Showing 18001 words to 21000 words out of 232912 words
Chapter 7 - Matar Haidar Hausa Novels By Maryam S Indabawa.txt
zauna tace
"Gani."
Juyawa yai ya dauko leda ya fito da magungunan ciki sannan ya mika mata, kallo ta tsaya yi, yace
"Amshi mana."
"Yaya na warke fa."
"Ina wasa dake ki amsa nace."
Ta karba ya zuba mata ruwa a kofi ya mika mata ta amsa yace
"Sha."
Ido ta runtse ta zuba ruwa sannan ta watsa maganin ido ta kara runtse wa tana dafe kirji da sauri ta mike jin amai na taho mata kamo ta yai ya zaunar da ita tana son mikewa ya hana wannan yasa ta hau yo aman a jikin sa, sai da ta gama gaba daya sannan ta jingina da kujerar mikewa yayi ya zare rigar sa ya rage dashi sai singlet, a hankali ta bude ido tana ganin sa a haka ta mike da sauri zata bar wajen yace
"Zo nan."
Jikin ta har rawa yake leda ya dauko ya mika mata ta amsa ta juya da sauri ta bar wajen dakin ta ta shiga ta kwanta a saman gado tafi minti biyar ta mike ta watsa ruwa sannan ta dawo ledar ta dauko tana budewa taga fura murmushi ta saki tana fadin
"Thank you Yaya."
Ita ta sha sannan ta mike ya fita dakin, wajen Ummi taje ta samu har ta kwanta Ummi ta dago tace
"Ai na zata a wajen Innan zaki kwana?"
"A'ah Haidar yai bacci?"
"Yana dakin sa."
"To sai da safe."
"Ya kan?"
"Da sauki."
Sai da safe."
"Allah tashe mu lagiya."
Ta juya ta tafi dakin ta.
Daga sama ta sauko sanye da doguwar riga marar nauyi sai hijab madaidaici ta zauna kusa da Ummi tace
"Ummi gidan su Jawahir nake son zuwa."
Da kallo Ummi ta bita har sai da ta saka Maryam dariya, Maryam tace
"Kai Ummi kallon fa?"
"Ji nayi kince zaki gidan su Jawahir yau shekarar ku uku tare amman baki taba zuwa ba meya faru?"
Fuska ta rufe da hannu tace
"Ummi ai na fada miki wannan satin gaba daya batazo makaranta ba to ashe bata da lafiya kinga ya dace naje na duba ta."
Kai Ummi ta gyada tace
"Gaskiya kam jeki ki shiya kizo kije ki mata sannu kinji."
Da sauri ta yi sama tana fadin
"Thanks Ummi na."
Kaya ta canja ta dauki wani less da akai mata dinkin doguwar riga dark blue ne mai adon peach da milk ta daura dankwali ta yafa peach mayafin ta, ta dauki milk din jaka da takalmi ta shafa turaren mai Oud Abiyad ta fito ta samu Ummi a falo, Ummi ta dauki purse din, ta mika mata dubu biyu tace
"Ki siya mata lemo a hanya."
"To Ummi nagode."
"Ki dubata da jiki."
"To."
Ta fita ta kira Baba Anas ya karaso yace
"Ina zamu?"
"Baba gidan su wannan kawar tawa Jawahir zamu, amman in ka ajiye ni zaka dawo zan dawo da kai na."
"To wacce unguwa ce?"
Nan ta fada masa yace
"Shikenan."
Ta shiga suka tafi, suna zuwa unguwar yace
"To wane gida ne?"
Wayar ta, ta dauko ta fara kiran Jawahir amman bata dauka ba tace
"Baba bata dauka ba ga ba mutane bare muyi tambaya."
Kallon unguwar suka tsaya yi kasancewar unguwar masu kudi ce so silent ba kowa ko shago babu masu gadi duk suna gidan su, wata mota ce tazo zata wuce da sauri Baba ya fito yana tsaida shi tsayawa yai ya bude tint glass din, ido Baba ya zaro yace
"Kai ne?"
Mutumin yai murmushi ya mika masa hannu suka gaisa, Baba yace
"Tambaya muke."
"Allah yasa na sani."
Ya juya yana kallon Maryam dake cikin mota sun hada ido tai sauri ta dauke kai, Baba Anas ya fada masa gidan da suke nema, yai wani murmushi yayi yace
"Wancan gidan ne."
Ya nuno musu
Baba Anas yace
"Mungode Allah ya saka."
A bakin gate tasa ya ajiye ta sannan ta fada musu inda tazo sai da aka kira cikin gida aka fada sannan aka barta ta shiga, tsaki tayi dan abinda ta guda kenan daman, bangare biyu ne ta tambayi nasu Jawahir aka nuna mata sannan ta wuce, tana shiga masu aikin suka fara mata sannu da zuwa a hanya suka hadu da Jawahir tana ganin Maryam ta rumgume ta tana fadin
"Da gaske ne ke nake gani ko Mafarki ne yau ga Maryam a gidan mu."
Ta kara rumgume ta sai ta jawo hannun ta ta fara kwadawa Momyn ta kira tace
"Momy Momy."
Dakin Momy suka shiga Momy ta fito da sauri tana fadin
"Lafiya?...."
Bata rufe baki ba taga Maryam da sauri ta karasa ta kamo ta tace
"Wa nake gani kamar Maryam."
"Momy ita ce."
Momy ta rumgume ta tace
"Ah lallai yau muna da babbar bakuwa."
Maryam ta zame tace
"Ina yini Momy?"
"Lafiya ya gida yasu Ummin taki?"
"Suna lafiya ya jikin Jawahir?"
"Ah Jawahir taji sauki sosai."
"Allah kara sauki Momy tace ai mata sannu."
"Mungode."
Ta ajiye musu leda tace
"Gashi inji Ummi."
Momy tace
"Kai har da wahala haka."
Tace
"Angode Allah saka da alheri."
Kamo hannun ta tayi tace
"Taso muje Momy zata kwacen kawa."
Wani hadaden daki suka shige wanda nan ne dakin Jawahir suka zauna Maryam tace
"Ai kinji sauki dama ban zo ba."
"Ah haba ai naji dadi wallahi in ina so kizo haka zan nayi wallahi ina cikin bargo ana min waya akace nai bakuwa Maryam na mike dan nasan ba wata Maryam da zatazo waje na sai ke, har naji zazzabin ya sauka."
"Ai kuwa har kin fada ya jikin?"
"Alhamdulillah ai zan shigo ckul monday."
"Allah kaimu amman naji dadi."
Nan masu aiki suka hau shigowa da kayan sha da na ci, kan kace me an cika gaban Maryam da kaya ta kalli Jawahir tace
"In kai wannan ina?"
"Cikin ki."
"Kema kinsan naci abinci ai."
"Ban yadda ba malama ki zage kici abinci ni a gidan ku bana bakunta kema feel free gidan mune fa."
Lemo kawai ta sha tace ba abinda zata ci nan suka hau hira, wanda sai kiran sallah sukaji na magariba Maryam ta mike tana fadin
"Na shiga uku dare yayi gashi nasa Baba ya tafi."
"To menene a gida fa kike."
"Bana son yin dare wallahi."
Sallah sukai, suna idar wa ta mike zata tafi Jawahir tace
"Ai sai kinci abinci kuma sai kin gaisa da Dady nasan sai after isha'i zai shigo."
Kamar zatai kuka tace
"A'ah Jawahir Ummi zatai fada."
"Kina gidan namune zatai fada kwana ne kawai banyi a gidan ku ba Maryam amman ni yaushe ma kika zo kyan ta ki kwana."
Masu aiki ne suka fara shigo da wasu kalar girki Maryam tace
"Ni da banci wannan bama kike bani wani."
"Ki zabi wanda zakici ko naje na fadawa Momy."
Kadan ta zuba taci tace ta koshi Jawahir ta mike tace
"Zo mu shiga daki na kiga."
Suka shiga bedroom din ta inda yake wata aljannar duniya zama tayi gefen gado, ta bude wani side na dorowar ta wanda sabbin kaya ne a ciki kawai ta kamo hannun Maryam tace
"Zabi wanda kike so."
Kai Maryam ta girgiza tace
"A'ah Jawahir."
"Wai meyasa kike min haka abu nawa naki ne ki zaba."
"A'ah na gode ni hankali na yai gida."
"Tinda a jeji kike ko?"
"A'a...."
Gani tayi Jawahir ta fara fito da riguna wajen biyar da sauri ta dakatar da ita tace
"Sun isa dan Allah."
"A'ah ba nace ki zaba ba kinki, sai ki barni na zabar miki."
Ta karo biyu ta debo turaruka ta ajiye ta debo kayan zaki dukka ta hada ta zuba a wata jaka Maryam dai kallon ta ta tsaya tana gamawa sukaji kiran sallah isha'i sallah sukai Maryam ta mike. Jawahir ta harare ta, ta mike tace
"Allah mun bata."
Ta fita tace
"Muje."
Wajen Momy suka je, Momy tace
"ba dai tafiya ba?"
"Eh wai tafiya."
"To yanzu Dadyn ki ya shigo kan ya zauna cin abinci ki kaita su gaisa ko?"
"Toh."
Ta kama hannun ta suka nufi sashen Dadyn wani sashe ne a ciki wanda yake mai kyau sosai yana falon sa zaune rike da carbi suka shiga ya dago yana amsa sallamar su fuska dauke da fara'a Jawahir ta karasa ta zauna a kusa dashi ta jaho Maryam suka zauna a kusa dashi ya kalli Jawahir yace
"Daugther me aka samu ne yau?"
Maryam ta nuna masa ya kalle ta sai yace
"Maryam ko?"
"Yess Dad itace gata dai yau tazo gidan mu."
"Welcome Daughter."
Sauka kasa tayi tace
"Ina yini Dady?"
Ya dago ta ya zaunar a gefen sa yace
"Ya kike ya su Ummin ki da karatu? Ina Haidar?"
"Yana gida."
"To ku taso muci abinci."
"Dady naci abinci."
Jawahir ta kalle ta tace
"Wai tafiya zatayi Dady."
"Tin yanzu?"
"Haka tace."
Jawahir ta fada kamar zatai kuka. Yai murmushi yace
"To menene ko zaki bita?"
"No Dady ita sai so take ta tafi ni kuma na bita."
Yai murmushi ya dauki babbar rigar da ya cire ya ajiye a gefe ya dauki bandir din 1k ya saka mata a hannu yace
"A dage da karatu Allah yai muki albarka."
Har kasa ta sauka tai masa godiya sannan suka fita dakin Momy suka koma. Momy tace
'Har kun dawo."
Jawahir ta daga kai, bude kofar dakin aka yi duk suka kalli kofar, zaro ido Maryam tayi tana kallonsa gabanta na faduwa, ya mata kallo daya ya dauke kai ya kalli Momy, Momy tace
"Son ba dai sai yanzu ba."
"Yes Momy."
Jawahir tace
"Yaa Khalifa kaga bestyna da nake baka labarin ta."
Ya dan juyo ya nuna Maryam da hannu yace
"Maryam ko?"
"Yess ita ce."
Maryam ta sunkuyar da kanta, yace
"Maryama ya kike? Bayan labarin ki da aka jima ana bawa yan gidan nan for more than three years yau sai gaki kinzo lafiya?"
Maryam ta kasa dago kanta sai wasa da take da yatsun ta a hankali tace
"Ina yini?"
yace "Lafiya lau"
Momy tace
"Ina zuwa."
Ta shiga daki shima ya juya ya fita, Momy ce ta fito da leda a hannu ta mikawa Maryam tace
"Ga wannan ba yawa ki gaishe min da Ummin taki."
Har kasa ta durkusa tayi godiya, Momy tace
"Kira min Khalifa tinda Khalid baya nan sai ya ajiye ta a gida ko?"
"Momy da kin barshi ma zan hau napep."
"A'ah a daren nan kuje zai kaiki gida. Ta kara godiya sannan suka fita Jawahir rike da ledar a corridor Maryam ta kalli Jawahir tace
"Waye wannan da ya shigo?"
*Allah ka yafe mana kasa muyi kyakyawan karshe Amin Yaa Hayyu Yaa Qayyum*
*Antty*
[10/23, 14:09] Maryam S Indabawa🥰: 💗💗 *MATAR HAIDAR* 💗💗
Page 6
By
*MARYAM S INDABAWA*
*HAKURI DA JURIYA ONLINE WRITERS*
HAJOW
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
Wannan shafin naki ne *SAMIRA MALAMI* ina godiya da addu'a da kulawar ki Allah ya bar kauna, nagode sosai😘😘
Jawahir tai murmushi tace
"Yaya nane fa sunan sa Yaa Khalifa."
"Tabbas kina min maganar sa amman ba sosai ba kin fi yin na Yaya Khalid."
"Yaa Khalid dan yayar Momy ne wanda ta jima da rasuwa so yana wajen Momy as u can see am the only female daugther to my father sai kanne biyu da nake dasu maza, Yaa Khalifa is my stepbrother, ga bangarensu can, kina shigowa compound part dinsu za ki fara gani, bai zama a kasar nan yanzu haka bai fi shekara da dawowa ba so shiyasa bamu wani shaku ba dan acan yai study nasa tin primary har yanzu da yake likita so kinga dalili but i love my brother "
Maryam tace
"Ayya!"
A haka suka karasa conpound Jawahir na biye da ita, a compound suka same shi Jawahir ta karasa tace
"Yaya Momy na kiran ka."
Maryam ya kalla yai ciki kawai, bai jima ba ya fito yace
"Muje to."
Maryam ta tsaya a baya, Jawahir ta kamo hannun ta tace
"Feel free sis Yaya nane fa."
Ta fada tana mata wani murmushi itama mayar mata tayi ta bude mata gaban mota ta shiga aka bude baya aka zuba mata kayan da wanda Jawahir ta bata da na wajen Momy. Jawahir ta rufe kofar tace
"Byee Besty sai mun hadu Monday, nagode sosai"
murmushin karfin hali Maryam ta mata bata ce komai ba, Jawahir ta kalli Yaa Khalifa tace
"Yaya ka kular min da Besty na."
Hararar wasa yai mata bai ce komai ba yayi horn ya bar wajen, a haka suka fita a gidan, har suka hau saman titi babu wanda yace komai cikinsu, bayan wani lokaci yace
"Wacce unguwar za ki?"
Kan ta a kasa tana wasa da yatsun ta ta fada masa, bai ce komai ba, sai da suka shiga unguwar sannan yace
"Wane layin?"
Ta gaya masa, daga nan kuma ta dinga nuna masa Inda zai bi har suka shigo gate din layinsu, dai dai gidan ta nuna masa yayi parking ya juya yana kallonta, bata yarda ta kallesa ba ya danna horn mai gadi ya leko yana ganin Maryam ya bude gate din suka shiga, sai da ya tsaya ta bude motar ta fita tace
"Nagode"
Ciki tayi ya bita da kallo zai reverse yaga kayan ta masu aikin ya bawa, sukai mata. Ciki ta nufa bakin gate din su, Aliyu ta gani bakin gate din alamar fita zai yi don makullin motarsa na hannunsa, ya kalleta ya kalli motar da ta ajiye ta ya sake kallonta, kai tayi kasa dashi tai ciki da sauri gabanta na faduwa, sai da ta kai kofar falon su ta juyo ganin sa tayi tsaye har lokacin yana kallon ta kai ta dauke tare da turo baki ta shiga da sallama, Ummi na sama dan haka itama can ta wuce direct dakin Ummi ta shiga, Ummi tace
"Ah Daugther sai yanzu ko?"
"Ummi kiyi hakuri kinsan Halin Jawahir kememe taki ta barni na taho wai sai na gaida da Dady kiyi hakuri."
"Daman Yayan ki ne yake ta fada yanzu ma gidan na fada masa ya tafi tahowa dake Allah yasa bai fita ba dan saukar sa kenan, sai fada yake dare yayi kuma baki fita da kowa ba driver ma haka, gashi ina kira baki dauka ba."
"Na ganshi a kasa kinsan wayar tawa tana silent amman komi lafiya, Yayan tane ai ya kawo ni."
Mai aikin su ce ta shigo da kayan ta ajiye Ummi tace
"Na menene?"
"Baba Anas yace a kawowa Maryam."
"Oh nagode."
Maryam ta fada tana fadin
"Ummi ji uban kayan da suka bani."
Nan ta hau babbudewa Ummi tace
"Angode Allah ya saka da alheri ya jikin nata?"
"Taji sauki."
"Allah kara sauki."
Motsi ta jiyo ta mike da sauri tai daki dan bata son ma ya shigo su hadu, zama yayi ya kalli Ummi yace
"Waye ya kawo ta?"
"Yayan Jawahir ne,."
"Ummi dan Allah ki daina barin ta fita ita kadai."
"Ba ita kadai fa ta fita ba kana gani Baba Anas ya kaita aka dawo da ita."
Mikewa yayi yace
"Ni fitar ma bana so gaba daya."
"To ina Maryam take zuwa in ba makaranta ba, kana gani shekarar su sama da uku da yarinyar nan amman sai yau ta taba zuwa gidan su, kuma na yaba da hankalin yarinyar shiyasa na barta ita ba wasu kawaye ne da ita ba kai ma ka sani."
Shiru yai kawai ya sauka. Maryam tana daki tana jin sa tai lakwas.
Tin daga ranar suka fara yar boya dan da taji shi zata buya ko bangaren Inna kan ya dawo taje ta taho sai da sukai sati daya a haka, wata rana da dare ta baro sashen Inna tana tafe taji tayi karo da abu da sauri ta dago tana ganin shine ta juya zata koma da sauri ya kamo hannun ta,
"Wayyo Yaya dan Allah kayi hakuri ba zan sake ba."
Fuska ya hade yace
"Waye ya ajiye ki ranan?"
"Yayan Jawahir ne fa."
"Ke Yayan ki ne?"
Kai ta girgiza yace
"To na kara ganin ki da wani namiji har ma naganki a motar sa sai na balla kafarki shige ki ban waje."
Hawaye ne ya kawo a cikin idon ta da dan gudu ta bar wajen tana zuwa ta wuce sama ta fada saman gado ta fashe da kuka, da kallo ya bita sai kuma ya dan cije leben sa ya bi bayan ta zuwa sashen su har yayi hanyar bene sai kuma ya juya kawai ya nufi dakin sa. Sai da tayi mai isar ta sannan ta share hawayen ta ta kwanta.
Bayan wasu watanni.
Ummi ce tsaye a kitchen tana rufe flask din da ta hada abinci, Maryam ta dauko jug ta saka a cikin katon gaske din da yake dauke da wasu manyan kuloli, dagowa tai tace
"Ummi an gama komai ko?"
"An gama je ki shirya tinda kince dake za a airport din."
Kan Ummi ta rufe baki ma ta fice ruwa ta watsa ta dauko wata golding yellow din doguwar riga wacce akabi wuyan da hannu da red stone mayafin rigar ta yafa ta dauki wani flat sandal ta zura ta shafa turare ta fito tana addu'a Allah yasa Yaya Aliyu bai fito ba tana kan stair tajiyo bude kofar sa da sauri ta karasa sakowa ya bita da kallo tana zuwa matattakala ta biyun karshe ta gurde ta zamo da sauri ya karaso ya taro ta, ta kamkame shi tana fadin
"Wayoo kafa ta."
Daga ta yai ya zaunar akan kujera yace
"Me ya faru da kafar?"
Hannu ta hau yarfewa tana fadin
"Zafi wayoo."
Da sauri Ummi ta fito shima ya mike yayi daki bai jima ba ya dawo da wani kwalba, budewa yai ya lakaci maganin ya shafa mata a kafar ihu ta saki tana yarfa hannu tana kiran sunan Ummi, Ummi tace
"Sannu!"
Sai da ya matsa wajen ta kara sakin wani karar sannan ta shige jikin Ummi, mikewa yai yace
"Sannu."
Ummi tace
"Garin yaya to?"
"Rashin tafiya a hankali sai kace wata yarinya."
Baki ta turo tace
"Ummi sauri nake fa kar ya tafi ya bar ni."
"To yanzu ba sai naga kafar zuwa ba."
Hawaye ne ya cika idon ta tace
"Dan Allah Ummi kice yaje dani dan Allah."
"To ke zaki iya ne?"
Kai ta gyada, Ummi ta kalli Aliyu tace
"To Yaya ayi hakuri aje da ita."
"Ummi da wannan kafar?"
"To ba tace zata iya ba."
Kofa ya nufa yace
"Minti daya na bata ta fito."
Da sauri ta mike sai kuma ta saki kara ya juyo da sauri yace
"Malama ki fito a hankali."
Ya juya ya fita.
Ummi ta kamata tace
"Da zaman ki kikai muka wuce can gidan Sittin."
"A'ah ni zani Ummi."
"Shikenan."
A bakin karamin gate ta barta dan bata fito da mayafi ba, Maryam ta fara tafiya a hankali dan gurdewar da tayi yana mata zafi, cikin mota ta hango sa, ido ya zuba mata yana ganin yadda take tafiya a hankali tana dingishi a haka ta karasa ta bude gidan gaba kai ya dauke tana rufe motar ya tayar da motar suka fice.
Suna zuwa sukaga har jirgin ya sauka matafiya sun fara saukowa, da dingishi ta fito Aliyu ya kalle ta, ta gefen ido yace
"Ki zauna a mota."
Kafada ta make yayi kwafa yai gaba abinsa, su Sitti ya hango ya karasa da sauri ya isa wajen ta ita da Najwa, rumgume ta yayi tace
"My Habiby."
"I miss u alot Sitti."
"To ba gashi na dawo ba."
Fuska ya bata yace
"Ni kuma zan tafi ba."
Yai maganar cikin shagwaba. Najwa ta dauke kai tace
"Wai kai kadai kazo daukar mu Yaya ina Sister ta?"
Hango Maryam tayi, wannan yasa ta saki jakar ta,