Showing 198001 words to 201000 words out of 232912 words
Chapter 67 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
da ita yace
"Me kike nufi ne? Kada ki manta fa ni mijin ki ne ba saurayn ki ba"
Fuska ta shagwabe kawai tana mammatse jikin ta, dan jin ta take a takure bata saba ba ko da yaushe da hijab suke ganin ta ko mayafi, sharewa yayi yace
"Me kike anan?"
"Anan zamu kwana."
"Ke dawa?"
"Rukayya."
Kai ya hau girgizawa yace
"No Matata a dakin mijin ta zata kwana"
***
Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)
Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji
Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata
Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219
Chat 08063114606
***
*Allah ya yafe mana yai mana rahma yasa muyi kyakyawan karshe. Amin*
*Antty*
[12/8, 12:31] My Airtel: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 78
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Dis page is ur Amina Yar'adua i really appreciate with all ur comment keep it up. I heart you Mamanah*
Ya kashe wayar tabi wayar da kallo sai ta mike, hijab ta saka har kasa sannan ta fice daga dakin, a compound ta same shi ta karasa tana fadin
"Ina yini Yaa Ahmad?"
"Lafiya lou, ya gida ina My son?"
"Yana can wajen su Ummi ina jin."
Sukai shiru sai kuma ya dago ya dan kalle ta yace
"A baya naso na maye gurbin aboki na amman Allah bai nufa ba, Allah ya karasa kin tabbata a matar Haidar din ba abinda zance sai fatan alheri."
Kan ta a kasa tace
"Nagode Yaa Ahmad."
Yayi mata murmushi
"Babu wata godiya mata zaki bani kawai."
Itama tayi murmushin tace
"Wacece nai alkawarin ni kuma Insha Allahu."
Yai murmushi yace
"Shi nazo na fada miki amman ina neman wata afarma."
Kai ta gyada yace
"Ina so ki dauken tamkar Alkasim wanda in kina bukatar taimako ko wani abu direct zaki fada min ni kuma zan ji dadi fiye da yadda zaki zato, kuma ina son ana bani Haidar yana zuwa gidana hutu."
"Insha Allahu Yaa Ahmad, Haidar kuma d'an ka ne."
"Haka ne sai batu na biyu."
Kai ta gyada yace
" 'Kawar ki nake so Maryam, a jiya na fara jin wani abu game da ita, ta kwanta min itama tana da sanyin hali kamar naki, ina fatan zaki tayani mika kokon barata, a gida an damen da batun aure ina ta dojewa dan ina sa ran dawowar ki to yanzu kin dawo a matsayin Matar aure kin ga dole nima na nemi mata ko?"
"Haka ne Yaya duk da mun jima ba tare ba amman har yanzu Rukkaya na nan a yadda na san ta, tana da sanyin hali da hakuri, tabbas kun dace da juna ba tin yau ba nake maka sha'awar ta, ashe dai da rabon, Allah nagode maka, Yaa Alkasim ya auri Aisha kai kuma Rukayya, nice dai na rasa Yaa Haidar, ko da yake nima ban rasa shi ba tinda ga wani Yaa Haidar din."
Tai magana hawaye na taruwa a idon ta sai yaji tausayin ta kai ya dauke yace
"Zan tafi yaushe zaku koma?"
"Jibi!"
"Ok zan zo muyi sallama gobe, ki turon number Rukuyyan."
Kai ta gyada ta juya kenan Yaa Haidar ya karaso kusan cin karo sukai ta dago da sauri, idon ta dake cike da hawaye ta dago suna kallon juna, gefen sa tabi tayi cikin gida ya karasa wajen Yaa Ahmad suka gaisa yace
"Ai ban san da aure a tsakanin ku ba sai jiya, ina maka fatan alheri da fatan Allah ya kawo zuria ta gari, muna godiya da dawainiyya Allah saka da gidan aljanna."
"Amin Amin Ahmad."
Ya saki hannun sa yabi bayan Maryam dan duk hankalin sa na kan ta, yana shiga falo ba kowa dakin ta ya nufa direct, yana shiga ya same ta kwance akan gado ko hijab din ta bata cire ba, karasawa yayi ya zauna a gefen gadon yana dago ta gaba daya, a zabure ta dago ganin shine yasa ta sauke ajiyar zuciya, a jikin sa ya matse ta yana fadin
"Menene?"
Kai ta hau girgizawa yace
"Fada min sirrin zuciyar ki."
Kin magana tayi, yasa hannun sa ya dago kanta, ta runtsa idon ta yace
"Ni dai na gaji wallahi dan Allah fada min abinda na jima ina gani a cikin idon ki."
Da sauri ta bude idon ta tana son taji me ya jima da gani a cikin su, ganin Maryam na son raina masa hankali yasa ya sake ta tare da fuskantar ta, hannun ta dukka biyun ya kamo ya rike ya dago fuskar ta ya saita da tashi yace
"Ki tsaya a haka."
Kallon sa take, ya kalle ta shima yace
"Akwai shekarun baya da zan tafi na fada miki komai akan ina karantar mutum, to saboda me ba zan karanci ma wacce nake so ba, a lokacin na so ki sanar dani sirrin zuciyar ki, amman kika ki, har kika yaudari yaron mutane, dan nasan ba son sa kike ba kin amshi shi ne kawai a rashi na, wanda naso nai wauta da na kasa fada miki sirrin zuciyata har wani yaso ya dauken ke, ni dake mun so muyi zurfin ciki, amman Allah ya kaddara cewa ke din Matar Haidar ce, in tambaye ki da kin aure shi yaya zakiyi da soyayya ta?"
Idon ta lumshe yace
"Fada min."
"Yadda zakaji haka zanji koma naji fiye da nakan."
"Kinsan da cewa ina sonki?"
Kai ta sunkuyar ya saka hannun sa ya dago kan nata yace
"Kin sani?"
Kai ta girgiza yace
"Karya kike Maryam, yadda nake mu'amalantar ki kadai zaki kawo akwai wani abu a kasa, kawai dai ke sai kin wahalar dani ko?"
Fuska ta kawar tace
"Aah."
"Gashi nan, kinsa sai wahala nake, shakara fiye da bakwai ina dawainiyya da son ki, na sha wahala akan sonki."
"Meyasa kaki ka fada min?"
Ido ya lumshe yana fadin
"Ban gama yadda da so bane a baya na zata tausayi ne dan tin da na fara ganin ki wani abu ya darsu a zuciya ta, ba wata soyayya mukai da matata kan ta rasu ba kafin aure sai da mukai aure nake matukar son ta bansan haka son yake ba, kin bani wahala Maryam a ko da yaushe da sonki nake kwana dashi nake tashi."
"Kai Yaa Haidar amman kake guje min in nazo waje ka bar wajen ko makamantansu."
"Hmmm so kike kisan sirrin komai dai ko, to zan fada miki amman kema sai kin fada min naki sirrin zuciyar.
Na fara gujewa haduwa dake bayan kin haifi Haidar dan a lokacin ko ganin ki nayi kasa bacci nake, nai ta mafarkanki da wasu sigogi kike zuwar min na rasa kwanciyyar hankali, ki tadan bukata ki tadan hankali, sai nai kwana biyu bana cikin nutsuwa ta ba abinda nake so sai kasancewa dake, duk lokacin da muka samu body content ko na taba hannun ki ni kadai nasan halin da nake ciki wannan yasa nake gudarwa ganin ki, amman daga baya ba wanda yafi ni son ganin ki, har ta window nake labewa na hango ki daga bangaren Inna ko na biki can, ke shaidace akan zuwan da kikai gidan Sitti kasa jurewa nake ina miki wani irin so da bansan yawan sa ba, ban taba jin son abu kamar yadda nake son ki ba. Kece buri na kuma Alhamdulillah sai gashi na same ki."
"Ka kusa kai asara."
"Ko muyi dai gaba dayan mu, nayi shiru na mi'ka komai ga Allah ne nasan shi zai iya min kuma gashi yayi min."
Ido ta lumshe hawaye na zubo mata ya janyo ta ya rumgume wanda sukaji wani sanyi gaba dayan su, yace
"Ki bar kukan nan."
Ajiyar zuciya ta sauke yace
"Tin yaushe kika fara so na?"
Kai ta girgiza tana fadin
"Na zata ba son ka nake ba, na zata kawai dan kana kyautata min da Haidar ne, tabbas nayi soyayya da Yaa Muhammad amman gaba d'aya hankali na da tunani na suna wajen ka, sai dai kai na kasa gane inda ka dosa...."
Tai shiru, kanta ya dago tai saurin runtse idon ta, kallon kyakyawar fuskar ta ya tsaya yi, wacce take dauke da dogon siririn hancin ta, sai mayan idanu da madaidaicin bakin ta wanda yake pink kala, daura idon sa akan lips din ta yasa yaji wani iri a jikin sa ba abinda yake sha'awa sai yin kiss bai san lokacin da ya matsar da fuskar sa zuwa fuskar ta ba, batai aune ba sai jin numfashin sa mai kamshi tayi na dukan fuskar ta da sauri ta bude ido dai dai lokacin da ya bawa bakin ta wani kiss wanda Maryam ta tsinci kanta a wata duniya ta daban da wacce ta manta da ita a rayuwar ta, abubuwa da yawa ke yawo a kwanyarta, zuciya da jikinta, Yaa Aliyu a wannan lokacin wanda shi kansa ya kasa sanin a ina yake, ya kasa daina sumbatar ta kuma ya kasa rabata da jikinsa.
Gaba daya sun manta a inda suke in banda kissing nata ba abinda yake, a hankali ta bude idon ta wanda ta hango Aisha na fita a dakin, wannan yasa ta tina a inda suke ta fara kokarin janye jikin ta amman sam Aliyu bai san ma tana yi ba, hawayen da ke fita a idonta su suka sanyayar da jikinsa, ya daina abinda yake yi din ba don ya gaji ko ya gamsu ba, he don’t actually know what he’s deriving in it but it’s something pleasurable ever in his entire life...., amma hakan bai sa ya rabata da jikinsa ba. Data samu hakan sai ta soma kokarin janye jikinta, amman ya hanata kan ta ya fara kokarin dagowa, yana dagowa takai tafukan hannunta ta rufe fuskarta.
Murmushi ya saki ya kai bakin sa yana mata rada a kunne, da sauri ta fara jujjuya kai tana rufe kunnen ta da hannayen ta, mikewa yayi yana kallon ta, ita kuwa fadawa tayi saman gadon tana rufe fuskar ta da filo, dan bata taba yadda Yaa Aliyu ne yai kissing nata ba, Yayan ta, wannan abun ya bata kunya.
"In dawo ne?"
Ya fada yana rakwafowa, da sauri ta girgiza kai, yana murmushi ya fita a dakin, ita kuwa kunya ta hanata ta fita a dakin tasan yanzu Aisha zata sata a gaba, Allah yaso da ya fita ba kowa a falo, dan Aisha kitchen ta shiga tana ganin fitar sa tai murmushi tana mai jin dadi ko ba komai tasan Yaa Aliyu zai maye gurbin Yaa Haidar a wajen Maryam dan shima ta ga yana son ta gashi yana da qaulities din da duk za a so mutum dashi. Sai da ta gama abinda zatai sannan ta nufi dakin da Maryam take, kwance ta same ta ta zauna tana fadin
"Bacci kike ne?"
Mikewa tayi tana kallon ta, Aisha tai murmushi tace
'Menene kike kallo nane?"
Mikewa tayi ta shige bandaki dan bata so Aisha ta sata a gaba, wanka tayo sannan ta fito Aisha ta bita da kallo, kai ta dauke ta fara shafa mai ta saka kaya ta kalle ta tace
"Kiran sallah dai ake kin zauna kin sani gaba kamar TV."
"Amarya Matar yaa Haidar."
Dan hararar ta tayi ta hau kan sallaya dan yin sallah, Aisha kuma ta shige bandaki dan dauro alwala.
*
Da dare, Aisha ta tafi sashen ta ita da Yaa Alkasim, Haidar ma ranar yana wajen Ummi, Ammi ta tafi sashen Abbi, ita kadai ce a dakin ta kwance ta kasa bacci sai juyi a kan gado. Jikinta, zuciyarta da kwakwalwarta ke karbar wani sabon sako mai kassara gabban jiki, wani irin feeling take ji, dan in ta tuna abinda ya faru tsakanin ta da Yaa Haidar tsigar jikin ta tashi take yi, tana cikin wannan halin, wayarta ta fara kara, dan tsaki ta saki dan bata san waye zai dame ta ba, har ta katse bata dauka ba wani kiran ya sake shigo, jin kiran ya isheta sai ta mika hannu ta dauko wayar ta saka a kunnen ta ba tare da ta duba me kiran ba.
"Bacci kike?"
Ya fada cikin muryar sa mai dadi da sanyi.
A hankali ta ji idanunta sun lumshe da kansu, saboda wani sanyi da taji, kan tai magana yace
"Na kasa baccin ni amman ke kina ta baccin ki ko?"
Da kyar ta iya cewa
"Eh"
"Anya kuwa? Fada min gaskiya ba boye boye tsakanin mu uhmmm."
Ido ta lumshe tai shiru kawai, yace
"Ni gani tunanin ki ya hanani bacci ke kuma kina ta bacci ko? To hira na kira muyi."
“Hira Yaya nifa bacci zan yi, hirar me zan maka da tsakiyar dare haka?"
Wani murmushi ya saki mai sauti yace
"Wannan lokacin yafi dadi ga ma'aurata Maryam."
Ji ta yi kamar ya kinkimo katon dutse ya dora mata aka. Don haka ba ta amsa mishi ba ma wannan karon. A sanyaye ya ce,
"Uhmm ki min hira wacce miji da mata suke yi ko na samu sassauci."
Shiru ta karayi, ya lumshe ido yace
“Maryam haka zamu yi da ke ko?”
Shirun ta karayi ya mike zaune yace
“Allah idan ba za ki bude baki ki yi min magana ba zan zo yanzu mu kwana tare, cikin bargo daya. Kin san kuma Ammi ba za ta ki hanani ba."
Shiru tayi dan ta rasa me zata ce, wayar ya kashe tabi wayar da kallo, baki ta tabe ta mike ta cire kayan jikin ta da ta kasa cirewa tin dazu take juyi akan gado, doguwar riga ta saka iya gwiwa ta saka hula akan ta sannan ta shiga bandaki, bata jima ba ta fito, dagowar da zata taga mutum tsaye a jikin kofa gaban ta ne ya yanke ya fadi, ta sunkuyar da kanta kasa. A hankali ya karaso sanye yake da kayan bacci wando da riga farare tas, wanda suke cotton masu laushi, karasawa yayi inda take tsaye yana binta da wani kallo, hannun sa na dama ya mika mata yace
“Zo mu yi hirar!”
Jikinta na makyarkyata ta ce,
“Ni bacci nake ji”
“Tunda na kasa kema ba za ki yi ba”
“Yaya don Allah ka zo ka tafi, kada Ammi ta fito, don Allah ka rufa min asiri, cewa za ta yi ni na kirawo ka. Cewa zatai ni nake kai kaina wajen maza.”
Dan murmushi yayi yace
"Ai da aure in ma kinbi."
Kafada ta make abin sai ya bashi dariya ma, Maryam kuwa gaba daya ta gama firgicewa kamar mai fargabar kada mijinta ya kamata da kwarto.
A tausashe ya ce,
“Zan tafi, but on one condition....”
Ido ta zazzaro masa tana jiran jin condition din. Hannu ya kara miko mata.
“I only want to kiss you again! matata don Allah.....!! Zan miki addu’a Allah ya saki a aljanna!!!”
Ina ma'abota son gyaran jikinsu yau ga maman sayeed collection tazo muku d gangariyar maganin gyaran breast (nono)
Maganinmu yayi fice gurin gyaran nono kikai amfani d maganinmu cikin 1week zakiga result maganinmu yana ciko d nono suyi bul² nono ko yakai silifas y mushewa kikai amfani dashi zakiga canji
Maganinmu Bashi d side effect mun hadashi d tsirrai d saiwoyi kala² domin Y'an uwa mata
Muna kano muna tura maganinmu ko wane state d yardar Allah meso yakira wannan number 08120337219
Chat 08063114606
*Allah yai mana rahna, Allah ya yafe mana yasa muyi kyakyawan karshe. Amin.*
.
*Antty*
[12/9, 18:20] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 80
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)
Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Ido ta zaro tana mai girgiza kai kamar zatai kuka tace
"Ni dai dan Allah Yaya kayi hakuri Allah ba zan iya ba."
Mikewa yayi batai aune ba sai jin tayi ya dauke ta gaba dayan ta da sauri ta fara kokarin sauka amman yadda ya rumgume ta a kirjin sa yasa ta hakura sai hannun ta da ta zuro ta wuyan sa, tana fadin
"Dan Allah Yaya kayi hakuri ni wallahi kunya nake ji dan Allah ka sauke ni."
"In baki min shiru ba har dakin Ummi zamu a haka."
Take tai dif kamar ruwa ya cinye ta a haka suka shiga falon, Allah yaso ba kowa har wata ajiyar zuciya ta sauke zasu shiga dakin kenan Ummi ta fito daga kitchen basu ganta ba dan sun juya mata baya, ita ce ta gansu kai kawai ta girgiza tana mai addu'a Allah ya tabbatar da alherin sa yasa Aliyu yaso ta su zauna lafiya ya basu zuri'a ta gari.
Har bedroom ya shiga da ita ya ajiye ta, akan gado matsawa tayi karshen gado tana takurewa ya karasa wajen kofa ya saka key sannan ya shige bandaki, sai da ya dauki wajen minti ashirin sannan ya fito sanye da armless riga da three quarter sai zuba kamshi yake, kayan sun masa kyau, wajen ta ya karaso ya zauna a gefen ta ya dagata ya daura akan kafar sa, motsu motsu ta fara dan duk ta kasa sakewa, kanta ya dago yana kallonta, ido ta lumshe sai ga hawaye na zuba a idon ta, harshen sa yasa yana share mata su yanayi wasu na zubowa, a hankali yace
"Menene?"
"Dan Allah Yaya ka bari kar Inna taje taga bana nan tazo kuma taga bana nan."
"Naga matata ce."
"Dan Allah ka bari Yaya ai ban tare ba."
Ajiyar zuciya ya sauke yace
"Kin fiso na kwana ina fushi dake."
Jikin sa ta shige tana girgiza kai, yace
"To ki shiru ni ba abinda zan miki kawai ina son na kwana a jikin matata ok?"
Ido kawai ta lumshe ya kwantar da ita ya tashi ya kashe fitila tana ji ya hawo gadon ya jata jikin sa, rumgume ta kawai yayi yana cusa kan sa a wuyan ta a haka sukai baccin dan ya ga duk ta takura taki sakewa, sai asuba suka tashi, ya shiga bandaki, kan ya fito ta fice ta bar masa dakin, sama ta wuce da sauri ta shiga dakin Haidar karami acan tai wanka tai alwala tai sallah. Sai karfe bakwai ta fita ta gaishe da su Ummi sannan ta koma dakin Inna.
Rukayya ta sama tana ta baccin ta, Inna kuwa na kitchen tana ta hada kayan karyawa a falo ta zauna tana sauraron azkar din da ake yi a TV, idon ta a lumshe bataji shigowar sa ba sai kamshin turaren sa da taji tana bude idon ta ta ganshi durkushe a gaban ta, zama ta gyara tace
"Ina kwana Yaya?"
Ido ya lumshe