Showing 174001 words to 177000 words out of 232912 words

Chapter 59 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt

29 Oct 2025

1290

Maryam ta karasa wajen Ummi ta rumgume ta, Ummi tace
"To menene na kukan Daughter?"

Kai ta girgiza tace
"Kije ki huta nan da sati biyu zamu zo insha Allahu."
Kai ta gyada sannan ta Kalli Najwa ta karasa suka rungume juna sai wajen Basma, sannan ta karasa wajen Yaa Farouk tace
"Yaa Farouk kaima zakazo gidan mu?"

Kai ya gyada ta dan saki murnushi tace
"Promise?"
Ya gyada kai yace
"I do."

Juyawa tayi tana satar kallon wajen da Yaa Haidar yake Ummi tace
"Ba za ai wa Yayan sallama ba?"

"Ummi ai ban ganshi ba."
Maryam ta fada tana juyowa, Ummi ta saki murmushi tace
"To gashi."

Ta nuna mata wajen da yake, karasawa tayi kanta a kasa tace
"Yaya mun tafi sai kunzo."
Kamar ba zai magana ba dan har ta juya taji yana fadin
"Allah ya tsare ki kular min da Haidar."

Kai kawai ta gyada ta bi bayan su Ammi, Mamah dake jiran ta ta karasa suka dunguma gaba dayan su.




*KANO*
Lokacin da jirgin su ya sauka a garin Kano bayan sun sauko ta kalli wajen wata ni'ima take ji na ratsa ta yau gata a mahaifar ta, cikin yan uwan ta, su Yaya Rabi, Yaya Hauwa, Yaya Ummulkairi da Yaya Zainab da Yaa Abdullah ne suka zo tarbar su gaba daya dan sun kasa tsayawa a gida lokacin da ta gansu hawaye ta hau yi, kowa so yake ta fara zuwa wajen sa, wajen yayyen nata ta nufa Yaa Abdullah sakon nata yazo ya rumgume ta yana fadin
"Ni zaki fara yiwa oyoyo."

Kamkame shi tayi tana sakin wani kuka mai taba zuciyar ta, dan ganin su gaba daya sai ya dawo mata da rashin Yaa Haidar, dan duk da Yaa Haidar ba dan gida bane amman in har zaka ga kowa to tabbas dashi a cikin su, lallashin ta Yaa Abdullah ya hau yi, Su Yaa Ummulkursun suka karaso duk suna bata baki, dagowa tayi tana bin daya bayan daya tana rumgume su ji take tamkar a mafarki yau gata a cikin ahalin ta bayan shekaru da ta kwashe ba tare dasu, ba, a baya ta manta da kowa nata a yanzu kuma ta tino da duk kansu wannan ma wata mu'ujizace ta Allah, a haka suka karasa gida kowa Maryam, Maryam kuwa sai kuka take dan da suka shiga unguwar tasu ma ta fara ganin sauye sauyen da aka samu, sai ta tuna fitowar ta ta karshe da ba zata manta ba, sai ranar da Haidar ya rasu da safe da Ammi tazo tafiya da ita wannan ne zata iya dorarwa da suka shiga gida kuwa taga yadda gidan ya kara kyau girma dan an gyara da abubuwan zamani, bayan sun fito a mota idon ta ya sauka a bangaren Yaa Alkasim bangaren da sukai dadabdala da Yaa Haidar take wani kukan ya kara taso mata, sai da ta kalli inda yake parking mota, ji tayi kamar zataga motar wajen ta kure da kallo hawaye na zubo mata Haidar ya karaso yace
"Adda meyasa kike ta kuka ko gun Abbi da Ummi zaki koma, Adda su Ammi ma fa suna son mu ki daina kuka suma zasu na baki sweet ko Ammi!"

Ammi ta karaso ta dauke shi tace
"Sosai ma Haidar duk abinda kuke so shi za ai muku dan haka kada ka damu kaji."
Ya kalli Maryam da hawaye ke bin kumatun ta yace
"To Adda Smile and stop crying."

Ya sa rigar sa yana goge mata hawayen murmushi ta dan saki wani hawayen na kara zubo mata Ammi ta kamo hannun ta tace
"Na san tunanin da kike yi, kiyi hakuri, ki rumgumi kaddara, ki dauki hakan a matsayin zananniyar kaddararki. Haka Allah Ya tsara ma rayuwarki kinji?"

Kai ta gyada hawaye na cigaba da zuba a idon ta ciki suka shiga bangaren Ammi an kara kawata shi an canja komai na ciki, har dakinta Ammi ta rakata a yayinda Yaa Fadima take binsu a baya dauke da Haidar. Maryam na shiga daskarewa tayi a tsaye tanabin dakin da kallo saboda haduwarsa, kallon dakin take cike da so da mamaki wanda da alama komai na cikin dakin sabo ne saboda walkiyan da yake, dakin yayi bala'in haduwa, komai na cikin dakin abun kallo ne, Maryam fadawa tayi a jikin Ammin hade da fashewa da kuka, da kyar Ammi ta rarrasheta tayi shiru, "Ki watsa ruwa sai ki fito kinji, bari naje na yiwa Haidar wankan shima."

Ta juya ta fita dauke da Haidar, bayan ta tabi da kallo hawaye na taruwa a idon ta, kayan jikin ta ta cire ta shiga toilet shi kansa toilet din ma abun kallo ne, acan ma sai da tayi kuka son ranta sannan tayi wanka ta fito, Gaban dressing mirrown ta dake cike da kayan kwalliya, jiki a sanyaye ta zauna akan karamin kujeran dake gaban dressing din, bata iya yin komai ba mai kawai ta shafa ta fesa turare sannan ta tashi a gurin, koda bataga akwatin da ta dawo dasu ba sai ta nufi wardrobe a tunaninta ko kila an saka mata kayan nata a cikin wardrobe din.

Wardrobe ta nufa ta bude, wani hawaye ne ya kara gangaro mata akan kuncinta a yayinda idanunta sukai mata karo da kayakin dake cike a cikin wardrobe din kuma gaba daya sabbi, cikin sanyin jiki ta zabi wata bakar doguwar riga a cikin kayan ta saka sannan ta hau kan sallaya sallah tayi ta idar tana addu'a wacce rabin ta Yaa Haidar takeyiwa, tana cikin addu'ar Haidar ya shigo a guje yana dariya tare da kwadawa mata kira yana fadin
"Adda! Adda!"

Juyowa tayi kan tai magana ya fado kanta ya fara nuna mata picture din dake hannun sa yace
"Adda wai wannan ma Abbi nane?"

Picture din ta kalla, wanda Yaa Haidar a tsaye a jikin mota sanye da bakin wando da jar t-shirt yai kyau yana murmushin sa mai kyau kumatun sa ya lotsa kamar ka kira sa ya zo hawayen da ke cikin idon ta ne ya fara zubowa Haidar yace
"Adda we look alike, ko?"
Ya fada yana dagowa ya kalle ta ganin hawaye a idon ta ya tada hankalin sa ya hau goge mata fuskar sa kanar zai kuka yace
"Adda, Abbi fa yace ba kyau ana kuka, ko nima inyi Adda?"

Hannu tasa tana goge hawayen amman wani na kara zubowa, rungume Haidar tayi tana jin wani son sa da kaunar sa, da tausayin sa. Yaya Fadima ce ta shigo tana fadin
"Wai Maryam har yanzu kukan nan kike?"

Ta zauna a gefen gado tana fuskantar ta, tare da fadin
"Haba Maryam ki bar wannan kukan dan Allah, yanzu godiya zakiyiwa Allah da ya hada ki da ahalin ki kika samemu lafiya. Kukan me kike? Na rashin Yaa Haidar ko na farin ciki? Yaa Haidar ya riga ya rasu ba abinda zaki masa a yanzu sai addu'a, adduar ki kawai yake bukata kuma kada ki manta ke matar aure ce a yanzu in har kikai tunanin sa ba ta hanyar dai dai ba haram ne, dan Allah Maryam kiyi hakuri ki dauki wannan kadaddar taki, ki sawa zuciyar ki salama kinsan kina da matsalar zuciya in har kika ce zaki na saka damuwa to tabbas ba zaki taba yin lafiya ba, muna murna munga yar uwar mu kuma sai ta dawo mana a cikin damuwa muna son ki bama son damuwa ki sam, dan Allah ki bar kukan nan. Wallahi tin daga ranar da kika bar gida bamu kara samun nutsuwa da jin dadi ba irin na yanzu kuma ace kizo da damuwa in kinsan yadda muka shiga na rashin ki bazaki taba dawo mana kina kuka ba, sam bana son damuwar ki har cikin raina abin yake damu na fada min me yake saki kuka? Yaa Haidar ne ko Auren da akai miki ne bakya so?"






*Allah ya jikan musulmai Allah yai mana rahma. Amin*



*Antty*
[12/3, 11:39] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 71

By
*MARYAM S INDABAWA*

*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
✍🏻✍🏻✍🏻
🌐🌐🌐🌐🌐🌐🌐
(United we stand, our aim is to educate, entertain and enlighten our readers in a adventurous manner.)

Facebook @Maryam Sulaiman
Instagram @Maryam S Indabawa
Wattpad @MSindabawa

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*


Kai ta girgiza kawai, Yaya Ummulkairi da Zainab dake bakin kofa suka shigo suka saka yar uwar tasu a tsakiya, Yaya Ummulkairi wacce take babba a cikin su tace
"In kika duba rayuwar ki ta baya tin daga haihuwa har ranar graduatin din ki me zaki ce ga Allah? Na tabbata godiya ce saboda a lokacin baki fuskanci ko wanne kalubale ba, rayuwa kike cikin gata da soyayya, komai naki sucess. To a haka bawa zai ci gaba da tafiya babu jarabawar rayuwa? A'a! In har Allah bai jarabtar ka ba ma to ka tuntubi imanin ka, amman ke kin tashi cikin gata sai ga wannan jarabar ta rasa miji a gareki wanda shine hope din ki, shine farin cikin, bayan nan ya dauke miki magana sannan ya jarabce ki da abubuwa masu yawa har kika bar gida kikaje wani wajen kikai rayuwa mai tsayi wanda suka rike ki da amana a karshe sai ya baki d'a duk da Allah ya dauke miki uban shi sai ya baki magajin sa, wanda gashi nan kikai masa takwara shin wannan ba wata ni'ima bace, bayan kin bar gida kinyi rayuwa mai kyau a wani waje wannan ba ni'ima bace a karshe rashin ahalin ki na asali duk da kin samu asalin su yasa ba a aure ki ba amman wadanan mutane masu karamci suka bawa dansu mafi soyuwa a gare su wannan ba ni'ima bace, wanda zai rufa miki asiri kinsan me, a yau da kika dawo wallahi ba kowa zai yadda da ina kika je ba wasu cewa zasuyi wayon karuwancu da makamantansu kika je amman ganin ki da miji zai cire wanna aransu dan haka abinda zance miki rayuwa juyi juyi ce yau fari gobe baki ki godewa Allah kuma ki amshi jarabarwar ki kinji."

"Kullum a cikin gode masa nake Yaya Ummu, amman yau zuwa na gida ya tadan hankali ji nake tamkar yau na rasa Yaa Haidar abubuwa da dama nake tunawa na rayuwar mu Yaya Ummu, kunsan wanenen Yaa Haidar kuwa?"
Ta fada tana binsu da kallo, murmushi sukai dan sun sanshi farin sani tinda tin ba a haife ta ba sukai rayuwa.

"Ku tayani da addu'a kawai amman zuciya ta ji nake tamkar zata tarwatse da gaske dai na rasa Yaa Haidar, da gaske ba zan sake ganin sa ba ya tafi inda ba a dawowa."
Ta fada taba kife kanta a jikin Haidar dake ta kallon picture Abban sa yana jin son sa a cikin zuciyar sa, hawayen da yaji na Addan sa yasa ya juyo yace
"Adda kalli Abbi na murnushi yace ba kyau kuka ki daina shima yace ki daina."

Yaa Alkasim ne ya shigo yace
"Tabbas Haidar kayi gaskiya abinda Abbin ka yafi tsana yaga Maryam tanayi kenan kuka, in har zai ga Maryam na kuka to tabbas hankalin sai yayi dubu ya tashi ba zai taba samun nutsuwa ba har sai yaga tana murmushi amman yau bayan idon sa ba zata masa wannan alfarmar ba wanda da yana nan yanzu tasan bashi da kwanciyyar hankali, ki godewa Allah Maryam da komai na rayuwar ki Haidar ya tafi ga wani ya dawo, kin tabbata *Matar Haidar* dan Allah ki kwantar da hankalin ki, ki daina kukan nan bana so sam bana son kukan ki."

Kallon yan uwan nata take ganin yadda duk suka shiga damuwa dan sunganta tana kuka, murnushi ta kirkiro tana goge hawayen idon ta hadi da fadin
"Insha Allahu ba za ku sake ganin hawayena ba da damuwa ta ba na daina kuma ku daina damuwa kalle ku dukka akai na kun shiga damuwa in kai hakkin ku ina, ni ma na daina insha Allahu kuna tayani da addu'a ina fatan kuna saka Yaa Haidar a addu'ar ku?"

Kai suka gyada tace
"Nagode Allah saka muka da gidan Aljanna Allah ya bar min ku."
Suka amsa da Amin. Yaa Alkasim ya kamo ta yace
"Taso muje muci abinci."
Ya dauki Haidar.

A parlour ta tarar dasu Yaa Muhammad suna zaune suna jiran fitowar ta, Rumgume juna sukayi itada Anty Rabi'a cikin jindadi kafin daga bisani suka nufi Dining dukkansu, Ammi duk wani abu da tasan Maryam naso shi aka dafa.


Cikin barkwanci da farin ciki suke cin abinci har suka kammala. A wannan rana dai wannan ahali haka suka yini cikin farin ciki har da matan su Yaa Muhammad Aisha ma tazo, a haka Abbi yazo ya tarar dasu shima aka dora hiran dashi, sai wajen karfe 11 na dare suka warwatse shima da kyar

Hakika Maryam taga kauna, kulawa da tattali dan sam ba a barin ta ita kadai da anga tai jigum za a hau tambayar ta da sata nishadi, baga Abbi ba, baga Ammi da yayyen ta ba gaba daya sun zama yan gata sai abinda suka so ita da Haidar. Haidar abinda yake nema ya samu dan ga yara a gidan yayan su Yaa Muhammad da Yaa Ibrahim, Yaa Abdullah ne kadai bai aure ba.


*
A gidan Mamah ma murna haka suka dinga kula da Yaa Abubakar da Matar sa da yayan su, Abba ne ya shiga bangaren Umma ya same ta a cikin daki, tana ganin sa ta mike ya karaso ya rumgume ta yace
"Albishirin ki?"

"Goro!"
Ta bashi amsa yace
"To bari kiga."
Ya kulle mata fuska da kyalle suka fito falon wanda anan Abubakar da Nusaiba suka zaune da yayan su biyar har da Haidar na shida, suna fitowa ta ji hayaniyar yara ya bude mata ido, idon ta akan Haidar ya fara sauka da sauri ta fara nunasa tace
"Alhaji wannan fa?"

"Wannan shine dan wajen Haidar da Maryam."
Da sauri ta dago tana kallon sa ya nuna mata inda Yaa Abubakar da Nusaiba suke zaune tana kallon wajen ta zabura tai baya ta fara fadin
"Na shiga uku shikenan yau asiri na ya tonu boka na kan tudu yace indai Abubakar ya dawo gidan nan shikenan zan haukace, lahhh wai Haidar ma ya bar baya daman? Wadan nan ya'yan fa Alhaji?"

Ta fada tana kallon su Arfat, wanda ga kamar Abubakar a tattare dasu wata dariya ta barke da ita tace
"Wai da gaske wadan nan ya'yan Abubakar ne ni da nai alkawarin tin da ban haifa ba itama ba zata ga jinin ta ba amman yau ga Abubakar ya dawo sannan ga jikoki har...."

Ta daga hannu ta fara kirgawa tana fadin
" 'daya, biyu, uku, hudu, biyar, shida."

Sai ta barke da dariya ta kalli Abba tace
"Nice nan na batar da Abubakar nice nan, sannan Aliyu ni na masa asiri ya kamu da wannan matsananciyar sha'awar wanda duk buri na shine yaiwa shegiyar yarinyar nan fyade da yake yana da tsoron Allah shine yaje ya dauke ta sukai aure....."
Ta kara sakin dariyar tana fadin
"Itama Maryam din, jin tana da ciki yasa na saka aka batar da ita aka kuma cire mata komai a kwakwalwar ta, uban wa ya gano ta dan an fada min in har taga wanda ta sani ne zata tino komai waye ya gano ta ya bata min aiki?"

Ta fada tana fashewa da kuka, sai kuma ta saki wata uwar kara ta zabura a guje ta fice a dakin da gudu Abba yabi bayan ta sai dai kan ya karasa har ta fice a compound din Yaa Abubakar ya bi Abba suka bi bayan ta amman wani uban gudu take yi a haka ta fice a layin Abba ya koma ya dauko Mota Yaa Abubakar shida suka bita suna karasawa titi ta hau saman titi dai dai zuwan wata katuwar daf ta ture ta tabi ta kanta ta tatse ta take kanta ya fashe, wanda bata kara shurawa ba ta mutu. A kan idon Abba abun ya faru haka aka dauke gawar ta aka tafi gida dan ai mata sutura akai ta gidan gaskiya inda in ka aikata mai kyau zaka girba in ba akasin haka ne same.



Haka su Abba suka dauko ta aka zo akai mata sutura, aka kaita gidan ta na gaskiya. Haka akai zaman makoki na kwana bakwai wanda ranar da Ummah tai kwana bakwai aka hada family meeting din gidan Abba wanda yan uwa suka zo sosai anan aka gabatar da Yaa Abubakar da matar sa da ya'yan sa, tare da Haidar.



*
Zaune take a dakin ta Haidar kwance a jikin ta yana ta game da wayar ta, ba bacci take ba amman idon ta lumshe ta lula duniyar tunani wasu lokaci da suke shede da mafarin komai


```Kwance take akan gadon makaranta waya kare a kunnen ta kuka take yi tinda ta dauki wayar, hankalin Haidar yayi dubu, cikin murya damuwa yace
" *Matar Haidar* dan Allah ki bar wannan kukan ki fada min me yake faruwa."

'Kin magana tayi yace
"Kina so nima nai miki kukan?"
A yadda yai maganar sosai rauni ya bayyana, a cikin muryar sa, kai ta girgizawa tamkar yana ganin ta, yace
"To *Matar Haidar* fadawa mijin Maryama abinda yake damun ta me take so fada min."

Wani kukan ta kara fashewa dashi tana fadin
"Yaya ba kai bane."
"Naji nine fadamin abinda nai miki ni kuma nayi alkawarin hukunta miki kai na"

"Au baka san mema kai min ba?"
Ta fada tana sheshekar kuka, ya sauke ajiyar zuciya yace
"Na sha'afa ne, *Matar Haidar* ."

Wani kukan shagwaba ta kara saki, wanda yake haifarwa da Haidar wani abu a jikin sa da zuciyar sa, tace
"Yaya yau kwanan ka nawa baka zo kaga Matar ka ba?"
"Baby amman na fada miki aiki ne ko?"

"Aiki yafi ni ko?"
Tana fada ta kashe wayar, wayar yabi da kallo ya dago ya kalli Ahmad dake gefen sa. Ahmad yace
"Kukan kaima zakayi ne yarinya karama na juya ka kamar waina."

Wani kallo Haidar ya aika masa yace
"Wayar fa ta kashe, shin kasan yadda nake ji na rashin ta kuwa nima da kyar na iya daurewa."
Dariya Ahmad yayi yace
"Shugaban soyayya."

"Naji."
Ya mike ya shige daki wayar sa ya dauka ya kara kiran ta, tana gani tana kuka taki dauka domin kuwa, ita kadai take jin kewar sa, ji take kamar tai tsuntsuwa taje wajen sa ta manta rabon da tai sati biyu bataga Yaa Haidar ba, amman yau ita ce tai sati hudu ba Yaa Haidar, hakika bata san haka ake ji ba in anyi kewa, a baya tana jin kewar sa amman na yanzu yafi na da ji take kamar ba ita ba, jin ta take incomplete, tana jin wayar na kara har ta gama bata dauka ba, da kyar ta katse bata dauka ba yana kara kira ta dauka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login