Showing 30001 words to 33000 words out of 232912 words
Chapter 11 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
yake mikewa tai ta dauke shi tana fadin
"Ummi fa?"
"Tana kitchen."
Dire shi tayi tace
"Bari naje naji dumin ta."
Tayi ciki tana fadin
"Ummi na kina ina na dawo."
Ummi dake kitchen na aiki ta leko tace
"Ah Daughter u re welcome."
Maryam ta karasa ta rumgume ta tana fadin
"I miss you."
"Miss u more yasu Sitti?"
Ta fada tana shafa bayan ta. Aliyu ne ya shigo Haidar a hannun sa sukai daki. Maryam ta shiga tace
"Me kike?"
"Girki."
"Yau zanci girkin Ummi."
"Sai kace wacce ta shekara."
"Wallahi ni ji nake kamar na shekara."
Tai murnushi tace
"Yasu Inna da Mami."
"Suna lafiya kullum Inna sai ta tambaye ki?"
"Ayyah bari naje na gaishe ta."
Ta juya ta shiga dakin Inna, tana bandaki dan haka ta dawo falo wayar Inna ta gani ta dauka ta fara rubuta number Muhammad kira ta tafi bai jima ba ya dauka tai sallama yace
"Kece?"
Kai ta gyada yace
"Ina wayar ki?"
"Ban ganta ba."
"Ah haba ko dai kin yar?"
"Kila since bata motar Yaya."
"To wannan wayar wace?"
"Ta Inna ce."
"Bari na kira kar mu cinye mata kudi."
Ya katse sai ga kiran sa dauka tayi yace
"Kin dawo gida ne?"
Kai ta gyada kamar yana ganin ta yace
"Yasu Ummi da Haidar?"
"Suna lafiya."
"Yau kin baro Sitti da kewa kamar yadda kika barni ko?"
"A'ah."
"Hmmm shikenan yanzu ya labari?"
"Yana wajen ka."
"Nawa akan ki ne kawai."
Tai murmushi yace
"Please ki barni nazo mu gaisa."
"To zan fada maka lokacin da zaka zo."
"Nagode to sai anjima."
"Eh."
Ta kashe wayar Inna ta fito tace
"Ke kuma dawa kike magana?"
Waya nai da wayar ki."
"Oh yaushe kika dawo?"
"Yanzu."
Ta sauka kasa ta ce
"Ina yini?"
"Lafiya lou yasu Hadizan?"
"Suna lafiya."
"Madallah ai bakya nan gidan shiru ba dadi."
Maryam tai murmushi tace
"Ina Yaa Farouk shi ko?"
"Yanzu zaki gansa shi ke dauken kewarki. Ali kuwa safiya safiya nake ganin sa. Motsi suka jiyo Inna tace
" kila gashi nan ma."
Aliyu ne yai sallama Inna ta amsa tana fadin
"Yau kai ne a sashe na?"
"Kaji Inna sai kace bana shigowa."
"Ka jima rabon ka dani."
"To yau gashi na shigo ko korata zakiyi."
"A'ah ya aikin?"
Zama yai yace
"Alhamdulillah."
Sallamar Farouk suka jiyo ya shigo tin da yaga Maryam yake binta da kallo ta hade rai tace
"Ni ba ruwa na dakai."
"Haba kanwata afuwan."
"Uhmm."
Zama yai yace
"To ba ina ta kira wayar a kashe ba, da farko ta shiga daga baya kuma a kashe, ina wayar ta shiga?"
Hannu ta daga alamar itama bata sani ba. Farouk yace
"Kamar yaya?"
Ta saci kallon Aliyu shima ita yake kalla ta kasan ido tace
"May be na yar ban sani ba."
"Ayyah Allah mai da alheri wannan watan akwai siya waya kenan."
Murmushi kawai tayi tace
"Ya aikin to?"
"Alhamdulillah yasu Sitti?"
"Tana gaishe ku dukka."
"Madallah."
Mikewa Maryan tayi tace
"Bari naje na gaishe da Mami."
Farouk yace
"Nima zanje sashen bari mu tafi tare"
Ta kalli Inna tace
"Inna sai anjima"
Sannan suka fita, suna zuwa kowa yai bangaren wanda zai je.
Da daren ranar fitar Maryam kenan nan daga dakin Inna. Ba kowa a dakin daga Inna sai Aliyu, wayar Inna dake gefe ce ta hau kara ta janyo tana fadin
"To waye haka cikin daren nan?"
Daukar wayar tayi ta danna inda ake picking ta kai kunne hade da sallama tace "Waye?"
Muhammad jin murya Inna yace "Ina yini Inna?"
Tace
"Lafiya waye?"
Yace
"Muhammad ne Maryam nake nema."
"Oh Maryam ai yanzun nan ta bar sashen nan sai dai ko ka kira wayar ta, au ashe fa tace an dauke to amman tinda ga Ali bari na basa sai ya kai mata zata kira in an kai mata kaji."
"To Inna nagode sai da safe."
Ta dago tana fadin
"Dan Allah Ali maza mikawa Maryam wayar nan, kaga kiran ta ake."
Amsa yai ya mike ya fita, number yasa a blacklist sannan ya shige dakin sa bai jima ba ya fito falo ya zauna anan dining space yana aiki.
Can wajen goma yaji ana saukowa daga bene yana dagowa yaga Maryam ce sanye da kayan bacci sai hijab karami a jikin ta da yake garin da sanyi doguwar riga ce mai kauri sai dan hijab din. Tana ganin sa ta dauke kai ta shige kitchen mikewa yai yabi bayan ta ta dauko fresh yoo ta fito ta kusan cin karo dashi da sauri ta koma ciki ya biyo ta, taja baya ya dinga binta har sai da taje da jikin cabinet sannan ta rasa inda zata, tsayawa yai a gaban ta kamshin turaren sa ya cika har wani ido take lumshewa, a hankalu ta dago ta kalle sa take da mamaki zai magana kawai ya juya ya fice hannu ta daura akan kirjin ta tana sauke ajiyar zuciya tare da fadin
"Shi Yayan nan."
Kujera ta sama ta zauna anan ta shanye fresh yoo din sai da ta gama sannan ta mike ta leko a hankali ba kowa a falon da sauri ta fito tayi sama ta shiga dakin ta ta kwanta.
**
Washe gari da rana wayar Ummi ce kare a kunnen ta suna waya da Muhammad sai da suka gama Ummi tace
"Da wa kike waya Daughter?"
"Abokin ya Abdul ne"
Ummi tace
"Wane Abdul?"
Kai tayi kasa dashi tace
" Saurayin Najwa."
"Me ya hada ki da abokin Abdul, a ina kika san sa?" Tace
"Ummi a gidan Sitti."
"Soyayya kuke?"
Kai ta girgiza Ummi tai murmushi tace
"A dai kiyaye."
Ta mike ta haye sama jingina da kujera tayi ta lumshe idon ta ita ba zatace ga abinda take ji game da Muhammad ba amman dai tasan yana burge ta gashi dan gayu ga tsafta ga sanyin hali ga iya kwalliyya da kula. ido ta bude sai ta kara lumshe idon ta wani abu taji tana son tunowa amman kuma ta kasa takurawa kan ta da tayi da son tuno abin ya haifar mata da ciwon kai dole ta hakura da tunanin ta kunna TV ko ta dauke mata kewa amman ina sam babu abinda hakan yayi sai ji tayi wani abu ya tokare mata a kirjin ta, gaba daya ta kasa jin ya daukar mata zamewa kawai tai ta kwanta ba tare da tasan tunanin me take da abinda yake damun ta takamaimai.
Har washe gari da ciwon kan ta tashi daga ka kalle ta zakaga alamun bata jin dadi ko tana cikin damuwa, da yamma tana kwance a falo, tai shiru kawai taji wayar Ummi na kara dan yawanci yanzu tana wajen ta, hannu tasa ta janyo, number Muhammad ce ta dauka bayan sun gaisa yace
"Ina kofar gidan ku."
Ido ta zaro tace
"Gidan mu kuma?"
Yace
"Yes ko na tafi?"
"A'ah bari na fadawa Ummi, ta mike ta nufi dakin Ummi ta jima tsaye a bakin kofar ta kasa shiga saboda batasan me zata ce mata ba, tuna yana waje yana jiran ta yasa ta runtsa ido tai sallama a dakin, Ummi ta amsa Maryam ta shiga ta zauna a kasa, Ummi ta kalle ta tace
"Lafiya?"
Kanta tai kasa dashi tace
"Ummi Muhammad ne wai yazo yana kofar gida."
Kallon ta Ummi ta tsaya yi can tace
"To kije kada ki dade kinsan Yayan ki yana hanya yanzu."
"To Ummi."
Ta mike ta fita, Hijab ta saka ta fita a gidan a hankali take tafiya har ta isa gate, Yana ganinta ya bude motar ya fito ya rumgume hannayensa yana kallonta daga glass din idonsa, sanye yake da Dark Ash kalar wanda da bakar riga kayan sun masa kyau sai tashin kamshin turarren sa mai dadi yake, ta sunkuyar da kai har ta isa kusa da motar, cikin sanyayyan murya tace
"Ina yini?"
Yace "Lafiya lau dear, ya gida?"
Tace "Alhmdllh"
Ido ya zuba mata yana murmushi can ya kira sunan ta da wata irin murya
"Maryam."
Dagowa tai, murmushi ya sakar mata yace
"Me yake damun ki?"
Girgiza masa kai tayi. Yace
"Amman yanayin ki ya nuna bakya jin dadi."
Murmushi tayi tace
"A'a lafiya ta lau"
yace
"To ina Haidar?"
"Yana school bai dawo ba."
"Ummi fa?"
"Tana lafiya."
Kai ya gyada, dagowar da zatai ta hango motar Aliyu na karasowa wani abu taji ya tsarga mata tai sauri ta dauke kai, tanaji ya karaso aka bude masa gate ya shiga, duk sai ta duburburce gane haka Mauhammad yace
"To ni dai na ganki naji dadi kewar kice tai min yawa wajen kwana nawa banganki ba shine nace yau ko dame sai nazo daga wajen aiki na sauka anan."
"Ayyah sannu."
"Yauwah wani satin zaku koma makaranta ko?"
Kai ta gyada yace
"To Allah kaimu yaushe zaki zo gidan namu?"
Ido ta zaro tana girgiza kai yace
"Saboda zamu cinye ki ko? Yadda Jawahir ta damu dake ke baki damu da ita ba da tana garin nan akai hutu da tini tazo yafi a kirga gobe ko jibi zasu dawo please ki daure kizo ki mata sannu da zuwa."
Murmushi kawai tayi yace
"Oh dan ina gidan?"
"A'ah nifa bana fita wancan ma da kyar aka barni na fita."
"Shikenan."
Zagayawa yai ya bude front seat ya dauko wata leda ya zagayo yace "Ga wannan ba yawa."
Dagowa tai tana kallon sa, kai ta hau girgizawa tare da fadin
"Aah nagode"
yace
"Karba please"
tace
"Aa Ummina zata min fada"
Shiru yayi yana kallonta, ta girgiza kai tace
"Dan Allah kayi hakuri."
Yayi murmushi yace
"Na yi."
Tai kasa da kai yace
"Zan wuce since na ga kyakyawar fuskar ki ki gaishe da Ummi."
"Zataji nagode."
Ya zayaga ya shiga mota ita kuma ta shiga gida. Tana shiga taga Aliyu ya hau mota zai fita da sauri ta shige ciki. Muhammad kuwa daga nan gidan Sitti yaje lokacin Abdul na gidan falo kai tsaye yaje yai knocking Sitti ta bada izinin shiga ya shiga da sallama tana ganin sa ta saki fara'a tace
"Ah Muhammadu ne?"
Ya zauna akan carpet yace
"Nine Sitti."
Tace
"A'ah ka zauna akan kujera."
"Nan ma ya isa Sitti."
Ta mike ta kawo masa ruwa da lemo ta ajiye yace
"Ina yini?"
"Lafiya lou ya gida ya aiki?"
"Alhamdulillah."
"Masha Allah."
Yai kasa da kai yace
"Daman Wayar Maryam ce ta 'bata so shine nace bari na kawo mata wannan."
"Ah haba Muhammad har da dawainiyya."
"Sitti ba komai ai Maryam kanwata ce."
"To angode Allah ya saka da alheri."
"Amin. Ni zan tafi."
"To baka sha ko ruwa ba ai."
Ya dauki ruwan yace
"Nagode sai ajima."
"To ka gaida gidan."
"Zasuji."
Ya fita ya shiga mota ya fita, motar sa na fita a gidan ta Aliyu na karasowa ya shiga yai parking ya shiga falon Sitti da sallama, ansawa tayi yana shiga ya zauna a akan kujera tare da lumshe idon sa. Sitti tace
"Lafiya?"
Kai ya girgiza mata kawai. Sitti tace
"Aliyu ya kamata kasan abun yi fa."
Yana jin ta yai mata shiru tace
"Zama haka ba zai yiyu ba ka samu kai aure ka zauna da iyalin ka."
Kai Sitti yazo da damuwa tana son ta dada masa wata, mikewa yai yana fadin
"Daga aiki daman nake za tafi."
"Oh dan na maka maganar aure ko?"
"Ba haka bane."
Ya nufi kofa tace
"To zo na baka sako."
Ya juyo ta mika masa ledar da Muhammad ya ajiye tace
"Ka kaiwa Maryam, waya ce Muhammad ya kawo mata saboda tata ta 'bata"
Kamar ba zai amsa ba sai kuma ya amsa ya fice kawai. Sitti tace
"Zama ka dawo ne."
Ya shiga ya tada motar ya bar gidan. Yana zuwa ya wuce dakin sa wanka yai yai shirin masallaci sannan ya tafi sallah.
Bayan isha'i yana zaune a daki ya aika haidar ya kira masa Maryam, gaban ta na faduwa ta karaso dakin, daga yanayin fuskar sa tagane ransa a bace yake, kai ta sunkuya tace
"Gani Yaya."
"Ai na ganki."
Ya mike ya shiga daki bai jima ba ya dawo ya zauna yace
"Waye kika fita wajensa dazu?"
K'in cewa komai tayi ya wani hade rai cikin tsawa yace
"Ba tambayar ki nake ba?"
Still ta'ki cewa komai zuciyar ta sosai bugawa take, motsowa yai yace
"Ke kurma ce?"
Ganin zai mike yasa tace
"Don Allah kayi hakuri"
yace
"Waye shi? nace"
cikin rawar jiki ta girgiza kai (to fa yau taurin kai ya motsa Maryam) Ji yake kamar ya sauke mata mari ya dinga mata wani kallo zuciyarsa na tafarfasa, so yake ya samu nutsuwar abinda yake ji amman ina, da kyar da ambaton Allah ya fara jin nutsuwa na zuwar masa yace
"Toh daga yau Maryam, I mean daga yau.... na sake ganin ki da wani a tsaye wllh sai na kusa sumar dake a gidan nan kinji na fada miki."
Kuka ne ya kwace mata, ta kifa kai tana yi ya buga mata wata tsawa yace
"Rufen baki dukan ki nayi?"
Shesheka ta fara yace
"Kuma shine kika roke shi waya ko? Kina son abu ni ba zaki tambaya ai miki ba na amshi wayar ki ba zakizo ki ban hakuri kiji dalili ba ke kinfi karfi ko?"
"Ni ba roka nayi ba kuma ai ban amsa ba."
"Baki amsa ba ai ya kaiwa Sitti tinda ita ta daure miki gindin kula samari to kinji abinda na fada miki wallahi na kara ganin ki da wani saurayi sai na lahira ya fiki jin dadi."
Wayar ta ya cilla mata yace
"Waccan din ba zan bayar ba tinda har ita Sittin ta amsa maimakon taki amsa to ba zan bayar ba tashi ki bani waje."
Ya fada da sauri ta mike ta bar wayar ta a wajen yace
"Bazaki zo ki dauka ba."
Ta juyo ta dauka ta fice a guje, dafe kan sa yayi tare da sakin tsaki ya mike ya shige daki ya fada saman gado ji yake kansa na sara masa.
Tana shiga daki ta fada saman gado tana kuka mai taba zuciya daman ga abinda yake damun ta gashi yazo ya dada saka mata damuwa wai tayi roko ita a rayuwar ta bata san wata roko ba ko tana son abu kan ta tambaya tana dadewa gwara ta hakura da ta roka amman wai tai roko ta jima tana kuka wanda daga baya ta rasa kukan me take dan sai gashi ya kara saka mata ciwon kai har da zazzabi, haka ta dinga juye juye da haka bacci ya dauke ta.
Washe gari da kyar tai sallar asuba, da safe kuwa Ummi ta shigo ta ganta a wani mayuwacin hali da sauri ta sauka ta kira Aliyu da ya fita, a sashen Inna ta samo shi yazo Ummi ta kama Maryam ta saka ta a baya suka tafi asibiti, suna zuwa ya hau bata taimakon gaggawa sannan ya saka mata ruwa anan office din sa, tin safe take bacci sai wajen daya saura ta farka, Aliyu ya kira wata nurse ta taimaka ta kaita bayi tai alawa akan sallaya tai sallah tana dafe da kai tana idarwa ta kwanta a wajen.
Karasowa yai ya zauna a gaban ta ya fara auna jini ta dagowa yai da sauri yace
"Tunanin me kike?"
Kai ta girgiza yace
"Ba yanzu ba."
"Babu."
Ta fada da kyar, yace
"Jini ki ya hau why? Fada min me yake damun ki?"
Hawaye ne ya hau zubo mata Aliyu yace
"Ni bance ki min kuka ba damuwar ki nake tanbayar ki?"
"Babu."
"To saboda me jini ki zai hau haka."
"Ciwo ne kawai."
Ta fada tana saka kanta a tsakanin cinyoyin ta kofa akai knocking ya bada izinin shiga abinci aka kawo masa ya amsa ya mika mata yace
"Kici zaki sha magani da allura."
Ya bude ya bata, a hankali ta fara ci cokali biyar tayi ace
"Na koshi."
Ya girgiza kai yace
"No me kika ci kara kadan"
Ta kara ci, yace kara mana. A haka ta danci da yawa sannan yace
"Magani."
Kamar zatai kuka tace
"Wallahi amai zanyi."
"To jeki kwanta."
Ta mike ta hau gado ya fara hada allura tana cikin bacci sai jin shiga allura tayi a bayan ta kuka ta saki tana yarfa hannu ya mulmula mata yana fadin
"Sannu yi hakuri."
Ya koma ya zauna Ummi ce ta kira tace
"Aliyu jikin ne har yanzu?"
"A'ah bacci take yanzu taci abinci ta kwanta."
"To ya jikin?"
"Da sauki."
"Allah kara sauki."
"Amin."
Sai bayan la'asar suka koma gida ba zazzabin sai ciwon kai Ummi ta kaita sama ta samar mata ruwa tai wanka sannan ta bata magani tasha da kyar ta koma ta kwanta. Wayar ta ta janyo ta kunna tana kunnawa kiran Jawahir na shigowa ta kai kunnen ta hade da sallama Jawahir tace
"Subhanallah lafiya?"
"Uhmm kun dawo lafiya?"
"Me yake damun ki kinji muryar ki kuwa?"
"Ciwon kai ne fa."
"Sannu bari yanzu zan zo."
Ta kashe wayar. Bacci ne ya dauke Maryam bata tashi ba sai kusan magariba Jawahir ta gani zaune kusa da ita ta mike tace
"Yaushe kika zo?"
"Tin dazu ya jikin?"
"Da sauki."
"Sannu."
Ta fada tana kama hannun ta dayan hannun ta daura akan ta tace
"Sannu me kike so?"
Kai ta girgiza Jawahir ta dinga mata sannu, haka suka zauna a dakin har wajen tara da kyar Jawahir ta iya tafiya. Tana kwance aka bude dakin bata juyo ba ya shigo ya tsaya akan ta yace
"Ya kan?"
"Da sauki."
"Allah kara sauki."
Washe gari da ta kara shan allurai da magunguna sai ta dan samu ta wartsake tana kwance a d'aki wayar ta ta hau kara tana dubawa taga Muhammad ta dauka yace
"Ashe baki da lafiya."
Kwanciyya ta gyara, tacw
"Eh."
Yace
"Yanzu zan zo me zan kawo miki?"
"A'ah kai zaman ka."
"Ba zan iya ba Maryam."
Shiru tayi yace
"Me kije so?"
"Ba komai nagode."
"To sai nazo."
Har bacci ya dauke ta sai ga kiran Muhammad sanar mata yayi yana waje tace
"Toh ka shigo"
Muhammad ya d'an buda ido yace
"Ni fa Ina jin kunyar Ammi"
Murmushi tayi tace
"Kai da kazo dubiya zan aiko a shigo da kai."
Ta kashe wayar Ummi ta shigo ta fada mata mai aiki ta aika ta shigo dashi, sanna Maryam ta sauko ta dawo falo sanye da hijabi har kasa, tana zama taji sallamar a bakin kofa, ta kalli kofar ta amsa sallaman sa, ya shigo parlon, sunkuyar da kanta tayi ya zauna saman kujera ya ajiye ledan hannunsa a kasa yana kallonta yace
"Sannu Maryam, ya jikin?"
'Dan murmushi tayi tace
"Ina yini"
yace
"Lafiya lau, me yake damun ki ne?"
"Ciwon kai ne."
"Sannu kina samu kina hutawa kinji?"
Kai ta gyada masa, mikewa yayi ta kalle shi tace
"Har me?"
"Tafiya."
"Ba zaka zauna ba daga zuwa."
"In ta nine na kwana anan Baby, amman kuma naji na kasa sakewa ina son na zauna kuma ina son na tafi."
*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*
*Antty*
[10/28, 16:29] Maryam S Indabawa🥰: 
💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 10
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Dis page is ur Jameela from Matar Haidar fans group, thank you so much.
Fuska ta bata ya sauko ya zauna a gaban ta akan carpet yace
"No Baby kar kiyi fushi zan shiga damuwa in kina so na zauna zan zauna shkenan."
Kai ta girgiza yace
"To menene?"
Kafada ta make yai murmushi yace
"Rigima ko Baby, kar ki damu ina son shagwaba, in kina son abu a waje na da kin mun yar shagwaba zan miki ko menene sai dai in ban dashi i love you Baby."
Fuska ta rufe tana murmushi yace
"Yes i really do love u kefa?"
Kai kawai ta gyada