Showing 75001 words to 78000 words out of 232912 words

Chapter 26 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1264

ya saka mata oxygen sannan yace
"A kula da abinda za a fada mata da zai sa ta shiga damuwa ko wani halin!"
Jiki ba dadi su Mamah suka tafi.

Washe gari da safe asibiti ya cika da yan uwa da abokan arziki saboda anji cewar Maryam ta farka. Wanda kowa yake murna sai dai me har goma da wani abu bata tashi ba. Abbi da kan sa yaje wajen likita dan jin ko lafiya Maryam bata kara tashi ba. Tare suka zo ya kara auna ta sannan ya basu tabbacin zata tashi a ko wanne lokaci. Wannan ya dan kwantar musu da hankali.

Karfe daya mazan duk sun tafi masallaci sai matan da wasu ke sallah wasu na zaune jigum jigum. Aisha ce zaune a kan kujera gaban gadon, tana rike da waya tana dannawa akai akai tana kallon Maryam. A hankali ta bude idon ta, ta dinga bin dakin da kallo da sauri Aisha ta mike tana fadin
"Besty kin tashi?"

Juyowa tayi ta kurawa Aisha ido, ko me ta tuna sai kuma hawaye ta bude mata hannu da sauri Aisha ta karasa ta rumgume ta. Yaya Fadima da fitowar ta daga bandaki kenan ta karaso. Mamah ma da idar da sallah ta kenan ta tashi tana fadin
"Alhamdulillah sannu Maryam!"

Ido Maryam ta dago ta kalli Mamah wani kuka ne mai karfi ya kwace mata. Mamah ta karasa ta rumgume ta tana shafa kan ta hadi dabata baki. Lafewa tayi a jikin Mamah. Ammi ma bayan ta idar ta karaso tazo tai mata sannu matan Yayen ta da Yayyen ta da kannen Ammi dake waje duk suka shigo sukai nata sannu.

Su Abbi bayan an idar da sallah suka dawo suka samu dakin cike dan Maryam ta tashi. Likita aka kira ya kara duba ta bayan ya gama yace
"Me yake miki ciwo?"

Kallon sa kawai tayi ta nuna kirjin ta, dubata ya kara yace
"Ya yake miki ciwon?"
Yan dakin ta kalla amman ta kasa magana, Abbi ya karaso yace
"Mama nah fada masa ya yake miki ciwo!"

Da hannu tai masa alama. Doctor ya kalla yace
"Ka gane?"
Kai ya gyada. Abbi yace
"Amman meyasa ba magana?"



*Wasu na fadin basu gane ba, to daga FLASH BACK na tafi rayuwar Maryam ne kan tazo gidan su Ummi da Yaa Haidar (rayuwarta ta baya) wanda a gaba na tabbata zaku gane, ba wannan Aliyun miskili bane ya mutu, wata rayuwar Maryam ce kan tazo wannan rayuwar da fatan kun gane, sannan ku cigaba da bina sannu a hankali, zaku gane komai insha Allahu.*

*Allah ya jikan musulmai Allah yasa muyi kyakyawan karshe, Allah kyautata namu zuwan. Amin*




Maryam Suleiman
*Antty*


ο»Ώο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 27

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*



"Muje office!"
Doctor ya fada ya fita. Abbi da Yaa Muhammad suka bi bayan sa. Yan dakin kuwa sai murna suke suna mata sannu Maryam kuwa ba magana sai hawaye dake zuba a idon ta kawai.


Abbi ne zaune shida Yaa Muhammad sai Doctor dake duba file din Maryam. Mikewa yayi yace
"Ina zuwa!"
Sannan ya koma dakin ta. Sallamar su yayi dan su basu waje aka barta ita dashi sai wasu nurses sawa sukai ta mike tayi tafiya sannan suka sa tayi motsi da wasu part din jikin ta, bayan ta gama yace
"Yi min magana Maryam!"

Idon ta ne ya kara cikowa da hawaye sai ta girgiza kai alamar ba zata iya ba. Duk yadda yaso tayi bata iya ba. Har suka gama suka kira Ammi akan abinda zasu iya bata taci wanda Nurse zasu kawo mata yanzun nan. Sannan ya koma office wajen su Abbi.

Zama yayi yai danyi rubuce rubuce sannan ya dago yace
"Kuyi hakuri dan Allah!"
"Ba komai!"

"A gaskiya Maryam ta shiga hatsari sai dai cikin hukuncin Allah, Allah ya kawar da hatsarin wanda halin da ta shiga wani daga shi yake mutuwa wani ya makance wani ya kurmance wani ya bebance wani kuma ya rasa wani bangare na jikin sa kamar rashin tafiya da sauran su. To yanzu daga can nake naje na duba ta Alhandulillah matsalar tata ba wata babba bace domin kuwa ciwon kadan ne dan naga magana ce ta dauke mata kuma insha Allahu zamu daura ta akan magani da yaddar ubangiji in da rabo sai ta warke amman gaskiya ba a fiya warkewa ba."

"Innalillahi wainna illaihir rajun! Alhamdulillah! Allah mungode maka da wannan jarabawar Allah ka bamu ikon cin wannan jarabawar wannan yarinya Allah bata ikon dauka da cinye ta. Amin!"
Abbi ya fada. Yaa Muhammad yace
"Toh Allah yasa a dace!"

Magunguna ya rubuta sannan ya mike yace
"Zan kawo mata maganin yanzu!"
Mikewa su Abbi sukai sukayi masa godiya suka koma daki inda Nurses suka shiga da ita bandaki Yaya Fadima ta taimaka ta gyara ta suka fito ta zauna akan kujera daya daga cikin nurse din tana hada mata abinci dayar kuma tana matsa mata kafafun ta. Maryam kuwa sai bin yan dakin take da kallo kamar bata san su ba.

Gama hadawa tayi ta karaso ta zauna zata bata abincin kai ta dauke, tace
"Haba My sister ki daure kici ko yaya ne?"

Kai ta girgiza. Yaya Fadima ta amsa tace
"Haba dai Kici kinji kanwata."
Dagowa tayi ta kalli Yaya Fadima sannan ta girgiza ka.

Aisha ce tace
"To me kike so?"
Hawayen dake makale a idon ta ne ya zubo ta daga hannu tai mata nuni da cewar Yaa Haidar shi take son ta gani.

Abbi da ya gane me take nufi ya karaso ya kama hannun ta yace
"Kiyi hakuri kinji Mama nah, Aliyu ya tafi inda ba zai dawo ba."
Kuka ta fashe dashi tana girgiza kanta, Aisha ta rumgume ta tana jijjiga ta.

Ammi ce tace
"Wai Abbi rashin maganar nan fa?"
"Zatayi da yaddar Allah!"

"Toh! Allah ya yadda!"
Haka kememe taki taci abinci, magani ma kin amsa tayi sai allura da akai mata har da ta bacci dan taki ta daina kuka tin da ta tashi kuka kawai take yi wannan yasa sukai mata allura. Kwana ta uku da farfadowa amman sam bata cin abinci sai karin ruwa kuka kuwa shi ya zaman mata abun yi ko da yaushe. Maryam ta rame sosai sai idanu da hanci da suka fito.

In suka zauna ita da Yaa Alkasim tai ta kuka shima sai kukan baya iya lallashin. Kullum cikin nasiha da lallashi su ake a haka ta kwana ashirin a asibiti wanda a lokacin aka sallame su. Lokacin da ta koma gida komai sai ya dawo mata sabo saboda tina yadda suke rayuwa da Yaa Haidar a lokacin baya wanda kullum suna tare.

Tana zaune a falo hannun ta rike da Kur'ani tana karantawa Ammi na kitchen tana hada mata kunu ko zataji dadin bakin ta. Yaa Alkasim da Yaa Abdullah suna zaune a gefen ta.
Da sauri ta dago sai kuma ta mike tana kallon kofa. Yaa Abdullah ne yace
"Menene?"

Kofa ta nufa tana nuna musu da, musu alamun Yaa Haidar ne. Kasa ganewa sukai Yaa Abdullah ya mika mata paper da sauri ta amsa ta rubuta masa
"Muryar Yaa Haidar ne yai sallama wallahi shine!"

Tana bashi ta nufi kofa da sauri Yaa Abdullah da Yaa Alkasin suka mike suka nufi ta suna fadin
"Ba shi bane Maryam gizo take miki!"

Kai ta hau girgizawa tana nuna musu tare da tafiya kamo ta Yaa Alkasim yayi ya rumgume ta yana kuka yace
"Wanda ya mutu baya dawowa Maryam ba Yaa Haidar bane? Haidar ya mutu kuma ba zai dawo ba."

Kuka ta kuma saki tana girgiza kai a haka Aisha ta shigo ta same su, karasowa tayi ta ajiye basket din hannun ta tace
"Menene?"
Yaa Abdullah ne yai mata bayani sai ga Aisha ma na hawaye. Ammi ce ta fito da cup dan ta gamai mata ta gansu a haka.

Ita har ta gaji da wannan kukan nasu kullum haka suke yini kuka a asibiti yau ma sun dawo gida wato zasu cigaba da musu ko?
"Me kuma ya faru?"
Duk suka juyo suka dawo dakin. Yaa Abdullah ya karai wa Ammi bayani. Kai Ammi ta girgiza ta kamo hannu Maryam ta zaunar tace
"Kina da sani fiye da tunani mai tunani kin taba ji inda wanda ya mutu ya dawo?"

Kai ta hau girgizawa. Ammi tace
"To dan me kike cewa shine?"
Paper ta dauka ta fara rubutu tace
"Wallahi Ammi muryar sa naji Ammi dan Allah kuje ku duba min ko shine ya tsaya a waje dan Allah Ammi!"
Ta mika mata Ammi na karantawa idon ta ya kawo ruwa ta dago zatai magana suka jiyo sallamar Mamah.

Amsawa sukai Mamah ta shigo da sauri Maryam ta mike tana nuna mata kofa tana mata da hannu alamar wai taga Yaa Haidar, Mamah tace
"Me take nufi?"

Kan su bata amsa ta dauki memo ta fara rubuta mata tace
"Mamah kinga Yaa Haidar a waje wallahi yanzu yazo yana sallama ni ban da bakin amsawa jin ba a amsa ba ya juya ina jin!"
Amsa Mamah tayi tana karantawa itama idon ta ya kawo kwalla sannan ta rumgume Maryam tana fadin
"Haidar ya mutu Maryam kuma ba zai dawo ba."

Kwacewa tayi a jikin ta, ta sake rubuta mata
"Mamah ke mahaifiyar Yaa Haidar ce kika sani ko Allah ya dawo mana dashi ko kuma zaki ji tsoro in ya dawo ne ni bazan ji tsoron sa ba Ammi dan Allah ku dubo ko shine ya dawo."
Ta bata takardar. amsa Mamah tayi ta karanta. Kai ta girgiza Maryam ta kama hannun ta tana roko. Yaa Abdullah ta kalla tace
"Kaga jeka ka dubo mana ko dai shi din ne?"

Ta fada tana kifta masa ido ya juya ya fita. Mamah tace
"Ya jikin nata Hajiya?"
"Da sauki!"

"Taci abincin kuwa?"
"Ina fa kunu nayo mata na fito na same ta tana wannan maganar!"
Ta mika mata kunun kai ta make. Mamah tace
"In har baki sha ba ko Haidar din ne bazai shigo ba


Da sauri ta amsa ta fara sha sai dai me bata sha rabi ba ta ajiye ta dafe ciki sai kuma ta fara juyi tana kuka, da sauri sukai kan ta wanda ta cigaba da juyi kan su farga har ta suma da sauri Yaa Alkasim ya dauke ta suka tafi asibiti suna zuwa suka aka amshe ta bayani sukai wa doctor ya duba ta ya bata gado kan ta tashi suga halin da take ciki. Bata jima ba ta farka tana ganin Mamah ta fara nuna mata da hannu wai Yaa Haidar din yazo.

Tana gama nuna mata kuma sai ta rike ciki tana kuka dan yadda yake mata ciwo. Doctor yazo ya duba ta ya kara bata magani sannan ya samu ya lafa bayan awa daya yace zasu iya tafiya amman kada ta sha abu mai tsami kila ulcer saboda rashin cin abincin da batayi.

Dakin ta Ammi ta kai ta, ta kwantar da ita amman duk bayan mintina sai ta tambayi
"Ina Yaa Haidar a kira mata shi."

Abbi yai mata rubutu amman abun sai dada gaba yake ba zaka taba ganin idon Maryam ba hawaye ba. Kullum cikin kuka. Kowa tausayin ta yake da kwantar mata da hankali dan yadda suka san tsakanin ta da Yaa Haidar dole ta shiga damuwa. Ta dada ramewa dan ba bacci ba cin abinci.




Tin daga ranar duk abinda zata ci sai ta amayar dashi, duk ta rame kullum suna cikin yawon asibiti.

Mamah ce zaune Maryam kwance a kan cinyar ta. Mamah tace
"Gobe zamu tafi Umrah Amman sati biyu zamuyi mu dawo zan roka miki Allah ya baki lafiya Maryam!"

Hawaye ne ya zubo Mata. Mamah tasa hannu ta goge mata. Ammi ce ta shigo ta zauna tana fadin
"Kukan ake ne?"

"Hmmm Hajiya gobe fa ne tafiyar!"
"To Allah ya kaiku lafiya Amin!"

"Amin ga amanar Maryam nan dan Allah a kular mana da ita."
"Insha Allahu."

Daga nan suka cigaba da hirar wanda kullum hirar dai ta Aliyu ce. Maryam na kwance tana jin su amman ba bakin magana.

Sai yamma Mamah ta tafi. Tana shiga ta hadu da Ummah zata fito kallon ta, ta tsaya yi tace
"Iska na wahal da me kayan kara, duk abinki ba zaki sake haihuwa ba Kuma yarinya ba zasu baki ita ba sai bibiyar su kike to zanyi maganin abun. Kuma ke da ake cewa mai haihuwa tinda kika haifi yara biyu kin kuma? Bama wannan ba yanzu ina yaran daya ya shiga duniya daya ya mutu kinga biyu babu daya kike da wacce bata taba haihuwar ba."

Kai Mamah ta dauke tayi cikin kawai. Ummah tai dariya tace
"Sai naga bayan ki da shegiyar yarinyar nan Maryam!"
Ta fita a gidan fuska ba walwala.

Washe gari dasu Mamah zasu tafi ta shiga yin sallama ta samu Maryam a bandaki tana ta amai tausayin ta bata bayan ta gama ta kama ta ta dawo ta zaunar da ita.

Ammi ta gyara wajen Mamah tace
"Amman ni da an koma asibiti wannan aman yai yawa ayi test da aune aune gaskiya."
"Wallahi ni har na gaji da zaryar asibiti kusan wata kenan ana fama da abu fa."

"To ya zamuyi, ai sauki sai a sannu yake zuwa da sannu zamu samu nasara."
"Shikenan gobe na fadawa Alhaji muje."
"Allah kaimu."
Anan Mamah ta zauna har sai da Abbah ya shigo ya duba Maryam sannan Yaa Alkasim ya tafi kai su Airport

Ranar kwana sukai Maryam amai dan da ta sha ko ruwa ne sai ta dawo dashi. Akan ta yan gidan suka kwana gaba daya sun tausaya mata. Ai kuwa ana dawo daga sallah asuba suka tafi asibiti amsar ta akai aka saka mata ruwa dan jiki ta yayi mugu weak bayan an saka mata ruwa wata nurse ta shigo ta dibi jinin ta dan yin test.

Dakin cike da yan uwan ta ita kuwa tana ramuwar bacci da bata samu tana yi. Wajen karfe sha biyu Nurse din ta shigo da file a hannun ta, bude na farko tayi tace
"Jinin ta ya hau dole a kula da ita dan yarinya ce bai kamata ace jinin ta ya kai har haka ba."

Ta dauki dayan file din tace
"Mun mata na malaria da typhoid all are negative!"
Ta dauki dayan file din ta bude sai ta saki murmushi tace
"Oh congratulation tana dauke da ciki ashe shiyasa take ta wahala har haka!"


*Ai ban san ana bibiyar labarin nan nawa har haka ba, amman shine fisabilillahi ba dan comment bare vote, facebook ne kadai masu yin kokarin yin comment da liking, haba to zan daina nima na koma na kwanta. Gaskiya ku gyara in ba haka ba to nima posting sai naga dama.*


*Allah ya jikan musulmai Allah ya kyautata namu zuwan yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*




*Antty*
Maryam Suleiman

ο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 28

By
*MARYAM S INDABAWA*
HAJOW


*Bismillahir Rahmanir Rahmin*


Dai dai farkawar Maryam wanda taji abinda Nurse din ta fada. Dummmmmm haka dakin ya koma babu wani abu da yake motsi na wani dan lokaci. Kallon kallo suka fara yiwa juna. Maryam kuwa zuciyar ta kamar ta fito daga kirjin ta dan yadda take bugawa da tsalle. A wannan lokacin da za'a sake auna jinin ta ba karamin hawa ya sake yi ba saboda tsananin firgicin da ta tsinci kanta a ciki.


Takardar hannun nurse din Yaya Zainab ta fizga tana karantawa jikinta ya hau rawa. Yaya Ummulkursum ta karbi takardar suka hada kai ita da Yaya Fadima da Yaa Abdullah suka karanta. Gaba dayansu takadar suka saki ta fadi kasa fuskar su cike da tsoro da fargaba.

Ammi dake gefe ta zaro ido tana tambayarsu me suka gani a takardar. Kasa magana sukai. Yaa Alkasim kuwa ko kallon takardar baiyi ba ya fita wurin likitan ya nufa ya samu Yaa Muhammad suna tattaunawa akan ciwon Maryam da rashin maganar har yanzu. Kamar wanda aka jeho haka ya shiga office din ransa ya gama baci. Yaa Muhammad ya mike da sauri yana fadin
"Menene ko jikin Maryam din ne?"
"Ina fa ba gwara jikin ta ba da abinda suka ce tana dashi. Wata mahaukaciyar nurse ce take fadin wai ciki ne da ita!"

Ya maida kan sa kan Doctor yace
"Ka taso muje ka duba ta da kan ka, dan ni ban yadda da aikin ta ba ko canjen result akai."
"Is ok ka kwantar da hankalin ka kaji zan kara duba ta, na gani kaji!"

"Is better!"
Ya biyo bayan sa, suka nufi dakin gaba dayan su. A tare suka koma dakin wanda yayi shiru kamar ruwa ya cinye mutanen cikinsa. Karar fanka kawai ake ji sai jefi jefi wannan ya kalli wannan. Suna shigowa likitan ya dauki result din ya karanta.

Kallon Yaa Alkasim yayi yace
"Ba an daura mata aure ba, mijin ya rasu?"
"Yes!"

"So shine me?"
"Kaga ka kara gwada min ita kawai."

Sirinji ya dauko a cikin aljihun lab coat din sa sannan ya karasa wajen gado inda Maryam ke kwance komai ya tsaya mata cak. Jinin ta ya dauka sannan ya fita da kansa ya shiga lab ya kara yin gwajin. Sai da yayi sau uku yana bashi result iri daya dan haka ya dawo dakin. Kowa yasa ya fita sannan ya karasa wajen gadon inda Maryam dake jin duk abinda ke faruwa take.

Ido ta bude wanda ya rine yai jajir, Paper ya bata yace
"Zan miki tambayoyi kinji kanwata?"
Kai ta gyada!

"Wata nawa da auren ku?"
Shiru tayi tana nazari kan ta ya kulle wanne zata fada to wannen ne dai dai in ta fadi wancan me iyayen su zasu ce.

"Kanwata!"
Ta dago ta kalli shi.
"Fada min kinji?"

A paper ta rubuta sannan ta mika masa. Amsa yayi ya gani yace
"Are you sure?"
Kai ta gyada yace
"When last did you saw your period?"

Abinda tin dazu kwakwalwarta ta kulle babu wani tunani da take iya yi sai yanzu ta dawo hayyacinta da taji wannan tambayar. Hankali a tashi dan zata ce tin kan su fara exam da tayi wani period marar ta tai ciwo har ta dawo gida bata karayin wani ba. Shin me hakan ke nufi kenan?

Taiwa kan ta tambayar
"Fada min kinji!"
Rubuta masa tayi ya amsa sannan yace
"Kin tabbata?"

Kai ta gyada masa ya jin jina kai yace
"Good"
Fita yayi ya kira Ammi da Abbi sannan ya kalle su yace
"A bisa binciken da nayi da kuma amsar da tambayoyi da nai mata, ya nuna tana da *CIKI* na kusan wata uku."

"Lahaula walaquwwata illabillah........ La'ilaha illalahu Muhammad Rasulillahi Sallalahu alaihi wasalam!"
Ammi ta fada. Mika musu result yayi sannan ya fita.

Amsa Abbi yayi da zuwan sa kenan bai san me yake faruwa ba. Takardar ya karanta sannan ya juya ya fita kawai. Ammi ta bishi da kallo sannan ta kalli Maryam dake fidda numfashi kadan kadan. Hawaye na zubowa a idon ta.

Zuciya ta kuwa bugawa take kawai tsoro, fargaba, farin ciki ta rasa wanne zatayi a duniya. Yaa Alkasim ne ya shigo da sauri yace
"Ammi me ya faru?"
Kai Ammi ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login