Showing 3001 words to 6000 words out of 232912 words

Chapter 2 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1217

bata dauki komai ba sai kallon kayan da take dan burge ta sun burgeta amman kuma abun da sukai mata yana da yawa banda dawainiyyar ta anya kuwa. A haka suka karaso wajen basket din su cike da kaya kallon ta Aliyu ya tsaya yi can yace
"Me kika dauka?"

Kan ta tayi kasa dashi a hankali ta girgiza
"Ba abinda kike so kenan ko?"
Shiru tayi ya kama hannun Haidar yace
"Muje!"

Suka bar wajen bayan su tabi suka bayar aka gama masa total ya biya sannan suka fita mota ta shiga, ya ajiye Haidar ya koma ciki bai jima ba ya fito rike da leda ya bude motar ya shiga ya tayar suka koma gida. Tara saura suka koma gida dan haka ta dauki Haidar sukai sama. Wanka tayi masa itama tayi ta shirya shi ya kwanta sallah ta tayar kan ta idar har yayi bacci. Sauka kasa tayi dan ta zuba abinci ta samu leda a bakin dakin su, kasa ta sauka ta dauki nono ta zuba suga ta sha sannan ta fito tayi sama, kayan ta kwashe ta shiga daki.

Akan gado ta zube su kaya ne masu kyau da tsada a cikin ledar dayar kuma under wears sai turarukan sa da su alawa biskit chocolate adana kayan tayi a wajen da ya kamata sannan ta kwanta.

Bata jima da kwanciyya ba taji an bude kofar dakin dagowa tayi Ummi ce ta mike zaune tace
"Kun dawo?"

"Eh Ummi."
"Abban ki ke son ganin ki."

"Toh!"
Ta fada tana mikewa hijab din ta ta saka ta bi bayan Ummi yana dakin sa ta shiga da sallama ta zauna a kasa tace
"Barka da dare Abba."

"Yauwah Maryam ya gida?"
"Alhamdulillah Abba ya aiki?"

"Alhamdulillah dazu Ummin ki ke fada min, Yayan ki ya samar miki addmision har da kudin registeration Allah ya bada sa'a ni gudunmawar me zan bayar tinda ya riga ya gama wadan nan?"
Kan ta a kasa tace
"Abba addu'a kawai nake bukata."

"Kullum muna miki addu'a Maryam sai kuma me?"
Kai ta girgiza. Yace
"To ya kamata ki bude account ko dan kudin makaranta da abubuwa ko?"

"Eh dazu Yaa Aliyu yasa an bude min."
"To ai sai a bani account number ko?"

"Nagode Abba."
"Ba komai ina Haidar din?"

"Yayi bacci."
"To sai da safe."

"Nagode Abba Allah tashe mu lafiya."
Ta mike ta fita. Komawa dakin Ummi tayi ta same ta tace
"Ummi na fito."


"To sai da safe."
Ta tafi dakin ta, ta kwanta tare da addu'a



***
Washe gari da yamma tana bangaren Inna suna hira Haidar ya shigo a guje ya fada jikin Maryam ta dago shi tana fadin
"Haidar ba zakana tafiya hankali ba ko?"

Dariya ya hau yi mata tace
"Yaushe ka dawo."
"Yanzu Abbi na kiran ki."
Ya fada yana zuwa ya zauna a cinyar Inna. Inna ta shafa kan sa.

Mikewa tayi ta fita yana dakin sa ta shiga da sallama ya amsa, ta dan kalle shi, sanye yake da wando cotton dogo ruwan omo sai riga ruwan madara mai dogon hannu, idon sa a lumshe bai ko bude ba tace "sannu da zuwa."
"Yauwah!"

Ya nuna mata wata leda dake kan kujera da hannu yace
"Dauki."

Dauka tayi ta tsaya, duk da idon sa a rufe yake yasan tana wajen a hankali ya bude idanun nasa ya zuba a saman fuskar ta, da sauri ya janye idon sa, itama tai saurin yin kasa da kanta dan Aliyu ba karamin kwarjini yake mata ba, bama in ya daura idon sa akan ta, wanda take jin su kamar me, baki ya dan cije yace......





*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*




*Antty*
ο»Ώο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 2

By
*MARYAM S INDABAWA*



*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)



Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa


*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Dauka tayi ta tsaya, duk da idon sa a rufe yake yasan tana wajen a hankali ya bude idanun nasa ya zuba a saman fuskar ta, da sauri ya janye idon sa, itama tai saurin yin kasa da kanta dan Aliyu ba karamin kwarjini yake mata ba, bama in ya daura idon sa akan ta, ji take kamar me, baki ya dan cije kamar ba zai magana ba yace
"Jeki."

Ta dan durkusa tace
"Nagode."
Ta fita Ummi ta sama a falo ta mike mata ledar tace
"Ummi Yaa Aliyu ne ya bani."

Amsa Ummi tai ta leka tace
"Madallah angode."
Sannan ta mika mata tace
"Jeki ajiye."

Tayi sama akan gado ta zazzage kayan da wata riga tai arba wacce tin jiya ta burge ta sai dai ganin kudin ta ya hanata dauka sai wasu rigunan da atamfofi da wasu cover shoe masu kyau kamar yasan tana so kamar yasan su suka burge ta, ta d'auka ta ajiye tana murmushi ita kadai.

Kasa ta sauka wajen Ummi suna hira har aka kira magariba. Suka wuce dan yin sallah.


*
Ranar lahadi da dare ya shigo falon, sanye da bakin wando jean sai riga longsleeve mai mabballi blue black ba karamin kyau kayan sukai masa ba sai hasken sa ya kara fitowa gashin kan nan nashi kwance sai shekki yake, fuskar sa tai wani fresh sai kyalli yake, kamshin sa kuwa ya gama cika dakin, Ummi da Maryam ne zaune Maryam na kallon Bollywood da suke wani indian film mai kyau. Akan kujera ya zauna Haidar ya karasa ya zauna kusa da Maryam yana mata surutu. Ta dago ta kallli Aliyu ta dauke kai tare da fadin
"Sannu da zuwa."

"Yauwah!"
Ya fada yana lumshe idon sa, sai kuma ya dago ya kalli Ummi yace
"Ummi dole fa yarki ta rage kallon nan in har karatun take son yi dan karatun su ba wasa a ciki."

Dagowa Ummi tayi ta kalli Maryam tace
"To ai gaka ga ta nan sai kai mata fadan ko?"

Ya juyo ya kalle ta, wanda yai saurin dauke idon sa yace
"To ban da kule kulen samari ki tsaya kiyi abinda ya kai ki."
"Insha Allahu."

Ya mike yana fadin
"Bari na shiga daga ciki Ummi."
"Kaci abinci ne son?"

Ciki ya shafa ya girgiza kai yace
"Ummi yau ciki na a cunkushe yake sam bana son cin komai."

"A'ah fadi me kake so sai ai maka yanzu."
"A'ah zan ci komai kukayi ma."

"Yauwah to"
Ta kalli Maryam tace
"Hada masa abinci ki kai masa."

Ta mike ta fara hadawa ta gama ta nufi dakin nasa. Ba kowa a ciki dan haka ta ajiye ta juyo tana kaiwa kofa ya fito juyowa tayi ta kalle shi sanye da jallabiyya yake blue black tace
"Ga abincin ka nan inji Ummi."

Tana fada ta juya ta fita. Shima daki ya koma ciki, gado ne kato wanda yake lullube da farin bedsheet dakin sai kamshi kan gado ya fada yana mai lumshe idon sa. Can ya mike ya dauki wayar sa ya fara neman layin sitti. Ba a jima ba ta dauka ya kai kunnen sa yace
"Ni dai sam yanzu Sitti bata so na bare ta damu dani."

"A duk duniya kana daya daga cikin wanda na fi kauna ba ranar Allah da zata bude ban yi maganar ka ba Abin so. Ina kaunar ka da tausayin ka, ina fatan kuma Allah ya baka mai kula da kai kamar marigayiyar matar ka. In ban kula da kai ba da wa zan kula Abin so?"
Kai ya langwabe kamar tana kallon sa yace
"Nayi kewar ki har ba adadi."

"Yaushe zaka taho din?"
"Tin da nai requesting har yau ba ai approving ba Sitti."

"Nima nan duk ya ishen so nake Najwa ta karasa jarabawa sai mu taho gaba daya."
"Yauwah Sitti dan Allah ki taho fa."

"Insha Allahu Abin so."
Tai murmushi yace
"Kawai Sitti ina cikin maraici."

"Maraici Abin so yau ko baka da uwa da Uba ai kana dani kafi karfin maraici bare kuma ga Ummin ka nan me yake damun ka."
Ido ya lumshe yana cusa hannun sa cikin sumar kan sa yace
"Sitti komai ma. Ji nake kamar nai ta kuka."

"Subhanallah akan me to?"
Ido ya bude a hankali yace
"Sitti......"

Ganin inuwa yasa ya dago Ummi ya gani tsaye akan sa yace
"Sitti mayi magana anjima."
Ya kashe wayar.

Ummi ta karaso dakin ta zauna a kusa dashi tana fadin
"Meyake damun ka Dr?"
Kai yai kasa dashi yace
"Ba komai fa Ummi ni kaina na rasa gane abinda yake damuna kwana biyunan."

Ajiyar zuciya ta sauke tace
"Amman baka fada min ba."
"Bana son hankalin ki ya tashi."

"Kasan ko ka fadan ko baka fada ba ina sanin halin da kake ciki ko? Dan haka ka daina boyen abu sai dai na ganka kawai nayi shiru."
"Na sani Ummi."
Ya fada yana kwanciyya akan cinyar Ummi.

Hannu ta daura akan sa tana shafawa tace
"Ka dauki komai a sannu, kuma komai zai dai dai ta zurfin ciki ba inda zai kai ka fito ka fada min abinda kake so."

"Ina kewar Matata Ummi...."
"Shiyasa nake so kayi aure ai. Shekara nawa da rashin matar ta ka amman ka kasa cire abun a ranka. Aliyu ina shiga damuwa a duk lokacin da na ganka cikin damuwa. Duk yadda zan magance maka damuwar ka ba kamar matar ka ba zatafi sanin yadda zata rage maka ka daure ka cire Maryam a ranka ka rumgumi rayuwa ka samu wata ka aura kara girma kake Aliyu ko dan kaga su Abba sun maka shiru ne?"

"Ummi ta ina zan samu mace kamar Maryam tinanin da nake kenan."
"Ba a rasa na gari Aliyu zaka samu zaka iya samun sama da Maryam kada ka fidda rai da rahamar ubangiji."

"Ki tayani da addu'a Ummi ki tayani da kai kuka na wajen ubangiji akan ya shiga lamari na."
"Insha Allahu Dr a kullum ina maka addu'a kayi hakuri kaji."

Ido ya lumshe ta kamo hannun sa tace
"Taso kaci abinci."
A baki ta fara bashi abincin har ya koshi tace
"Dan Allah Son ban da tunani kaji."

Murmushi yayi mata yace
"Insha Allahu."
Ta mike ta fita da kwanukan. A falo ta samu Maryam da Abba sai Haidar dake hawa kan Abba yana sauka sai wasa yake. Ummi ta kai kayan kitchen ta dawo tace
"Sannu da zuwa."

"Yauwah. Yau kuma rigimar dan taki ce ta motsa?"
"To ya zanyi Aliyu yana bukatar me kula dashi."

"Hmmm ba yaki yai aure ba da yai aure da matsalar sa zata ragu."
"Kasan Aliyu ai kamar tsoron mata ma yake."

Maryam tai murmushi tace
"Hmmm Ummi baki ga yan matan dake son sa ba wallahi kyawawa fa yan gayu."
"Hmmm Maryam ai shi Aliyu ba komai yake burge shi ba kin sani."

Jingina tai da kujera tana fadin
"Anty Maryam tayi fama."
Haidar dake jikin Abba yai bacci. Wannan yasa ta mike ta dauke shi tai musu sai da safe tai sama.

Abba ya bita da kallo sannan ya juyo ya fuskanci Ummi yace
"Dole Aliyu ya fitar da matar aure fa. Ga kanin sa nan shima ko tunanin fitar da mata bayayi saboda ya gansa zaune shima ba auren."

"To Abba zan masa magana."
"Ya dai kamata."


**
Ranar monday suka fara lecture sosai sukaji dadin makarantar bama da ya kasance suna tare department dinsu daya dan haka basu wani damu ba haka suka cigaba da zuwa makaranta. Aliyu ya bata ATM din ta wanda take yai mata transfer din kudin abubuwan makaranta da gudun ta tafi wajen Ummi ta nuna mata Abba ma da ya dawo yasa ta bashi account number shima ya tura mata kudi. Ummi tace
"To ni dai duk abinda kike bukata ki fada min kinji?"

Kai ta gyada tana murmushi tare da rumgume Ummi tana fadin
"Nagode Ummi na Allah saka muku da gidan aljanna."

A lokacin kuma Aliyu ya saka Haidar a makaranta duk da ba baki ne dashi sosai ba dan Ummi ta tafi aiki, shima aiki sai shi kadai sai ko wajen Inna da yake sata bari bari da aiki wannan yasa ya kai shi makaranta karfe biyu ake dauko shi lokacin kuma Ummi ta dawo dan bata fiya kaiwa yamma ba.



Da dare Maryam suka fito daga bangaren Inna sukayo bangaren su, Abba ta sama zaune a falo ta zauna tana fadin
"Abba sannu da zuwa."

Ya dago yana mata murmushi yace
"Yauwah daga ina?"
"Wajen Inna."

Farouk ne ya shigo da sallama suka amsa ya karaso ya gaida Abba, Abba yace "Engineer kai ba a ganin ka."

Yayi murmushi yace
"Ina nan Abba haduwa ne bama yi dai shiyasa nace yau dai bari nazo na gaishe da Abba na."
"Toh Madallah ya aikin?"

"Alhamdulillah!".
Suka dan taba hira Farouk bai wani dade ba ya mike yace zai wuce, Abba yace
"Baza ka tsaya mu ci abinci ba"

Yai kasa da kai tare da fadin
"Alhmdulillah Abba na ci abinci"
Ummi dake dinning tana jera abincin tace
"Anya Yaya Farouk"

Dariya yayi yace
"Ummi wllh na koshi"
Tace
"Toh shikenan"

Sallama yayi ma Abba ya fita yana satar kallon Maryam da ke wasa da yatsun ta. Mikewa Maryam tayi ta nufi sama. Abba yace
"Dawo nan Maryam nasan kina hawa ba saukowa zaki kici abinci ba."

Kai tai kasa dashi tana murmushi tace
"Abba na koshi ne."
"Ban yadda ba shiyasa muke fada da Aliyu dan wani lokacin bai son cin abinci zo nan."
Ta karasa ta zauna a kasa wajen kafar sa. Yace
"Kinga kar ki zama kema yayan naki, kina cin abinci kinji."

"Toh Abba."
"Yauwah yar albarka ya makarantar ba dai matsala ko?"

"Babu Abba."
"Allah bada da sa'a ki tsaya kiyi karatu sosai kinji?"
Kai ta gyada Ummi ta fito tace
"To ku taso muci."

Abba ya mike Maryam tabi bayan sa. Kujerar gefen daman sa ta zauna. Abba yace
"Je ki kira su dan suma in ba a kira su ba baci zasuyi ba."
Mikewa tayi ta nufi dakin Aliyu dake kusa da dining falon ta shiga kamar yadda ta tsamaci ba kowa dan haka ta karasa kofar bedroom tai knocking ji tayi yace
"Yes come in!"

Batai niyyar shiga ba so tai yazo ta fada masa abinda zata fada ta juya amman kuma bai zo ba, a hankali ta daura hannu akan mabudin kofar ta murda kofar ce ta bude ta tura ta a hankali, bata shiga ba a bakin kofar ta tsaya tana kallo shi zaune a bakin gado System a gaban sa akan stool sai Haidar dake sakale da wuyan sa yana kallon system din shima, ganin ba wanda ya dago yasa tace
"Assalamu alaikum!"

Haidar ne ya fara dagowa yana kallon ta ya sauko a gadon yazo ya rumgume ta, Aliyu kuwa a ciki ya amsa. Baki ta dan tabe tace
"Abba yace ka fito kaci abinci yanzu."

Tana fadar haka ta juya rike da Haidar dake tai mata surutu tana fita ta tadda har Ummi ta zuba mata abinci tare suka fara cin abincin ita da Haidar can sai ga Aliyu ya fito kujerar kusa da ita yaja zai zaune sai kuma ya mayar ya ja ta kusa da wacce zai zauna din ya zauna tare da jan plate din sa. Shiru wajen yai kowa ya dinga cin abinci kadan Maryam taci taji ta koshi sai Haidar da take bawa shima nan da nan ya koshi. Aliyu ma haka dagowa Maryam tayi ta kalli Abba sai ta kalli Ummi lokacin Ummi itama ta kalle ta marairaice mata fuska tayi kamar zatai kuka Ummi ta dauke kai. Abba ne ya kalle ta yace
"Ah ya haka naga kin ajiye spoon."

"Abba wallahi na koshi."
Kai ya girgiza yace
"Me kika ci? Ban yadda ba maza ki cinye shiyasa gaki na bakya gaba bakya baya, dauki ki karasa."

Spoon ta dauka kamar zatai kuka ta fara turawa spoon biyu tayi ta kalli Abba idon ta har ya ciko da kwalla tace
"Abba wallahi na koshi Inna ta ban fura nasha dazu."
Dagowa tayi Abba yai murmushi yace
"To shikenan."

Ta mike tana murmushi ta dauke plate din ta kai ta juye sauran a wani abu da suke zuba ragowa sannan ta wanke plate din ta fito tace
"Abba sai da safe."

"Allah tashe mu lafiya."
Tai sama. Daki ta shiga ta cire kayan ta ta watsa ruwa tana fitowa ta saka kayan bacci tare da shafa turarukan ta. Alwala ta dauro ta koma kan kujera jakar ta ta janyo ta fara duba aikin ta wanda kullum haka take kan ta kwanta takan dubawa. Har karfe goma ta mike ta dauki wayar ta suratul Bakara ta kunna dai dai nan Ummi ta shigo rike da Haidar, Maryam ta mike ta amshe shi, kaya ta canja masa sannan ta kwantar dashi sukai addu'a suka kwanta.

Karfe biyar saura kwata ta mike ta dauro alwala sannan ta zo tai sallah Alkur'ani ta dauka ta fara karanta har aka kira sallah ta mike ta tada sallah. Tana idarwa tai azkar sannan ta mike ta fito falon sama ta gyara sannan ta sauka kasa ta fara gyara falon da dining. Tana cikin yi Ummi ta sauko ta durkusa ta gaishe ta, Ummi ta amsa cike da kulawa tare da tambayar ta ya ta tash ta amsa da Alhamdulillah. Turare dakin tayi ta nufi kitchen dan taya Ummi aiki, ta samu Ummi da mai aikin su na wanke wanke dan har ta gama fere abinda za a soya ta tafasa kayan ciki.

Maryam ta karasa zata hada farfesun Ummi tace
"Ba zaki makara ba?"
"Eh Ummi ai shi kadai zan hada."

"To."
Nan da nan ta hada ta barshi saman wuta bayan ta rage wutar ta juye ruwan tea a flask sannan ta wuce sama. Ummi kuma ta karasa soye dankali ta kai dining.

Tana shiga wanka ta shiga tayi, ta fito ta dauki Haidar tai masa wanka sannan ta gyara gadon ta shirya Haidar ya fice itama ta zauna ta shafa mai ta dauki wata doguwar riga pink kala ta saka, Mayafin ta three in one ta saka blue black sannan ta dauki jakar ta da takalmi ta shafa turare mai sanyin kamshi ta fito falo.

Kasa ta sauka tai breakfast sannan ta koma sama dan yiwa Ummi Sallama. Haidar ta gani kwance yana wasa akan gado tace
"Ummi na gama zan tafi."

"Kin karya?"
"Eh Ummi."

"To a dawo lafiya Allah bada sa'a a tsaya ai karatu dan Allah banda abokan banza."
"Insha Allahu."

"To kiyi addu'a kan ki fita."
"To Ummi sai na dawo."
Ta karasa wajen gado ta sumbaci Haidar a goshi sannan ta wuce tana daga masa hannu har ta kai kofa ta juyo tace
"Lah Ummi an bamu wani aiki zanje a typer min ban san nawa zai ci ba in na dawo zan fada miki."
"Allah bada sa'a."





Sannan ta fita Aliyu ta gani zai shigo sanye yake cikin wando baki da shiga long sleeve peach sai top din rike a hannun sa. Kan ta a kasa ta durkusa tace
"Ina kwana?"

"Lafiya lou."
Ta mike ta fita da sauri. Tana fita ya shiga ya zauna a gefen gado Haidar ya mike yace
"Good Morning Dad!"

"Morning My Son ya kake?"
"Alhamdulillah!"

Ya durkusa yace
"Ina Kwana Ummi?"
"Ka tashi lafiya?"

"Alhamdulillah."
Ya mike yace
"Me naji tana cewa zatai a ckul?"

"Assignment zata fitar."
"System din ta tana daki tin ranar friday

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login