganin Muhammad yasa ya saki murmushi yana fadin
"Bismillah!"
Ya bashi waje ya zauna, zama yayi yana mika masa hannu sukai musabaha yana tambayar ya iyali, sosai suka gaisa Yaa Haidar ya zura kafa ya dan taka kafar ta dagowa tayi cike da shagwaba tana aika masa da wani kallo, murmushi ya saki ya kamo hannun ta yana murzawa yace
"Sorry sorry, kinga Muhammad fa."
Dagowa tayi suna hada ido ta dauke kanta tana fadin
"Ina yini Yaa Muhammad?"
"Lafiya Ahamdulillah ya taro?"
"Alhamdulillah."
"Allah sanya alheri ina Haidar?"
Dube dube ta fara tace
"Yana nan cikin hall din nan."
"Ya kara girma ko?"
Yaa Haidar ya amshi da fadin
"Gaskiya kam ba laifi kusan shakara daya fa."
"Haka ne, Allah yayi masa albarka "
Amin suka fara hira abinsu, sun jima suna hira sannan ya mike yace daman gaisawa yazo suyi, ya tafi.
Abinci aka kawo musu Maryam ta sa hannu zata dauki spoon Yaa Haidar yace
"Abincin zaki ci?"
"Wallahi Yaya ina gani yawu na ya tsinke."
Yasan babu ta yadda zai hanata ci dan haka sai ya saki hannun ta ta dauki spoon din ta fara yagar naman kazar tana ci tana lumshe ido tace
"Yaya Allah da dadi kaci kaji."
Kai ya girgiza yace
'Wannan sai ke Baby."
Haka ta cinye tata half kazar da aka kawo ta koma kan tasa itama ta fara ci, shi lemo kadai yasha bayan ta gama Najwa tazo ta janye ta, idon sa na kan Maryam suna can ana musu picture kala kala da kawayen nasu da su Najwa da su Yaya Hannah, Aisha da Rukky, kamar daga sama yaji tana fadin
"Sweet bro."
Dagowa yayi yace
"Tasleem amarya."
Zama tayi tana yamutsa fuska tace
'Yaya amman dai kasan ina son ka ko? Ni wallahi kai nake so ba shi ba."
Dan murmushi ya saki yace
"Ki hakura da zabin iyayen ki, kila ya zamo alheri a gareki kamar yadda Maryam ta zama alheri a rayuwa ta, ni dai kinsan ba iya rike mata biyu zan ba, bana son hayaniya ku kuma mata daga an hada ku ba abinda kuka iya sai hayaniya."
Kamar zatai kuka tace
"Yaya ni dai in har ka yadda ba zanyi ba."
"Ita kuma matata fa?"
"Sai ka sake ta in zatai."
Wani kallo ya bita sashi, tace
"Allah yaya ina son ka nasan nafita son ka."
Kallon ta yake cike da mamakin kalaman ta na ya saki Maryam, to shi yanzu wa zai saka shi ya saki Maryam babu, shi da Maryam mutu ka raba amman dan ya samu su rubu ta sanyi yasa yace
"Kinsan me? Yanzu ina abinda nace ki fara."
"Me?"
"Canja shigar ki da daukar halin yar uwar ki."
Fuska ta shagwabe tace
"Wallahi Yaya sam bana iya saka Hijab damu na yake yi."
Dai dai lokacin da Maryam ta hango su kenan, take hakalin ta ya tashi zamewa tayi tayo wajen da suke fuska ba walwala ta karaso ta kamo hannun sa da sauri ya mike yana tambayar ta menene? Duk ya damu ganin fuskar ta ba walwala, rakwafawa yayi yana mai tambayar ta, a hankali tace
"Mu tafi gida."
"Tin yanzu kuma?"
Kai ta daga tana kallon sa, idon ta cike da kwalla wanda da sauri ya kamo hannun ta suka fice da daga hall din wajen motar sa suka karasa suka shiga gidan baya ya rumgume ta yana fadin
"Menene to?"
"Kake cewa tin yanzu saboda kana hira da budurwar ka ko?"
"Nifa ba hira muke ba magana muke kinsan Tasleem kanwata ce ai."
"Ni bana so to, kana ganin abinda take maka ai kasan son ka take ni mu tafi gida kawai."
Ta fada hawaye na zubo mata, jikin sa ya jata yana lallashin ta yace
"To naji ki bar kukan uhmm!"
Kai ta gyada ya goge mata hawayen ya fita ya kamo hannun ta suka koma gidan gaba sannan ya tada motar suka bar wajen dinner, a gida ma rigima ta dingai masa ya rasa gane kan ta, har da su kuka yayi tambayar duniya menene amman taki tai magana, da kyar da lallashi ya samu tai bacci yana rumgume da ita, idon sa a lumshe yake tunanin me yasa meta amman ya rasa ganewa sai yake ganin ko cikin nata shi ya fara sata wannan abun, kara rumgume ta yayi yana ji har tana dan kara ya kissing goshin ta tare da mata addu'a ya shafe su sukai baccin su.
Tasleem kuwa bakin ciki kamar ya kashe ta ganin yadda Yaa Haidar duk ya shiga damuwa daga gani sauyi akan fuskar Maryam, da suka bar wajen kuwa kan ta ta kife akan table din tana sakin kuka mai taba zuciya.
*
Washe gari yini, tin safe taso ta tafi gidan Ummi amman Yaa Haidar sam ya hana ta sakat sai lugwigwita ta yake, sai yamma bayan ya dawo daga massalaci suka hau shiryawa cikin ankon atamfar da sukai ta dasu Anty Hanna, Anty Asiya, Anty Bilksu da Najwa wanda dinkin riga da siket din cikin jikin ta da yasa ta dan kara jiki siket din ya zauna cif a jikin ta, rigar ma ta kamata daga kirji tai kyau sosai tana cikin parking gashin ta, wayar ta ta hau kara, Yaa Haidar dake zaune yana kallon yadda take shiryawa ya dauki wayar yana fadin
"Najwa ce."
Ya danna received ya saka mata a kunnen ta, tace
"Yar uwa ya akai."
"Kina ina ne?"
"Yanzu nake shiryawa."
"Tin dazu ake miki waya kina gaki nan, gaskiya kya same mu acan dan har amare fa sun shirya."
"Kai Sis."
"Ba wani kai Sis kin makale a wajen Yaya ma hadu acan."
"Shikenan sai mun karaso."
Ta zare wayar ta juyo kamar zatai kuka tace
"Ai ka kyauta gashi nan sun tafi sun barni."
"Shine me? Sai na kai matata."
Baki ta turo ta dauki dan kwalli ta daura, ta shafa soft perfurm ta dauki mayafin ta ta yafa ta dauki takalmi zata saka ya amsa ya saka mata ta dago tana shafa sajen sa tace
"Thank you."
Yai kissing lips din ta, yana rumgumota,
"Ni dai mu tafi."
Ta kamo hannun sa, jakar ta ta dauka suka fita, a mota ma sai da ya gama jan aji sannan suka tafi. Su Najwa basu dade da zuwa ba suka karasa, wanda sukai sallama da Yaa Haidar ta fito suka rumgume juna ita da Najwa, Aisha da Rukky suka karaso ta amshi Baby tace
"Mai gida na."
Sukai cikin wajen, basu jima da zuwa ba amarya da ango suka shigo su suka shigo da