Showing 90001 words to 93000 words out of 232912 words
Chapter 31 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
ta, shin ya manta daga gidan da na fito ne ko? Bayan kwana biyu da aka sallamo mu yace sam bai yadda Maryam ta zauna masa a gida ba, ki fada min tayaya haka zata faru, bama wai gidan sa ba har gidan yan uwan sa, a ranar na tura ta gidan Fadima kam na shrya mata tahowa nan, to shine fa tinda ta tafi ba a ganta ba ba duban da ba ai ba, amman ba a ganta ba."
"Innalillahi waina illahir rajiun me ya samu Muhammad ya yanke wannan danyan aikin da ilimin sa da sanin sa?"
"Shaidan."
Mahaifin Ammi ya fada yana shigowa dakin, zama yayi yana kallon Ammi yace
"Shine a lokacin kika kasa kiran kowa ki fada masa sai a yanzu da abin ya lalace, kun batar da yarinyar ku me kika zo yi anan to?"
"Abbu ba zan koma ba har sai ya nemon 'yata."
Wani murmushi Abbu ya saki yace
"Kinsan dai ba a yaji bare saki a gida na ko?"
Kai ta gyada yace
"Yauwa."
Ya mike ya fita, Ummu tace
"To yanzu cikin waye da Maryam din?"
"Ummu nima ban sani ba bamuyi maganar ba ina son muyi ba lokaci."
Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Na yadda da Maryam, alamarin cikin nan tabbas akwai wani boyayyen abu a ciki, Muhammad bai kamata yai haka ba ya kamata ya bata dama ta fadi na wane in ma nemo sa ne ayi amman ba ace ita taje ta nemo sa ba sam wannan bai yi ba. Ina Malam shi me yace?"
"Daga can muka taho nan yace lallai su nemo Maryam cikin kwana biyu ransa ya baci sosai."
"Dole ai hukuncin da Muhammad ya yanke sam bai dace ba Allah ya kyauta Allah ya bayyana min Maryam dole a tashi da rokan Allah, Allah ya kare ta ya bayyana ta Amin."
Shiru sukai, Ummu tace
"Amman kema baki kyauta ba da kika taho me kike nufi kenan?"
"Ummu tayaya zan iya zama ba Maryam yarinya karama shekarar ta duka duka nawa ko sha takwas fa batai ba Ummu na kasa samun nutsuwa kullum tunani na tana ina, wane waje take, wane hannu ta fada, kar abinda ake zato taje ta aikata dan na tabbata Maryam ba a son ranta ta aikata abinda ta yadda ta aikata ba."
"Haka ne duk da ance ba'a shedar yaro amman nima ina ji a jikina Maryam ba zata taba aikata abinda ake zargi ba wannan boyayyen abun dai Allah ya kawo mai bayyana shi."
"Amin."
Ammi ta fada tana hade kai da gwiwa, dafata Ummu tayi tace
"Ba kuka zaki ba addu'a zaki mata kinji?"
Kai ta gyada tana mikewa ta shiga daki, kwana ta biyu Abbi yazo, zuri'a Alhaji Ahmad suka amshe shi hannu bibbiyu ba tare da nuna komai ba, sai da aka bashi masauki, da dare suna tare da Abbu, Abbi ya dukar dakai yace
"Abbu nayi kuskure wanda tin ba aje ko ina ba nayi nadama wanda bansan har yaushe zan daina wannan nadamar ba."
"Me ya faru?"
Nan Abbi ya bawa Abbu labarin komai, Abbu ya girgiza kai yace
"Muhammad ai hannun ka baya taba rubewa ka yanke, kayi kuskure kamar yadda ka fada wanda akace bakin alkalami ya riga ya bushe sai dai addu'a Allah ya bayyana Maryam da bayyana wannan gaskiyar."
"Amin Amin."
Sukai shiru, Abbi ya kara dukar da kai yace
"Daman tahowar Ammin tasu yasa nace bari na biyo bayanta na bata hakuri."
Murmushi Abbu yayi yace
"Ba komai ai ta sani ba'a yaji a gida na bare saki dan haka dole ta koma ko tana so ko bata so, me kayi mata ai kaima yar kace in za taji ciwo kaima zakaji, ni ba zan yadda akan ta a farai min yaji ba, ko zalunta ake ci gwara ta zauna tayi ibada bare bata taba kawon karar ka ba, sama da shekara kusan arba'in dan haka dole ta koma a cigaba da hakuri, Maryam kuma mun bayar da addu'a insha Allah za a ganta kuma tana cikin waje mai kyau da izinin Allah."
"Allah ya yadda."
Daga nan suka fara hira a tsakanin su, har suka kusan raba dare, washe gari da safe da Abbi ya shiga gaishe da Ummu, Ammi na zaune a falon sam bata san yazo ba dan ba wanda ya fada mata sai ganin shigowar sa tayi, kai ta dauke suka amsa sallamar ya gaishe da Ummu, Ammi ta gaishe shi ba tare da ta kalli inda yake ba ya mike tayi ciki, da kallo ya bita sai da ta shige ya sauke kai yana fadin
"Ummu ayi hakuri nima nasan nayi kuskure sharrin shaidan ne."
"Ba komai Muhammad wannan tamu kalar kaddarar kenan yanzu fatan mu kawai Allah ya bayyana Maryam, kuma yasa tana hannu na gari."
"Amin Ummu."
Bai jima ba ya bar wajen, Ammi da Alkasim kuwa kwana suke yi a harami suna addu'a Allah ya tsare Maryam. Kwanan Abbi biyu yacewa Abbu zai koma dan ya cigaba da cigiyar Maryam, Abbu yace tare da Ammi zasu tafi, sam Ammi bata so ba har da hawaye haka tabi Abbi suka bar kasar har da Alkasim.
*
Bauchi
Tinda aka fita da ita sai daya aka dawo da ita lokacin ta farka. Tea matar ta hada mata ta bata amsa tayi idon ta na cikowa da kwalla dan tasan ba iya sha zatai ba kuma yunwa take ji.
"Menene?"
Kai ta girgiza. Tace
"To kisha kinji!"
Baki ta kai tea din bata sauke cup din ba sai da ta sha kusan rabi dan yadda take jin yunwa tana gama sha ta mike a guje ta shiga toilet ta fara kwara amai tin tana iya yi har ya zama sai kakarin kawai. Ummi na dafe da ita har ta gama sannan ta dauraye mata baki ta fito da ita ta kwantar ta gyara wajen. Dankalin ta dibar mata tayo wajen gado dashi. Maryam na ganin haka ta juya mata baya tana girgiza kai.
"Ki tashi ki daure kici rashin ci shi yake sawa kike wahala a aman da ba komai a cikin ki."
Ta fada, tana dagota kuka ta sakar mata, Matar tace
"Dan Allah ki daure kici kinji!"
Ta dauki fork ta dauki dankali daya takai bakin ta, bata gama hadiyewa ba ta fara kakarin amai kan ta kai bandaki ta dawo dashi a tsakar dakin. Anan kasa ta kwanta tana dafe kanta da kirjinta. Ummi ta kamata ta shiga bandaki da ita ta dauraye mata baki ta dawo da ita kan gado wajen ta gyara sannan ta fita ta kira doctor dan ya saka mata ruwa tinda ba abinda take iya ci. Ruwan ya saka mata sannan tace
"Ya gwaje gwajen?"
File din da ya shigo dasu ya dauka yace
"Yadda nayi bincike na gane rashin maganar ta ya samu asali ne na shiga shock da tayi, sai ciki da take dashi na wata uku, bayan nan jinin ta ya hau sosai, ga ciwon zuciya dake son kama ta. Ko cikin zai sa jinin ta ya hau ya saukar mata da zazzabi da ciwon kai to bare ga hawan jini kuma gashi ba ruwa sosai a jikin ta dan bata iya cin abinci and she is too young tana bukatar kulawa sosai dan tana bukatar abubuwan gina jiki, dan ba jini da yawa a jikin ta."
"To yanzu ya za ayi, bata iya cin koma fa da taci abu sai amai ya za ayi da haka?"
"Babu wani magani da zai magance hakan sai dai tana samun abunda take so zan dai bata maganin rage aman."
"Toh nagode ya sallamar tamu fa!"
"A gaskiya halin da take ciki gwara ku kara zama a dan kula da ita sosai zaman ta a gida hatsari ne"
"To shikenan!"
Ya ajiye magani yace
"In ta tashi ta daure ta sha wadan nan."
"To insha Allahu!"
Abba ta kira tai masa bayanin komai yace to bari ta farka suji inda yan uwan ta suke dan ba zasu tafi su barta a haka ba.
Bayan sallah la'asar tana zaune akan sallaya Maryam ta farka. Ummi ce ta taimaka mata tai wanka ta dauro alwala wata doguwar rigar ta, ta bata ta saka tayi sallah sannan ta zuba mata abinci da juice a cup.
Juice din ta dauka ta kurba da yake na orange ne da dan tsami tsami sai taji dadin bakin ta ita ce har da shanye cup daya ta lumshe idon ta.
Gyaran murya Ummi tayi wanda yasa Maryam bude idon ta. Ta gyara zama Ummi tace
"Mu ma tafiya ne munzo Bauchi satin mu biyu a jiya zamu juya muka samu accident dake wanda yasa har muka kwana anan. jiya da na baki waya da nace ki kira gida baki kira kowa ba saboda me?"
Idon ta ne ya kawo ruwa. Matar ta bata paper ta amsa ta rubuta
"I don't have anybody to call, ni bansan ko ni wacece ba i only know two people in my life My Ammi and Yaa Haidar, bansan inda Ammi na take ba da Yaa Haidar ba....."
Ta kasa karasa rubutun dan yadda kuka ya kwace mata. Amsa matar tayi ta karanta sannan tace
"What is your Name?"
"Maryam Muhammad Jabeer!"
Ta rubuta. amsa tayi tace
"Where is you Father?"
Da hannu tai mata alamar bata sani ba.
"Your relative?"
Nan mata tai mata haka.
"Ina ne garin ku?"
Shima tai mata alamar bata sani ba.
Kallo ta sosai Matar tayi tace
"Ki fada min gaskiya Maryam bana son karya kinga taimakon ki nayi."
Paper ta dauka ta fara rubutu
"Wallahi bansan komai ba na ganni ne kawai anan ina rayuwa i can't recall my past My Ammi kawai nake tunawa ita ce Mama na. Sai Yaa Haidar my husband, wamda i know i loss him."
*Allah ya jikan mu yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.*
*Antty*
💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 35
By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW
*Bismillahir Rahmanir Rahmin*
Wata ajiyar zuciya Matar ta sauke duk da bata gama yadda da yarinyar ba amman jin cikin ta yana da uba yasa ta dan ji dadi. Kallon ta tayi tace
"Na fada miki bana son karya ki fada min gaskiya."
"Wallahi Allah gaskiya na fada miki ban san kowa da komai ba wadan nan mutane biyun su kadai na sani. Wallahi da gaske nake ba karya nai miki ba. Dan Allah ki taimaken ki kai ni gidan marayu na karasa rayuwa acan ba wanda na sani anan. Am just suffering here ba inda na sani please help me"
Ledar magani ta janyo ta miko mata ta bata idon ta ne ya kawo ruwa. Ummi ta dan bata fuska tace
"Bazaki sa nayi asarar kudi a banza ba daga jiya zuwa yau an rubuta magani na sama da dubu goma sannan ace ba zaki sha ba in baki sha ba tayaya zaki samu lafiya. In baki amsa kin sha ba bazan taimakeki ba zan tafi na barki kinji ko?"
Amsa tayi ta bata ruwa ta watsa maganin ta sha kirji ta dafe tana son ta mike dan amai take ji. Da sauri Ummi ta kamo ta, ta fara shafa bayan ta a hankali a hankali. Ahankali taji ya fada mata amman da yake ita makiyar maganice har da kukan ta. tace
"Tashi kije ki kwanta."
Mikewa tayi ta hau gado tana kwanciyya ta lumshe ido take bacci ya dauke ta.
Wayar Ammi ce ta fara ringing ta dauka tace
"Ya akai My Son!"
"Ummi banji daga gareki ba."
"Name fa?"
"Na tasowar taku!"
"Oh Aliyu... In mun taso zan sanar maka wallahi yarinyar nan ce she is suffering tana bukatar kulawa daga likitoci sosai da sosai."
"Ummi where is her relative!"
"Aliyu yarinyar ce sosai bama wannan ba abubuwan dake damun ta suna da yawa na daya bata magana a yadda na lura kamar tayi losing memory tana rayuwa ne ita kadai gata yarinya tana cikin hatsari ban san ya zanyi ba."
"Ummi ki bata duk kulawar da ya dace but please Ummi your Son is missing you wallahi ko abinci bana iya ci you know abincin ki nake iyaci kawai"
"Ina na Innar ka!"
"Kai ki bar innan nan ai kinsan halin ta dan bakya nan rowa take min in tai abu ta boye bata sammin"
"Kai kuma bakin kwadayi ko?"
"Ummi kinsan Inna ai tasan all what i likes eating to da gayya in ina dakin ta take girkawa kamshi yana busoni taki sammin."
"Ai gwara tai maka haka kaga kayi aure a huta ko?"
"Kai Ummi wane aure ana zaune kalau. Ai ni na gama aure Ummi."
"My son shekaru na tafiya fa shekarar Maryam nawa da rasuwa amman ace bazaka kara aure ba. Shekara sama da takwas fa, auren shine cikar ka na babban mutum gaka har babban mutum amman baka cika ba dan auren shi zai sa ka zama babban mutum."
"Ummi ya jikin yarinyar da kuke tare?"
Kallon Maryam dake bacci tayi tace
"Da sauki."
"Allah sauwake."
"Amin"
"Please Ummi duk yadda za ai gobe ki dawo."
"Insha Allahu my Son."
Sukai sallama. Abbah ne ya shigo tai masa bayanin komai. Shiru yayi yace
"Ya kike ganin za ayi!"
"Alfarma zan nema a wajen ka!"
"Ina jin ki!"
"Zan tafi da Maryam na cigaba da kula da ita har ta sauka lafiya tayi recovery in ta tino komai sai mu maida ta ga ahalin ta."
"Aisha kenan. Kina son taimako. Allah baki ikon kulawa da ita kinsan ba zan hanaki ba kuma yarinyar na bukatar taimako. Allah baki ladan taimakon."
"Amin!"
Washe gari da safe.
Da kan ta, ta taimakawa Maryam tai wanka ta fito ta shafa mata mai sannan ta bawa wata rigar tata ta saka. Tea ta hada mata ta miko mata. Fuska ta bata. Ammi tace
"Ki daure ki sha kinji ko zaki dawo dashi wani zai samu ya zauna. Ko akwai abinda kike so?"
Kai ta gyada. Matar ta mika mata wani paper Maryam ta amsa ta rubuta mata. Amsa tayi tace
"To ki fara shan tea din kan na bayar a kawo miki."
Amsa tayi ta sha kadan ta ajiye. Ammi tace
"Koke fa kinga bai dawo dan dada kadan."
Kai ta girgiza mata sai ta mike tayi bandaki a guje sai da ta amayar da duk tea din sannan tazo ta bata magani shima da kyar ya zauna. Likita ne yazo ya kara duba ta sannan matar ta bata, lemon da tace tana so irin na jiya. Amsa tayi ta sha sosai sannan ta kwanta tana mai da numfashi.
Wayar Ammi ce tai kara ta dauka. Tace
"My son will never leave me to rest!"
"Hmmm na kasa nutsuwa da hutawa Ummi na. Ina kwana?"
"Lafiya lou ya gida dasu Inna?"
"Tana lpy ni ba ruwana da ita."
"Ah haba kai da Innan taka zama kai ruwa da ita ne."
Yai dan murmushi yace
"Ya me jikin?"
"Da sauki!"
"Allah kara sauki."
"Amin!"
"Nayi muku booking flight a Kano nan da karfe uku zai tashi dan Allah duk yadda za ai ku karasa kan three!"
"But Kasan muna da patient ko?"
"Ummi yaushe kika ga warkewar ta ku dawo gida zan kula da komai nata na miki alkawari."
"Da gaske?"
"Yes Ummi i promise."
"Shikenan bari na fadawa Abban ku sai mu nemi transfer ko?"
"Yes Ummi yau zanga My Ummi!"
"Ji ka sai kace wani karamin yaro."
"Ummi duk girman yaro a gun iyayen sa yaro ne kamar yadda nake daukar kai na 5 years old child a gun ki!"
"In da kayi aure ka haifa kai ma ai ka samu wanda zai na maka haka ko?"
"Ummi su Yasmeen, Hanan, Afanan, Afrah, Annur, Ayman duk sun ishe ni wallahi."
"Shikenan nidai bari naiwa Abba maganar."
"Ok Ummi nah."
Suna kashe waya ta kira Abba dauka yayi yace
"Kun tashi lafiya?"
"Alhamdulillah! Ya jikin?"
"Da sauki!"
"Allah kara sauki!"
"Amin! Yanzu d'an ka ya kira ni."
"Aliyu kenan!"
"Yayi mana booking flight a kano by 3pm zai tashi shine yake son mu tafi yanzu!"
"Ya condition din jikin yarinyar zata iya wannan tafiyar mai yawa?"
"Zan tambayi doctor duk yadda mukai sai na fada maka."
"Alright ina jiran dan in da hali kada muyi rana ko?"
"Haka ne ranka ya dade."
Ta kashe wayar ta nufi office din doctor bayan ta shiga suka gaisa sannan tace
"Muna son mu tafi ne shine muke son transfer dan mu koma gida can a cigaba da kula da ita. Sai abu na biyu zata iya tafiya mota nan da Kano."
"No problem akan transfer zan baku tafiya ma zata iya insha Allah!"
"Yauwah to please a gama komai a bamu copy din file din dan kar a samu matsala wajen cigaba da kula da ita."
"Insha Allahu Hajiya yanzu duk zan gama komai."
Nan ta koma ta kira Abba kan ya taho. Bai jima ba ya zo, Maryam na bacci sai da ta tashi doctor ya basu duk abinda zasu bukata suka biya kudin su sannan suka fita dan tafiya
*
Gaba daya Ammi sai tarasa walwala dan kullum tunanin ta inda Maryam take, satin su daya da dawowa su Mami mahaifiyar Haidar suka dawo, wanka kawai tayi ta nufi gidan su Ammi domin acan duk bata samun wayar Ammi. Ammi na zauna a falo rike da carbi tayi nisa cikin tunani Mami ta shiga tana ta kwada sallama amman bata ji ba har ta shiga ta ganta a wannan halin cike da damuwa ta karasa ta zauna tare da dafa Ammi da sauri ta juyo sai ta sauke ajiyar zuciya, tace
"Hajiya ashe kun dawo."
"Meyake faruwa ne? Ko har yanzu jikin Maryam din ne? Ina can hankali na duk yana nan na kasa samun wayar ki gaba daya bare naji ya jikin nata?"
Hawaye ne ya zubo daga idon Ammi, take Mami ta shiga cikin tsoro tace
"Menene Hajiya ki fada min jikin Maryam din ne? Tana ina?"
Hawayen Ammi ta goge tace
"Hajiya Maryam ta 'bata, yau kwana Maryam sha uku rabon ta da gidan nan."
Wata zabura Mami tayi tana fadin
"Innalillahi wainna illahir rajiun! Bangane ba Hajiya bangane Maryam ta 'bata ba."
Sai kuka, Mami kuka Ammi kuka aka rasa me lallashin wani sai da sukai mai isar su sannan sukai shiru Ammi ta bawa Mami labari komai, shiru Mami tayi tana nazari, tabbatas in har za a ce Maryam tana da ciki to ko wanene zai ce cikin Haidar ne, Mami zata so haka amman ba ta wannan hanyar da suka same shi ba, amman duk da haka zata rike jinin Haidar ko dakuwa shege ne, zata nema masa gafarar ubangiji dan tasan daga Maryam har Aliyu ba mazina ta bane sai dai in kaddarar su ce, shekarar Aliyu nawa tare da Maryam ba a taba ganin wani abu na Allah wadai a tsakani su ba.
"Ina ma ina nan ina da no zan riki Maryam da cikin ta ko da ace ba na Haidar bane ballanta na ina da yakinin cikin nan na Haidar ne, bani da kowa a duniya a yanzu iyaye na kadai suka rage min yaran da Allah ya bani shi Abubakar ya bace shi kuma Aliyu Allah ya amshi abunsa hakika bani da