Showing 123001 words to 126000 words out of 232912 words
Chapter 42 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
sai ya rage daga Inna sai Mama da Ummi da Maryam. Aliyu ma acan ba zama yai ba kullum yana harami yana sallah da addu'a ga matar sa da Maryam akan Allah ya bata lafiya. Kullum zai kira Ummi sau uku ya tambaye ta ya jikin Maryam kuma a tafiyar sa taje an kara dubata tare da cigaba da shan maganin ta. Sosai ta dan samu sauki dan cikin ya kara kwari.
*
Bayan Sallah da sati daya su Aliyu suka dawo, Ummi ce ta hada musu abinci na tarba, kala kala, lokacin da Aliyu yaga Maryam yai mamaki domin kuwa ta dan murmure ba kamar da ba.
Inna ta mike ta fita tana fadin
"Bari naje na bar wajen nawa ba kowa!"
"To Inna sai anjima angode! Maryam tai ma mata godiya ta tafi. Ummi tace
"Kina shiga kuna gaisawa da safe kinji?"
Kai ta gyada. Suna zaune a haka Aliyu ya shigo ya hangi Maryam zaune da dan cikin ta a gaba. Kai ya dauke dan ganin ta a wannan yanayin ya tino masa da Maryam matar sa. Ido ya dauke da sauri ya shiga dakin sa. Da kallo Ummi da Maryam suka bishi, yana shiga ya fada saman gado yana lumshe idon sa. Maryam kawai yake gani tana masa gizo a indon sa. Ido ya runtse yana fadin
"May your gentle soul continue to rest in peace Hayyaty"
Da kyar ya mike ya shiga ya watsa ruwa ya dauro alwala kiran sallah yaji ana yi ya fita da sauri, rike da ledar da ya shigo da ita. Ba kowa a falo Dan haka ya ajiye akan dining ya fita.
Bai dawo ba sai wajen Tara. Ummi, Abba da Maryam zaune akan dining. Ummi da Abba na cin abinci, Maryam Kuma gaban ta gashin kaza ne sai lemo da take Sha.
Aliyu ya karaso yana kallon ta, ta gefen ido sannan yaja kujera ya zauna a gefen Ummi. Yace
"Barka da dare Abba!"
"Ya kake Aliyu?"
"Alhamdulillah!"
Ya kalli Ummi yace
"Sannu da gida Ummi!"
"Yauwah Aliyu ka dawo lafiya?"
"Alhamdulillah!"
Ya kalli Maryam ya dauke Kai da sauri tare da fadin
"Ya jiki?"
Da hannu tai masa Alama da sannu. Abba ya kalle ta yace
"An samu abin Dadi ko motsin ta ba a ji."
Sukai murmushi gaba dayan su. Aliyu ya mike Ummi tace
"Abincin fa!"
"Ummi zanci amman sai anjima."
Ya fada yai cikin daki. Ummi plate ta dauka ta zuba abinci sannan ta kalli Maryam tace
"Kisha maganin ki fa!"
Fuska Maryam ta bata. Ummi tace
"Kin fison allura ko?"
Kai ta girgiza. Ummi tayi dakin Aliyu kwance ta same shi a kan gado ta ajiye abincin ta karasa ta dafa shi ya juyo yana kallon ta. Ta kamo hannun sa suka dawo kan kujera ta mika masa plate. amsa yayi ya fara ci sai da ya cinye ya sha ruwa sannan ta mike ta fice a dakin da kallo ya bita yana mai kara jin son Ummi yau da ba Ummi ya rayuwar sa zata kasance. Ummi itace hope din sa yana godiya ga Allah da ya bashi Ummi kamar yadda Ummi ke godiya da Allah da bai bata haihuwa ba amman ya bata yaro mai son ta da jikan ta.
*
Washe gari kafin Ummi ta tafi aiki tace mata tashi ta gaida Inna. Ta amsa bayan mai aikin su tazo ta gama aikin ta ta rufe sashen ta tafi wajen Inna. Sosai Inna taji dadi komai ta zakulo a dakin in ta dauko ta ajiye mata sosai Inna tai tayi mata hirar. Tin fa daga ranar kullum Ummi ta tafi aiki Maryam wajen Inna take zuwa su sha hirar su sosai Inna ke son Maryam dan akwai biyayya ga aiki duk da bata magana amman Inna zata cikata da hira wanda Maryam sai dai nuni da hannu ko murmushi a haka suke rayuwa. Tin safe in taje sai Ummi ta dawo da yamma take komawa sashen su. Dan haka tsakanin Inna da Maryam sun saba da shakuwa da juna ba tsawon watannin da suke kasancewa tare.
Cikin Maryam na dada girma jikinta na wani murjewa da kara kyau a lokacin cikin ta wata bakwai in dai zata awo Aliyu ke daukar ta suje a duba ta daga nan a asibiti suke zama sai zai dawo suke tahowa tare. Sosai ta saba da Aliyu ta kuma ji ta aminta dashi domin yadda yake dawainiyya da ita ba dare ba rana da kudin sa da jikin sa. Dan ba zata manta ba lokacin da tana kan laulayi sun sha kwana akan ta shi da Ummi. Abu da zata iya cewa shine Aiyu bai da fara'a sosai amman akwai biyayya da kyautatawa.
Zaune take a falon Inna bayan ta idar da sallah magarib din ta, mikewa tayi ta kalli Inna tai mata nuni da zataje taga ko Ummi ta dawo. Inna ta ce to. Ta fita a hankali ta nufi sashen nasu ba kowa dan haka ta juyo tayo sashen Inna.
Fitarta kenan ya shigo ya nufi sashen Inna. Wanda bai jima da zama ba ta bude labuye ta shiga da sauri ya dago dan ganin wanda zai shigo ba sallama. Kai yai saurin daukewa yana son ya tuna a ina yasan fuskar nan tata. Ta shiga ta wuce kusa da Inna tai mata nuni da basu dawo ba Inna tace
"To Allah sa lafiya har yanzu!"
Farouk ya mike kenan Ummi tai sallama ya amsa yana komawa ya zauna ta shigo dakin Maryam ta mike ta karaso ta amshi jakarta tana mata murmushi. Itama murmushin tai mata tace
"Ya jikin?"
Ta amsa mata da kai. Ta kalli Inna suka gaisa Farouk ya gaishe tana yana satar kallon Maryam.
Inna tace
"Ai sai zarya take baki dawo ba."
"Allah sarki mantawa nai ban fada mata ba yau munyi meeting ne amman lafiya kalou!"
"To Allah kyauta."
Suka yiwa Inna sai da safe sanna suma fita. Suna fita Fatouk yace
"Inna wannan ba dai yarinyar na bace?"
"Ita ce me ya faru?"
Baki ya tabe kawai ya mike ya fita. Maryam ce ta taya Ummi girki suka gama suka wuce sama ta watsa ruwa ta kwanta. Karfe tara da minti biyar Aliyu ya shigo gidan a gajiye. A falo ya zauna yana lumshe ido dan bacci ya fara ji.
Ummi ta sauko tace
"Ah ka dawo?"
Kai ya gyada yace
"Eh wallahi Ummi na gaji ne"
"To fa ga Maryam can na jiran ka wai ice cream din ta ya kare!"
Maryam ce ta sauko daga bene tai masa sannu da zuwa da hannu tai masa alama ido ya lumshe ya mike ya nufi kofa tabi bayan sa.
A parking space ya tsaya yana kara wayar sa a kunnen sa, bayan ya dauka yace
"Kana ina?"
"Ok tsaya nazo na baka sako!"
Ya nufi kofar tsayawa tai ya juyo ya kalle ta. Yace
"Menene?"
Tai masa alamar fita take son tayi.
"Muje sai kuje tare ni wallahi na gaji wanka nake son naje nayi na kwanta "
Bayan sa tabi a bakin gate suka samu Farouk a cikin mota. Aliyu ya karasa gefen taga yace
"Gata nan kuje zata siyo ice cream!"
Dagowa yai yana hango Maryam a bayan Aliyu, fuska ya tsuke. Ya mika masa Atm din sa yace
"Kuje sai kun dawo!"
"Hamma Aliyu ta fadi abinda take so zan siyo mata. Ka bar kudin ka."
"A'ah so take ta dan ga wajen! Kuje kawai."
Aliyu ya bude mata mota tashiga gaba ta zauna ya rufe yace
"A tafi a hankali!"
Ya juya ya koma ciki. Kallon ta, ta gefen ido yayi ya dauke kai ya tada motar. A bakin super market din yai parking ya fita itama ta fita. A bakin wajen ya tsaya yace
"Kije ki dauki abinda kike so na baki minti goma!"
Ita dai ciki tayi ta je ta zabi ice ceam din da take so da wasu chocolate sannan ta taho, wani saurayi ya amsar mata basket din duk da ba wasu kaya bane amman yadda take tafiya ga ciki ga kayan ya bashi tausayi ya amsa. Shi ya biya mata kudin ma dai dai lokacin da Farouk ya karaso yana tambayar nawa? Saurayin ya mika kudin yana
"Na biya mata ai!"
"Akan me?"
"Saboda Allah!"
Saurayin ya fada ya mika masa ledar kallon sa yayi yace
"Ka bata abar ta!"
Hannu Maryam ta mika zata amsa yace
"Zaki iya?"
Kai ta gyada tai masa alama da hannu cewar ai ba nauyi. Mika mata yayi ta amsa tana godiya sannan ya fice. Bayan sa tabi ta tsaya a jikin mota, Farouk ya karaso ya bude motar ya shiga ta sa hannu ta bude itama ta shiga ta zauna.
Da gudu ya fusgi motar ya bar wajen suna shiga parking space Mama na dawowa parking tayi shima Farouk yayi ta fito ta tsaya kallon sa taga an bude dayan sashen. Maryam ta zuro kafa, Mama ta kalla sai ta tuna karshen haduwar su tinda taki aminta da bukatar ta bata kara ganin ta ba. Wani kallo ta dinga binta da shi. Maryam ta durkusa ta mata alama da hannu da ina yini ko kallon ta batai ba ta kalli Farouk tace
"Daga ina kake?"
"Uhmm Hamma ne daman....."
"Ka samen a daki yanzun nan!"
Tai gaba Farouk ya bi bayan ta, Maryam tayi sashen su. A dining ta hangi Aliyu na shan coffee ta karasa fuskar ta dauke da murmushi ta ajiye ledar nata agaban sa ta karya wuya.
"To aje aci lafiya!"
Hannayen ta, ta hade tana godiya ya mike rike da cup din hannun sa yace
"Gud nyt!"
Ya shiga kitchen tayi sama tana murmushi. Ummi ta sama a falo ta zube mata kayan da ta siyo a gaban ta. Ummi tai murmushi tace
"To kije kici abinki ko?"
Tura mata gaban ta tayi alamar ta dauka hannu ta sa ta dauki chocolate daya tace
"Nagode!"
Daukar kayan tayi ta saka a firij sannan ta shiga tai wanka ta fito ta saka kayan bacci. Ice cream din ta sha tai alwala ta haye gado tai addu'a ta tofe jikin ta.
*Allah ya jikan musulmai ya kyautata namu zuwan yasa mu cika da kyau da imani Amin.*
*Antty*
[11/22, 13:46] Maryam S Indabawaπ₯°: ππ *MATAR HAIDAR* ππ
Page 50
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
βπ»βπ»βπ»
πππππππ
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Tana shiga ta cire mayafin jikin ta ta juyo tana kallon sa. Kai yai kasa da shi tace
"Kai me ya hada ka da wannan yarinyar?"
"Nifa ba komai. Kawai Hamma Dr ne yace na kai ta super market!"
Wani kallo ta jefa masa tace
"Kada na kuma ganin ka tare da yarinyar nan."
"Mama..."
"Mama me? Kada na kuma nace!"
"To Mama!"
Ya mike yace
"Bari naje nai wanka."
Bata kalle sa ba ta shige daki ya mike ya fice shima.
*
Tinda cikin ta ya shiga wata takwas kuma sai hankalin ta ya fara tashi dan da ta kwanta bacci ba abinda take sai mafarkan Yaa Haidar da Ammi. Dan haka bata bacci sam, kwana take sallah duk ta shiga damuwa da ka ganta zaka ga tana cikin damuwa da kuma ta kadaita sai kuka.
*
Yau lahadi yawancin kowa yana gida yana hutun karshen mako, tin safe Maryam bata sauko ba Ummi ce ke ta aikace aikacen ta Aliyu na dining area tinda ya gama breakfast yake aiki a system din sa shi kan sa da yaji motsi a stair yake daga kai yaga ko Maryam ce amman shiru har wajen 12. Dan ba karamin sabo sukai da Maryam duk da bai fiya magana ba amman a irin wannan lokacin suna tare wani lokacin tana kwamce akam kujera shi kuma yana zaune a dining ko tsakiyar falo yana aiki duk wani motsi da za tai akan idon sa abu kadan zai juya ya kalle ta, sannan duk abun na bukatar mai ciki na kwadayi bata rabo dasu shiga dari fita dari sai ya shigo mata da abu.
Ummi ce ta fito a kitchen ta kalle shi tace
"Wai lafiya har yanzu bata sauko ba?"
"Kila bacci take."
Ya fada yana pressing system dinsa. Kallon sama tayi tace
"Let me go and check dai!"
Ta nufi sama ya bita da kallo. Dakin ta nufa ta bude kofar dakin, acan kuryar dakin ta hango ta akan sallaya ta hade kanta da gwiwa. Karasawa tayi a hankali ta dafa ta, da sauri ta dago idon ta duk hawaye. Zamewa Ummi tayi ta zauna tana fadin
"Lafiya meyasa kike kuka ko wani abu kike ji?"
Kai ta girgiza ta hau goge hawayen idon ta. Ummi tace
"A yanzu baki da kowa sama dani ki dauke ni as your Ammi, u should call me Ammi, come to me with all ur problem i promise to help you out insha Allah. So now tell me what is wrong with you?"
Hawayen idon ta, ta kara gogewa tana girgiza kai. Paper Ummi ta miko mata tace
"Fada min kinji!"
Amsa tayi tace
"Ummi i miss my past, i want to recall back."
"Dole kiji haka Maryam amman fada min wani abu akai miki?"
"No Ummi bana son na mutu ban gansu ba, ina tsoro kada wajen haihuwa na mutu."
Hannun ta Ummi ta kama tace
"Wa yace miki zaki mutu. Mutane nawa ne suka haihu shin mutuwa suke. Bazaki mutu ba insha Allahu sai kin tuno kowa kin koma gida cikin yan uwan ki. But before than ki dauke mu as your family kinji mu kan mu mun dauke ki yar mu kinji ko? Ki kwantar da hankalin ki."
Rumgume Ummi tayi tana kuka sosai. Ummi na lallashin ta da kyar tai shiru.
"Me kike so?"
Kai ta girgizawa Ummi.
"Akwai abinda kike ji?"
Nan ma ta girgiza kai. Tace
"To ki sauko kasa zama waje dayan ba dadi ai ko?"
Mikewa tayi ta dauko Alkur'ani da carbi ta biyo bayan Ummi. A dining ta hange sa bata kalle sa ba ta nufi falo ta zauna akasan carpet dan tafi jin dadin zaman kasa ta mike kafafun ta ta fara karantun Alkur'ani idon ta kan Alkur'anin take karantawa a zuciyar ta.
Tin da ta sauko yake kallon ta. Sanye take da hijab har kasa dan three quarter wando da wata armless riga ce a jikin ta shiyasa ta saka Hijab dan yanzu duk bata iya saka kaya duk da an dinka mata masu fadi amman tafi gane saka kananu budaddu. Cikin nata ya kara kasa kuma yaga yadda fuskar ta tadan daga da kafafun ta.
A hankali ya mike ya koma cikin falon a gaban ta ya durkusa ya kai hannun sa kan kafar ta ya latsa kallon wajen yayi ya dago ya kalle ta itama shi take kalla suna hada ido duk suka kawar da kallon junan su.
"Me ya samu idon ki?"
Kai ta girgiza hawaye na ciko idon nata.
"Bakya exercise ko? Anjima zamu fita sai kin zagaye unguwar nan sau uku dan kiji sannan gobe ki min wanki kinji ko?"
Dagowa tayi tana kallon sa a razane murmushi ya dan saki ya mike yace
"Ki shirya ya kamata kina motsa jiki kada haihuwa tazo kina a haka ba wani motsa jiki da kike."
Ya koma dining yana cigaba da aikin da yake. Ummi ce ta fito ta karaso tanan fadin
"Dr ina son anjima ka kaimu super market mu kara shopping."
"Me zaku siya kuma?"
"Kayan Baby!"
"Kai Babyn nan dan gata ne. Har yanzu ba a gama masa siyayya ba. Zai kwacen fada wajen Ummi na. Ko da yake Ummin sa ta kwacen ma."
Kallon Maryam yayi bama ta san me suke yi ba dan ta lula duniyar tunani. Yace
"Ummi ina jin jinin ta fa ya hau."
"Na shiga uku bana son hawan jini da ciki fa."
"Ai illa ne Ummi. Kuma naga alamar tana cikin damuwa me yake faruwa ne?"
"Kawai fargaba ce."
Shima ji yai jikin sa yai sanyi da tunawa da Marym da yayi. Shiru yayi Ummi ta koma kitchen tana fadin
"Sai kace kaine da cikin har ka shiga damuwa ai Allah zai raba lafiya mutane nawa ne suka haihu lafiya."
Komawa yayi ya jingina da kujera tare da lumshe idon sa hakika yana tausayin mata tin bai aure ba da yai aure sai abun ya dadu haka da matar sa ta samu ciki nan ya kara tausayin mata da masu ciki hakika yana tausayin Maryam. Mikewa yayi ya koma daki ya kwanta kawai. Bai fito ba sai da akai sallah azahar yai alwala ya tafi massalaci bai dawo ba sai bayan sallah la'asar a falo ya same ta zaune gaban ta flask din abinci ta kasa ci tayi shiru tana jan carbin hannun ta.
Karasawa yayi ya zauna a gaban ta ya tankwashe kafa yana fadin
"Kinci abincin kuwa?"
Ya dauki plate ya fara zuba mata abincin a ciki. Kallon sa tayi har ya gama ya tura mata gaban ta yace
"To kici."
Kasa tayi da kai, ya dauki spoon ya debo ya nufi bakin ta dashi yana fadin
"To bude nai feeding naki."
Dagowa tayi ta kalle shi idon ta cike da kwalla, ya girgiza kai yace
"Open ur mouth!"
Budewa tayi a hankali ya bata ta amsa ta fara ci. Tana cinye na bakin ta ya kara debowa ya nufi bakin ta da spoon din dai dai shigowa Farouk dauke da jaka a hannun sa. Tsayawa yai yana alajabin abin Hamman sa ke bawa wata abinci a baki har sai da ya mutsuka ido amman ya tabbatar da gaske abinci yake bata a baki. Sallama ya karayi ya juyo yana kallon sa wanda hakan yasa yai saurin yin kasa da kai
"Kai min daki."
Ya juya ya tafi ya ajiye ya fito ya same sa yana bata lemo kai ya dauke ya fice a dakin da sauri shi ka dai ya rasa sukuni akan abinda ya gani shi dai yasan yayan sa bai shiga harkar mata sam to amman menene halakar su da yarinyar nan.
Bayan ta gama ya dauke kayan ya kai kitchen sannan ya dawo falon ya zauna. Ummi ce ta sauko tace
"Biyar saura ya kamata muje ko?"
Maryam ya kalla yace
"Zaki iya zuwa?"
Kai ta girgiza dan yau ko fitar ma bata so. Yace
"Kada ki manta anjima ma zaki zagaye unguwar nan three times sannan ki min wanki."
Ummi tai murmushi tace
"To ai ko kai akace ka zagaye unguwar nan sau biyu an hade ka da aiki bare ita."
"Ummi bata son motsa jikin ta kullum fa tana zaune anan ko part din Inna ta dan daina zuwa."
Kallon Maryam tayi cikin damuwa dan yanzu Maryam na cikin damuwa da son kulawa ta jima da sauyawa tin da cikin ta yai wata takwas ta fara sauyawa ta rage walwala da kuzari akan kan ta wanda tin lokacin kan taje wajen Inna hira sai ta kwana biyar ko sati ma kan taje ta gaishe ta Ummi na kula da ita sai a yau da kuma ta same