Showing 159001 words to 162000 words out of 232912 words

Chapter 54 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1235

bacci da ya dauke ta, gida suka nufa suna shiga ya bude mota ya dauke ta sukai ciki, dakin sa dake kasa ya shga da ita ya ajiye ta akan gado, first aid box ya dauko yana dubata sannan ya dauki wayar sa ya fara neman layin Farouk.

Yana dauka yace
"Ga text nan na maka kai sauri ka kawon magungunan."
"To Hamma."
Ya kashe wayar, Ummi ya juyo ya kalla yace
"Ummi me yake damun Maryam?"

Zama tayi a gefen gadon tace
"Bata fada min ba, kamar yadda kai ma kaki ka fada min, Aliyu ka ganka kuwa? Kalli yadda ka rame Aliyu me yake damun ka dan....."

"Kar ki hadani da Allah Ummi, zan fada miki insha Allahu."
Kai ta girgiza tace
"Zurfin ciki ba inda zai kai ku, gwara ku fito, ku fadi abinda ke damun ku ko a taimaka muku."

Murmushi yayi ya mike yana fadin
"Bari nai wanka."
Ya dibi abinda zai bukata ya shiga bandaki, da shirinsa ya fito ya samu Ummi bata dakin sai Haidar, ya dauke shi suka fita yana tai masa surutu shekara daya kawai amman sai yaga yaron ya girma sosai, a falo suka zauna Ummi ta sauko tace
"Dr Abinci fa?"

"Ummi sai anjima bari naje wajen Hajiya Inna."
Ya fita rike da Haidar, bai jima da fita ba Farouk ya shigo rike da ledar magani, amsa Ummi tayi tace yana wajen Inna can ya tafi yai masa sannu da zuwa tare suka tafi wajen su Mami da Mama da ta amsa masa sallamar ba yabo ba fallasa.

Sai da akai isha'i suka dawo kuma har lokacin bacci Maryam take, da kyar Ummi ta matsa masa yaci abinci sannan ya koma daki, a yadda ya barta a haka yazo ya same ta, ya zauna a resting chair yana danne danne a waya, motsin ta yaji, ya kalle ta mikewa tai zaune tana kalle kallen dakin,
"Sannu."

Taji muryar sa da sauri ta juyo sai ta dauke kanta ya karaso ya zauna agefen ta yace
"Me yake damun ki?"
Kai ta girgiza ya kure ta da ido tai saurin yin kasa da kai yace
"Fada min."

"Yaya ba komai."
"Haba My Baby Sis tell me kinji."

Da sauri ta dago tana kallon sa shima ita yake kalla, ya rame sosai, kai ta dauke tace
"Yaya baka da lafiya ne?"
"Me kika gani?"

"Duk ka rame."
"Kema haka?"
Kai ta kas dashi ta dire kafar ta a kasa tana fadin
"Bari naje daki."

Kan yai magana ta fice, ya koma ya zauna yana jingina da kujera, daki ta shiga ta cire kayan ta tai wanka, tare da daura alwala, tana fitowa ta saka kaya ta hau yin salla sai da ta idar ta fara addu'a sannan ta dafe kanta, tunani ta fara me ya same ta haka? Kasa tuno komai tayi wannan yasa ta mike ta haye gado, tana kwanciyya ana bude dakin, ta dago tana kallon Ummi, ta shigo, mikewa tayi tana kallon ta, Ummi ta zauna a gefen gado, ta kamo hannun Maryam tace
"Me yake damunki Daughter?"

Kai ta hau girgizawa sai hawaye kuma, Ummi ta daura hannun ta akan fuskar Maryam tana goge mata hawayen dake kan fuskar ta, kai ta girgiza mata tace
"Ki daina kuka kinji daughter me yake damun ki fada min."

Ta bude baki zatai magana kenan aka bude dakin Aliyu ne ya shigo hannun sa rike da leda, ya mikawa Ummi yace
"Ummi taci abinci ta sha maganin nan kan gobe mu shiga asibiti."
"To Aliyu."

Ya juyo ya kalli Maryam, karasowa yayi gaban gadon yace
"Ki daure ki sha maganin kinji?"
Kai kawai ta gyada masa ya mike ya fita, Ummi ce ta kawo mata abinci da kyar taci sannan ta bata magani ta sha da kyar ta koma ta kwanta.

Wasu irin mafarkai ta dinga yi wanda ta kasa gane abinda ya faru, da ta tashi kuma da safe ta manta, cikin kwana daya kawai tayi zuru zuru. Zaune take a falon sama tayi nisa cikin tunanin da take taji an tafa hannu, da sauri ta dago taga Yaa Aliyu, ajiyar zuciya ta sauke ya zauna a kan kujera yana bin ta da kallo, kanta tayi kasa dashi tace
"Ina kwana?"

Bai amsa ba sai kallon ta da yake, jin bai amsa ba yasa ta dan dago, ido suka had'a tai saurin kautar da idon ta, yace
"Tunanin me kike?"
Kai ta girgiza yace
"Daman baki da lafiya ne?"

Kai ta kara girgizawa, kallon ta yai yace
"Ciwon baki kike ne?"
Kai ta girgiza tare da fadin
"A'ah."
kamar zatai kuka.

Wannan yasa ya dogo yana kallon ta, matsowa yayi yace
"Maryam yanayin ki kawai ya fada min kina cikin damuwa fada min me yake damun ka?"

"Yaya yanayin ka yafi nawa nuna kana cikin damuwa, kaga yadda ka rame kuwa?"
"Kar ki damu da nawa, ciwon da nayi ne amman Alhamdulillah naji sauki."

"Allah kara sauki."
"Amin kefa?"
Ya fada yana zuba mata narkakkun idanun sa wanda tana dagowa ta mai da kan ta kasa.....




*Allah ya jikan musulmai Allah ya kyautata namu zuwan, Allah yai mana rahma ya yafe mana. Amin*




*Antty*
[11/30, 12:53] Maryam S IndabawaπŸ₯°: ο»Ώο»Ώο»Ώο»ΏπŸ’—πŸ’— *MATAR HAIDAR* πŸ’—πŸ’—
Page 65

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*



Dagowa tayi tana kallon sa, ya dage mata gira yace
"Yes common tell me."
Idonta ta saukar kasa tace
"Yaya bansan me yake damu na ba, kwanakin nan duk banajin dadi bana jin nishadi bana jin farin ciki, rayuwa kawai nake yi Yaya."

Ta karasa maganar murya na rawa saboda yadda kuka ya taho mata kan ta ta hade da kujera tana sakin kukan ta, ya taso ya durkusa a gaban kujerar da take yace
"A yadda na san ki, kina da addini da karatun Alkur'ani shin kina kan yi har yanzu?"

Dagowa tayi tana kallon sa dan yadda yai maganar cikin damuwa, duk da tasan Aliyu na son ta, ido ta lumshe hawayen dake cikin idon ta ya gangaro, a hankali yace
"Bana son damuwar ki, in har na ganki cikin damuwa ina daura alhakin damuwar akai nane, in da yadda zanyi naga na cire miki ko wacce irin damuwa yanzu taso muje kinji."

"Ina zamu?"
Mikewa yayi yace dauko mayafin ki ya juya ya sauka, a hankali ta mike tana tafiya da kyar ta shiga ta dauki mayafin ta tayi rolling, ta saka flat takalmi ta fito, a hankali take tafiya har ta fito falon nasu yana tsaye rike da mukullin mota, Ummi ya kalla yace
"Ummi zamu fita?"
"A dawo lafiya."

Maryam ta karasa ta zauna kusa da ita, Ummi tace
"Menene?"
Kai ta langwabe tace
"Jikin ne?"

Kai ta girgiza, Ummi tace
"To tashi kije yana jiran ki."
Mikewa tayi ta daga mata hannu tace
"Sai mun dawo."

"Allah ya kiyaye hanya."
"Amin."

Ta fita, a wajen motar sa ta same sa tsaye ya bude mata gidan gaba ta shiga ya zagaya ya shiga cikin mota ya bar gidan, Wani waje ya kai su, ya fito ya bude mata mota ta fito tana bin wajen da kallo, wani murmushi ta sakar masa shima ya mai da mata, dan tina wajen, wajen ya kawo ta kusanin lokacin haihuwar ta, lokacin taji dadin wajen ya debe mata kewar wajen, shima Maryam matar sa yake kawo wa wanda tin da ta mutu bai kuma zuwa ba sai da ya kawo Maryam wancan karan sai wannan karon.

Harabar wajen yalwace take da shuke shuke ga haske da ya kawata wajen. motoci ne manya a wajen yai gaba ta bi bayan sa. Wata Kofa suka nufa security dake wajen yai sauri ya bude musu hanya ya bata tai gaba yabi bayan ta, suka shiga. Wani sanyi da kamshi ne ya doke ta. Wajen take bi da kallo murmushi shimfide a fuskar ta tin a haka ta samu nutsuwa da ragin damuwar ta sosai da sosai.

Yana kallon ta yace
"Mu shiga park ki hau lilo?"
Kai ta gyada suka nufi wata hanya suka shiga, a bakin kofa ya tsaya ya biya suka shiga, liluka ne kala kala a wajen ta shige ta barshi tsaye yana kallon ta ita ce hau kan waccan ita ce ta sauka a ta hau kan wancan a haka suka kwashe sama da awa daya, wanda suna fitowa suka shiga wani waje lemo aka kawo musu da menu sukai selecting abinda suke so, aka kawo musu sai da suka gama sannan suka fita suka fara zagaye wajen sune shiga can fita can haka sukai sha yawo sai da suka gaji suka shiga wani wajen suka zauna lemo aka kara kawo musu da menu na abinda suke so basu zabi komai ba dan a koshe suke, lemon kawai suke sha, ya dago ya dan kalle ta yace
"Fada min me yake damun ki?"

Fuska dauke da murmushi, ta kalle shi tace
"Ka kawar min da komai."
"Nagani amman before fa?"

"Yaya ban sani ba, na fada maka yanayin da nake tsintar kai na a ciki, Yaya wani lokacin ji nake kamar nai ta kuka, a jiya na shiga rudani na wani mafarki da nayi, ban gane komai ba naso na tina amman na kasa komai ya gudar min amman abun ya tsaya min a rai."

"Mafarki ba gaskiya bane dan haka ki daina damuwa akansa, nidai abu daya zan fada miki shine ki kara mikewa da addu'a kinji Allah ya kawo mana dauki."
Ajiyar zuciya ta sauke tace
'Insha Allahu."

Agogo ya kalla yace
"Magariba ta gabato muje muyi sallah ko?"
Suka mike masallacin mata ta nufa shima ya nufi masallacin, sai da suka idar da sallah sannan suka fita yace
"Mu tafi?"

Kai ta gyada sai kuma tace
"Yaya!"
Juyowa yayi yace
"Menene?"

"Yaya wannan popcorn din nake so."
"To muje."

Haka ya siyo mata sannan suka fita suka nufi wajen motar su, kamar ance ta dago ta ga Muhammad yana kallon su, kai ta dauke da sauri, murmushi ya dan saki ya yo wajen da suke ya karasa wajen Aliyu ya mika masa hannu, fuska ba yabo ba fallasa, ya mika masa hannu sukai musabaha yace
"Ashe ka dawo."
"Yes na dawo jiya."

"To Allah taimaka"
"Amin nagode."
Ya bude mota ya shiga, Maryam ya kalla wacce kan ta ke kasa, karasowa yayi yace
"My dear ya kike?"

"Alhamdulillah."
"Nazo amsa sako ne, bari naje sai munyi waya."

Kai kawai ta gyada ya juya ta shiga motar ta rufe, jiki a sanyaye, dan bata so Muhammad ya gansu da Yaa Aliyu ba daman kullum yaba cewa son ta suke kada ya saka wani abu a ransa, wannan yasa tafiyar tasu ta zama ta kurame ba kamar dazu ba dan suke hira ba, yanzu gaba dayan su tunani suke.


*
Haka suka dinga rayuwa tsakanin Maryam da Aliyu Ummi ta rasa gane kansu dan duk sun sukurkurce bata gane kansu sam. A haka bikin ya karato wanda ya rage sauran wata daya a lokacin yar gidan Inna autar su Abba ta sauka a kasar da mijin ta. A bangaren Inna ta fara sauka, lokacin Maryam na dakin suka shiga ita da yaran ta da mai gidan nata wanda yake tamkar yaro a wajen Inna. Lokacin da Maryam ta ganshi sai da gaban ta ya fadi domin wani abu da ta gano wanda yake mata kama da Haidar din ta, sai dai dan Haidar fari ne sosai kuma shi yaro ne amman duk wanda ya nutsu yaga Haidar yaga Yaa Abubalar mijin Yaya Nusaiba yasan tabbas sun haka da jini. Jiki a sanyaye tai masa sannu da zuwa Yaya Nusaiba ta rumgume ta tana fadin
"Amaryar December."

Tai murmushi suka karasa daki, nan suka hau dawainiyya da su cikin so da kulawa, yaran na wajen Maryam suna ta wasan su, nan suka hau gaisawa da Inna tana tambayar su ya hanya. Sai da suka ci suka koshi sannan Yaa Abubakar ya bar bangaren Inna ya tafi bangaren Ummi wanda take uwa sannan marikiyar sa.

A falo ya same ta ya karasa fuskar sa dauke da fara'a, Haidar dake gefen ta ya mike yana fadin
"Oyoyo Uncle."
Ya daga sa yana fadin
"Son ya girma."

Haidar yace
"Ina yini Uncle ina su Sultan?"
Suna wajen Inna."

Da gudu ya fice Ummi ta bishi da kallo tana fadin
"A daina gudu Haidar."
Yaa Abubakar yabi, yaron da kallo kallon sa ya dawo dashi kan Ummi yace
"Ina yini Ummi?"

"Lafiya lou Sadik ya hanya kuma?"
"Alhamdulilah mun same ku lafiya?"

"Lafiya lou ya bayan rabuwa?"
"Sai godiya shekara biyar kenan rabon mu."

"Ah gaskiya ai kun jima."
Yai murmushi yace
"Yanayin aikin namu ne ga yara suna makaranta lokacin da zasu samu hutu kila bana nan in na samu su kuma suna tsaka da karatu."

"Haka ne amman dai ko yaran ai kwana turo mana su amman ace baku basu gaba daya ai hakan bai ba ko dan bamu muka haife ka ba amman ai ita Nusaiba zata so taga magaifiyar ta ko?"
Matsawa yai wajen kafar Ummi yana fadin
"Dan Allah kada kice haka Ummi, ke ma uwa tace ban taba kin zuwa gareku dan cewa baku kuka haifen ba kullum ku nake dauka a nawa saboda ban san ina nawa ahalin suke ba, kune gata na kun min abin da ba zan taba mantawa daku ba kun inganta rayuwa ta kun bani mace ta gari da gata da na rasa tayaya zakice dan baku kuka haifen ba dan Allah Ummi ki daina fadar haka."

"Na daina Sadik Allah ya taimaka yai muku albarka."
"Amin."

"To ai ka samu kaje ka watsa ruwa ko?"
"Eh Ummi gida ma zan je anjima zan dawo Ina Aliyu?"

"Yana asibiti."
Ya mike yace
"Bari na shiga wajen su Mami sai na tafi."

"To sai anjima"
Ya fita.


*
Sauran sati uku biki.
Tana zaune a daki taga kiran Muhammad dauka tayi takai kunnen ta yace
"Amaryar Ina waje ina jiran ki."

"Gani nan."
Ta kashe wayar ta mike ta saka Hijab ta shiga dakin Ummi bata nan kasa ta sauko ta same ta a kasa ta karasa tace
"Ummi Muhammad ne yazo."

"To kada ki dade dan nasan yanzu zakiga mai gyaran nan tazo kinji ko?"
"To Ummi."

Ta mike ta fita. Baya compound wannan yasa ta fita, a waje ta same shi jingine da motar sa, sanye yake da bakin wando sai t-shirt ja yai kyau sosai sai tashin kamshi yake, tinda ya daura idon sa akan ta ya kasa daukewa ta karasa kan ta a kasa tai masa sallama sannan ta gaishe shi

Muhammad dake rike da waya ya mayar aljihu yana kallonta yace
"Invitation na kawo Gimbiyya ta Thursday za ayi dinner...."
Yana magana ya bude mota ya fiddo hadadden IV mai yawa sosai ya mika mata ta risina ta amsa, yace
"Akwai na daurin aure da na yinin ku da kika ce wenesday ko?"

Kai kawai ta gyada yace
"Ina son account number ki saboda ko zaku bukaci kudi."
Kai ta girgiza tace
"Ba abinda zanyi dasu."

Dagowa yai yana kallon ta yace
"Mijin ki zan zama a yanzu meyasa har yanzu kika kasa bani matsayin nan, ko matsayin Yayan ki baki bani ba bare friend din ki, ba zan matsa miki ba amman ya kamata ki sauya wannan dabi'ar taki, tinda kince haka zanje wajen Najwa duk abinda ake ciki zan sanar mata tin da naga na zama sirikin ki ace bikin mu ba zaki bude baki kiyi min bayanin abinda kike so ba komai sai kice duk yadda nace."

Idon ta ne ya ciko da kwalla tabbas gaskiya ya fada to amman ita tana rasa me zatace me zatayi ita fa rayuwar take amman gaba daya hankalin ta da nutsuwar ta suna wani wajen daban, dan haka murya na rawa tace
"Kayi hakuri."

Matsowa yai yace
"Dago kan ki."
A hankali ta dago kanta yace
"Kinga ko, hawaye ne fa a idon ki, nace ki fada min me yake damun ki amman kullum kice min ba komai to yanzu menene na kukan?"

"Ni dai kayi hakuri."
"In kina so nai hakuri ki turon."
A take ta dauki wayar ta ta tura masa yana tsaye taji shigowar sakon ya dago yana murmushi yace
"Ko kefa."

Sannan ya danyi danne danne wayar ta taji tai kara tana dubawa taga alert ne na 1m da sauri ta dago tana fadin
"Amman ai sunyi yawa."
Hannu ya daura akan lips dinsa yace
"Sam ko daya, ki tambayi su Ummi me suke bukata venue dukka na samar karki damu kinji amarya ta."

Ta dan saki murmushi yace
"To ni zan tafi."
"Nagode ka gaishe dasu Ammi da Momy."

"Zasuji bye."
Ta juya ta fara tafya sai yace
"Baby."

Juyowa tai tana kallon sa yace
"Ki sani ina son ki ba zan taba daina son ki ba har karshen numfashi na, in kina fargabar wani abu ne ki sani Muhammad naki ne ke kadai."

Wani murnushi ne ya sauka akan fuskar ta tace
"Ina godiya da soyayyar ka a gareni."
Ya daga mata hannu itama ta daga masa ta juya tai cikin gidan.
Akan idon Haidar duk abinda ya faru, ido ya lumshe kawai ya bar unguwar.


*
Ita kadai ce kwance a daki, sai kuka take sai kace wacce aka doke ta, Ummi ce ta shigo dakin tana fadin
"lafiya kike kuka?"

Maryam bata tanka ta ba sai hawaye da take gogewa wani na bin wani, Ummi tace "Maryam ko auren ne bakya kike ta kuka?"
Jikin Ummi ta fada tana kara fashewa da wani kukan.

Murmushi Ummi tayi mai ciwo ta kara rumgume Maryam tace "Haba daughter, kuka kuma haka?? Ko kina da damuwa ne?"

Maryam bata ce komai ba ta sunkuyar da kanta, "Kiyi hakuri kar ki sake kuka kinji, it's always like this for every lady, duk a haka muka saba uhmm?"

Maryam ta fara wani sabon hawayen, Ummi ta rungume ta tana lallashinta, Aunty Nusaiba ta shigo dakin ita ma ta dinga kwantar mata da hankali, sai da suka tabbatar tayi shiru gaba daya sannan suka fita dakin.


Mama kuwa gaba daya hankalin ta a tashe yake akan auren da taga ana ta shirye shiryen sa dan gani take in har Maryam ta samu jin dadi Ummi ma zata nutsu taji dadi ita kuma a duniya ba wanda ta tsana taga yana cikin jin dadi kamar Ummi, dan haka ko zatai yawo tsirara tayiwa kan ta alkawari cewa sai ta sakawa Ummi kunci a ranta. Da wannan tunanin ta bar gidan cike da zulumin abinda zatai masa.


Ranar litinin akaje akai kafi, wanda ba karamin kudi aka kashe ba, Aliyu ba karamin kudi ya kashe ba duk wanda ya dawo daga gidan sai sambarka, su Basma duk sunzo gidan ya cika da yan uwa.

Washegari talata da safe driver ya kai su Maryam saloon, inda ake mata gyaran kai, Sai ta kara ftowa a cikakkiyar amarya ta kara yin wani haske da fresh sai glowing ko ina na jikinta yake kamar balarabiya, da yake da Jawahir aka je Yaa Khaifa yasa ta amshi account number matar ya tura mata kudin gyaran da akai musu dukkan su.

Sai kusan azahar suka koma gida suna komawa gida mai lalle da aka kira ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login